Tsanin Kaddara Complele Book Zahra Star.docx

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   22 / 40

63K to 66K   out of 118.4K words

ido.

Maryam da baƙin ciki ya gama cika ta ganin yadda Intee ɗin ke ƙara kyau da cika cikakkiyar Mace, duk da yanzu Hijab ce sanye a jikinta, saita ga ma Hijab ɗin tafi mata kyau fiye da kowanne kaya.

Wani abu ta haɗe daya tsaya mata a wuya tana kallon Intee da kyar ta buɗe baki saboda wani irin baƙin ciki daya tokare mata maƙoshi ta ce.

"Ban taɓa ganin butulu irinku ba, daga ke har wacce ta kawo ki gidan nan kike zaune a matsayin Agola".

"Mi kike nufi ne Maryam?, kisan da waye kike magana, idan har zaki yi rashin kunyarki ko rashin mutumcin ki karki sake ki sako da Mahaifiyata".

Wani kallon sama da ƙasa ta shiga yima Intee tana sake matsowa inda take sosai, kamin ta dawo da dubanta inda Ammi take tana kallon Maryam ɗin mamakinta ya rufeta tama kasa yin magana ita.

"Kuna nan zaune kuna jin daɗi burinku zai cika na auran Y Hammad da wannan abar?".

Ta ƙare faɗar hakan tana nuna Intee da yatsa, kamin ta ƙara faɗin.

"To idan kun manta bari na faɗa maku, komin lalacewar Ummu dai itace ta haifi Y Hammad, dan haka bazai taɓa son Mahaifiyarsa tabar gidan Mahaifinsa ba, amma ta sanadiyyar ku ga Ummu can wai yau ita ce da barin gidan nan, kuma koda kin aureshi Intee idan har Abbi ya saki Ummu bazai taɓa sonki ba, na tabbata zai rinƙa kallonki ne ke ce wacce ta sanadiyarki aka sakar masa uwa. Kunzo keda uwarki kun hargitsa mata gida, tunda take bata taɓa yin Yaji ba sai ta sanadiyar ki".

Ta ƙare maganar tana nuna Ammi.

Ammi data ruɗe ta gama shiga halin ruɗani ta fara girgiza kanta bata san lokacin data kamo Maryam tana faɗin.

"Ita Ummu ɗin ce ta bar gidan nan saboda auran da za'a haɗa da Intee?".

Fisge kanta Maryam tayi daga hannun Ammi data riƙe ta tana cewa.

"Ai kunji daɗi ko?, tabar maku gidan sai ku zuba ruwa ƙasa kusha, idan kuma auran Y Hammad ne ni da ke Intee shege ka fasa, kishi ne ni dake sai aje kowa ta iya allonta".

Tana faɗin haka ta juya zata fice sai kuma ta dakata tana ɗan waigowa ta ce.

"Kwata-kwata bakwa da adalci, ya kamata ku rinƙa duba rayuwar da kukai a baya, ku ɗin fa ba kowa bane face ƙasƙantattu wa'inda basu da galihu d.......

"Keeeee Maryam ki iya bakin ki wallahi id.......

"Intee karna sake jin bakin ki a nan".

Ammi ta faɗa tana saurin katse Intee ɗin daga niyar faɗin abunda take son idasa faɗama Maryam ɗin.

Maryam kuwa kwafa tayi kawai tana ficewa gaba ɗaya daga Part ɗin ranta a mugun ɓace.

Tana fita Intee wasu zafafan hawaye suka shiya rige-rigen zubo mata tana kallon Ammi data dafe kanta ta ce.

"Ammi dan Allah ki roƙi Abbi yaje ya dawo da Ummu, kar duniya ta sake zagin ki, a baya da an zage ki naji ciwon abun ba ƙarami ba, amma a yanzu bazan iya jurewa ba, saboda yanzu nasan miye rayuwar, a baya banma san mi ake nufi da rayuwar ba, naji ciwon abunda jama'a ke faɗa akanki bare a yanzu. Ya haƙura da haɗa ni Y Hammad aure, tunda dai Mahaifiyarsa ba so take ba".

Ta ƙare maganar tana jin wani irin zafi a zuciyarta data faɗi hakan da kanta na a fasa auranta da Ya Hammad, tabbas tasan idan har ta ce tana ƙin Y Hammad to tayi ma kanta ƙarya ne, amma kuma bata ce tana sonsa ba, bata dai ƙinsa bata koma son nashi, ita dai tasan zata iya zama dashi a hakan, ta rasa wane matsayi ne zuciyarta tabawa Y Hammad ɗin.

"Kije kawai zanyi magana da Abbin naku".

Juyowa take ƙoƙarinyi domin ficewa daga parlon taji muryar Ammi na ƙara cewa.

"Ki tsaya ki share hawayen naki kamin ki fita, bana so a fahimci kinyi kuka Please".

Dakatawa tayi tana share hawayen nata kamin ta ɗan ƙaƙaro murmurshin daya fi kuka ciwo tana ficewa daga parlon.

"Aunty Intee mun kusa makara fa".

Faɗin Hanan bayan tasa key ta buɗe Motar suka shiga tana shiga itama tana aje jakarta a bayan motar ta ce.

"Am sorry yanzu zamu ida ai bazaku makara ba".

Ta faɗa tana tayar da Motar suka fice daga gidan gaba ɗaya.

Ba wani nisa bane a tsakani dan haka dandanan ta aje su a school ɗin itama kuma ta wice zuwa Campany.

Koda ta isa Campany nin kamar yadda ta saba gaisawa da ma'aikatan da yanzu suka riga da sun saba da ganinta, amma duk da hakan wasu har zuwa yau kamar baƙuwa suke ganinta, domin wasu ƙara masu kyau take, kullum shigar da zatayo to sai ta yau tafi ta gobe, shi yasa take da wani irin farin jinin jama'a bare ma Maza, Mata ko da yawansu haushinta suke ji ko hassada ce oho masu ma?.

Kamar yadda ta saba tana zuwa dai-dai zata shiga wajan da zai kaita zuwa nata Office ɗin taci karo da wacce ke tsaron wajan wacce dole sai kayi magana da ita zaka iya shiga cikin ainafin Office ɗin nasu, (Sakatariyarsa) kenan, ba wani magana suke sosai ba, dan haka bata tankama mata ba buɗe ƙofar ta shigewarta kawai, ita ko tabi bayanta da harara tana jin haushinta a kullum idan zata ganta sai taji wani irin haushinta ya kamata.

Tana shiga ta zauna ta fara aiki babu daɗewa wayar dake aiki a Office ɗin nata ta fara ƙara, ɗauka tayi kawai tana kallon cikin computer da take aiki a gabanta tana amsa wayar.

Jin muryarsa yasa ta aje aikin tana amsawa da Okay kawai tana aje wayar ta miƙe jiki a sanyaye ta buɗe ƙofar Office ɗin ta shiga.

Damuwa ce danƙare a ranta dauriya kawai take tana aikin.

Yana zaune kamar yadda ta saba ganinsa yana aiki bai ɗago ba ya amsa sallamar da tayi masa.

Tana tsaye har tsawon minti goma baice mata komai ba, wani ƙaramin tsaki ta saki ciki-ciki yadda tasan bazai ji ta ba.

Ɗagowa yayi yana zuba mata ido, da sauri ta duƙar da kanta ƙasa tana turo masa baki.

Kallon ƙasan ido tayi masa gani tayi ya sake mata wani irin bala'in kyau ga wani irin bala'in kwarjini da haiba da yake dashi a kullum kamar ƙara masa su ake. Zuciyarta har wani tsalle take jinsa ya taso ya matso kusa da ita ƙamshinsa ne ya bata tabbacin kusa yake da ita.

A hankali ta ɗan ja baya kaɗan jin kusancin nasu kamar zai so yayi yawa.

"Mi yasa baki son zuwa da wuri?, mi ya tsayar dake yau baki ƙaraso da wuri ba?, and you came instead of coming and starting to greet me before you start your work, sai kikayi zamanki night?".

Ƙara turo baki tayi kanta a ƙasa ta ce.

"Kayi hakuri ba.....".

Sai kuma tayi shuru tana jin wasu hawaye na tarar mata a cikin ido tunowa da abunda ya faru a tsakaninsu da Maryam.

Batai aune ba taji tattausan hannunsa akan fuskarta ya ɗago da ita suna fuskantar juna, cikin idonta yayi nasarar jefe ƙwayar idonsa, wadda yasa Intee jikinta fara rawa kaɗan haɗe da jin wani irin sanyin jiki da wata irin muguwar kasala data rufeta lokaci ɗaya.

Lumshe idonta tayi saiga hawaye yaga suna zubo mata.

Hankali a tashe yake dubanta, a hankali bai san lokacin daya jawota jikinsa ba yana faɗin.

"Ke mike faruwa ne?,something happened in the house?".

A ruɗe yake jefo mata tabbayar zuciyarsa na masa zafi ganin yadda hawaye ke mata zubo sosai, bai san lokacin daya kai hannunsa yana ɗauke mata so ba.

Kallonsa kawai take ganin duk yadda ya shiga cikin wani hali ganin hawayenta kawai, tabbas tasan dama baya son ganin kukanta tun tana ƴar mitsitsiyarta, kukan Mace kamar shine rauninsa bare ace nata ne ma.

"Y Hammad pleaseeee....".

"Ya Salammmm pleasee mi?, ki faɗa min, ina jinki".

"Please Y Hammad kaje wajan Abbi ka ce ka fasa aure na dan Allah".

Sakinta kawai yayi ya koma baya yan runtse idonsa da ƙarfi yana dafe kansa daya ji lokaci ɗaya ya sara masa jin maganar da take faɗa masa.

"Why Intee whyyyyy".

Ya faɗa har Muryarsa na tashi.

Kamar zata koma hannunsa ganin irin halin ruɗanin daya shiga sai kuma mita tuna ta fasa, tana jin wasu hawaye na sake zubo mata. Tasan yana bala'in sonta tun kan takai haka, ta sani sone yake mata wadda faɗarsa ma ɓata baki ne, ba abu bane mai yiwuwa ya fasa auranta, amma yaya zaiyi tunda Mahaifiyarsa bata so?.

"Y Hammad ka gane ba laifi na bane, Ummu fa yanzu haka tabar gida saboda kawai Abbi yaƙi amincewa da fasa auranka dani, bana so a kaina da kuma Ammi ace wani saɓani ya sami Abbi da Ummu, dan Allah ka fahimce ni".

Bai san lokacin daya waigo ba idonsa jawur har sai da Intee taja baya da sauri ganin yadda idonsa ya koma abun tsoro.

"Ummu she left home?".

"Yesss Y Hammaddddd".

Jijiyoyin kansa ne suka sake tashi kansa ya sake sarawa da ƙarfi ya dafe kansa, yana jin Ummu so kawai take taga ya mutu, why wouldn't she understand him?, mi yasa bazata gane Intee da take kyamata ita ce rayuwarshi gaba ɗaya ba?, shi ɗin dai da take so kamar ranta take duk wannan abun akansa, then Intee is his life, ita ce farin cikinsa, idan har babu Intee a cikin rayuwarsa to zaiyi rayuwa ne kamar Gawa babu wani farin ciki a rayuwarsa.........

Chapter 26

Ɗagowa yayi yana zuba mata ido kawai bayan ya gama jin abunda ta zo masa dashi.

Sauke lumfashi yayi mai zafi yana ɗan dafe kansa ya sake dubanta sosai kamin ya ce.

"Kin tabbatar Mansura da kanta ta bar gidan nan a sunan yaji tayi kuma?".

Sauke ajiyar zuciya Ammi tayi kamin ta maida kanta a ƙasa ta ce.

"Ba wannan ne damuwa ta ba ni Abbin Yara, please kaje ka maido Ummu a cikin gidan nan, kuma kayi ma girman Allah a fasa auran nan da Intee da Hammad please ka duba abun nan fa, ace kullum rigimar yau daban ta gobe ma daban?".

Murza goshinsa yayi da hannunsa yana runtse idonsa da ƙarfi yana cewa.

"Bazan je gidan su Mansura ba ko kaɗan, ita tabar gidan nan da ƙafafunta dan haka da kanta zata dawo, saboda bance Mansura tafi gidanku ba, bada yawu na ba ta tafi, dan haka bazan je ba".

"Amma Abbin...".

"Kinga Nuratu mubar wannan zancen".

"Ya za'ai mubar wannan maganar?, naga fa kai abun kamar ba wani damunka yayi ba fisbilillahi Abbin Yara ka duba wannan lamarin, banma ji ka ce komai dangane da fasa auran nan?".

"Idan kinga an fasa aurar nan to mutuwa nayi kawai, amma mundun ina lumfashi a duniya saifa anyisa, ni zata nunawa isa da gadara hmm".

Riƙe bakinta kawai Ammi tayi zuciyarta ta cika da tsoro da kuma mamakin kafiya irinta Abbin Hammad ɗin da kuma ita kanta Mahaifiyarsa.

Sauke lumfashi tayi kawai yaga ta miƙe ta fice bata ƙara magana ba, ya bita da kallo kawai shima yana girgiza kansa.

*******************

"Yanzu ke da kika kwaso ƙafa kika taho da sanin mijin naki ko kuwa?, shi ya ce miki ki zo gida ne?".

Faɗin Abbu yana duban Ummu cikin ido babu wasa.

Zatai magana kanta a ƙasa Umma ta rigata cewa.

"Wai Malam kamar yaya shi ya ce ta taho?, baka ji abunda take faɗa bane shin wai?, kana fa ji ta ce wai so yake ya haɗa aure da Hammad da Ƴar kishiyar nan tata Agola fa, haka kawai baida ma kunya wannan Yaron wallahi, ya manta irin cin kashin da yayi mata akan auran Nuratun a can baya ne?, sai yanzu babu kunya babu tsoron Allah ya ce wani zai haɗa aure da Ƴarta kuma ya ce ta amince?, ai shima yasan ba abu bane wadda zai taɓa yiwu ba".

"Tayaya bazai yiwu ba?, akwai haramun ne a ciki?, ko kuma akwai aya ko hadisi da aka ce kar Muhammad ya auri Inteesar ɗin idan akwai ku kawo min ina sauraron ku?".

Abbu ya faɗa ransa ya fara ɓaci da lamarin nasu danya lura ba wadda ke daurema Ƴanƴan nasa gindi sai ita Mahaifiyarsu Umma.

"Amma Malam kafa duba wannan abun fa tsakani da Allah, shima ai yasan ya nuna son kai ne".

"So nake ku kawo min hujjar da zan tunkari shi Mijin nata da hakan ai, amma babu wata hujjar hana hakan babu abunda zan iya cewa. Kuma ma shi Muhammad ɗin ne ya ce baya son Inteesar ɗin ne?, da ace shi Yaron baya sonta da to baza'ai wannan haɗin ba, amma kuma tun yarinya na ƙarama yake ɗawainiya da ita, tun kan tasan kanta yake sonta, to banga dalilin da zaki shiga haƙƙin Yara ba, ku hanasu abunda suke so ba wannan ma ai kamar ɗaukar alhakinsu ne".

Kan Ummu a ƙasa dan tana mugun shakkar Mahaifinta ta ce.

"Abbu kullum fa akan Matar nan tasa yake min wulaƙanci, baya taɓa tuna cewar ni ce Matarsa ta farko, ɗauka ma yake kamar Nuratun ta fini komai, ɗauka yake kamar ita ya fara sani a duniya bani ba. Sana Abbu ga Maryam wacce nake son haɗasa da ita Ƴar uwarsa ta jini bawai bare ba".

Gyara zamansa Abbu yayi yana sake kallonta ya ce.

"Nasan da batun Maryam ai, ba yanzu kika gama gaya mana cewar ya amince sai dai a haɗa su duka biyu a aura masa su ba?, koba haka bane?".

Ɗaga kanta tayi tana cewa.

"Hakane Abbu".

"To danmi yasa bazaki amince da hakan ba?, tunda har ya aminta da hakan".

"Ni gaskiya Abbu bazan iya zuba ido naga Hammad ya auri Ƴar kishiyata ba wacce duk duniya ta tsane ni gaba da baya, ita fa kishiya duk inda take ba mutuniyar arziƙi bace".

Wani murmurshin manya Abbu ya saki yana sake cewa.

"Da yawanku Mata irin tunaninku kenan, kuna ɗaukar kishiya abokiyar gabarku ce, wata ko harga Allah har cikin ranta saboda Allah take zaune dake, ki ce shaiɗan zai rinƙa zugawa kina ganin kamar ta mallake miki miji ne, amma kwata-kwata idan kika tsaya kika bincika kikai nazari zaki gane ba haka bane, kawai tsantsar kyautatawa ce a tsakaninta da mai gidan, wadda idan kika fahimta ƙila ke akwai abunda baki iya ba wadda ita ta iyasa take ma mai gidan naku wadda ta saye zuciyarsa. Bari kiji Mansura duk da ni Mahaifinki ne, baki zo kika iske Mata biyu ba a cikin gidan nan ba, bawai yi ne banda ra'ayin yi ba, a'a babu wacce zan iya haɗata da Mahaifiyarku, saboda Mahaifiyarku ta zauna dani tun ina al'majiri na, tun ina fakiri na, bawai saida na tara uwar dukiyar nan na same ta ba a'a, tare duk mukai gwagwarmayar rayuwar nan da ita, duk wasu wahalhalu da Mahaifiyarku mukayi, hatta garin kwaki nasha zuwar mata dashi bata taɓa ɗaga kai ta kalla ba, saima tayi min godiya ta sake bani kwarin gwaiwar neman na kaina gobe, dan haka bazai yiwu nayi arziƙi na ce zan auro wata daga sama ba, kuma ace tazo ta ce zata saka na juya ma mahaifiyarku baya ba, duk irin haka nake hange shi yasa ma banda niyar ƙara wani aure ni, sana bazan iya da ciwon kanku ku mata ba. Kar kiga na faɗi haka ki ce kema mine-mine, ki sani fa ke da arziƙinsa kika auresa bawai a tare kukai arziƙin ba, danya kawo wata wacce ƙaddara ta faɗa masu ai baiyi laifi ba, idan ma bai auri Nuratu ba ai sai Allah ya tabbaye shi, ciki kuma harda ke wadda Allah zai tabbaya ɗin".

Zuciyar Ummu ba abunda take sai kunbura, dan ita har yanzu bata jin wannan haɗin zata amince dashi a cikin zuciyarta, bata jin zatayi murna dashi har abada.

Maganar Umma data ji ne ya katse mata tunaninta.

"Amma Malam duk da haka dai, lamarin kishiya fa daban yake fisbilillahi, baima kamata ya kawo mata wannan maganar ta haɗa aure da Ɗiyar kishiya ba, ga dai Ɗiyar Ƙanwarta nan Maryam ina laifi ma".

Dawo da dubansa yayi kan Umma dake maganar ranta a ɓace daga ganin yadda take maganar itama, ya ce.

"Ke mi kika sani akan lamarin kishiyar?, ke da baki taɓa zama da ita ba, ki bari wa'inda suka santa suka zauna da ita sune zasu faɗi magana na yarda, suma ɗin sai na auna zancan su da ma'aunin hankali".

Shuru kawai Umma tayi danya gama rufe mata baki kuma tunda ya faɗi hakan.

Ya sake kallon Ummu da jikinta ya riga yayi sanyi danta lura gudun gara ne tayi ta koma gidan zago, dan nan ɗin data taho bata jin za'a goya mata baya, Umma ce kaɗai ta iya fahimtarta ita kuma bata da iko da Abbu duk abunda ya yanke a gidan ta sani ya yanku ne.

"Abunda nake so dake shine Mansura ki tashi ni da kaina zan mayar dake gidan naki, zanji duk abubuwan da suka faru a bakin shi mijin naki, idan har ba wata cikakkiyar hujja to ki sani ni ne nan zan basa goyan bayan ayi haɗin nan kinji na gaya miki?".

Idonta cike tab da ruwan hawaye ta ɗago da kanta tana kallon Abbu ta ce.

"Amma Abbu dan All......".

Dakatar da ita yayi wajan ɗaga mata hannu, shi yasa ta yin shiru kawai tana maida kanta ƙasa zuciyarta na zafi sosai ta rantse da Allah baza taɓa sama auran nan albarka ba, zata bari ayi ne kawai domin anfi ƙarfinta.

"Basai kin ƙara cewa komai ba, tashi zaki yi yanzu mu wuce muje".

Ya faɗa yana miƙewa tsaye, Umma ma ta miƙe sai Ummu data miƙe da kyar jikinta a mugun sanyaye.

Bubbuga bayanta kawai Umma take yi tana bata baki har suka fice Umma na tsaye tana tausayin Ummu ɗin, tabbas tasan akwai ciwo kam, tasha shanye abu makamancin wannan, tayi kusan hauka ta kwanta a gadon asibiti na tsawon watanni a lokacin data gano gaskiyar cewar Alhaji ya auri wata can daban bada saninta ba

22 / 40