Tsanin Kaddara Complele Book Zahra Star.docx

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   37 / 40

108K to 111K   out of 118.4K words

na watsa ruwa nazo kisha labari, yau nayi alƙawarin baki labarin waye Mijinki da ahalinsa, sana na ɗansa ana yimin bincike da halin dashi Sadeeq ɗin yake ciki a yanzu, zanyi miki albashir da cewa Mijinki ya dawo ainafin waye shi a baya, ya dawo da dukkanin tunaninsa na baya, sai dai fa duk abubuwan da suka faru dashi yana cikin jinya bai iya tuna komai ba, sana naji ance Doctor ɗin daya ci gaba da kula dashi har ya dawo dai-dai ya ce ayi ƙoƙari a rinƙa tuno masa da abubuwan da suka faru dashi yana cikin ciwo wa'inda suka zama dole ya sani, wa'inda kuma babu fa'idar sanar dashi ɗin gara a barshi kawai basai ya sani ba, amma kinga Haj Hauwa da yake ke basu ɗauke ki a bakin komai ba sun barki da auransa a kanki, kuma sunƙi sanar dashi komai yasa har yanzu bai san ma wace ke ba, naji raɗeɗin cewa wai suna shirye-shiryen aura masa Huda ne, sai wani nuna masa soyayya suke, amma fa zaki sha mamakin wadda ya binciko min bayanan na ce tabbas Sadeeq na yawan faɗawa tunanin kamar akwai abunda ya rasa wadda ya zame masa rabin rayuwarsa, amma su Haj Hauwa kwata-kwata sun datse duk wani abun da zaisa ya tuno ki, ko ya iya tunowa kunyi wata rayuwa a baya. Hmm Sakina wa'innan mutanen sun wuce duk tunaninki kawai bari naje na fito, zaki sha labarin su waye su, sana idan sun san wata ai basu san wata, da yardar Ubangiji ki kwantar da hankalinki Huda bazata taɓa zama Matarshi ba, mudun ina lumfashi, kin kusa haihuwa kina haihuwa lafiya zamu koma gidan nasu ayi duk wacce za'ayi, kowa ta girbi abunda ta shuka".

Wata irin zufa ce ke yankoma Sakinaa idonta sun kaɗa sunyi jawur na tsabar tsanar su Haj Hauwa, yanzu ashe Sadeeq ɗinta ya dawo normal cikin hankalinsa amma yanzu baima san da zamanta ba?, bare yasan da zaman cikinsa dake a jikinta?. Wasu hawaye ne masu zafi suka shiga tsiyayo ma Sakina tana jin wani iri a zuciyarta, tunowa da wai Huda yanzu suke shirin bashi, yasa ta sakin kuka marar sauti, tana jin yadda zuciyarta ke mata wani irin bala'in zafi, ƙirjinta na soya, wani kalar kishin Mijin da bai san da ita ba a yanzu yana taso mata, haɗe da wani irin tausayin kanta.

Halisa bata daɗe ba ta fito riƙe da lemo a hannunta, sanye take da rigar shan iska ta fito ta zauna kusa da Sakina ganin irin halin ruɗu da baƙin ciki data shiga, yasa Halisa dafa kafaɗarta tana cewa.

"Kifa kwantar da hankalinki, komi suke ciki kamar a tafin hannuna suke yanzu, domin tunda kika bani shawarar karna kashe wayata, idan sun kira kai tsaye na ce masu canjin wajan aiki na samu, hakan yayi aiki, domin da yanzu sun gama gano ƙila nice naje na ɗauke ki, koma su ɗiga wata ayar tabbayar a tare dani, haka kuma kinyi dai-dai da kika ce a gaya ma Iyayenki, ba gashi ba suma hankalinsu ya kwanta ba, duk wadda ya kira su kai tsaye su nuna basu san zancen ba. Yanzu dai gyara zama ki fara shan labari kawai Sakina".

Gyara zaman kuwa Sakina tayi tana ƙara maida duk wani hankalinta wajan Halisa data fuskanci Sakinar sosai ita ta fara da cewa.

"Zakiyi mamaki idan na ce miki Mahaifiyar Sadeeq data kawo sa duniya da Haj Hauwa uwa ɗaya suke hakama uba ɗaya?".

Sosai maganar tasa Sakina sakin baki wani irin mamaki ya rufeta data kasa cewa komai, kawai sai bin Halisa da take da ido kawai da zallar mamakin abun ta ce mata ɗin.

Ganin haka yasa Halisa sakin murmurshin gefen baki kaɗan tana girgiza kanta ta ce.

"Hmm akwai rikitarwa, kai tsaye mu kusa cikin labarin kawai".

*WAIWAYE*

"Tunda nake ban taɓa ganin fakiri irinka ba Ismail, na ce Ismail ka sake ni kawai ana dole ne?, ba ƴa ɗaya bace a tsakaninmu ba?, na ce zan riƙe Ƴata ka sake ni kawai, idan banda ƙaddara mi zaisa na aure ka, kana talaka futuk da kai, dube ka wai ka rasa mi zaka kawo min na ci da ranar Allah tsage-tsage sai garin kwaki?, wallahi Ismail kaji tsoran Allah ka sake ni kawai Malam".

Idonsa sun kaɗa sunyi jawur ya dube ta yana kallon Huda dake raɓe a waje tana jin duk abunda ke faruwa, yarinyar da bazata wuce shekara sha huɗu ba a lokacin, kamin ya dawo da dubansa inda Hauwa take ya ce.

"Yanzu Hauwa dan kawai Allah ya jarrabe ni da talauci shine bazaki iya zama dani ba?, a da can baya miye bana miki?, mi yasa baza ki hakura mu zauna tare ba har Allah ya kawo mana sauyi, kema gudun nawa zakiyi kamar yadda ƴan uwana sukayi?".

"Ubangiji Allah ya kiyaye Ismail na sake zama da kai, har gaban abada wallahi, ni ka sake ni kawai na ce, ƴan uwanka kuwa wannan kunfi kusa, babu abunda yasha min kai a ciki".

Wani irin abu ya haɗe mai zafi mai raɗaɗi daya riƙe masa wuya, yana tuno irin son da take masa a baya, lokacin da yayarta Sa'adhatu ta auri hamshaƙin mai kuɗin da duk faɗin Nigeria aka san da zamansa, tun lokacin Hauwa ta shiga mugun halin ciwon hassadar ƴar uwarta ta fita samun gidan hutu, babu irin abunda bata nuna ba, wani lokacin ta shanye da yake ƴar duniya ce, tasha su tattara kayansu daga ita har Huda su tafi gidan Haj Sa'adhatu suyi hutu mai tsawo amma Isma'il idan yayi maganar bata jin kunyar zuwa gidan Yayarta da auranta taje tayi zaune?, saita hayayyaƙo masa cewar ai bashi da abunda zai ciyar dasu koya shayar dasu idan sun zauna masa a gida, gara su tafi inda zasu sha jar miya ta bi masu jiki. Babu irin taimako da Sa'adhatu bata bawa Hauwa, amma dandanan ta cinye komai ta koma sake koma mata, zuciyar Hauwa ba abunda ke ciki saina ganin yaya zatai ta fita daga gidan Isma'il ya sake ta, ta auri mijin Yayarta, amma fa dole ta sani sai idan har Sa'adhatu bata raye ne zata iya auransa, dan haka ta uzzura ma Ismail ya sake ta, ta yadda zata ji daɗin tarewa gidan Sa'adhatu gaba ɗaya ta yadda zata shirya komai yadda take so ba tare da matsala ba, tunda suma marayu ne bata da inda zata je sai gidan Yayar tata, idan har ta fita daga gidan Isma'il ya sake tan.

Tuni ta fara shirin irin abunda zata aiwatar akan Yayar tata tare da haɗin gwaiwar wata Doctor da Hauwar tayima alƙawarin kuɗi masu mugun yawa idan har aka samu nasara a shirin nasu.

Ganin yadda take masa tujara yasa shi dawowa hayyacinsa akanta ya kamo da ciwon zuciya mai tsanani, dan haka yana ganin gara kawai ya sake ta data idasa kashe masa rayuwa a banza. Ya sake ta burinta ya gama cika, domin har wata buɗa ta saki lokacin da yake furta mata kalmar saki.

Sosai abun nata ya bashi mamaki wai dama haka Mata suke ne idan kana da arziƙi ka aure su kazo ka talauce sai su guje ka?.

Ranar har gadon asibiti ya kwanta, ya fara wata irin jinya mai wahalarwa, gashi baida kuɗin kulawa da lafiyar tashi, gashi babu Mata babu ƴarsa, tunda suka ɗauke ƙafa suka tafi bai sake jin ɗuriyarsu ba.

Ƴan uwansa ma zai iya cewar kusan halinsu ɗaya da Hauwar, sunma fi Hauwa mugun hali, domin da yana dashi sunyi masa sun kula dashi, amma banda yanzu dai-dai da tsinke baya jin wani ya kawo masa a asibitin da yake kwance, baƙin cikin hakan yasa yayi sanadiyar mutuwar shi, bayan yasha dogowar jinya mai cike da wahala da rashin kula, sau ɗaya Hauwa tazo Jana'izar Isma'il daga lokacin bata sake waiwayarsa ba, tunda dama ya riga da ya saketa kamin ya mutu, Huda ce kaɗai taji mutuwar Mahaifin nata, duk da irin ƙiyayyarsa da uwar tata ta dasa mata akansa, amma da yake uba ba wasa bane sai da mutuwar tashi ta dake ta, ita ko sharholiyarta kawai take dan haka babu Idda a kanta, lokacin ne ta fara baza capacity nata a gidan Yayarta Sa'adhatu dake da Yaro ɗaya tak a duniya, wadda take mugun su ita da mijinta Alhaji Abubakar Imam, suna yima ɗan nan gata na gani na faɗa bai taso a Nigeria ba, amma duk da hakan yana yawan zuwa inda suke, bai wani daɗe ba ya dawo gaba ɗaya Nigeriar da zama, tunda ya dawo ƙasarmu Nigeria ƴan mata ke uzzara masa tako ta ina da sunan so, shi kuma wani irin miskilin mutum ne wadda kwata-kwata al'amarin Mata basa sha masa kai ko kaɗan, shi yasa da yawan ƴan matan ke masa kallon mai girman kai da izza, sai dai yana da sauƙin kai da raha kaɗan amma ga wadda ya sani su kai sabo.

Haj Sa'adhatu ta fara wata irin jinya kaɗan-kaɗan ciwon yake cinta, an rasa wane ciwo ne dake cinta a tsaitsaye, kuma taƙi yarda suje asibiti saboda ita dai bata jin ciwon komai a jikinta sai ramar da take yi a tsaitsaye, tana wata irin muguwar ramewa kamar mai ciwon ƙanjamau.

Duk wani abu da tarairaya Hauwa na mata kamar ta damu da ciwon nata sosai, bata san cewar Hauwar ce sanadiyyar jefata a halin da take ciki ba, domin ita ce suka haɗa gwaiwa da Doctor Halisa ta rinƙa kawo mata wasu magunguna ba tare da Sa'adhatu ta sani ba, ta rinƙa zuba mata su a abincin cinta da lemo shanta, hatta masu girkin gidan saita hana su ita ke yi, Doctor ɗin dake kula dasu kuwa sai da Hauwa tayi duk yadda tayi aka maye gurbinta da Doctor Halisa a gidan.

So kawai take ta mallake komai na gidan, ga wani son Alhaji ya aureta ba wai ƴan uwarta ba, so take ta buɗe ido taga ita ce a gidan a matsayin Matar gidan ba wai ƴar uwarta ba.

Hatta Sadeeq da take gani so take ta kauda sa ta haifi nata ƴaƴan ta yadda ita zata mallake komai ba tare da wani yayi mata shigar sauri ba.

Wani irin baƙin buri ne danƙare a zuciyar Hauwa wadda ya riga da ya gama rufe mata ido da zuciyar imani, kwata-kwata yanzu bata da burin daya wuce taga gawar Sa'adhatu a hannunta, gefe guda idan ta kauda ta, ta dawo ta kan Ɗanta, yanzu matsalarta kawai taga Haj Sa'adhatu ta kwanta ta mutu.

Sannu a hankali ciwon ya ci gaba da bin jikin Sa'adhatu, ba yadda Sadeeq baiyi ba domin a fitar da ita ƙasar waje aga miye yasa take wannan uwar ramar babu dalili, amma taƙi, abun dama kamar yazo da ajali ne shi yasa ma taƙi bin shawarar kowa, hakan kuma ba ƙaramin jin daɗi Hauwa tayi ba, ita da Ƴarta Huda an zama ƴan gida sai abunda ake so akeyi, ko Sadeeq wani lokacin da yake ɗan gida baya yin ikon da Huda take yi a gidan.

Akwai wani ɗan uwansu Baffa dake yawan zuwa gidan shike son ɓata mata shiri dan haka shima a shirye take domin kauda shi idan har ta samu ta shigo gidan.

Wata rana da baza su taɓa mancewa da ita ba, ranar wata juma'a da safe, Hauwa taje ganin ya Sa'adhatu ta tashi?, sai dai mi? ta iske gawarta a kwance ta kalli sama fuskantar na fitar da wani irin annuri, idonta a rufe yake, ta ƙara wani haske idan ka kalleta a lokacin zaka ɗauka ko murmurshi ma take yi, amma nan tsabar annuri ne ke fita daga fuskar tata.

Faɗin irin halin da Sadeeq da Mahaifinsa suka shiga mutuwar nan ɓata baki ne, domin shi Sadeeq sai da ya kusa da zaucewa, da kyar da addu'a aka du'ufa kansa kamin ya dawo dai-dai, jinyar da yayi asibiti kuwa tafi ƙarfin wata ɗaya, duk ya fice daga hayyacinsa, daga shi har Mahaifinsa, rashin Matarshi wacce yake matuƙar so da burin suyi rayuwa tare mai tsawo har mutuwa, sai gashi ta tafi ta barshi cikin wani irin halin kewarta.

Hauwa ko duk ta fisu nuna shiga tashin hankali da ɗimuwar mutuwar ƴar uwarta, itama har jinya ta kwanta ita da Huda da suka nuna mutuwar tafi bugunsu sosai fiye da kowa.

Da wannan damar tayi amfani da rinƙa nunama Sadeeq wata irin kulawar da har Alhaji Abubakar yaga mi zai hana ya auri Hauwar tunda dama ƙanwar matarsa ce?, ƙarin daɗawama jini ɗaya ne uwa ɗaya uba ɗaya ne a tsatso ɗaya suka fito, bai wani duba abunda kaje ya dawo ba, saboda zamanta gidan har na tsawon shekara biyu da mutuwar Sa'adhatu da yadda take kula da gidan ba nuna ha'inci ko gajiyawa, tana bawa Sadeeq wata irin kulawa da riritawar dake ƙara sawa Alhaji Abubakar ɗin son auranta, shima kansa kulawa take basa sosai, shi yasa ma wasu daga cikin manya suka ga babu wacce ta dace daya aura sama da Hauwar, sai tafi riƙe masa gida, tunda tasan komai dangane da gidan nasa, dan haka yabi shawarar manya ya fara neman yardar Hauwa dama kuma kamar zan iya cewa jira take dama ya furta hakan da kansa, domin saboda da hakane ma ta fara yin wannan kulawar da nuna soyayya tsantsarta akan Ɗansa.

Bata wani ɓata lokaci ba ko jan aji ta aminta da auran, a ranar ita da Huda kasa bacci sukai tsabar murna da burinsu zai cika.......

Chapter 45

Wasa-wasa Hauwa ta fara mallake komai ta sanadiyar kissa tsantsarta, karin farko ita da ƴarta suka lula Makkah daga can suka famtsama yawon shakatawa a can ne kamin ta dawo tunaninta ya sauya na cewar zata kauda Sadeeq, tunaninta ya sauya ne gara kawai tasa Sadeeq ya auri Huda lokacin ta hanyar da ita kanta Hudar zata samu abun duniya idan har ta auri mutum kamar Sadeeq.

Huda ta aminta domin itama harta fara son nashi, suna dawowa Haj Hauwa bata sha wahala ba wajan Sadeeq da Mahaifinsa kai tsaye Alhaji Abubakar ya aminta har yana babu dama wacce ya dace ya aura ɗin sama da Huda ƴar uwarsa, ba wai dan yana sonta ba Sadeeq ya amince da auran.

Sai dai fa wata irin ƙaddara da Allah ya aikoma ma Sadeeq ɗin ko ƙaddara ce wacce Allah ya hukunta cewar Huda ba zata taɓa zama Matarshi ba ce Allah ya aiko ta, domin ana shirye-shiryen fara biki Sadeeq yaje taron ɗaurin auren wani shaƙiƙin abokinsa hanyar Kaduna zuwa Kano yayi wani irin mummunan haɗari da yayi dogowar jinya a sume bai san inda kansa yake ba, da kuma ya farka ya tashi ba'a dai-dai ba, saboda dama Doctor ya ce kansa ya bugu zai iya samun cutar mantau, ya manta komai na rayuwarsa.

Hakan ce ta kasance lokacin sosai Alhaji ya shiga tashin hankali aka ci gaba da kulawa dashi, nan fa ne Haj Hauwa ta fara janye jikinta daga auran Huda da za'a haɗa dashi, sai da tasan yadda tayi ta tura Alhaji ya bar ƙasar tare suka tafi, ita ta rigasa dawowa saboda wani business daya taso masa a can, sai Allah yasa tayi masa wani mugun abunda ya manta cewar ɗansa kwaya ɗaya tak baida cikakkiyar lafiya yana kuma buƙatar kulawarsa a yanzu, tayi sanadiyar watsa auran, ita kanta Hudar babu kunya babu tsoron Allah ta bigi ƙirjin ta ce tafi ƙarfin auran mahaukaci irin Sadeeq ɗin a yanzu, domin ciwon nasa sai ya zama kamar baida cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa ne, saboda wani lokacin zai tashi yayita fashe-fashen abubuwa idan da mutum a kusa kuwa yasha ɗan banzan dukan a wajensa, idan kuma ciwon ya lafa ya babu uhum babu uhum-uhum, sai hakan yasa wata mugunta ta darsu a zuciyar Haj Hauwa ta hanyar ƙara ɗura masa muggun magunguna domin ma har abada karya warke ya dauma a matsayin mahaukacinsa.

Sannu a hankali aka fara samo masa mai kulawa dashi saboda irin magungunan da ake basa yasa idan wani ciwon ya tashi baya iya yin komai kashi nan fitsari nan, dan haka Haj Hauwa ko inda yake basa shiga, muguwar ƙyamarsa suke haɗe da wata irin hattara sa suke masa, duk wadda zaizo domin kula dashi da ƙafafunsa yake guduwa, saboda kwata-kwata babu mai jimirin kulawa dashi, wasa-wasa sai da aka kawo mutane sama da ashirin suna guduwa, dan haka ne yasa na basu shawarar mai zai hana su samo masa Mata a aura masa ta ci gaba da kulawa dashi, a aura masa wacce bata da galihu gaba da baya wacce bazata iya gudunsa ba har Allah ya kawo ƙarshen zamanta dashi wato ranar daya bar duniya, domin ita Haj Hauwa ƙwaƙwalwarta da tunaninta sun bata gara ya mutu kawai kowama ya huta, abu ɗaya ne ta manta Sakina cewar lafiyayye ne zai iya kasancewa tare da Mace, yabar tsatsonsa, ranar da Huda ta kai mata maganar itafa alamun ciki ne take gani tattare dake, ta shiga wani irin tashin hankali ba ɗan kaɗan ba, har sai da ta furta tabar aiki baya, sai dole tayi duk mai yuwuwa tasa ya daina sha'awar kowacce Mace da sunan ya kasance da ita, sai dai rana tsaka guduwarki, ta hargitse ƙwaƙwalwarsa Sakina ta hanyar nemanki da yayi ya rasa, ya saba dake sosai ya rasa ki ya rasa inda zai saka kansa, yayi kuka haukansa lokacin gaba ɗaya sai da suka tashi, ya hargitse komai dake Part nashi, ance har yana buga kanshi da banko, dama kuma Doctor ɗin da farko ya fara kulawa dashi ya ce masu idan ya ƙara haɗuwa da wani hatsari koda bana Mota ba idan kansa ya bugu zai iya dawo da tunaninsa, zai iya warkewa gaba ɗaya, a lokacin sunso dakatar dashi ita da Huda, sai dai ya tafi dogowar suma kamar waccan lokacin a baya da yayi haɗarin, lokacin da Doctor ya shaida masu idan har ya farka zai iya dawowa cikakken mai lafiya kamar kowa, yasa burin Haj Hauwa na baya ya sake dawo mata a zuciyarta, na haɗa aurensa da Huda, duk wani mugun abu tare suke ƙullasa da ƴarta, shine dawowarsa suka kwashe komai dake Part nashi aka

37 / 40