Tsanin Kaddara Complele Book Zahra Star.docx

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 40

21K to 24K   out of 118.4K words

ta aje mata a kitchen ɗin ta ɗibarma su Inna nasu ta kai masu taje ta saka nata.

Zata fito kenan taji saukar muryar Ma'u bayan ta ɗakko abincin nata, ta wani dubeta a shaƙaƙe ta ce.

"Da kika gama dafa abincin safen ita Maami uban wani zai dafa mata nata abincin kike nufi?, biyan uwarku fa ake kuɗin aikin nan da kuke mana".

Humaira ta ɗan murmusa kaɗan tana duban Ma'u akan fuskarta ko kaɗan bata nuna taji haushin abunda ta faɗa ya ɓata ranta ba, ta daure ta shanye duk da ji take kamar ta fallawa Ma'un mari kota gyara kalamanta, tunda taga kwata-kwata su dukansu daga Ma'un har Maryam ɗin basu iya magana ba, faɗin magana kawai suke basa taunata ta ce.

"Ai na zuba mata ɗanwaken na aje".

"Ohh an gaya miki Maami na cin ɗanwake ne?, ko kuwa kin zata tunaninki zata rinƙa cin duk wani abincin da kika dama kika dafa a son ranki?, to bata ci, dan haka idan kin gama kamin ta tashi ki fere mata dankalin turawa da kwai da ƴar miya ki aje mata idan ta tashi zata ci".

Wani abu mai ɗaci Humaira ta haɗe tana ɗan kauda fuskarta gefe ta sake shanye wani takaicin kamin ta dawo da dubanta inda Ma'u take ta ce.

"To"

Kawai zata juya ta tafi ta sake jin Ma'u ta ce.

"Yawwa ki haɗa mata da ruwan shayi dan tafi so tana tashi ta fara shan ruwan shayin".

Bata tsaya ba ta amsa mata da insha Allah kawai tayi saurin shigewa ɗakin Inna.

Inna ta dubi Humaira ta ce.

"Kin daɗe wallahi da yanzu nake cewa Sakina ta tashi mu wuce kawai kar rana tayi mana bamu shiga Kano ba, kuma ni yau nake so naje na dawo, dan bazan iya kwana gidan Sakina ba".

Zama Humaira tayi a hankali tana miƙama masu ruwa da Mai da bata ɗakko ba shine taje ɗakkowa ta taho na nata ɗanwaken ta zauna ta zuba masu suka fara ci, basu daɗe ba suka gama.

Inna ta dubi Humaira tana tashi tana goya Ummi sai Sakina dake tsaye da jakarta, Humaira ta miƙe tana jin Innar na cewa.

"Dan Allah Humaira kar kiyi wani abun magana har naje na dawo".

Da to kawai Humaira ta masa da faɗin.

"Insha Allah Inna bazanyi ba, yanzu ma zanje na dafa ma Maami abincin da zata karya da safe wai bata cin ɗanwake inji Ma'u".

Murmurshi kaɗan ta saki Inna ta ce.

"Ba wai bata ci bane kawai bata cinsa da safe ne shine yasa, kije kiyi aikin mu mun wuce sai Allah yayi min dawowa".

Kamar Humaira zatai kuka ta kamo hannun ƴar uwarta Sakina kawai ta jawota ta rungume sai ga hawaye su dukansu sun fara Inna ta kauda kanta tana jin itama hawayen na sun zubo mata tayi saurin mayar dasu, da son ranta ne ace har Bilkisu dake can Dutsanma ta haɗa su waje ɗaya suna zaune tare da ita, amma sai gashi yanzu ba damar hakan a gare ta, tunda kowanne da nashi Uban, su Humairar ne da Sakina kaɗai suke Uba ɗaya, kowanne da ƙaddarar da yake fuskanta a cikin ƴaƴan nata, daga su har ita kuwa suna fuskantar kalubale, tana fatan nan gaba su duka su samu sauyin rayuwa, ko da ita bata samu ba su, su samu shine kawai burinta.

"Miye na kukan ne haka Humaira?, ya isa haka nan muje Sakina waje na ƙure mana".

Sakin juna sukai suna share hawaye Sakina ta fice daga parlon Inna na biyo bayanta sai Humaira data fito zata wuce kitchen har sai da taga sun fice daga gidan sana tana saka hannu tana sake ɗauke wasu hawaye data ji suna zubo mata, sauke ajiyar zuciya tayi haɗe da jan lumfashi kaɗan ta juya jiki a sanyaye ta wuce kitchen ɗin tana binsu da addu'a.

Tunda sukai ɗauki hanyar Kano yanzu Sakina ke jin gabanta na faɗuwa haka kawai, ɗaurewa kawai take dan da kyar take jan lumfashi kamar wacce ke shirin kamuwa da rashin lafiya, haka kawai gangar jikinta ya kama tsoron komawarta Kano.

Bata dai gaya ma Inna ba dankar ta tada hankalinta har suka shiga garin Kano wajan ƙarfe Goma na safe.

Kai tsaye Tudun Yola suka nufa mai Ɗan Saho na sauke su Sakina ta fara bin gidan Aunty Sakina da kallo tana wani irin takaicin komowarta gidan, a lokacin da tayi mata wannan rashin mutumci da tayi alkawarin bazata sake zuwa inda take ba, sai gashi wata ƙaddarar ta sake maido da ita.

Sai da Inna ta kamo hannunta suka nufi ƙofar gidan, wacce take a rufe.

Tsayawa sukai suka fara ɗan bubbugawa sun jima a tsaye kamin aka zo aka buɗe masu.

"Lahhh aunty Nana kune da safen nan?"

Murmurshi kaɗan Inna ta saki tana duban Sawwama ɗiyar Aunty Sakina ɗin wacce itama duk duniya ita kaɗai ce a wajanta ta ce.

"Ai kuwa Sawwama mune".

Murmurshi ta saki tana duban Sakina ta ce.

"Ayyah Sakina ke daga jiya kinzo zan tafi Islamiyya sai kuma na dawo na iske bakya nan wai Umma ta ce min ai har kin tafi dama saƙo ne kika zo kawo mata".

Murmurshi kawai Sakina ta saki tana girgiza kanta, da ace Aunty Sakina ta ɗakko hali irin na Ƴarta ne da kuwa an zauna lafiya da ita, sai dai ko wanne da halinsa Sawwama yarinya ce mai sun jama'a wacce bazata wuce sa'ar su Sakina ɗin ba.

Matsa masu tayi suka shigo har cikin parlon gidan wadda yaji kayan more rayuwa ba laifi, Auntyn Sakina tana cikin rufin asiri, amma fa Inna duk ta fisu cikin rufin asiri a yanzu, amma sai dai duk da hakan babu ta yadda za'ai ta iya riƙe ƴaƴanta a cikin rufin asirin nan, tunda rufin asirin ba nata bane na mijinta ne.

Suna zama Aunty Sakina ta fito sanye take da kayan bacci a jikinta, tana hamma ta fito, sai dai ganin su Inna da Sakina dake zaune ƙasa sai Innar data zauna akan kujera tana kwanto Ummi data farka yanzu tunda suka taho dama take bacci.

Hammar da take ce ta tsaya ta wani bisu da wani irin kallo kamin ta ce.

"A'a wa nake gani kamar Aunty Nana?".

Da yake ta girmi Aunty Sakina ɗin kusan ita ce Ƙanwarta ta huɗu ma a gidansu.

Murmurshi kaɗan Inna ta saki tana kallon Sakina data matso ta zauna tana binsu da kallo kawai.

"Ni ce dai Sakina na tako da kaina".

Taɓe baki tayi kaɗan ta waiga inda Sawwama take tsaye ta ce.

"Sawwama je ki fara haɗa masu abinci ki ɗakko masu ruwa yanzu".

"A'a sai dai ruwan gaskiya domin a ƙoshe muke ma".

"To ai shikenan Madallah yayi kyau".

Murmurshin dai Inna ta sake yi tana sake kallon fuskar Sakina yadda ta wani haɗeta tayi kicin-kicin da ita tunda ta fito ta gansu a cikin gidanta.

Gyara zama Inna tayi ta ce.

"Ba wani abu bane yasa na zo gidan ki Sakina sai na roƙe ki dan.....

Tsaida ta Aunty Sakina tayi da sauri da cewa.

"Ki roƙe ni na riƙe miki Sakina ba?, kinga fa yadda ake rayuwa da kyar ake samu a ci na yau dana gobe, sana mijina mai yawan tafiye-tafiye ne dan yanzu hakama baya nan, kuma babu yadda za'ai na ɗauki Yarinya a cikin gidansa na riƙeta bai sani ba".

"Sakina shin ai kin tsaya kiji dami na zo ai ko?".

"To ai ina jinki".

Wani kalar takaici ne ya rufe Inna badan tana son inda Sakina zata samu ta zauna ba, da wallahi yau saita nunama Sakina ita fa ce Yayarta ba wai ita ce ƙanwarta ba, ji yadda take wani gaya mata magana kai tsaye, kawai dan tazo neman alfarma a wajanta, a zuci Inna ta ce.

"Kai jama'a Allah Ubangiji ka hanamu neman alfarma a wajan ƙananun mutane wa'inda basu san darajar ɗan Adam ba".

A fili ta shanye komai ta maida komai ba komai bane ta ce.

"Abunda nake so na ce miki shine, ba dole sai kin riƙe min Sakina ba, zuwa nayi dan Allah ki nemarma Sakina gidan da zata rinƙa aiki ana biyanta".

"Aikatau kike nufi fa?".

"Shi nake nufi, ki samar mata gida wadda a can zata koma da zama gidan aikin kenan, shine dama abunda ya kawo Ni".

Sauke ajiyar zuciya Aunty Sakina tayi kaɗan tana faɗawa tunani.

To ai data san hakane da tun farko bata kori Sakina ba, da ace wannan tunanin yazo mata da tuni ai Sakinar da daɗe a gidan aiki, amma kwata-kwata ita hakan bai zo mata.

Can ta nisa ta ce.

"Ai Aunty Nana indai wannan ne karki wani damu, akwai wata Aminiya ta Haj Bharaka dake samoma ƴan mata aiki gidajen masu kuɗi, zan kira ta zuwa gobe muyi maganar kuma insha Allah zata samu ne karki wani damu".

Murmurshi dai Innar tayi tana kallon yadda yanzu fuskar Aunty Sakinar ta sake ba kamar farkon zuwansu ba, kai ɗan Adam sai Allah kawai ke iya masa.

Inna ta ce.

"To yayi na gode ni yanzu zan wuce komi kenan sai ki kira ni".

"A'a Aunty ai kin bari kici abincin rana ko kamin ki tafi?, kin ɗan huta kuma".

"A'a wallahi gara na wuce kawai bana son yin dare".

Babu yadda Aunty Sakina batai ba Inna ta tsaya taci wani abu amma taƙi, da kanta ta raƙota har ƙofar gida Inna ta wuce ta bar Sakina da tsananin kewarta, idonta sunyi jawur, har saida Sawwama tazo ta jata ɗakinta tana tausayin rayuwarsu. Miye a ciki idan Ummanta ta riƙe Sakina?, ita bata ga wani abunda zai hanata hakan ba, kuma babu ko ɗaya daga cikin arziƙin da suke dashi da zai ragu dan kawai an riƙe Sakina a gidan.......

*TSANIN ƘADDARA*

*©Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 9

*Unguwar Hayin Ruwa, Dutsanma local government Katsina State Nigeria*

"Kina ina baƙar munafuka algunguma fito nan?".

Da wani sauri Inna Ladidi ta yaye labulan ɗakinta ta fito har zananta na shirin cirewa tayi saurin kamoshi tana ɗaure shi a ƙugunta.

Ta wani dubi Inna Asabe tana taɓe baki ta riƙe ƙugu ta ce.

"Ke tunda sanyin safiyar nan zaki wani fito kina tada jijiyoyin wuya lafiya zaki rinƙa kwaɗa min kira?, naji kina wani baƙar munafuka wacece munafukar?, fatan dai ba dani kike ba?".

Inna Asabe tsabar baƙin ciki daya cika mata zuciya bata san lokacin data ce.

"Dake ake ko akwai wani abunda kika isa kiyi".

"Hmmm"

Kawai Inna Ladidi ta ce tana sakin wani shu'umin murmurshi kamin ta ce.

"Faɗi abunda ya kawoki har ƙofar ɗakina dan banda lokacin irinku".

"Ai dole ki ce baki da lokacin irinmu mana, mai baƙar zuciya annamimiya kawai mai zuciyar fir'auna".

"Kee kee kee Asabe dakata nanfa ɗaya, bazai yiwu kizo har ƙofar ɗakina kice zaki rinƙa zagina nayi shuru na kyale ba, dan haka wallahi Allah ki iya bakinki tun kamin zuciya ta kaini yanzun nan mu fara abunda muka saba dake"

"Yo mu fara ɗin tsoranki nake ji ne?".

"Kinga baiwar Allah zaki zo ki faɗi abunda yasa kikazo har ƙofar ɗakina kina min wa'innan maganganun banzar taki ko kuwa na shige ɗaki na barki kina ɓaɓatunki ke ɗaya?".

"To ai wallahi ko kin shige ɗaki har cikin ɗakin naki zan biki dole ne ma sai munyi wannan maganar. Bai zai yiwu ace kin san yarinyata ke son Sule kuma ace rana ɗaya kwatsam wai Binta ta shigo min da kuka gata can kamar zata mutu wai yanzun nan take ganin Amina da Sule suna kalaman soyayya, kuma ta tsaya ta tabbayesu sai ma mari da Sule ya wanketa dashi, haɗe da ce mata wai sati na sama zai aiko da iyayensa neman auran Amina".

"Ahehehehe to sai mi idan kinji hakan kuma kin gani?".

"Na rantse da Allah bazai taɓa saɓuwa ba bindiga a ruwa ba, idan na yarda Ƴarki ta auri Sule ki ce shegiya nake Ladidi".

Ladidi ta wani dubi Inna Asabe a shaƙe tana mata wani irin duba kamin ta ce.

"Kin daɗe baki bari Amina ta auri Sule ba dan Allah, to bari kiji ko zanyi yawo tsirara sai nasan yadda nayi Amina ta auri Sule, ke kuwa taki Ƴar ai dama kwace kukai ma Bilkisu dama kuma ance ai alhaki kwaikwayo ne, dan haka kin daɗe baki ɗau mataki ba, yo yama akai har kika bari na shallake ki aikina ya kama naki aikin baiyi ba?, ke mai uwa a bakin murhu, Uba fa gare ki Malami kuma kamar Boka yaya akai haka ta faru?, yaya akai kikai sanya haka?, heheheeee gaskiya kin bani kunya ma, duk wannan cika bakin naki ashe na banza ne?, mtswww dan Allah daga yanzu karki sake zuwar min har ƙofar ɗaki kina min wannan sokiburutsun naki".

"Idan aka ƙara fa akwai uwar da zaki iyayi ne?, kuma da kike wannan ba sai kinga anyi auren ba tukunna sai ki fara tutuya da jijji da kai".

Wata irin shewa Inna Ladidi ta ƙara saki harda su tafa hannu kamin ta ce.

"Ai kamar yadda na gaya miki aure ne gashi can Amina tayi da Sule, taki Ƴar ko sai dai abi wani zargin kuma, amma wannan zargi ya tashi yayi nesa da ita nesan da babu yadda za'ai ya dawo kanta".

"Ke wallahi Ladidi idan banci uwa......

"Keee dalla can Asabe dakata yafa isheki haka nan tom, kika sake kika ƙara zagin iyayena na rantse da tsarkin mulkin Allah sai na tuɓe yanzu nan mun daku ni ke dama ai mun saba, amma na yau dole ne a goge raini tsakanina dake".

"Uhmmm Ladidi kenan banda lokacin yin faɗa dake yanzu akwai lokacin da zan tuɓe ɗin mu dakun ai kin san dai ba tsoronki nake ji ba ko?, kuma ni da ke shege ka fasa".

"Hhhh ɗan halak sai yanka, na idasa Miki".

Ko sake kallonta Inna Asabe batayi ba ta juwa jiki a sanyaye ta nufi ɗakinta. Ace duk irin kulle-kullen data je Babanta ya bata tayi akayi na wanka akayi na turare akayi harda kwalli nasawa a ido amma duk da hakan Sule babu uwar data kamashi ace sai yau rana tsaka Ladidi taje tayo nata shirin wadda ya take nasu ya ci uwar nasu kuma, ace lokaci ɗaya ta canza tunanin Sule?, hatta hankalinsa ya koma kacokan akan tata Ƴar Amina, anya-anya Ladidi akwai wani abunda ta taka shi yasa har ta zage tana mata shirin kunyar nan, dole ne ma saita canza Malami idan ba haka ba tana ji tana gani Amina zata auri Sule tata Ƴar ko sai dai baƙin ciki ya kasheta.

"Inna kinje kin gansu ko a ƙofar gidan?, wallahi da gaske nake yi sune na gani bawai Bilkisu bace dan Bilkisu tana can tallar da kika sa mata har zuwa yanzu bata dawo ma unguwar nan ba".

Tunanin data faɗa mai zurfi ne ya katse jin maganar da Binta keyi tana kuka.

"Naje na gani da ido na na leƙa har ƙofar gidan, shine naje wajan ita baƙar munafukar wacce duk ita ce taje tayo mugun abun da Sule ya koma wajan ƴarta, amma wallahi ko zanyi yawo tsirara saina nunama Ladidi nafita sanin Malamai dole ne ma naje na canza wani takun na canza sheƙa dole ne wannan".

"Yawwa dan Allah Inna kiyi duk mai yuwuwa kar Amina ta auri Sule sai ni".

"Ke ni yanzu bawai ki aure shi nake so ba, a'a so nake kota halin yaya ne kar Amina ta auri Sule, koda ace ku duka zaku rasa shi hakan bai dame ni ba, ni dai kawai buri na ace Ƴarta bata aure shi ba, bani zata nunawa isa da gadara ba akan shirinta yayi aiki ni nawa baiyi aiki ba?, hmmm zata gane da Asabe take magana ne wallahi".

Amina ce tafe ta shigo cikin gidan tana wani washe baki tana tsallen murna, ganin babu kowa a tsakar gidan yasa ta sake sakin wata ƙarar murna haɗe da sakin shewa dan kawai mutanen gidan suji tana ɗan karkaɗa baƙar ledar da Sule ya bata wacce yayo mata ƴar sayayya a cikinta.

Sarai sunjita amma sukai kunnan uwar shegu da ita, hakan bai dameta ba ta ci gaba da yada maganganu na Rashin kunya kamin ta shige ɗakinsu.

Tana shiga Inna Ladidi ta sakar mata murmurshi ta ce.

"Idan banda abunki Amina ai ko kwana zakiyi tsakar gidan kina yada habaici baza su taɓa fitowa ba, saboda baƙin ciki ne ya rufe masu zukata, suna can yanzu haka zuciya ta kumbura kamar zata fashe tsabar baƙin ciki daya cika ta, ai yanzu muka gama uwar watsi da Asaben tabar nan da ɓacin rai ni ko ko a kwalar rigata kin ganni nan".

Dariya kawai mai sauti Amina ta saki tana zama ƙasa ta wani rarrashe tana cewa.

"Ai na rantse Inna kin gama min komai da har kika saka Sule ya dawo waje yana sona, wai kinga kayan maƙulashen daya kawo min yau ma?, duba ki gansu".

Matsowa Inna tayi tana faman washe baki ta ce.

"Kai harda su naman Kaza?, kai shi yasa Matar can Asabe kenan ta dage saboda tasan Sule akwai rufin asiri?, ehh lallai ba shakka ai ko dole na sake miƙewa tsaye na sake karkato da hankalinsa gare ki ayi sauri ayi bikinku ko kin tare a gidansa, wannan kayan daɗi haka?".

Amina data yago naman kaza tana cika bakinta dashi ta miƙama Inna ta fara ci itama sai wani gyaɗa kai take tana lumlumshe ido tsabar yadda naman Kazar ke kai mata, baki cike da Kaza Amina ta ce.

"Gaskiya kam Inna sai kin sake dagewa, dan naji yadda Binta ke gaya min maganar cewa ko zata mutu sai taga bata bari na auri Sule ba, dan haka yanzu zuciyarsu a hasale take komai suna iya yinsa domin cikar burinsa suma, dan haka dole Inna mu sake ɗaura ɗamara muma".

"Kware ko abunda kika faɗa haka ne, ai bata san wacece Ladidi ba har yanzu, gani na kawai take amma bata san abunda zan iya aikatawa ba, amma bata san hatsabibancin Ladidi bane, da ace tasan ni wacece da to tun farko

8 / 40