Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
Allah Alhaji Ahmed bai isa ba baki isa ki shigo min gida a matsayin kishiya ba, kuma tare da ƴanƴanki ƴan gaba da fatiha ba, harda ƙarin Agola aka zo mana da ita har cikin gida".
Runtse idonta Ammi tayi tana jin wani mugun ɗaci a zuciyarta da wani irin yanayi marar daɗi, ƙirjinta na wata irin soya ta buɗe idonta data rufe tana tunano abubuwa da dama marassa daɗi da suka dunga faruwa shekarun da suka wuce wadda dai-dai da rana ɗaya a ko yaushe sai sun rinƙa dawo mata daki-daki tunda ta shigo gidan a matsayin Matar mai gidan baccin ƙalubalen data fuskanta kala-kala kamin ta samu ta samu kanta a cikin gidan a matsayin Mata har komai ya zama dai-dai, sai dai wannan irin zaman da suke kullum na nuna isa da gadara da Ummu ke nuna ga Ammi a ko yaushe.
Intee dake tsaye jikinta ba abunda yake sai rawa tana jin wata muguwar tsanar Ummu da shi kansa Hammda ɗin wadda ya kasance jininta da kyar ta buɗe baki ta ce.
"Ummu kiyi hakuri amma idan Maza sun kare a duniyar nan bazan taɓ.......
Wata irin daka tsawa Ammi tayi ma Intee tana nunata da yatsa ta nuna mata hanyar saman bene kawai bata ce mata komai ba.
Da wani irin gudu Intee ta wuce tana sakin kuka mai tsuma rai.
"Uhmmm ai da kin barta ta amayar da abunda take so ta ce, ai koda bata faɗa ba har gaban abada Hammad yafi ƙarfin Ƴarki, yo mima zaiyi da ƴarki wacce ba'a san asalin waye ubanta ba, garama su Hassan ɗin da suka zo ƴan gaba da fatiha".
Ummu ta ƙare maganar cike da isgilanci haɗe da zallar wulaƙanci.
Tana gaba faɗar haka ta wani juya tana sakin dogon tsaki ta fice daga parlon, tana sake jin wani mugun haushin Ammi ɗin yadda ta gama ɓaɓatunta Ammin ɗin bata ce mata komai ba, duk da dama komi zata ce ma Ammi ɗin bata taɓa ɗaga kai ta kalleta ba bare ta tanka mata.
Tana fita Ammi ta zube akan kujera tana sakin wani irin kuka, bakin cikin magungunan Ummu na sasaƙar zuciyarta da ruhinta........
*TSANIN ƘADDARA*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
Chapter 2
*House No: 23, Gaweye Estate, Niamey Niger*
A hankali ta tashi ta miƙe zata bar parlon wayar dake aje a gefen kujera ta shiga yin tsuwwa.
Ɗan dakatawa tayi tana juyowa gaba ɗaya ta nufi wayar dake ajiye.
Murmurshi kaɗan ta saki ganin sunan mai kiran.
Cike da zumuɗi ta ɗauki wayar, sai dai abunda taji ne a cikin wayar yasa gaba ɗaya fuskarta sauyawa zuwa wani tsantsar ɓacin rai da takaici.
"Shin wai Aunty Nuratu mi yasa baza ki bani Intee ta taho nan Niamey ba ta ci gaba da zama?"
Daga cikin wayar Nuratu taja wani dogon lumfashi kaɗan kamin ta ce.
"Sadiya kinga bawan Allahn nan Abbinsu Hanan ya riga da ya ce shine kamar wadda ya haifi Intee, idan na ce zan ɗauketa na miƙa ta wajanki sai nake ganin kamar zaiga dan ba shine ya haife ta ba, da har zan rinƙa yanke hukunci kai tsaye a kanta, kin riga da kin san irin gudunmawar da Hammad da Abbi suka bada akan rayuwar Intee a sadda bata da gata a lokacin da rayuwarta ke gaf tarwatsewa sune suka taimaki ni suka taimaki rayuwarta, wallahi Sadiya bana son tuno duk wata rayuwa da irin baƙin ciki da tashin hankalin da muka fuskanta daga ni har Intee harke ma, wannan Matar ta kasa ganewa kullum cikin gaya min magana mai mugun min ciwo take akan Yaran nan su Hassan tun basu fahimta ba har sun fara gane inda maganarta ta dosa, dan ma yaran akwai hankali basu taɓa tara ta suka tabbaye ni ainafin miye yasa Ummu take ce masu ƴan gaba da fatiha ba".
Wani irin huci Sadiya ta saki ta ce.
"Wallahi Allah na rantse da Allah na tsani wannan Haj Mansurar, dan dai babu yadda ta iya damu ne, kin ganni nan ba dan ta so na auri Wan mijinta ba, nima har muke zaune a nan Niamey, ni naji daɗi saboda babu kishiya a gidan Alhaji Abbakar, kwanciyar hankali kullum muke ciki, amma ke duk masifar matar nan ta ramar dake kullum daɗa komawa baya kike".
"Uhmmm ai ke Sadiya kinji daɗi kam amma kishiya irinsu Ummu masifar ne. Kinga ina su Babana dasu Khairat?".
"Wai Mai sunan Baba, ai ko bai daɗe da fita ba, kin san shima wani miskilin kanshi ne idan ya abun nasa ya motsa, Khairat kuma tare suka fita zai sauke ta school, sai da ma ya jajjamata kunne da masifar wai ta raina shi ta barshi aje yana jiranta, daga yau ta nemi drivern ta shi ba driver bane".
Dariya kawai Ammi ta saki ta ce.
"Kai jama'a har yanzu dai yana nan da halinsa na rashin ɗaukar raini?, ai ya burgeni wallahi gara da yake jan girmansa, ita kuma ina drivern nata ya tafi ne ko tsabar rigima ce irinta Khairat?".
"Wallahi Aunty Driver ɗinta yaje Maraɗi ne can gidansu anyi masu rasuwa shine kawai na ce masa ya tafi da motar yayi kwanakinsa ya dawo, shine ni na ce ma Japhar ɗin ya miƙa min ita shine fa yake ta irin wannan mazure".
"Hhhhhhh Babana kenan na kaina, wai ni yaushe zai zo min ne da Khairat ina kewarsu fa?".
Zama Sadiya tayi a hankali cikin sakewa da ƴar uwarta sosai ta ce.
"Gaskiya Aunty zuwansu zaiyi wahala saboda Abbansu da wuya ya bari su zo Nigeria gidan nan naku, Haj Mansura yadda take nuna masu suma hakan baya masa daɗi dan zasu iya hawa sama akan Yaransa, shi yasa kawai idan an samu hutu a turo min su Hassan ɗin kawai dasu Ameera da Hanan".
Wani iri Ammi ta saki tana jin babu daɗi haƙiƙa tana bala'in son Yaran ƴar uwarta kuma kamar aminiyarta wacce take share hawayenta da duk wata damuwarta yanzu kiran nan da tayi mata har damuwar da Ummu tazo ta saka ta a ciki harta gushe, bata da kamar Sadiya duk faɗin duniyar nan tunda Inna ta rasu shikenan suka rasa kowa dama kuma Babansu basu tashi suka ganshi a tare dasu ba, sun tashi ne a wajan Inna Mace mai masifar bala'i da mitar tsiya, yawanci duk ita ce masabbabin jefa su cikin tashin hankalin da duk suka fuskanta a baya.
"Kina tare da ni aunty kina ji na?".
Faɗin Sadiya daga cikin wayar jin yadda Ammi ɗin tayi shuru tana faɗawa kogin tunani.
Ɗan wata ajiyar zuciya ta sauke ta ce.
"Shikenan karki damu insha Allah da anyi hutu zasu taho amma banda su Hassan saboda Abbinsu yana shirin fara ɗora su a harkar ɗaya daga cikin Companyn sa, idan akai hutu yana so duk hutu su rinƙa zuwa aiki suma, shi yasa duk Ummu tabi ta gama tada hankali take ta irin wannan abu fa".
"Karki damu Aunty sai sun zo ɗin komai fa zai wuce ne kamar ba'a yi ba, nama baya suka wuce wadda suka fi na yanzu bare wannan da yake da ɗan sauƙi akan irin abunda muka gani a baya hmm rayuwa kenan, ke munga rayuwa da tashin hankali iri-iri, da ace rayuwar baya bata wucewa da lallai mutane da dama sun mutu cikin baƙin ciki".
Da sauri Ammi ta datse Sadiya da maganar rayuwar da sukai a baya, dan ko kaɗan bata wani son tuno ta dai-dai da sakon ɗaya.
Sallama sukai tana sauke wayar wani kiran ya sake shigowa mata.
Ganin sunan dake yawo a saman wayar wato My Son Hammad, yasa ta ɗan saki murmurshi haƙiƙa tana son Yaron ko banza ya bada wata irin gudunmawa a rayuwarsu ta baya bare ta Intee, ya so Intee tun bata san wacece ita ba, tun bata san miye duniyar ba, ya bata kulawa duk da irin kyara da Mahaifiyarsa ke yawan masa akan shiga harkar Intee da yake yawanyi abun na mugun baƙanta mata sosai, kuma a kullum bata gajiya wajan zuwa ta zazzaga ma Ammi ɗin tujara da rashin mutumci iri-iri haɗe da gaya mata maganganu masu zafi da ɗaci.
Ɗaukar kiran tayi cike da kulawa ta amsa gaisuwar da wata irin muryarsa mai masifar taushi haɗe da natsuwa ya ce.
"Ammi Please a turo Intee ta zo ta ɗauki kwanonin nan na abinci na gama dasu".
Kamar zata ce Intee bazata samu zuwa Part nashi ba, sai kuma taji wani irin nauyi har abada Hammad ɗin nada wata irin kima da daraja a gareta daga shi har Mahaifinsa Abbi, bata taɓa masu musu akan abunda suke so, shi yasa shi kansa Hammad ɗin yake ganin kima da Mutumcin Ammi ɗin da ganin darajarta sosai yana son irin halayen Ammi ji yake inama ce ita ce wacce ta kawosa duniya Saboda irin hakurinta da yawan kawaicinta, yafi kowa sanin irin hakurin da take da Ummu a cikin gidan, ba kowacce Mace ce zata iya kauda kanta ta jure ta haɗe baƙin cikin da Ummu ke tusama Ammi ɗin ba, bata ɗau wani mummunan mataki ba, amma ita kullum bata taɓa ɗaga kai ta tanka mata ba.
"Okay Hammd insha Allah zan turo ta yanzu".
Zai katse wayar sai kuma ya tsaya ya ce.
"Ammi Please ta sanyo Hijab idan zata fito. Sana Ammi naga kamar Ummu ta shigo Part naki dan Allah Ammi ki ƙara hakuri da Ummu wallahi na rasa mike damun Ummu bana jin daɗin abunda ke faruwa a tsakaninku ko kaɗan".
"Haba Hammad babu fa abunda ta shigo tayi Ƙanwar ka kawai ta shigo gani Intee ta fita shikenan nan fa".
Murmurshi kawai ya saki yasan Ammi ɗin faɗa kawai take ɗanta kauda maganar amma yasan tabbas ta shigo ne dan tayi wulaƙanci ga Ammi ɗin da Intee, dan yasan tafi tsanar Intee akan sauran Yaran Ammi ɗin.
Ammi na sauke wayar ta miƙe ta nufi sama inda Bedroom ɗin Intee yake.
Tana kwance a tsakiyar gado tayi ɗai-ɗai har bacci ya fara ɗaukarta, murmurshi kaɗan Ammi ta saki tana ɗan matsawa a kusa da ita sosai, zama tayi a gefen gadon, tana saka hannunta a hankali ta shiga tattare mata uban gashin kanta daya watse mata har saman fuskarta, tsabar yawansa ko kitseshi ba'a iya yi, da anyi ma sai sulɓil gashin yasa kitson warwarewa, hular dake kanta tayi gefe shi yasa gashin babbazuwa har saman gadon bayanta.
Ƙamshin turaren Ammi da kuma yanayin yadda take mata yasa Intee gane Ammi ɗin ce a ɗakin dan haka ta buɗe idonta daya gaji da kuka, dan harda ƴan guntun hawayen da suka riga suka bushe mata akan kyakkyawar farar fuskarta.
"Ki tashi kije Yayanku Hammad na son ganinki a part nashi".
Da wani irin sauri ta miƙe a tsakiyar gadon, gashin kanta har yana rufe mata fuska, da sauri tasa hannunta ta maida shi baya, tana ma Ammi wani irin kallo na mamaki. Yanzu duk irin wulaƙanci da Ummu ta zo tayi akan Ɗan nata shine kuma yanzu Ammi ke ce mata ta sake zuwa inda yake, duk ba akansa bane ake zuwa ana ci masu Mutumci ba?, mi yasa baza su ja waje su kyale ta daga ita sai Ɗanta bane kamar yadda take so?, mi yasa Ammi keda kawaici har haka ne?, tsakani da Allah haƙurin Ammin nata yayi yawa, ai idan ka cika haƙuri da yawa cutar da kai ake har yayi yawa.
"Kinji abunda na ce ai ko?".
Ammin ta faɗa tana neman miƙewa zata bar Bedroom ɗin.
Da sauri Intee ta turo baki cike da shagwaɓar data zame mata jiki kamar zata sakar mata kuka ta ce.
"Amma Ammi.....
"Amma mi? Ki tashi kije kawai na ce".
"Ammi nifa na rantse bazan sake zuwa inda yake ba".
"Rantsuwar taki ta banza Intee kin kuwa san irin abunda duniya Hammad yayi miki?, wallahi da kin sani da baki buɗe baki kika ce haka ba, ko da yake lokacin baki da wani hankali da wallahi baki da bakin masa rashin kunya ko musu akan abinda ya ce kiyi masa, dan haka bana son sake magana ki tashi kije kawai".
Wasu hawaye ne suka shiga zubo mata a mugun hassale ta miƙe tana bin Ammi data fice daga bedroom ɗin da kallo, wani irin haushin Hammad ɗin na rufe mata zuciya, ita fa duk tana sane da irin abunda yayi mata a rayuwa gani take tunda yanzu shima ya nuna baya sonta Ummunsa bata sonta, to mi yasa baza su rabu da duk abunda ya shafe su ba?, ana wulakanta su akansa mi yasa Ammi take sake tusata wajansa?, mi yasa Ammi keda kawaici ne?, mi yasa bazata iya gaya masa yayi nesa da su bane?.
Wani irin tsaki ta ja tana miƙewa kamar zata fita haka sai kuma ta tsaya ta dawo daga baya ɗauki Hijab ɗinta ta saka, wani irin mahaukacin kyau Hijab ɗin ta sake mata kamar wata ɗiyar Larabawa.
Tunda ta fita take faman turo baki gaba, bata iske kowa a parlon nasu ba ta fice kawai harabar gidan nasu.
Tunda ta fita bata kalli kowa ba ta sake murtuke fuskarta tamau tana sake turo ɗan ƙaramin bakinta.
Tana shiga part ɗin babban parlon ƙamshinsa duk ya cike parlon wani irin mugun yanayi yake saka ta a ciki, wannan mugun turaren nasa yana tuno mata abubuwa masu yawan da suka wuce a baya, wani irin sanyin jiki yake sakar mata idan har tana shaƙar mayen ƙamshinsa.
A hankali ta shiga bin parlon da kallo, idonta ne ya faɗa akansa, dake zaune akan kujerar parlon ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya, akan cinyarsa Computer ce yana faman aiki a cikinta cike da kwarewa yake latsa Computer yadda kasan shiya ƙera ta yadda yake sarrafata da hannunsa da sauri kamar wani Injin.
Sake turo baki tayi gabanta na dukan Uku-uku taja ta tsaya nesa dashi a hankali cike da jin haushinsa ta ce.
"Y Hammad gani Ammi ta ce kana son gani na".
Bai tanka mata ba har tsawon lokaci, hakan yasa Intee sake turo baki gaba wani bala'i haushinsa na sake rufe mata zuciya ji take da tana da dama saita kama shi ta masa mugun duka, yadda take jin bala'in haushinsa a ranta.
Wata harara take zafga masa kamar idonta zasu faɗo, batai tsammani ba ya ɗago a hankali yana sauke idonsa akanta.
Da wani irin sauri tayi saurin ɗauke idonta akansa jikinta na ɗaukar rawa.
Idanunsa masu kaifin masifa na yawo a jikinta hakan ya sake haifar mata da bugawar zuciya mai tsananin gaske.
Wani irin kwarjini ne da Y Hammad ɗin mai masifar fisgar mutum, idan ya watsa maka idanuwan nan nasa dole nan take kake rasa duk wata natsuwarka.
Muryarsa taji mai bala'in taushi da wani irin zurfi haɗe da wata irin haiba a cikinta ya ce.
"Uhmmm ni na ce ina son ganinki ne marar kunya?".
Ai Intee bata san lokacin data wani irin ɗago tana zuba masa idonta ba itama, kallon kyakkyawar fuskarsa take da yanzu ya ɗauke nasa idon akanta yana sake maida hankalinsa akan aikin da yake a Computer dake akan cinyarsa.
Kyakkyawan Sajensa baƙi siɗik da ya zagaye fuskarsa ɗan siriri marar yawa bai wani cika masa fuska ba, hakama gemunsa daya haɗe da siririn Sajensa baida yawan azo a gani, hakan kuma ne ya sake ƙawata kyakkyawar fuskar tashi, fari ne amma ba wani can ba, farin nasa ba sosai bane tsaka tsakiya ne, sai dogon hancinsa ɗan siriri ƙarami shima wadda ya dace da kyakkyawar fuskar tashi, sai uwa uba kuma idanuwansa masu masifar girma sexy eyes ne dashi masu masifar tasiri a jikin Mutum idan har ya tsareka da su, sai kuma girarsa mai yawa data kusa haɗewa da ƴar uwar ta.
"Kallon fa Malama?".
Sake ɗauke kanta tayi daga kallon da take binsa dashi tana jin wani takaicin kanta itama, miye na tsayawa tana wani kallon wannan mai ji da kan nasa da wulaƙanci cike da ciki?, da alama can wajan Ummu ya gado wannan isasar da jin kai, domin itama duk haka take da wannan izzar da jin kan.
"Idan kin gama tsayuwar kallo na zaki iya zuwa ki kwashe wa'innan tarkacen naki da kika kawo".
Haushi takaici ne suka rufe Intee tana kallon saman darning table da ya gama cin abincin data kawo masa, amma wai yanzu yake kiran wai da abunda ta kawo masan da tarkace?, lallai Y Hammad ya cika ɗan rainin wayo wallahi.
Wani siririn tsaki taja, sai kuma tayi saurin saka tafin hannunta ta rufe bakinta dashi, tana faman zare ido waje, ƙirjinta na bugawa da mugun ƙarfi.
Tunowa Y Hammad ya tsani tsaki duk duniya baya son raini abunda yasa take shan wahala a wajansa kenan ko kaɗan baya ɗaukar raini.
Ganin har lokacin aikinsa yake a Computer kamar ma bai san tana wajan ba, sai ta sauke ajiyar zuciya tana hamdala duk zatonta baiji bane, sai dai sarai yaji siririn tsakin nata, saboda Allah yayosa da wani irin ji sosai sai kace ɗan Maciji.
Tazo zata giftasa ta wuce kawai bata san hawa ba bata san sauka ba taji yasa ƙafa ya taɓiye ta, tayi taga-taga zata faɗi ƙasan tayis ɗin, ta saki wata ƙara jikinta na rawa harta sadaƙas zata kai ƙasa kawai taji an ruƙo hannunta da ƙarfi an jawota zuwa baya, faɗowa kawai tayi ɗare-ɗare akan cinyarsa da yanzu ba Computer ya aje ta saman table ɗin dake kusa dashi.
Da wani irin sauri ta shiga kiciniyar miƙewa daga jikinsa, jikinta na ɗaukar wata irin masifaffiyar rawa haɗe da bugawar zuciya har ƙirjinta na ɗagawa.
Bai bata damar hakan ba, saboda ya danne ta ne sosai a jikinsa.
Kuka kawai ta sakar masa domin jikinsa da nata idan ya haɗu yana haifar mata da wani irin abu, ga shegen ƙamshinsa ɗin nan dake kassara mata duk wani karfin jiki.
Saka hannunsa yayi yana ruƙo fuskarta haɗe da riƙe ɗan ƙaramin bakin nata ya murɗesa da ƙarfi, Intee bata san lokacin data saki ƙarar azaba ba, hawaye kuwa kamar an buɗe fanfo suka shiga zaryar zubo mata.
Sake ɗago