Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
hawaye ne suka shiga zubo mata tana jin gaba ɗaya mafarkin da tayi tare da Nuratun ta ganta a cikin mawuyacin hali yana dawo mata sabo fil kamar yanzu ne take yinsa.
Ganin gari ya fara yin haske yasa ta miƙewa da sauri kamar an tsikareta ta fice waje tana ɗauro alwala, sallah ta idar tana Allah-Allah gari ya ƙara yin haske taje ga Nuratu domin hankalinta kwata-kwata yaƙi kwanciyar da irin halin data ganta a cikin mafarkin nata.
Kasa haƙuri tayi danji take gabanta na sake yankewa ya faɗi haka kawai tana zaune, dan haka da sauri ta rarumi takalminta ta saka tana niyar ficewa daga cikin gidan kawai taji murayar Inna ta fito daga ɗakinta tana hamma.
Ganinta zata fice yasa Inna ware idonta da sauri ta wastsake tana kallonta ta ce da sauri.
"Saurin mi kike kuma?, ina zaki je?".
Runtse idonta da ƙarfi Sadiya tayi tana haɗiyar zuciya ɗaurewa tayi ta juyo tana fuskantar Inna ta ce.
"Zanje wajan Nuratu ne".
"Ahh keda kika ce kinfi ƙarfin zuwa gidan da aka kaita?, miye na zuwa kuma yanzu ki ce wani zaki je gidanta?, ko dai akwai wata ƙullalliyar da kike shiryawa ne ban sani ba iyee?, idan ba haka ba ubanmi zaki je yima a gida tunda sanyin safiyar nan?".
"Kawai zuciyata ce ke bani Aunty Nuratu na buƙatar taimako na, tabbas akwai wani abu marar daɗi dake faruwa da ita, dan Allah Inna ki barni naje ina ɓata lokaci a nan ne ma".
"Sannu uwarta na ce kinji?, ke asuwaye da har idan wani abu ya sameta zaki wani ce kina ji a jikinki?, ni ya akai banji abunda kike cewar ba iyee?, tunda ni na ɗauki cikinta har na tsawon wata tara na raine ta duk ni banji ba sai ke?".
"Inna saboda baki damu da ita bane mana, ga amsa nan a bayyane Inna".
"Lahh ha'ila ha'ilallahu, ni Sadiya kike gaya ma cewa ban damu da Nuratu ba?".
Tafiya Sadiya ta soma yi tana faɗin.
"Bari dai na dawo Inna domin hankalina yanzu baya tare dani, yayi wajan ƴar uwa ta".
Ta ƙare maganar haɗe da sassarfar barin gidan da sauri, tana iya juyo ɓaɓatun Inna tana danna mata ashir ta inda take shiga bata nan take fita ba.
**************
"Kai mutunen ka ce jiya ka kwashi gara?".
"Bari kai dai ai ban san ma lokacin da mayen Giyar dana sha ya sake ni ba".
Zai sake magana wata Mace mai kama da ƴan duniya ta tsaya akansu tana kallon Sagir, ta wani sake saka hannunta tana turo kallabin dake akanta tayi ɗaurin ture kaga tsiya, ta turo shi sosai har saman goshinta, tana taunar Chingum tana yin kwai dashi haɗe da bada wani sauti ƙasss ƙasss.
"Ke kuma Luba miye haka?".
Wani duba tayi masa tana banka masa wani shegen kallo kamin ta ce.
"Kai kaga bada kai nake yi ba ka gane Jafaru?, da wannan ɗan hau ɗin nake".
Tashi Sagir yayi yana wani basarwa ya tako har inda take sosai kamar zai shige mata jiki ya ce.
"Haba Luba, miye nayi ma sarauniyar mata kuma?".
"Kai kaga ɗan rainin wayo zuwa nayi nasan matsayina a wajanka, ashe da gaske dai aure kaje kayi ka barni ni gani ƴar iska?, wacce ka gama da ita ko?, to wallahi bazai yiwu ba".
"Haba Luba wannan auran fa kawai nayi ne amma badan wata manufa ba".
"Mtswww to ka sake ta mana mudun kana son zaman lafiya ka datse igiyar auren dake tsakaninku mana, tunda ba sonta kake ba dama".
"Zan sake ta mana mi kike ce na baka na zuba ne?, dana gama da ita na gama kwasar garaɓasa zan yanka mata jan kati tayi gaba".
"Yawwa koda naji, dama abunda yasa na zo maka a haka naji ana raɗe-raɗin wai kyakkyawa ce, na ɗauka ko sonta kake ne ai".
"Ba wani so, idan kyau ne a gidansa ta zo ko Luba?".
Kallonsa Luba tayi tana murmurshi tabbas Sagir mai kyau ne kamar wadda ya haɗa iri da larabawa, sai dai shan Giyar da yake yi da taba dasu wiwi, duk sun dafar da wannan farar matar tashi, bakinsa da yake ja akan lips ɗinsa yanzu ya koma baƙi, duk ya rame taba ta fara tsutsesa, dan har wani tari yake marar daɗi wadda duk alamun shaye-shaye sun gama tsutse masa ruwan jiki.
"Hmm hakane kam ba laifi danma ka rage kyan nan naka ba kamar da ba".
"Ai kin san yau da gobe ke kawo haka".
Harta buɗe baki zatai magana suka ga shigowar Sadiya tafiya take da mugun sauri tana nufar ɗakin da wata ta kwatanta mata shigowar tata, bata ma lura da su Sagir ɗin ba dake zaune can ƙarshen gidan ba suna zuƙe-zuƙensu.
"Wancan kuma miya kawo ta?".
Faɗin Luba tana nuna Sadiya tana shiga ɗakin Sagir ɗin.
"Ohho mata ƙila wajan ƴar uwarta ta zo ko?".
"Amma dai ka bata taimako ko?, dan jiya har ihunta naji tana raki?".
"Mtsww ni nama manta da al'amarinta ai, tunda na fito nama manta dana aje wata aba wai Mata".
"Hhhhh baka da mutumci fa Sagir, yanzu haka kabar ƴar mutane a yashe kayi mata jina-jina".
Faɗin Jafaru daya miƙe shima.
A wajan Sadiya tana shiga ɗakin taja wani uban birki hankalinta a mugun-mugun tashe take bin ɗakin da kallo tana hango Nuratu dake kwance ƙasa idonta lumshe ya ƙunbura ɗayan idon kamar wadda aka kaima mugun duka a yadda ya haye yayi suntun dashi.
"Na shiga uku na Aunty Nuratu mi zan gani haka?".
Sadiya ta faɗa tana saurin ƙarasawa inda Nuratun take kwance.
Jin motsin mutum haɗe da jin saukar muryar Sadiya yasa Nuratu ƙoƙarin yinƙura tana son tashi zaune, sai dai nauyi da jikinta yayi mata haɗe da tsami yasa ta komawa ta kwanta ba shiri, tana jin hawaye masu zafi nabi mata gefen fuska.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Aunty Nuratu miye wannan ɗan iskan yayi miki ne haka?".
Sadiya ta ƙare maganar jikinta na rawa na tsabar kiɗima da razani.
Kallon jikin Nuratu ta farayi zuciyarta na bugawa da masifar ƙarfi, ba dai abunda take tunani bane ya faru da ita, ba dai abunda tayi mafarki bane ya faru da Nuratun ba?.
Idonta ne ya faɗa akan ƙafar Nuratu da jini ke bi, ga zanin kadon data jawo da kyar ta rufe jikinta dashi shima kansa ya lalace duk jini ya ɓata shi.
Sadiya bata san lokacin data rushe da wani irin kuka mai sauti ba, rungume Nuratu tayi tana ƙara sakin kuka mai cin rai zuciyarta na bugawa sosai fiye da misali.
"Ya akai kika bari hakan ta faru iye Aunty Nuratu mi yasa dan Allah?".
Ta ƙare maganar muryarta na rawa da shashshakar kuka.
Nuratu maganarma ta ƙasa yinta sai lamo data yi a jikin Sadiyar.
Da sauri Sadiya ta miƙe kamar wacce aka tsikara, tana niyar ficewa waje, taji Nuratu ta riƙe mata Hijab ɗinta.
Tsayawa tayi tana waigowa hawaye na daɗa zubo mata shaaaaa.
Girgiza mata kai ya shiga yi tana faɗin.
"Yanzu zan dawo Aunty Nuratu ki bani minti kaɗan da yardar Ubangiji yau kin gama kwana a gidan nan, yau ne kwananki na farko kuma na ƙarshe a yau kuma sai ya sake ki, sai dai duk abunda zai faru ya farun, duk maganar da jama'a zasuyi akan an kawo ki washe garin ɗaurin aurenki an sake ki, sai dai aita faɗar hakan".
Sake riƙe mata Hijab tayi da sauri tana girgiza mata kai hawaye masu zafi na zubo mata.
Runtse idonta Sadiya tayi da ƙarfi, dan duk ta fahimci Nuratun bata son ta aikata wani abun da Inna zatai fushi dasu, amma bata jin zata tsaya ta saurareta a yau ɗin, sai fa tayi abunda zuciyarta take kissima mata, danta rantse da tsarkin mulkin Allah yau sai ta raba ƙaddarar auran da aka ɗaura shi jiya yau ya mutu.
Saka hannunta tayi tana janye hannun Nuratu dake riƙe da Hijab dinta a hankali ta ja baya tana kallon Nuratu data zuba mata ido daga kwancen da take.
"Kiyi hakuri Aunty Nuratu amma tabbas sai yau nayi sanadiyyar mutuwar auran nan naki, wadda babu abunda ke cikinsa sai wahala da dana sani, kiyi hakuri kawai da abunda zan je na aikata".
Tana faɗar haka tayi saurin juyawa ta fice daga ɗakin, tabar Nuratu na ƙoƙarin kiran sunanta amma muryar bata fita sosai sai hawayen dake mata ambaliya kamar an buɗe fanfo.
Sadiya na fita bata ja birki a ko ina ba sai a gaban su Sagir dake tsaye har lokacin, yanzu yana zaune sai zuƙar taba suke suna fesar da hayaƙin tabar.
"Wajanka na zo annamimi marar imani kawai".
Da wani irin sauri Sagir ya miƙe yana nuna Sadiya da yatsa yana cewa.
"Keee ƴar marassa mutumci, ni zaki kalla kina faɗa wannan maganar banzar?".
"Ɗan marassa mutumci gaka nan, akwai ma wadda ya kaika rashin mutumci ne iye Sagir?. Zuwa nayi ka sakar min ƴar uwata ka bata takardar ta yanzu nan ina a tsaye a wajan nan".
"Ke kika aura min ita da zaki sa na sake ta?, akwai sisinki a ciki sadda na bada sadakinta?".
"Kai dalla can rufe ma mutane baki, wallahi Allah Sagir sai ka sake ta, idan kaga nabar wajan nan to ka furta kalmar saki ga Aunty Nuratu. Baccin kai dabba ne zaka afkama Matarka a bigenka, sana ka tafi ka barta a cikin jini cikin jinyar kanta, ko ka ma taimaka mata, tunda kaine ka sakata a cikin halin da take ciki, da yake kai marar imani ne a lokacin da ake raba imaninma wata ƙila bacci kake ko baka zo duniya ba ida......
Tassss ƙarar marin da zafin marin suka haɗe ma Sadiya a mugun-mugun ruɗe ta runtse idonta tana dafe kumatunta inda taji zafin marin da saukarsa. Zuciyarta na bugawa da masifar ƙarfi ta shiga buɗe idonta tar ta ajesu a cikin na Sagir daya ɗauketa da marin.
Sadiya bata san lokacin data ɗaga hannunta taci kwalar rigar Sagir ba, idonta ja jawur bakinta na kunfar bala'i har jikinta na jijjaga take faɗin.
"Idan na yarda Allah ya tsinan Sagir, kai na rantse da tsarkin mulkin Allah sai ka saki ƴar uwata, a haka zata zauna da kai baka ganin darajar kowa nata?, wallahi Allah saika furta mata kalmar saki".
"Innalillahi ke baiwar ki sake shi mana".
Wani irin kallo Sadiya ta jefama Luba tana mata wani irin gargaɗi da ido kamin ta ce.
"Ke asuwa?, harda su Kaza a cin danƙo dama?, karna sake jin kin sako mana baki, babu ruwanki a ciki, idan ba shawara zaki basa ya sakar min ƴar uwa ba to kiyi shuru da bakinki, ke har akwai wani salati da zaki faɗa a bakin nan naki kina Karuwa dake?. Baccin cin mutumci da zubar da daraja ka rasa inda zaka kawo ƴar uwata sai wannan gidan mai kama da gidan Bariki?".
Ta ƙare maganar tana dawo da dubanta wajan Sagir da yayi wiƙi-wiƙi da ido yana kallonta.
Jafar dake gefe ya riƙe baki yana mamakin ƙarfin halin Sadiya, dama fa sun san an daɗe ana faɗin Sadiya duk gidansu tafi kowa zafi, dan ko a gidan nasu bata barin ta kwana, dan haka da sauri ya matsa kusa da Sagir daya sha Shaƙa a wajan Sadiya data riƙe masa gaban riga ta shaƙe masa wuya ya ce.
"Kaga abokina ka saki wannan yarinyar kawai, domin naga fa wannan ƴar uwar tata itama fa idonta a tsaye yake, babu abunda bazata iya aikata maka ba a bainar nasi, kaga fa har mutane sun fara fitowa ɗaya bayan ɗaya suna ganin yadda taci maka kwala ai mutumcinka sai ya zube".
Wani kalar tsaki ya buga yana dawo da dubansa ga Sadiya dake wata jijjaga ta zallar rashin mutumci.
"Dalla can ni sake ni, kuje na saki ƴar uwar taki saki biyu, sai mi idan na rabu da ita?, dama ai ƙaƙabamin ita akai badan ina so ba, dan haka na sake ta sai ki rabu dani ko?".
Sakinsa tayi tana sauke wata irin ajiyar zuciya ta banka masa wata uwar harara ta ce.
"Tafi nono fari, kuma ai daka idasa sakin guda ɗayan daya rage ai da sai yafi nake ganin ko?".
"Wai ke kam wacce irin ƴar neman magana ce ne wai?, shin baya saki ƴar uwar taki bane?, ba sai ki kyalesa yasha iska ba".
"Bana ce karki sake sako min wannan bakin naki bane dalla can Malama?, zanyi miki rashin mutumci fa. Kuma kai Sagir saika cike ɗayan daya rage a tsakaninku danma kar Inna ta nemi cewa wai Nuratu ta dawo maka a matsayin Mata, danna rantse kaida auran Nuratu har abada".
"Kai kuma marar zuciya ka idasa mata ɗayan mana, da ni ne kai da tuni nayi mata Ukun lokaci ɗaya".
Faɗin Luba tana bankama Sagir harara.
Bakinsa na rawa ya idasa sakin ɗayan daya rage a tsakaninsu.
Wata shewa Sadiya ta saki tana juyowa ta bar wajan haɗe da cewa.
"Tafi nono fari wallahi Alhmdllhi mun rabo da alaƙaƙai haba wannan aure ko jaraba".
Da kallo suka bita kawai suna jadadda rashin tsoro irin na Sadiya da ƙarfin halinta da rashin barin saita kwana, dan daka kalleta dama zata aikata..........
Chapter 35
A hankali ta kamo ta suka fito daga abun hawan da suka sauka a ƙofar gidansu.
Idonta ta ɗaga tana kallon ƙofar gidan nasu wadda duka jiya ne ta barshi a matsayin ta barshi ne zata je gidan aure, sai gashi yau ta sake dawowa a matsayin ƙaramar bazawara, saboda duk abunda Sadiyar tayi taji da kunnanta, komai kamar akan idonta ne ya faru, koda Sadiya ta shigo bata iya ce mata komai ba, saboda bata da abun cewar, a haka tana ji tana gani ta kamata da kyar suka fice daga gidan, tun a can ake binsu da kallo haɗe da haɗa kai ana ƙananun maganganu.
Jiki a sanyaye Sadiya ta sallami mai abun hawan da suka hau tana sake riƙe Nuratu sosai da kwata-kwata bata iya tsayawa da ƙafafunta saboda irin azabar data sha a hannun Sagir jiya.
Hawaye ne Sadiya taga Nuratu nayi, a hankali ta shiga girgiza mata kai tana sake damƙe hannunta tana bata kwarin gwaiwa a cikin idonta tana mata magana da ido.
Lumshe idonta tayi ta buɗe su akan Sadiya data fara tafiya da ita tana nufar cikin gidan nasu da ita.
Tana sake jin wani sabon tashin hankali na tunkaro ta taku ɗaya idan tayi saita sake jin wata muguwar faduwar gaba na sake riskarta.
Tsaye Inna take tunda Sadiya ta fita take zarya a tsakar gidan tana damƙe hannunta tana kaima iska naushi, cije baki take tana mamakin daɗewar da Sadiya taje tayi.
Sallamar da Sadiya tayi ce tasa Inna saurin juyowa tana duban ƙofar shigowa gidan.
Wani irin zare ido waje Inna tayi tana hangame baki buɗe tama kasa magana saboda mamaki daya kusa kashe ta.
Tunda suka shigo gidan Nuratu tayi ƙasa da kanta bata yarda ta kalli koda saitin inda Inna take tsaye ba.
A hankali Sadiya ta shiga zaunar da Nuratu akan tabarmar dake shinfiɗe a tsakar gidan nasu.
Sai da Nuratu ta yatsene fuska tana sakin ƙarar azaba jin yadda ta zauna da kyar jin jikin nata take kamar wacce akasa wuƙa aka yanka mata ƙasanta.
"Innalillahi mi zan gani haka ni ko?".
Inna ta faɗa tana ƙara shiga cikin mamaki haɗe da zallar mamakin miya kawo Nuratu wacce aka kai jiya-jiya?.
"Ina magana Sadiya kinyi banza dani?, ubanmi yasa Nuratu ta dawo gidan nan baccin jiya ne aka miƙata ɗakin Mijinta?, ba dai kaso mata ɗan auren da aka samu da kyar akayi mata ba kikai?".
Inna ta faɗa tana sake matsowa sosai inda Sadiya take tsaye kanta a ƙasa.
Ɗagowa tayi tana kallon Inna kamin ta haɗe wannan irin miyau mai zafi ta ce.
"Inna bama zaki fara tabbayar irin halin da kika ga mun shigo tare da Nuratun ba?, ki duba fa ki gani yadda ya haike mata a cikin Maye yayi mata mummunan taɓo a jikinta, gashi nan ko tafiya da kanta ta kasa, ki duba fa ki gani yadda duk ya kunbura mata fuska da duka da jikinta".
Da wata irin hargowa haɗe da muguwar tsawar da Sadiya bata taɓa ɗauka Innar zata mata ita ba ta fara faɗin.
"Zaki gaya min abunda na tabbaye ki ne ko kuwa zaki cika ni da surutu marassa tushe?, dan ubanki mu ba a haka muka saba ma'amalar auran ba iyee?, ai kowacce Mace da haka ta fara a haka ake sabawa ko?, dan haka bani amsar da nake so naji kawai".
Turo baki Sadiya tayi babu ɗar a cikin ranta tana kallon yadda Nuratu ke cikin halin ruɗu da zallar tsoron abunda zai iya biyowa baya akan idan aka sanar da ita auran da take tinƙuho anyisa da kyar ya mutu.
"Inna ya sake ta ne saki uku ma kuwa".
Gani sukai Inna taja da baya da wani irin sauri ta tafi zata kifa ƙasa ta faɗi tsabar yadda kalaman da Sadiyar ta faɗa suka razana ta ainun.
Da wani irin mahaukacin sauri Sadiya tayi kukan kura ta tarbo Inna a jikinta zuciyarta na bugawa.
Da wani irin mahaukacin haushi haɗe da fushi Inna ta ture Sadiya batai wata-wata ba Inna ta ɗaga hannunta bayan ta ture ta da ƙarfi a jikinta ta shiga ɗauketa da mari ta dama ta haggu kota ina marin take kai mata.
Ƙarshe Innar ta shaƙe wuyan Hijab ɗin Sadiya tana sakin wani irin kukan daya hautsina ƴan hanjin cikin Sadiya da Nuratu.
Da wani irin bala'in sauri suka shiga zare ido waje suna runtse idonsu da ƙarfi, Nuratu bata san lokacin data fashe da kukan ba itama muryarta kwata-kwata bata fita, ita ko Sadiya idonta ne ya kaɗa yayi jawur.
Ƙirjin Inna na bugawa kamar wacce tayi gudun tsere ta shiga kallon Sadiya ta fara magana cike da zallar ɓacin ran da basu taɓa gani a tare ita ba.
"Sadiya so kike ki kashe ni da raina, kinje kin kaso auran nata kinji daɗi ko?, saboda kin raina ni?, babu damuwa kin nuna min yau bani ce na haife