Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
bai san ubanki Malamin zaure bane, kinga kuwa Malamin zaure babu maraba dashi da Boka, dan haka ki fita ido na rufe Asabe".
"Naƙi na fita daga idon naki Jaririya, ke fa ni bafa kunyar ki zanji ba, tunda dai yarinyar nan tawa yanzu ba sonshi take ba, to ko miye dai-dai nake dake, ga dai lusara nan mai son tusa Ɗiyarta ga Ɗanki ita ce zaki zo ki taka a gidan nan ta kasa ce miki komai amma banda Asabe na rantse".
Wani irin kalar bakin ciki ne ya taru yayima Ladidi yawa, shikenan ta gama rushe komai wallahi Asabe tattacciya ce ta fagen iya munafurci da baƙin ciki.
"Ku duka ban cire ɗaya ba, na dai gaya maku aje maza ma ko miye akai ma Yaro na a warware shi, idan ba haka ba na sake jaddadawa wallahi ga Office ɗin ƴan Sadda zanje idan yaso azo ama kama kowaccen ku babu abunda ya sha mini kai".
Ƴan hanjin Inna Ladidi ne suka hautsina, dan harga Allah ta tsani duk wani lamari da za'a saka ƴan Sadda a ciki ko a saka Hukuma, bata ƙaunarsa, dan haka ta haɗe wani miyau tana duban Jaririya dake tsaye riƙe da Hijab ɗinta a hannu tana niyar ɗaurata a ƙugunta wai da sunan a shirye take idan ma dambacewar za'ai.
"Kinga Jaririya miya kawo maganar hukuma kuma a nan ciki fisbilillahi?, kiyi dai hakuri komai zai wuce ai indai Yaronki ne an hakura dashi koba shikenan ba?".
"Hehehee ahayeee nanayeee, tafi nono fari, gara da kika ce hakan, dan wallahi Allah haɗa iri dai da irin gidan nan gara zuwa gidan Karuwai kawai kaje ka samo Karuwa ka aura shine yafi, ko banza ka cirota daga aikata alfasha ka samu ladar hakan".
"Ke dalla can Jaririya kike kowa ce?, nan fa ɗaya, bafa zai yiwu kazo har gidan nan ki ce kuma zaki rinƙa jifarmu da irin wa'innan maganganun banzar naki ba, bafa zai taɓa saɓuwa ba yawwa, tun wuri tun muna shaidar juna Jaririya kizo ki kama kanki kibar cikin gidan nan".
Inna Ladidi ta ƙare maganar tana nuna ma Jaririya hanyar fita, dan itama yanzu ta fara kaiwa wuya, cin mutuncin ya fara yin yawa kuma.
Wata dariya Asabe ke cinta kamar zata saki saita maze tana harɗe hannunta a ƙirji, ko yanzu Kasuwa ta tashi ɗan koli yaci riba, inji masu iya magana.
Ta wutsiyar ido kawai Inna Ladidi ke hango Asabe tabbas kota rantse duk ita ce musabbabin zuwan Jaririya gidan nan, bari Jaririyar tabar gidan idan yaso su dambace ita da ita, danta rantse bazata ci banza ba, ta rushe auran cikin ruwan sanyi kuma ta ƙyaleta haka nan wallahi bazai yiwu ba.
"Mtssww aikin ɓirrr inji tusa, daga baya kenan wai anyi sadaka da Karuwa, ni dai tunda an ƙyale min Yaro na can maku".
Jaririya ta faɗa tana saka Hijab ɗinta tayi gaba.
Sauke lumfashi kaɗan Inna Ladidi tayi, danta ga fa itama Jaririyar ba daga baya ba wajan iya wulaƙanci da faɗa dai-dai take da kowa.
"Na dawo wajanki ke kuma annamimiya baƙar munafuka mai baƙar zuciya kawai".
Inna Ladidi ta ƙare faɗar haka tana matsowa kusa da Inna Asabe tana riƙe ƙugunta tana jefama Inna Asabe wani mugun kallo.
Gyara tsayuwarta Inna Asabe tayi tana ma Inna Ladidi wani irin duba kamin ta ce.
"Ina jinki dami kika zo?, koma miye dai-dai nake dake wallahi".
"Zuwa nayi ki gaya min miye abunda kika je kikayi har waccar Matar matsiyaciya ta zo gidan nan tana min cin fuska?".
"Tana mana cin fuska dai, ko kin manta haɗa mu tayi gaba ɗaya ta zage iyee?".
"Ohho miki koma miye na kona rantse bazanyi kaffara ba ke ce silar zuwan Jaririya a cikin gidan nan Asabe, nafa san wace ke, nasan abunda zaki iya aikatawa fiye ma da wannan".
"To sai akai yaya Ladidi?, ko akwai abunda zaki iya yi ne akai idan ma ni ce nayi hakan?".
Zatai magana lokaci ɗaya su Binta da Amina suka shigo gidan suna faman zage-zage a tsakaninsu kamar wa'inda zasu dambace suma.
Juyawa Ladidi tayi tana cewa.
"Kai dalla can miye haka ku kuma?".
Da gudu Amina ta je inda take tana fashewa da kuka ta ce.
"Wai Inna kinji yadda Binta ke ce min wai ko zata mutu saita rusa aure na da Sule kuma a yau zan gani".
"To ai sun riga da sun rushe shi Amina, dan yanzu nan uwar Sule ta fita daga gidan nan, ta zo tana zaginmu wai duk abunda akaima Yaronta aje a warwaresa idan ba haka ba Hukuma ce zata rabamu da ita, shi yasa kawai na ce mata taje ba dai Yaronta bane an hakura dashi".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, Inna kika faɗa mata hakan kuma?, na shiga uku shikenan burinki ya cika Binta".
Ta ƙare maganar tana jin wata irin juuuwa na ɗibarta tayi ƙasa zata faɗi da mugun sauri Inna Ladidi ta taro ta tana sakin wani salati da ƙarfi tana cewa.
"Na shige su ni Ladidi mi zan gani haka?, ke Amina akan wani can zaki sume min haka kawai?, ba dai muna lumfashi ba kima kwantar da hankalinki dole ne ki auri miji irin na kece sa'a, ƴan baƙin ciki sai dai su mutu wallahi".
"Mtswww to ba sai ayi ba mu gani".
Binta ta faɗa ciki-ciki.
"Mi kike cewa ne marar kunya dangin rashin kunya?, nafi ƙarfin nayi dake wallahi da uwar data kawo ki duniya ita ce dai-dai ni kin gane?, dan haka yanzu yanzun nan zan iya barin ki kwance Binta bana son raini".
Inna Ladidi ta faɗa tana nuna Binta da yatsa jikinta har wani kyarmar masifa yake.
Da kyar Amina ta miƙe tana ganin jiri kaɗan tana duban Binta ji take kamar ta kamo ta tayi mata ɗan banzan dukan da zata kasa tashi.
"A'a ban gane ba Ladidi?, ki barta fa kwance kike faɗe?".
"Kware kuwa ko gani kike bazan iya bane?".
"Ai wallahi Allah uban kuturu yayi kaɗan ma bare na makaho, da taki Ɗiyar ma jikinta sai ya gaya mata, domin ni ba lusara bace na tsaya kina dukan Ƴata ban ɗauki mataki ba, ashe ma kenan bansan ciwon haihuwar ba ko?".
"Can miki Asabe amma ki gaya ma Ɗiyarki idan tana cin ƙasa ta kiyayi ta Suri, dan na rantse bazai yiwu ƴar ciki na ta tsaya tana gayan magana ba banci Ubanta ba".
"Ke kuma muje ciki".
Faɗin Inna Asabe tana kamo hannun Binta suka shige ɗaki.
Suna shiga suka saki wata shewa a tare wacce sarai su Inna Ladidi sunji ta.
"Inna kinji shewar da suke saki?, suna murnar abunda ya faru damu".
"Hmmm lallai Asabe ta cika shaiɗaniya, amma da ni take wasan, wallahi Allah sai nasa Binta tayi baƙin jinin Samari, saina saka duk ma wadda yazo neman auranta sai abun yayi nisa zasu rinƙa neman mutum su rasa, yau-yau ɗin nan zan tafi cikin gari nasan abunda zanyi ne".
"Wallahi Inna shi yasa nake gaya miki komi yana iya faruwa, yanzu gashi komai ya ruguje na rasa Sule, wayyo Allah na Sule".
Amina ta faɗa tana ƙara sakin kuka mai sauti.
Inna Ladidi ta kalleta danta fara bata haushi kuma ta ce.
"Shin wai Sulen nan ubanki ne?, ko kuwa dashi aka haife ki?, ko kuwa Sulen nan ni ne da zaki wani zauna kina ta rusa uban kuka harda su shirin suma a gaban maƙiyanmu, ba ma shi yasa suka shige suna mana dariya ba, ace kamar ke zaki kasa daurewa?, ita tata Ɗiyar data jure fa, bana son rashin jarumta fa".
Da sauri Amina ta shiga share hawayenta, dan ita harga Allah yanzu ta fara son Sule ne da gaske, ga kuma yadda ta fara hango kanta a cikin gidansa tana cin daɗi har tana kawo ma Innar suna ci a tare suna ma su Binta dariya, sai gashi komai ya rushe tunanin nan tana ya zama gaibu, ba dole tayi kuka ba an rushe mata mafarkinta.
"Inna kiyi hakuri na daina".
"Da dai yafi, ai kina jin abunda na ce zanyi ko?, zan ɗauki mataki mai tsauri akansu, to banga dalilin da zaki wani rinƙa tada hankali ba".
"Shikenan Inna hakan ma da zakiyi mata yayi, ko miye ma ayi mata wallahi ai su suka saya da kuɗinsu".
"Yawwa ko ke fa, je ki ɗakko min Hijab ɗina yanzu nan da wasu kuɗi dana aje akan gado, zan biya ta wajan Ƴar burin can wacce tayi ma Sule abunda ya zo gare ki, zanje a warwaresa da kar ma matar can uwarsa ta sake mana sallama a cikin gida, daga nan kuma zan wuce gidan Lantana ta rakani can wajan na kan Tudu ance shima ya iya aiki".
"Kai Inna wajan na kan Tudu kuma?, Inna naji fa ana cewa wai sai yayi amfani da kai shifa yake baka maganinsa".
"Sai akai yaya to idan yana hakan?, ke da nake son kwato ma ƴanci kike gaya min haka?".
"Amma Inna shi yasa fa mutane basa zuwa wajansa saboda haka, amma tabbas idan yayi aiki da wuya kaga ya warware cikin sauƙi".
"Au ashe kin san da haka kike tsaya min wasu maganganun banza?, ita Asaben Allah kaɗai yasan miye take badawa har take iya fitar da kowacce Mace data shigo gidan nan, Mace nawa ta fitar da tsiya?, dan haka babu abunda Asabe ba zata iya sallama shi ba indai akan cikar burinta ne, dan haka nima ki kyale ni kawai saina nuna mata ba ita kaɗai bace wacce ta iya shaiɗancin ba ai.............
Chapter 16
*House No: 34, Tudun Wada Estate Funtua Local Government Katsina State Nigeria*
A hankali ta juya tana kallon ƙofar bedroom ɗinta da Humaira ta shige tun ɗazu tana kumbure-kumbure, ta shiga kiran sunanta.
"Humaira!! Humaira!!".
"Na'am Inna".
Ta faɗa tana fitowa gaba ɗaya.
Inna ta kalle ta ta ce.
"Humaira baki zuwa ki gaida Yayan naki?, ba tun ɗazu naji ya shigo bane?".
Turo baki tayi kaɗan ta ce.
"To ni Inna gaskiya kin san bana son rainin wayo, kuma naga shima kamar irinsu ne fa".
"Kinga bana son jin komai wuce kije ki gaida shi kinji na gaya miki ma".
Kamar zatai magana sai kuma kawai ta fice tana ƙara haɗe fuska dan ita kam an taƙura ta.
Kai tsaye part nashi dake kusa dana Abba ta nufa tana iya jiyo tashin maganganun su Maami da Ma'u da suka cika shi da surutu, amma shi kam zata iya rantsewa baka jin ko tarinshi.
Taɓe baki tayi tana shiga gaba ɗaya Parlon nashi.
Tunda tayi sallama kusan gaba ɗaya har Maami ne suka ɗago suna kallonta, kallo irin na rainin wayo haɗe da wani irin kallon banza.
Shi ko baima juyo ba yana zaune ne can daga kan kujera sai table na tsakiyar parlon da aka matso mashi dashi an aje kayan abincin data girka mashi yana cin abincin kaɗan-kaɗan duk da yayi masa daɗi sosai, amma dama haka ɗabi'arsa take, komai cikin tsantsar natsuwa yake yinsa.
Tunda Humaira ta shigo idonta ke kansa tana kallonsa cike da mamakin irin kyawunsa kamar ba wadda ya fito ciki ɗaya dasu Ma'u ba, duk da idan ka kallesa lokaci ɗaya zaka shaida kamarsu da Maryam amma Ma'u ba wani sosai suke kama ba sai dai ta jini kawai wacce daka gani zaka san jini ɗaya ne ya haife su.
"Ke kuma lafiya?".
Maami ta faɗa a ɗan tsawace.
Humaira ji tayi kamar ƙasa ta tsage ta shige kota huta da wannan cin fuska.
Sai lokacin Harun ya ɗago da kansa bai sauke idonsa a ko ina ba sai akan Humaira da hankalinta ke akan Maami tana bata amsar.
"Maami Inna ce ta ce na zo na gaida Y Harun".
"To ai gashi sai ki gaisar dashi ɗin ki gama gabanki kuma ai ko?".
Tunda ta fara magana gaba ɗaya Harun yake bin ɗan ƙaramin bakinta da kallo, baby face ɗinta gaba ɗaya ta gama tafiya dashi, amma da yake mugun miskilin ne baka taɓa gane ma kallonta yake.
Muryarta yaji a hankali tana cewa.
"Y Harun barka da dare, fatan ka dawo lafiya?".
Shuru kusan minti biyar harta fidda ran zai ma amsa, dan har ta fara fusata dashi, sai kuma taji muryarsa mai kaushi da zurfi wacce tasa bata san lokacin data ɗago gaba ɗaya ba tana kallonsa shi kam bama ita yake kallo ba lokacin ya ce.
"Lafiya".
Abunda taji ya iya faɗa kenan.
Dan haka jiki a mace ta tashi tana ficewa daga parlon tana murguɗa masa baki, a zuci take mitar cewa.
"Mtsww aikin banza shi wannan ai yama fisu iya wulaƙanci ai, tabɗi jam ko shi yasa Bilkisu take gaya min yanayin yadda yake naƙi saurararta?, ashe da gaske take?, duk ya fisu kyau tabbas da cikar zati ga wata izza da nake gani a tattare dashi hmmm".
Ta ƙare maganar zucin tana taɓe baki ta ɗan juya tana kallon ƙofar parlon ta sake taɓe baki haɗe da hararar ƙofar parlon sai kuma ta juya da sauri tayi Part ɗin Inna.
"Wace wannan ɗin Maami?".
Faɗin Harun yana ɗan kurɓar ruwan da aka aje masa yana sake kallon Maami da manyan idonsa masu mutuƙar gaske kamar madara daga cikinsu.
"Hmm Y Harun wai fa Agola ce Ɗiyar Aunty ce man, kusan su nawa ne ma Mata suke zuwa gidan nan wai da sunan duk ƴaƴanta ne, danma Abba ya ɗan dakatar da zuwan nasu sai wannan marar kunyar da kake gani ita ce zata zauna a gidan nan dindindin".
"Mtsww kin cika surutu da yawa Ma'u".
Ya faɗa yana ɗan yamutse baki kaɗan dan har kansa ya ɗan fara sara masa, dan harga Allah baya son mutum mai magana sosai yanzu nan sai kansa ya fara masa ciwo, abunda yasa kenan ma baya son zuwa Nigeria amma yanzu tunda ya dawo gaba ɗaya yasan dole ne ma yazo Abba ya fara binsa Campany ninsa dake can cikin garin Katsina bazai iya zaman gidan nan ba, dubi daga ita har Maami tunda ya dawo sunƙi barinsa yama huta sun cika sa da surutu wannan ta ce kaza wannan ta ce kaza.
"Kai Y Harun dan Allah......".
Ta faɗa tana kallonsa sai kuma tayi shuru ganin yadda ya ɗago yana zuba mata idanuwansa, dole tasa tayi shurun tana yin ƙasa da kanta tana turo baki.
"Ke wai baki girma ne?".
Shuru tayi sai Maami data amshe da cewa.
"Kaifa Harun mai zama da kai sai ta shirya wallahi Matarka dai kam ta bani da wannan miskilincin naka, yo anyo mutum ace bazai magana ba, kuma bazai bari na kusa dashi shi yayi ba, haka ake yi rayuwa iyee?".
"Maami please zan ɗan huta a bedroom".
Ya faɗi hakan yana miƙewa gaba ɗaya ya nufi hanyar da zata sadashi da bedroom nashi.
Bin bayansa sukai da kallo Ma'u na sauke lumfashi ta ce.
"Wayyo Allah Maami wai dama Y Harun aljanu ne dashi a cikin idonsa ne shin?".
"Ban gane ba kanki ɗaya kuwa Ma'u?".
"A'ato Maami tsakani da Allah fa, idan har ya zuba maka idon nan nasa Allah tsabar ruɗewar da nayi ni dai kusan sakin fitsari nayi a zaunan nan fa, haba ace ayo mutum da ido kamar bana mutum ba, idan yana kallonka dasu kamar an jona maka wutar lantarki".
Dariya kaɗan Maami ta saki ta ce.
"Nima ina ganin hakan tattare dashi amma baiwa ce kawai Allah ya basa ita, ƙila ma bai san yana da ita ba".
"Hmm hakane Maami, mu tafi kar ya dawo yana mana mazurai ya ce mun dame shi da surutu a parlo".
Tashi saukai gaba ɗaya suka fice.
"A'a harkin dawo?".
"Eh Inna na dawo".
"Kun gaisa ko?".
Zama Humaira tayi tana faɗin.
"Eh Inna mun gaisa, shima sai baƙin hali irin nasu, yo Inna ashe ma ya fisu iya wulaƙanci".
"Ohhh ni Humaira, kinga Humaira bana son irin haka da kike yi ko?, ina ruwanki dashi ne shin wai?, ba dai gaisawa kukai bane?".
Turo baki tayi tana kallon Inna ta ce.
"Eh man Inna, amma sai dafa ya wani sha ƙamshi ya amsa min gaisuwar, daga gani miskili ne ma na bugawa a jarida, wallahi Matarsa ta bani wancan mutunan".
"To faɗi ba'a tabbaye ki ba, ina ruwanki da matar da zai aura iye?, dama indai Harun ne kaɗan kika gani haka yake shi baya son yawan magana haka idan yana waje baya so ana masa surutu, haka ɗabi'arsa take".
"Uhmmm lallai ma wannan mutunan haka kawai sai mutum kar yayi maganarsa?, shida ba shi ya halitta masa bakin maganar ba".
Humaira ta faɗa a zuci a fili kuma ta ce.
"Tabɗi jam shi kuma haka yake hmm?".
"Haka yake fa sai ki kama kanki dashi ai ko?, idan kuma ya kamaki ya hukunta ki zaki gane shayi ruwa ne".
"To ni Inna ina ruwana dashi dan Allah?".
"A'a wai dai gaya miki nayi kawai sai ki shiga hankalinki yanzun, domin ma ya dawo gida kenan daga wannan tafiyar".
Humaira zatai magana suka jiyo kukan Ummi dake bedroom ɗin Inna ta tashi daga baccin da yanzu Inna bata daɗe da kwantar da ita ba.
"Kinga ɗakko min Ummi ta tashi yanzu zata fara min rigimar tata".
"Ba yanzu da zan fita ne aka kwantar da ita ba?".
"Ai kin san baccin nata dama haka yake rabi da rabi ne, gashi nan ta tashi dai kin gani".
Ta faɗa Humaira na shigewa bedroom ta ɗakko Ummi ta fito tana mata wasa ta ɗan cillata masa yarinyar ta fara walgale baki tana dariya, domin sunyi bala'in sabo da Humairar danta fi sanin Humairar ma akan su Bilkisu da ba ganinsu take ba.
Ajeta tayi a cinyar Inna Ummi har lokacin tana kallon Humaira tana murmurshi irin na Yara.
"Kinga marar kunyar dariya ma take yi".
Murmurshi Humaira ta saki ta ce.
"Wasan da ake mata ne yasa ai".
Inna ta gyara mata zama tana fiddo nono ta bata ta shiga sha tana kallonta kaɗan sai kuma ta dawo da dubanta akan Humaira ta ce.
"Ni ko ya wajan Sakina yau kusan kwanaki biyu tun lokacin data tafi gidan nan?".
Fuskar Humaira ce ta ɗan canza zuwa