Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
kanta yayi yana saka idonsa cikin nata, yasan abunda ke sake kashe mata jiki haɗe da hukuntata da kaifin idanunsa, ya sani idonsa suna da wani irin tasiri a jikin mutum koda kallo kawai zai iya hukuntata, kuma abunda take masifar tsoro kenan, jikinta mutuwa yake murus, tana mugun tsoron irin wannan hukuncin da hukuntata da kaifin idonsa.
Wani irin kallo yake ma tsakiyar idonta sosai, idonta da nashi suka sarke waje ɗaya, jikin Intee na ɗaukar rawa jikinta yayi mugun sanyi gaba ɗaya lakkar dake aiki a jikinta ce ta mutu, hawaye ne suka sake ɓulɓuluwa daga cikin idonta, fara girgiza masa kai ta farayi so take ya ɗauke idonsa daga cikin nata amma ina, tana so ta janye nata amma yaƙi bada damar hakan, kamar wani maganaɗiso ne yake saka mata ya hanata koda motsa kwayar idon nata da sunan ɗaukewa da kallon tasa kwayar idon.
Sai da ta kai da sakar masa wani irin kuka jikinta ya gama mutuwa sosai dan da kyar take shashshakar kukan ma.
A hankali ya sake ta, yana sakinta da mugun sauri ta miƙe amma jikinta yadda ya mutu da kyar ta iya dai-daita natsuwarta ta tsaya tana dafe kanta da ƙirjinta dake lugudan daka, baice mata komai ba ya ɗauki computer sa ya shige bedroom nasa, yana wata irin tafiya tasa mai cike da zallar natsuwa haɗe da isa da kuma izzar dake yawo a cikin jininsa.
Yasan ya gama hukuntata gobe ma bazata sake ba, sai idan tsautsayi ya sake kamata tayi masa tsaki.
Bin bayansa tayi da mugun kallo tana haɗe miyau haɗe da jan majina.
Da kyar ta iya takawa taje inda kayan suke da kyar ta iya saka hannunta da har yanzu yake ɗan rawa kamar wacce Kura ta biyo zata halaka ta tana gudun ceton ranta, haka jikinta ke rawa har lokacin kamar kuma wacce yunwa tayi ma mugun kamu.
A hankali ta ɗauki kayan tana ficewa daga Part cike da jin zafinsa a ranta sosai, tana tafiya tana mita a ranta, tana ja masa Allah ya isa.
Murguɗa baki tayi a fali ta furta.
"Mugu kawai Allah ya isar min wallahi, wannan ai mugunta ce, da shegun idanunsa kamar wadda aka je akaima asiri".
Ta faɗa tana sake mamakin yadda cikin ruwan sanyi yake hukunta mutum ba bugu ba zagi da kaifin idonsa kawai ya isa yasa Mutum ya ladabtu......
*TSANIN ƘADDARA*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
Chapter 3
*House No: 34, Tudun Wada Estate, Funtua Local government Katsina State Nigeria*
"Tunda kika zo Humaira kike kuka kinki ki gaya min abunda ke faruwa".
Humaira taja lumfashi haɗe dasa hannunta na dama ta ɗauke hawayen dake mata zuba kamin ta dubi Mahaifiyarta ta ce.
"Inna, na gaji wallahi na gaji da zama a gidanku, komai mu ake ɗora ma laifi daga yin abu ƙanƙani su Kawu Ismail suka kamani sukai min duƙan kawo wuƙa, daga ƙarshe ma suka koro ni wai na bar masu gida tunda ai babu gadonmu a ciki"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"
Abunda Inna ta iya furtawa kenan tana jin wani irin tashin hankali ya rufe mata zuciya.
Sake ware idonta tayi tana kallon Bilkisu dake zaune itama kusan satinta biyu a gidan.
Ta ce "kinga Bilkisu itama kusan satinta biyu a gidan nan"
Humaira hankali a tashe ta dubi Bilkisu wacce ba Uba ɗaya suke da ita ba uwa ce suka haɗa ta ce.
"Bilkisu amma hutu kika zo ko".
Bilkisu ta tashi a hankali ta ce.
"Kware hutu nazo naga Innarmu kawai, dama kuma Baba ya ce sati biyun kawai zanyi na koma gida Dutsanma. Uhmmm Humaira haƙiƙa muna ganin jarabawa kala-kala ai ku gara ku ni Matan Babana babu irin muguntar da bana gani a gidan nan".
"Hmm Bilkisu kenan har yanzu ke yarinya ce su Humaira sun fiki ganin jarabawar rayuwa, ke gara Mahaifinki yana sonki yana kuma kula dake sana ya baki mafaka a gidansa, bai barki kina yawon neman inda zaki fake ba, ni kam dai aure-auren da nayi ne ba ɗaya ba ba biyu ba kusan wannan shine na uku kuma duk inda naje ace zai na haihuwa na aje Yaro dole dama naga irin wannan jarabawar, Yarana kuyi hakuri duk ni naja maku wannan tozarcin da kuka tsinci kanku a ciki".
Inna ta ƙare maganar tana sharce wasu guntun hawaye.
Hankali a tashe Humaira ta matsa kusa da Inna sosai ta kamo hannunta ta ce.
"Inna ko kaɗan bana jin haushinki akan duk wani abu dake faruwa damu, ai kema ba yin kanki bane ƙaddararki ce a haka, bake kika zaɓama kanki hakan ba".
Inna ta nisa hankalinta kwata-kwata ba'a kwance yake ba ta dubi Humaira ta ce.
"Ina Sakina na ne kar dai itama su koro min ita?".
Humaira ta sauke wata irin ajiyar zuciya kamin ta ce.
"A can na baro ta, ban san abunda zai iya faruwa ba kawai Inna".
Inna hankalinta a tashe ta aje Ummi yarinyar data haifa a gidan da take aure yanzu wacce bata wuce shekara ɗaya ba ta miƙa ma Humaira ita zata yi magana akai sallama a ƙofar ɗakin Inna ɗin aka wani shigo ba ko sallama.
"Maryam l......
"Kinga Aunty dama Abba ne ke son ganinki".
Wani irin kallon wulaƙanci Maryam ke aikama su Humaira, Humaira data cika da haushinta dan Allah ya sani Humaira bata daukar raini da rainin wayo ko kaɗan bata da hakurin shanye a wulakanta ta ta kyale, shi yasa ma a baya tasha wahala sosai a gidan Mahaifinsu a wajan Matar ubansu.
Maryam ta juya ta fice tana ƙananun maganganu na faɗin.
"Aikin banza kawai an wani zo an tare mana a cikin gidan Uba, Agololi sun cika mana gida za'a cinye mana abinci cikin gida a karya ma Ubanmu tattalin arziki".
Sarai Humaira taji abunda Maryam ɗin ke faɗa, wani irin abu taji ya riƙe mata maƙoshinta ta ɗauke idonta daga kallon inda Maryam ɗin tabi tana duban Inna ta ce.
"Inna dama haka Yaran gidan nan ke miki magana gatsal?".
"Hmm Humaira kenan, tunda nazo gidan nan Matarshi Sha'awa itama ke yin abunda take so a cikin gidan nan, hakuri kam tabbas saifa kinyi idan har kina tare dani a cikin gidan nan, ni yanzu bari naje naji kiran da Abban nasu ke min na dawo".
Inna na faɗin haka ta fice daga ɗakin nata.
Tunda ta tunkari parlon mai gidan take jin hayaniyar maganar Sha'awa na tashi da ƙarfi, harta shiga bata daina zazzaga masifa ba inda take faɗin.
"Bafa zai yiwu ka kawo tsohuwar Mata ba wacce ta gama haihuwa a titi ka ce zaka haɗa ni gida ɗaya da ita harda ma guzirin Agololi ta zo mana gida, bai zai yiwu Agololi su tare gidan nan ba su zo ɗaya ƴaƴana ba, haka kawai an wani kwaso Yara tili guda an jifge mana su a gida haka kawai".
Abba ya nisa yana zaune akan kujera ya dubi Inna data shigo ta samu waje ta zauna kamin ya dubi ta a tsanake ya ce.
"Nana yaushe ne Bilkisu zata koma?, ita kuma Humaira miye ya kawo ta a yanzu nake ganin ai bata daɗe da komawa ba can Katsinar daga nan ko?".
Wani irin abu Inna taji ya riƙe mata ƙirji na tsananin tausayin kanta dana ƴaƴanta ta ce.
"Bilkisu yau nake sa ran naje Dutsenma na mayar da ita. Ita kuma Humaira hutu ne ta sake zo min saboda wata hatsaniya da suka faru a gidan namu, kamin komai ya zama dai-dai zata koma itama insha Allahu".
"Da dai yafi haka kawai anzo an hana Yara na sakat".
Faɗin Sha'awa dake zaune sai wani buɗe hanci take.
Inna da kanta ke ƙasa tana mamakin rashin kirkin Sha'awa ko kaɗan akan Ƴaƴanta saita yima mutum rashin mutumcin da bai taɓa zato ko tsammani daga gare ta ba, duka Yaran nata nawa ne a gidan su Uku ne fa ɗaya baya nan Babban ɗanta Harun dake ƙasar waje aiki, sai Maryam wacce tafi kowa iya rashin kunya, sai kuma Mai bima Huran ɗin Asma'u wacce take aure a cikin garin, duk da itama wani lokacin idan tazo ko magana arziki bata haɗata da Innar Yanzu kawai Maryam ce kaɗai ke zaune a cikin gidan, amma shine take kiran wai Yaranta an hanasu Sakat.
"Zaki iya tashi ki tafi Allah ya kyauta".
Tashi kawai Inna tayi ta fice daga parlon tana jin kamar ba matarsa ba kamar ba matar gidan ba, an maida ita wata ƙasƙantatta a cikin gidan, ba kowa bace tasa ta koma hakan sai Sha'awa.
"Inna mi ya faru?".
Faɗin Humaira ganin Mama ta dawo jiki a sanyaye.
Zama tayi ta miƙa hannu zata amshi Ummi dake kuka a hannun Humairar ta karɓe ta tana kwantar da ita akan cinyarta ta fara shayar da ita kamin ta ce.
"Ba komai kawai dai bazaki daɗe a gidan nan ba, zaman bazai yiwu ba Humaira, ita Bilkisu yau zan maida ita".
Bilkisu ta turo baki ta ce.
"Inna amma ba sai gobe mu kai zan tafi ba"
"A'a Bilki gara ki tafi wallahi gidan nan kaɗan ake jira na dama, banyi wani abuba ma Matar can na kai zuga wajan Mai gidan inaga nayi kuma"
"Shin wai Inna kema fa Matar gidan nan ce, akanmi za'a rinƙa maida ke kamar wata ƴar aiki ne?".
Inna bata ce komai tana faɗawa tunani kaɗan haƙiƙa taga kishiyoyi iri-iri kala-kala marassa tsoron Allah har zuwa yanzu batai dacen abokiyar zama ba, garama Sha'awar tunda ita bata bin wasu Malamai kawai isa ce da iko da kissa da kisisina da kuma tana da aikinyi kuma mai kuɗi ce ita kanta bata ma jiran Mai gidan ya bata wani abu kamin tayi hidimar gabanta, shi yasa baka taɓa jin kansu, sai Innar idan zata tabbayi wani abu sun kama faɗa dashi kenan a rayuwarsa ya tsani Mace ta rinƙa yawan tabbayarsa kuɗi, shi yasa kawai ta roƙi da Sha'awa ta rinƙa mata aiki duk ranar girkinta aka sallami mai aiki sai ta rinƙa biyanta, ita nata aikin zata yima kanta kawai, shine fa take samun ƴan kuɗi duk wata dubu goma take bata, shi yasa take rage wasu abubuwan, shi yasa kuma Sha'awar ke latsata yadda taga dama, dan gani take kamarfa ƴar aikin ce ta kawo kawai a cikin gidan ba wai Matar Mijinta ba.
Tunanin Inna ne ya katse jin sake shigowar Maryam inda take cewa.
"Aunty ya kamata fa a ɗora mana girki dan gaskiya na fara jin yinwa, idan bazaki iya wannan aikin ba sai na sanar da Maami a sake wata babu lallai babu dole".
"Kan uban can, Inna wane irin aiki kuma".
Humaira ta faɗa tana miƙewa babu shiri.
Inna zatai magana Maryam ta watsa ma Humaira wani banzan kallo kamin ta ce.
"Ke Agola kafi ɗan gida iya shege, to Mahaifiyar taku aiki take mana a biyata a cikin gidan nan, ai taimaka mata ma ake idan kuma ba'a baƙuta dama akwai masu buƙatar aikin ruwa a jallo gasu nan suna yawo a cikin gari wallahi".
"Keee.....
"Humairaaaa karki sake na sake jin bakin ki a wajan nan, zuwa kikai dama gidan nan dan kawai ki hanani zaman lafiya iyee Humaira?, yanzu baga ƴar uwarki ba Bilkisu tasan ina aikin miye ta ce min? babu abinda ta faɗa, sai ma tunda tazo ta amshe ni ita ke min abincin gidan gaba ɗaya, sai ke daga zuwanki?, to ki shiga hankalinki Humaira bana son tashin hankali".
Zama daɓas kawai Humaira ta koma tayi a ƙasa durshen sai ga hawaye suna mata zuba akan fuskarta, wani malolan baƙin ciki ne ya tokare mata wuya tama kasa faɗin komai, wane irin tozarci ne haka dan Allah?, wane irin abu ne yake samun Inna haka a rayuwa wadda baya karewa?, har zuwa yanzu bata samu ƴanci ba sai yaushe zata samu hutu ta koma kamar kowacce Matar aure dake aure a cikin gidan auranta ne?, amma ace kullum jiya iyau dai, abubuwa da yawa Innar ta shanye su na baƙin cikin kishiyoyi iri-iri, sai yaushe zata huta?.
Wani tsaki ne da Maryam taja ne ya dawo da Humaira duniyar data lula na tunani.
Bin bayan Maryam tayi da kallo irin na baƙin ciki da takaicinta.
Dawo da dubanta tayi inda Inna take zaune tana aje Ummi akan gado zata fita domin ɗora abincin rana Humaira ta ce.
"Inna amma kina ganin yadda wannan Maryam ɗin marar kunya mai ido a tsakar Kai ke gaya miki magana harda tsaki bazaki iya ce mata komai ba, Inna kifa sani kefa Matar Ubanta ce, komin lalacewarki kinfa gama da ita tunda har kika zama Matar Ubanta".
Juyowa Inna tayi tana duban Humaira kamin ta ce.
"Har zuwa kawo yanzu Humaira ke Yarinya ce tabbas, shi yasa rashin hakurinki ke ja miki shiga wahalar rayuwa, idan har bazaki daina wannan halin naki na rashin hakuri ba da idan anyi abu ke shanye ki nuna komai ba komai bane to kuwa tabbas zaki rinƙa ganin matsaloli iri da iri kala-kala, dan haka ki kyale ni kawai, kuma daga yau na gaya miki komi zaki gani a cikin gidan nan bance ki saka bakinki ba".
Tana ƙare maganar zata juya ta fita Bilkisu ta miƙe duk itama tana jin wani baƙin cikin abunda yake samun Innar tasu amma babu yadda ta iya ta ce.
"Inna ki tsaya zan ɗora girkin".
Inna ta ci gaba da tafiya tana faɗin.
"A'a kiyi zamanki ki ƙarasa idasa haɗa kayanki ina gama aikin zamu wuce na maida ke".
Ta ƙare maganar tana idasa fita daga ɗakin kwata-kwata.
Komawa Bilkisu tayi ta zauna tana duban Humaira da kanta ke a ƙasa baƙin cikin duniya ya cika mata zuciya.
"Humaira baza ki gane sunyi mana nisa nesa bama kusa ba, sai kinga wani Yayansu Harun dake zuwa gidan nan duk sa'a-sa'a, wallahi Humaira wannan Yayan nasu maƙura ne wajan iya wulaƙanci da izza, izzar ma a jininsa take, ga ɗan banzan kyau kamar shine yayi kansa nake gaya miki g.....
"Kinga Bilkisu riƙe labarinsa kawai a bakinki bana son ji, yo waiye zai nunama isa da jin kai?, ai gidan ya zo, ni harma kin sa tun kan na ganshi naji tsanarsa a zuciyata ma haka kawai".
Dariya kawai Bilkisu ta saki tana girgiza kai ta sake cewa.
"Hmm bazaki gane bane sai idan kunyi ido huɗu dashi zaki bani labari ne, amma fa gaskiya bazan ɓoye miki ba duk gidan nan shine kawai yake girmama Inna yana kuma sonta ba laifi, domin bai taɓa gaya mata magana wacce bata dace ba, yana da ɗan kirki amma fa baya son raini shi yasa kinga Maryam ɗin can take mugun tsoronsa da shakkarsa, sai ma idan yana gidan yazo ƙasar take tsoron yima Inna magana gatsal".
Shuru kawai Humaira tayi bata sake magana ba.
Ummi ce dake akan gado ta motsa ta ɗan kuka tashi Humaira tayi ta ɗauke ta tana ɗan rirrigata, tana kallon Yarinyar ta dubi Bilkisu ta ce.
"Wallahi Bilkisu bansu Inna ta sake haihuwa a wani wajan ba, dubi ki gani a gidan nan ma sai da ta bari ta haihu ni wallahi nayi baƙin ciki da hakan".
Ɗan fiddo ido waje Bilkisu tayi ta ce.
"Lallai ma Humaira yo saita ƙi haihuwa, ai gara Mahaifin Ummi gata nan ita ko banza yafi sauran Iyayenmu".
Shuru kawai Humairar tayi ma Bilkisu.
A ranar Inna taje maida Bilkisu bayan ta gama aikace-aikacen gidan. Inna taje gidansu Bilkisu taga yadda har lokacin Matan ubansu ke zaman jahilci da kishin hauka, har lokacin ba'a daina rigimar data baro suna yi ba a gidan, da yake daga gidan su Bilkisu data fito sai tayi aure a gidan su Maryam harta haifi Ummi, Babansu Humaira shine wadda ta fara aure a rayuwarta, da suka ganta hankalinsu yayi mugun tashi domin sunga nesa ba kusa ba Innar na aure gidan rufin asiri ba kamar nasu ba, shikenan fa hassada da gori ya fara tashi suka fara rigima, inda Inna ta tsaya tana kallonsu ta ce.
"Wai ku Ladidi har yanzu baku daina wannan rayuwar ta rashin wayewa ba?, idan danni kuka gani kuke shirin dambacewa to yanzu zan bar maku gidan, Yarinyar ce na dawo da ita gidan Mahaifinta, dan haka ni kunga tafiya ta sai Allah ya sake haɗamu kuma".
Ai Inna na fita suka sake kace miyewa da faɗa ko wacce na zagin ƴar uwarta, Bilkisu dake raɓe waje ɗaya idonta sunyi jawur tana kewar Inna ta samu waje a ƙasa ta zauna tana kallon yadda suke tada jijiyoyin wuya.
Inna Asabe ce ta waigo inda Bilkisu ke zaune tayi mata wani kallon banza ta ce.
"Kinga Bilki kin dawo ai ga aikin dambu na can na akan wuta maza je ki ƙarasa min shi, ki gama ki ɗaure shi a leda kamar yadda aka saba yi, ki zo ki wuce tallarsa yanzun nan".
Ladidi tayi tsaki ta shige ɗakinta tunda dama ita ce ƙarama a cikin gidan, to bata shiga harkar Bilkisun bata sata wani aiki amma itama tana yawan hantararta.
"Amma Inna Asabe yanzu na dawo na gaj...
Ai bata ƙare maganar ba taji saukar wani gigitaccan mari akan ƙuncinta.
A mugun gigice ta miƙe jikinta na rawa dafe da ƙuncinta tana duban Inna Asabe dake huci a tsaye kusa da ita.
"Ke har kin isa ina faɗa kina faɗa dan uwarki?, Ohoo ko dan kinje wajan uwarki tayi miki karatu kizo ki raina mu ko?, to wallahi kinji na rantse sai lallasa ki a cikin gidan nan".
"Lahh Inna shikenan Bilkisu ta dawo na huta da fita talla".
Faɗin wata matashiyar Yarinya bata wuce sa'ar Bilkisun ba.
"Ai kuwa Binta ta dawo kinga zata min rashin kunya".
Wacce aka kira da Binta ta wani matso tana duban Bilkisu rai a mugun ɓace cike da baƙin cikinta dama Binta take kullum saboda kawai Bilkisun ta fita kyau shikenan take jin haushinta kamar ta kasheta.
"Ke har kin isa ki tsaya ido cikin ido kina gaya ma Inna magana?, bari naci uwarki kinga gobe ma ki sake gayama uwata magana dan Allah kinji ko?".
Binta na ƙare maganar ta wani sake