Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
ai bazan taɓa miki ƙarya ba, danma naje nagansu yanzu ai da idan banda haka da yanzu tana inda yake".
Wata irin zabura Maami tayi wufff ta fice daga parlon nata bata doshi ko ina ba sai Part ɗin Harun.
Ma'u dake bin bayanta ta buɗe baki ta ce.
"A'a Maami ina kuma zaki je?, ga inda ya kamata ki fara zuwa nan".
Ta ƙare maganar tana nuna ɓangarensu Humairar.
Maami bata wani tsaya jinta ba tayi gaba.
Harun dake zaune yana kurɓar coffeen da Humairar ta kawo masa wadda har shine Ma'un ta shigo ta gansu a lokacin, ko kaɗan kawai ta same su ne a lokacin da yake ma Humairar mitar bata kawo masa Coffeen da wuri ba har ya fara gajiya, ita kuma Humaira zata basa hakuri ne bata san ita kanta tayi magana da wata manufa ba amma shine ita Ma'u daga ji wai shagwaɓa ma take masa tana kashe masa murya.
Shi kuma Harun harga Allah haka kawai Humairar rigimarta da ƙiriniyarta da rashin son raininta yake birgesa, haka kawai dan yaja ta da magana ma wani lokacin zai ce ta haɗo masa Coffee, wannan ƙunƙunin da take masa haɗe da turo baki shine kawai yake tafiya dashi, har idan ta bar waje yake samun kansa cikin sakin murmurshi haɗe da wani irin nishaɗi, shi ko kaɗan bata bashi haushi, ba kamar su Maami da Ma'un daya lura sunyi mugun tsanar yarinyar haka kawai ba.
Shigowar Maami parlon ne yasa shi ɗaga kansa yana katse tunanin daya lula, a hankali ya aje cofin dake hannunsa ya miƙe tsaye yana duban Maami dake tsaye akansa.
Cikin faɗan da bai taɓa jinta tayi masa shi ba bare tsawa ta fara magana.
"Harun mike tsakaninka da wannan ƴar iskar yarinyar mai kama da Karuwai?".
Ɗan matse idonsa yayi fuskarsa na cika da wani irin mamaki ya ce.
"Maami wacce yarinya kuma?".
"Kai karka raina min hankali mana?, da wani zaka ce baka gane wacce yarinya nake magana akai ba, wacce yarinya zanyi magana akai idan banda wannan yarinyar Humaira".
"Amma Maami mi yasa kike wannan tabbayar?, bayan kin san babu abunda ke tsakaninmu?".
Wata ajiyar zuciya ta saki tana sake faɗin.
"Idan ma akwai ko akwai niyar ƙulla alaƙa da ita, to tun wuri tun kan dare yayi maka kama canza sheƙa, domin mudun ina raye bazan taɓa bari ayi wannan kwamacalar ba wallahi, bazan taɓa bari ayimin yadda akai ma Aunty Mansura ba, aka haɗa Muhammad aure da agolar gidan ba, ni nan baza'a taɓa yimin wannan haɗin ba, kaji ma na gaya maka tun wuri idan ma kana niyar hakan, dan naga kana wani murmurshi kana sakar mata fuska".
Saida zuciyar Harun ta wani irin buga kaɗan kamar ɗan tsoro ya ɗarsu a cikin ransa sai kuma yayi saurin waskewa ganin yadda Maamin ta zuba masa ido tana son gano wata gaskiyar da Ma'un take sanar da ita, ba dai da gaske bane son nata yake ba?, amma sai taga ya saki ƙaramin murmurshi na gefen baki kaɗan wadda baka isa ka gane yayisa ba idan ba ƙura masa ido kayi ba.
"Maami ai ni banga aibu a cikin auran da za'ai ma Hammad da Intee ba, kifa tuna yayi hidima da yarinyar kuma ita kanta Aunty Nuratu bata da matsala kamar dai Inna a nan, please Maami duk abunda kuke ɗin nan bai kamata ba kwata-kwata, kun samu abokan zama na gari amma kun kasa kwantar da hankalinku wajan gane gaskiya d........
Wani kyakkyawan mari data wankesa dashi wadda tunda ya girma da wayonsa har ya mance rabonsa da Maami tasa hannunta ta maresa, dan haka marin yazo masa a mugun bazata yana riƙe ƙuncinsa yana kallon Maami da mamaki, ita ko kallonsa take tana fitar da wani irin huci na zallar ɓacin rai wadda bai taɓa gani a tattare da ita ba sai a yau ɗin.
Tabbas tayi nisa a tsanar wannan abun ya gani a cikin idonta, duk wani abunda take faɗa gaskiya ne bawai faɗa kawai take yi ba.
"Har ni Harun zaka tsaya ka dubi tsabar idona kana gaya ma magana haka?, ni ce na haifeka ko kai ka haife ni ne na kasa fahimta?".
"Am sorry kiyi hakuri Maami, ni ban faɗi haka dan kiji haushi ba, gaskiya ce kawai na faɗa amma kiyi hakuri baza'a sake ba".
Ya faɗa yana shinye duk wani mamakin Maami ɗin da kuma Ummu da suka ɗora ma kansu wahala da tsanar abunda bashi kenan ba.
Wani irin duba take masa dama tasan Harun duk iya abunda zakai masa ko yankasa zakai zai iya buɗe baki ya faɗa maka iya gaskiyarsa, koda kuwa ka bashi girma ne ka haifesa idan har abun nan gaskiya ce yake gani tofa sai ya faɗa maka, sai dai idan daga baya kayi masa koma miye amma sai ya faɗa.
"Ni dai na gaya maka danma kaji da kyau bazan taɓa bari haka ta faru a kaina ba, ta dai faru da Aunty Mansura amma kam a nan gidan har abada bazai faru ba. Idan ma zaka shiga hankalinka ka shiga tun wuri, tun kan ajimu da kai".
Tana ƙare maganar ta juyo fuuuu ta wuce ta barshi da zallar mamaki.
Tana fita ta iske Ma'u riƙe da ƙugi tana jiran fitowarta, danta rantse bazata bita part ɗin Y Harun ɗin ba, domin idan ya gano ita ce ta kai zugar nan to tabbas saita gane kuranta.
"Maami ga inda ya kamata ki fara shiga nan ki bige masu wornig ba wai wajan Y Harun ba".
"Ai suma yanzun nan zanje gare su, gara na fara ta kansa shima".
Ta faɗa tana yin gaba Ma'u na take mata baya suka nufi Parlon Inna kai tsaye.
Zaune take a parlon tana ma Ummi kalaba da ɗan gashin daya fara fito mata akai yarinyar nayi tana wasa ita kuma Humaira na binta a hankali tana kitse mata kan.
Kawai bata san hawa ba bata san sauka ba taji an faɗo parlon ba ko sallama, dan haka ba ƙaramin tsoro ma hakan ya bata ba.
A hankali ta miƙe tsaye tana kallon su Maami da Ma'u dake jefa mata wani irin ɗan iskan kallo.
"Ke ina uwar taki take?, ta kanta zan fara kamin na dawo ta kanki ƙaramar marar kunya kawai ballagaza".
Da wani irin sauri Humaira ta runtse idonta kalmar ballagazar da Maami ta jefeta dashi ta dake ta sosai a zuciyarta.
Idonta ta buɗe daya kaɗa yayi jawur na ɓacin rai zatai magana Inna ta fito, zuciyar Inna na addu'ar Allah yasa ba wani abu bane Humairar taje ta jawo masu ba yau ɗin tunda sanyin safiyar nan?.
"Yawwa dama ke nake nema ai, ke ce sa'ar yina ba wai wannan Ƴar taki ba".
Inna cike da wata fargaba ta ce.
"To mi kuma tayi?".
Ta faɗa tana haɗe hannayenta waje ɗaya.
Wani irin abu mai ɗaci Humaira ta haɗe a maƙoshinta tana jin wani irin bala'in ɗaci akan harshenta.
"Mifa zata yi?, baccin abunda ta sabayi a can a gidan tsoho, tana zuwa tana kashe ma Maza murya suna binta, shine zata zo nan tana ma Ɗana haka dan kawai ta saye zuciyarsa da asirin da aka je aka saba yo ma mutane. Mu kam mun gode Allah mu ba dangin asiri bane da Allah muka dogara kuma munfi ƙarfin ko wanne shege ko shegiya, dan haka tun muna shedar juna kiyi ma Ƴarki gargaɗin ta kiyaye Ɗana, shi ɗin ba sa'an yinta bane, nesa tayima Yaro nisa, sai dai ya ɗaga yayi hangi, dan haka idan ƙunne yaji gangar jiki ta tsira".
Tana ƙare faɗar haka ta juya tana sakin wani irin tsaki tayi gaba tabar Ma'u tana masu kallon banza su duka kamar zata juya sai kuma ta tsaya tana nuna Humaira da tsaya ta ce.
"Ke baccin tsaurin ido ma irin naki har kin isa ki fara tunanin haɗa huɗɗa da Y Harun?, ai ke kanki kinsan zaren ba kalar yadin bane, dan haka sai a kama gaba aje inda ya dace amma nan dai babu ta inda haɗin yayi dai-dai ma".
Ta ƙare maganar tana wani bankama mata wata uwar harara kamar idonta zasu faɗo ƙasa tana sakin tsaki itama ta juya tayi gaba barsu a tsaye sake da baki da tsananin mamakinsu..........
Chapter 30
*SAKINA POV*
"Ki nutsu please karki tona mana asiri fa".
Faɗin Doctor Halisa tana sake waigowa sosai tana kallon harabar gidan ganin ma'aikatan dake aiki a bakin get ɗin wasu bacci harya fara surarsu saboda kusan biyun dare ta shigo gidan.
Da kyar ta lallaɓa Sakina ta ɓanɓareta daga jikin Sadeeq data ƙanƙamesa yana wani irin bacci mai nauyin gaske kamar wadda aka zubama wani abun.
Tayi kuka tayi kuka kamar zata shiɗe da kyar Doctor Halisa ta jawota tana wani irin kuka har jikinta jijjiga.
A hankali ta shiga sauke ajiyar zuciya ganin sun fice daga cikin gidan Motar Doctor Halisa dake can bakin titi bata yarda ta shigo da ita har wajan gidan ba, shigar data yo fuskarta a rufe bata yarda ta barta a buɗe ba.
Saboda tasan za'a iya samun Camera a cikin gidan to komai na iya faruwa.
Bayan sun zauna a cikin motar Doctor Halisa ta fara ƙoƙarin tayar da Motar domin subar wajan, ta dubi Sakina dake kuka har lokacin, tana waigen hanyar da suka biyo danji take kamar ta baro wani ɓangare ne dake cikin jikinta.
Tsaida tayar da motar tayi tana dafa kafaɗar Sakinar ta ce.
"Sakina ki ɗaure ki daina wannan kukan please, nasan tabbas ko baki faɗa ba kina son Mijinki, wadda idan har ya dawo dai-dai babu lallai ma ya iya tunowa dake, shi ɗin nan da kike gani yana da sauƙin kai a baya, amma fa ko Mace baya kallo bata ma gabansa, zaki sha mamakin irin yawan ƴan matan dake ɗawainiya da sonshi amma baya taɓa ɗaga kai ya dube su, sai dai kashh lokaci ɗaya ya koma haka kowacce kuma ta gujesa dama abun hannunsa da kyan da Allah ya zuba masa ne ke ruɗarsu, dan haka addu'a ce taki idan har ya warke ya iya tunowa dake a cikin sabuwar rayuwarsa. Zai iya warkewa a kowanne lokaci, saboda tunda ƙaddarar hatsarin Motar ya faɗa masa ƙwaƙwalwarsa ta juye ta koma haka, shi mai hankali shiba mai hankali ba gashi nan dai.
Da sauri Sakina ta waigo tana duban Doctor Halisa bakinta na kyarma ta ce.
"Dama ciwonsa ta sanadiyar accident ne?".
"Kware kuwa, ko kin ɗauka dashi aka haifesa?".
"A'a ɗaukata ko ciwon nasa bai danganci na Hospital ba kwata-kwata, amma mi yasa za'a barsa gida a haka?, kamata yayi a kaisa asibiti yayi jinyarsa a can, sana su kansu magungunan da ake basa kamar akwai ƴar matsala tattare dasu".
Wani murmurshin gefen baki kaɗan Doctor Halisa ta saki ta ce.
"Bama ƴar matsala bace, wa'innan magungunan ita da kanta Mome tasa na kawo su daga Asibitin mu aka canza masu kwalabe ta yadda babu mahaluƙin da zai iya gane na miye, amma wa'innan maganganun da kike gani ƙara rikita mashi ciwon da yake fama dashi yake, yana sake hautsina tunaninsa da ƙwaƙwalwarsa, komai na dawo masa baya ne ba wai ya warke nan kusa ba, idan har ana basa magungunan to bazai taɓa samun lafiya ba".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, mi mutane ke son zama ne a duniyar nan?".
"Hmm ke mima kika ji ne Sakina?, tukunna ma dai wannan labarin sai an samu zama zaki sha labarin waye Sadeeq da ahalinsa gaba ɗaya".
Jan lumfashi tayi tana jin wani iri a cikin ranta tausayinsa ne dana kanta ke damun zuciyarta, dafa cikinta tayi wadda ya fara ɗan girma kaɗan tana jin wata irin bala'in kewar mahaifin cikin na nuƙurƙusar zuciyarta tun a yanzu.
Ɗaga kanta kawai tayi tana share hawayen dake zubo mata, tana sharewa wasu na zubo mata, gajiya tayi da sharewa kawai tabar su suna zuba, tana kallon titi da yanzu Doctor Halisa ta tayar da Motar suka fara tafiya.
Har suka isa gidan da take da tabbacin gidan Doctor Halisar ne saboda komai akwai haɗe key na gidan suka shiga ta nuna mata wani ɗaki ta shiga ta zauna kawai bata ce komai ba, babu kowa a gidan da alama ita kaɗai take rayuwa a cikinsa.
Tana fita ta dawo mata riƙe da abinci ta ce.
"Ki daure ki ci abincin nan kamin ki kwanta, dan nasan babu lallai kinci abinci, ki daure kici kamin ki kwanta, saboda gobe ƙarfe tara na safe zamu bi jirgi mubar garin nan".
Da sauri Sakina ta ɗago tana kallon Doctor Halisa ta kasa hakuri ta ce.
"Mubi jirgi kuma?, ina zamu je?".
"Ki kwantar da hankalinki dole ne mubar garin nan, domin tun lokacin da mu kai magana dake nasa a maida ni aiki a Lagos wani asibiti dake can cikin garin Lagos, to a can zamu koma zama da ke, kinga babu yadda za'ai duk faɗin Lagos su iya gano inda nake, zan cire duk wasu layuka da suka sanni, dan hatta wajan aikina na bada hakurin duk wadda ya zo nema na kar a sake a basa information ɗin inda nake, duk da suma ban gaya ma kowa unguwar da zan koma da zama ba a can ɗin".
Girgiza kanta Sakina tayi tana kallon Doctor Halisa ta ce.
"Amma Doctor please ki bani aron wayarki na sanar da Inna ta abunda ke faruwa dani, kar labarin barin gidan da nake ya riske su hankalinsu zaiyi mummunan tashi ne, ya kamata ace su sun san inda nake".
"Naji zaki sanar dasu inda kike amma ba yanzu ba".
"Saboda mi Doctor ba yanzu ba?".
"Saboda shirinmu na iya rushewa ta sanadiyar sanar dasu a yanzu ɗin".
"Amm......"
"Kinga kibar komai a hannuna nasan mi nake yi, ina bin komai daki-daki ne, ta yadda baza'a samu wata matsala ba, har mu kai inda muke son kaiwa".
Shuru kawai Sakina tayi dan zuwa yanzu ta yarda da Doctor Halisar ko banza ita mutum ta farko data fara taimaka mata a cikin wannan halin data tsinci kanta a ciki.
Kamar yadda ta ce mata da kyar ta samu ta ci abincin shima ɗan kaɗan duk da irin yinwar da take ji sosai, amma saboda tunanin halin da Sadeeq ɗin zai iya shiga idan har ya tashi yaga babu ita ya hanata sukuni ko kaɗan bare natsuwar cin wani abinci.
Washe gari tunda safe Doctor Halisa ta shigo da kanta ta haɗa mata kayan abinci tayo wanka ta shirya da wasu kaya da Doctor Halisa ta sayo mata tun jiya saboda babu ko tsinke data ɗakko a gidan data baro.
Basu bar cikin gidan ba sai wajan takwas da rabi sadda zasu isa Airport har lokacin tashinsu yayi, sanye suke da facemask a fuskokinsu har suka shiga cikin jirgin waje ɗaya suka zauna kujerarsu a jere take.
Tunda Sakina take bata taɓa ganin koda filin jirgi bane kai da idonta ma bata taɓa ganin jirgin ido na ganin ido ba, amma sai yau dalili mai ƙarfi da ƙaddara zata sa ta fara shigarsa a karo na farko a tarihin rayuwarta.
Har jirgin ya tashi bata cikin natsuwarta ita dai gata nan dai.
****************
"Innalillahi Huda mi kike cewa ne?".
"Mome abunda kika ji na faɗa shine dai abunda ya faru".
"Yaya za'ai ki ce kinje Part ɗin Sadeeq baki ga Sakina ba?, sana ki ce shi kansa Sadeeq ɗin gashi can yana hargitsa part ɗin nashi saboda kawai ya tashi bai ganta ba?, wannan labari da kike bani abun kamar a mafarki kika gansa ne fa, yaya za'ai Sakina ta iya fita daga cikin gidan nan?".
"Zo muje Mome ki ganema idonki".
Huda ta ƙare maganar tana jan hannun Mome keeee suka nufi Part ɗin Sadeeq.
Suna shiga Mome tayi saurin yin baya-baya saboda wani gilas da Sadeeq ɗin ya wallo ta wajan saura kaɗan ya sauka a goshin Mome, saurin gocewar data yi ne bai same ta ba.
"Innalillahi mi zan gani?".
Ta faɗa tana bin parlon da kallo ganin yadda ya maida shi kamar wani Juji ko ina a hargitse ya fasa duk wasu abubuwa na gilassai dake a cikin parlon.
Ƙarshe ya zube a ƙasa yana yin wasu irin surutai wadda suka kasa gane kansu.
"Mome anya yarinyar nan ba guduwa tayi ba danta san tayi ma Ya Sadeeq asiri?".
"Asiri kuma wanne irin asiri?, ai babu abunda tayi masa, kawai sabo ne da yayi da ita, kuma duk inda ta shiga sai ta dawo cikin gidan nan ta iske ni, sana kisa a kira min wacce tayi sanadiyar zuwanta gidan nan yanzu nan ina son ganinta".
Mome na rufe baki suka ga Sadeeq ya miƙe kamar wadda aka tsikara ya tashi bai nufi ko ina ba sai jikin bango a mamakinsu yana zuwa ya fara buga kanshi da bangon yana wani irin kunji.
"Innalillahi Huda muje mu dakatar dashi zaima kanshi illa".
"Mtswww to Mome sai mi idan yayima kanshi illar?, dama ba abunda kike so bane ki barshi yama mutu mana".
Wani kyakkyawan mari Mome ta ɗauke Huda dashi daya sa Huda zaro ido tana dafe kuncinta da mamakin marin da Momen ta sharara mata.
"Mome.....".
Ta faɗa da zallar mamaki.
"Kware na mare kin, kin san mi kike faɗa kuwa?, a baya nayi kuskuren nakasa rayuwarsa a lokacin daya gamu da mummunan haɗari ya samu kwancewar kai, sai na sake bada gudunmawar idasa rikicewar kansa, da yanzu ke ce a matsayin Matar Sadeeq ba wai wata ba, amma ko yanzu ya dawo cikin yaccinsa dole ne Huda sai kin auri Sadeeq domin shine ya dace dake".
Shuru kawai Huda tayi tana tunanin yama za'ai Sadeeq ya iya dawowa kamar yadda yake ada can baya?, mai ji da gayu da isa da izza, amma duk yanzu babu su duka, abunda yasa ma ta gujesa itama kenan taji babu yadda za'ai ta iya zama dashi a yadda yake.
Kamin suyi wani yunƙuri ma ya zube a wajan a sume saboda yadda yake buga kan nashi a jikin bango yasa goshinsa fashewa jini mai yawa ya shiga zubo masa akan fuskarsa duk ya ɓata masa fuska, wani