Tsanin Kaddara Complele Book Zahra Star.docx

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   5 / 40

12K to 15K   out of 118.4K words

faru ba".

"Eh Kawu Ismail ya kira ni ban ɗauka ba saboda bana kusa, to kuma banbi kiran nashi ba saboda aiki daya shamin kai".

Gyara zama Sakina tayi ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar Aunty Sakina.

Aunty Sakina ta wani gyara zama tana duban Sakina tana ƙanƙance ido ta ce.

"To nan da kika zo miye kike so nayi miki?".

Gaban Sakina ne ya faɗi tana kallon Aunty Sakinar cike da ɗan mamaki, ta ɗauka ai zata ce ga waje ta zauna har lokacin da komai zaiyi dai-dai, amma sai gashi tana cewa yanzu mi take so tayi mata ma?.

"Dake nake magana fa Sakina?".

Ajiyar zuciya Sakina ta saki a bayyane, tana yin ƙasa ta da kanta kamin murya na rawa ta ce.

"Aunty Humaira na wajan Inna bazai yiwu ace mu duka mun tafi gidanta mun tare ba, saboda gudun rigima a can tunda kishiyarta da mijinta basa son mutune".

"Ohhoo na gano nufinki, ni kenan nan kinzo ne na riƙeki ki zauna a gida na kenan?, ni ce karkatacciyar kuka mai daɗin hawa kenan ba?, ni ce wacce mijinta ke son jama'a ko?, ko kuwa tsabar an raina min hankali zaki wani kwaso ƙafafu kizo waje na, ina su Hadiza suke su da baki tafi gidajensu ba?, saini da kika raina?".

Ƙirjin Sakina ya buga bata san lokacin data ɗago tana kallon yadda Aunty Sakina ke ruwan masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, sai kace an kawo mata annoba a gida.

"Kiyi hakuri Aunty".

"Keee ba wani hakurin da zanyi zuwa zaki gobe-goben nan ki koma inda kika fito, ko kuma can kije gidan uwar taki, ni banda ƙarfin riƙe ɗan wani yawwa".

"Shikenan Aunty zan tafi yau ma, ba sai an kai goben ba".

"Ahhhh ni zaki nuna ma zuciya?, to zuciyar ma taci Ubanta kinji, Allah raka taki gona tafi nono fari wallahi. Idan kin tashi tafiya ga kuɗin Mota nan Allah ya tsare hanya".

Aunty Sakina ta faɗa tana miƙewa tsaye, ta miƙa mata wasu kuɗi ko a jikinta.

Sakina ta miƙe jiki a sanyaye ta ɗauke jakar kayanta dama a kusa take da ita.

Idonta cike da hawaye bata waigo ba tana takawa zata fice daga parlon bata amshi kuɗin da Aunty Sakinar ke miƙa mata ba. Aunty Sakina ta saki baki tana duban Sakina dake shirin fita daga gidan taji Sakina ta ce.

"Aunty ki bar kuɗinki Kaka ta bani kuɗin Mota dama kuma sun rage zasu kaini har Funtua na gode kawai".

Sakina na ƙare maganar tayi saurin barin parlon dan kuka ne ya sarƙe ta.

Tana iya juyo yadda Aunty Sakina ke faɗin.

"Aikin ɓarr inji tusa, sun ƙara auki wallahi kada Ubangiji yasa ki amsa shegiya mai mugun hali irin na uwarta. Wani yasa uwar taku taki zaman aure ne a gidan Ubanku?, duk ba hakuri ake a gidan auran ba, amma ita ce ta fito daga wannan gida taje wannan gida da sunan aure ba'a daɗewa sai kiji an sake ta tsabar mugun halinta, mu da muka riga ta ma auran gamu nan zaune a gidan Mazajenmu tun auran farko bamu sake wani ba, ko yaji tana ganin muna yi ne?, ba hakuri ake ba a ko ina kowa fa da matsalarta gidan auranta haƙuri kawai ake ana shanyewa".

*House No: 34, Tudun Wada Estate, Funtua Local government Katsina State Nigeria*

"Humaira ki tashi kije ki zubo tuwon nan kici bana son abin ɓacin rai kin sani dai ko?".

Humaira ta miƙe haɗe da turo baki ta dubi Inna ta ce.

"Amma Inna kinga fa tunda Asma'u tazo gidan nan muke faɗa da ita, Maryam ta tafi ita kuma wannan ta wani kwaso ƙafa daga gidan auranta tazo ta wani tare a gidansu, haka ake rayuwa, dan kawai tana aure a cikin garin nan sai ace mutum yayita zarya a gidansu?".

"Kinga bana cike da rashin kunyarki, babu ruwanki dasu, gidan Ubanta ne babu wadda ya isa ya ce danmi ta zo, dan haka bana son irin wa'innan maganganun kinfi kowa sani".

Lumfashi kaɗan ta sauke tana miƙewa ta fice daga ɗakin Innar ta nufi kitchen.

Tsayawa tayi a bakin ƙofar kitchen ɗin tana kallon Asma'u dake juye ragowar tuwon daya raye ta cinye sa tass tazo tana sake juye wadda yayi saura, dama gata da ciki kusan wata bakwai shi yasa take shegen ci kamar Gara.

Riƙe baki kawai Humaira tayi kamin ta dubi Asma'u ta ce.

"Asma'u banfa ci tuwon nan ba, kuma ni na girka shi".

Ma'u ta wani juyo tana ma Humaira wani irin banzan kallo kamin ta taɓe baki ta ce.

"Allah sarki harda su Kaza a cin danƙo?, ke har wuyanki ya isa yanka? nida gidan Ubana na zuba abinci ki wani zo kina faɗin ke kika girka?, to na cinye abincin ko za'a bige ni ne?, baki da iko a cikin gidan nan tunda gida dai ba gidan Uban wani bane, idan kinji haushi ki koma gidan naki Uban mana".

Wani malolan baƙin ciki ne yazo ya tokare ma Humaira wuya da kyar ta iya buɗe baki ta ce.

"Kware kuwa ba gidan Ubana bane".

"Ahh ashe kinsan da haka Mtsww aikin banza kawai dalla can ni matsa min a nan na wuce".

Zata wuce sai kuma ta dawo baya tana sake duban Humaira da takaici ya rufeta ta ce.

"Yawwa sana daga yau karna sake jin kin kira sunana gatsal kowa a cikin gidan idan kika cire Y Huran kowa Aunty yake faɗa min, sana ki cire wata Asma'u a sauƙaƙe ki ce Aunty Ma'u kin gane?. Sana please kamin ki fito daga kitchen ɗin nan ki ɗan dafa min shayi mai na'ana'a Please ina ɗakin Maami ina jiranki".

Kutumar Ub*n can kayyasa.

Kawai Humaira ta faɗa a zuci, a fili kuwa bata san lokacin data ce mata.

"To Aunty Ma'u an gama".

"Yawwa good Madallah".

Ta ƙare maganar tana wucewa.

"Kan Buji, lallai kuwa Aunty Ma'u zaki ga dafa shayi mai na'ana'a ganin idonki".

Ta faɗa haɗe da yin kwafa ya shiga kitchen ɗin kamar abun arziƙi ta fara kiciniyar haɗa shayin, sai da ta gama ta saka a Kofi sai ta ɗakko farin wani abu a leda ta buɗe ta juye kusan rabi a cikin shayin kamin ya motsa da cokali sai ta gama motsawa kamin ta ɗebo a cikin cokalin ta ɗan kai bakinta wani irin mugun tsami ne ya gauraye bakinta da sauri tayi saurin furzo dashi tana saka bakin rigarta ta shiga goge harshenta da ya ɗauki mugun tsamin babu daɗi, yamutse fuska take saboda har lokacin tsamin bai bar bakinta ba.

Sai ta saki murmurshin mugunta ta fitowa daga kitchen ɗin haɗe da kofin shayin data haɗa ma Ma'u tana nufar ɗakin Maami ɗin tana tafe tana sakin murmurshi na mugunta.

Tana shiga bata iske Maami a ɗakin ba sai isassar Ma'u dake zaune a tsakiyar parlon tana tusa tuwo a baki kamar wata mayinwaciya.

"Aunty Ma'u gashi".

"Ki ajesa mana kusa dani bana fa son rashin daraja".

"Hmmm"

Kawai Humaira ta furta ƙasa-kasa a zuci take faɗin.

"Idan ban gyara ma wannan Ma'un zama bama ai wallahi yau ko baccin arziƙi bazan samu nayi ba, yau zaki gane shayi ruwa ne".

Ajewa tayi a gabanta tana ƙoƙarin fita taji saukar maganar Ma'u.

"Ke dawo nan kizo ga kwanon dana ci abinci nan ki ɗauke su".

Dawowa kawai Humaira tayi tana danne ɓacin ran dake taso mata, bata so ta ɓata shirinta Allah yau da sai ta gaggayawa Ma'un nan magana komi zai faru sai dai ya faru.

Tana fita ta aje kayan a kitchen ta dawo ɗakin Inna.

Bata tsaya parlo ba tayi cikin bedroom na Innar tana faɗawa Inna taci tuwon a kitchen shi yasa taga ta daɗe bata dawo ba, bari yanzu ta ɗan kwanta ta huta.

Inna amsa mata kawai tayi tana ƙoƙarin sauke Ummi dake goye a bayanta, shigar Humaira bedroom ba daɗewa Inna taji an bango ƙofar parlo an shigo a hargitse.

Inna ta ɗaga kai tana duban Ma'u dake nishin azama tana ta furzar da miyau a bakinta sai yamutse fuska take tana nuna Inna tana faɗin.

"Aunty ni Humaira zata ma haka?, wallahi yau saina ci ubanta, saita fito nan ta iske ni tana ina ne ma?".

"Innalillahi Asma'u miya faru?, mi ya haɗa ku?".

Faɗin Inna gabanta na faɗuwa lokaci ɗaya.

Maami ce ta shigo ɗakin itama tana duban Ma'u, jin tashin maganar Ma'u a ɗakin Innar yasa Maami shigowa ba shiri tana haɗe fuska ganin yadda Ma'u take a gigice yasa Maami riƙeta sosai tana cewa.

"Ke Ma'u mi ya faru?".

"Maami wai ni zan saka Humaira ta dafa min shayi shine ta saka min ɗan tsami a cikin shayin a maimakon sugar, Maami karkiji bakina kamar ba nawa ba nake ji, kuma wallahi har haɗe shayin nayi a ciki na, saboda da garaje na kurɓi shanyin, Allah ya isa tsakanina dake Humaira wallahi bazan yarda ba".

Ma'u ta ƙare maganar ta ɓarkewa da wani kuka.

Hankali a tashe Maami ta nuna Inna data yi mutuwar tsaye baƙin ciki ya rufeta, mi Humaira take son zama ne?, kashe mata auren nan take son yi shima?.

A hargitse cike da hargowa Maami ta fara masifa tana cewa.

"Kima rufe bakinki kiyi shuru kawai Ma'u, Allah wallahi yau saina nunama wannan ƴar taki marar kunya marar hankali kalata, kuma wallahi ta sake wani abu ya sami Ma'u da abunda ke cikinta na rantse da Ubangiji saina saka an daureta har gidan gyaran hali kuwa, tunda na lura bata da hali ko kaɗan, ba tashen rashin kunya take ji ba?, to na taka ta na shanye".

Hankali a tashe Inna ta shiga kiran Humaira a tsawa ce.

Humaira cike da ɗan tsoro da kuma fargaba ta fito tana dakewa tana wani sunne kai.

Cike da wani irin takaici Inna ta matsa inda take tana nunata da yatsa ta ce.

"Abunda naji suna faɗa haka ne iyee?".

Inna ta faɗa da wata irin kakkausar murya babu watsa.

Wacce tasa ƴan cikin Humaira hargitsawa.



Bakinta na rawa kai a ƙasa ta ɗan ɗago tana satar kallon Inna data haɗe rai babu wasa akan fuskarta, da kyar ta fisgo magana ta ce.

"Inna wallahi ita ce taja ni har....

Tassssss tassssss.

Wani irin kyakkyawan mari da Inna ta ɗauketa dashi ne ya shanye ragowar maganar da take son idasa faɗa.

Dafe ƙuncinta tayi hannu biyu-biyu a gigice tsabar yadda marin ya gigitata.

Nunata Inna tayi da yatsa a faɗace take cewa.

"Wato Humaira ban isa dake ba ko kike nuna min?, ban isa na ce kiyi abu ba sai kin tabbatar kin tsallake abunda na ce ɗin kinje kinyi radin kanka ko?".

Maami ta taɓe baki ta ce.

"Koma miye bake ce ke ɗora su a hanya ba?, yara sun taso ba wadda ya isa yayi masu magana suji shi yasa suka gagari zama gidan uban kowa, to ni dai wallahi ba dai a gidan nan ba a'ato".

Maami na idasa maganar taja hannun Ma'u dake aikama da Humaira wani irin kallon tsana.

Suna fita Inna ta haɗe miyau na takaici ta dubi Humaira da tai tsamo-tsamo ta sake faɗin.

"Shikenan kinzo ne dama dan kawai ki kashe min aure Humaira?, kinga sai mu tafi ni da ku a titi muna kwana haka kike so ai ko?".

Kuka mai sanyi Humaira ta saki ganin Inna yadda idonta su kai ja na tashin hankali ta kamo hannun Inna, Innar ta zame hannunta tana kauda kanta riƙe da Ummi wacce ta saki kuka yanzu saboda yadda Innar ta riƙeta, tunda ta sakkota daga goyon bata aje ta ba Ma'u ta faɗo parlon.

"Dan girman Allah Inna ki yafe min bazan sake ba Allah".

"Hmm Humaira kenan, nafi kowa sanin wace ke, ko kince haka sai wannan rashin hakurin naki yaja kin sake, ai mudun ba zaki rinƙa hakuri ba a rayuwa kina maida komai ba komai bane to kuwa kin rinƙa ganin matsaloli kenan a rayuwarki, ina sake faɗa miki".

"Dan Allah kiyi hakuri".

"Uhmmm naji amma ki tabbatar kinje kin bata hakuri, kuma daga yau ki tabbatar ko miye ta saka ki kiyi mata shi kamar yadda ta ce idan ba haka ba Humaira wallahi zaki rinƙa ganin ɓacin raina".

"Insha Allah Inna na daina zanyi abunda kike so".

Inna bata sake cewa komai ba ta koma ta zauna akan kujera tana fiddo nono ta sakama Ummi a baki dake faman rigima Yanzu.

Tunda abun ya faru su Maami suka fice daga gidan zuwa asibiti sune basu dawo ba sai cikin dare.

Tun lokacin Humaira bata sake fita waje ba tana ɗaki a kusa da Inna.

Suna zaune Inna na jiran tsammani danta san tabbas sai Abbansu Ma'un sai ya aiko yana son ganinta, tasan tabbas zuwa yanzu labarin abunda ya faru ya riskesa.

Suna cikin haka suka ji sallamar Sakina kamar saukar aradu haka suka ji ta, kamar wacce aka wurgo ta shigo parlon a hargitse fuskarta tasha kuka ta kumbura.

Inna da Humaira basu san lokacin da suka miƙe tsaye ba suna kallon Sakina hankali a mugun-mugun tashe.

Inna saura kaɗan ta saki Ummi dake akan cinyarta tana wasa da zafin nama Humaira ta kai inda Innar take ta amshi Ummi wacce ta firgita ta saki kuka.

"Sakina kece a cikin daren nan?, mi kuma ya sake faruwa ne?, ni yau na shiga uku".

"Baki shiga uku ba Inna dan Allah ki daina faɗa".

Faɗin Sakina tana ƙara sakin kuka.

Sakina tana kuka ta sanar dasu abunda Aunty Sakina tayi mata na cin mutumci.

"Wai dama fitowa ta kema kika fito?".

Faɗin Humaira tana kallon Sakina.

"Ai kina fita daga gidan naji muryar Kawu Ismail na cewa nima na fito na bi ƴar uwata mubar masu gida tunda babu gadon ko ɗaya daga cikinmu, ko zaman gidan ya zame mana kamar kurkuku".

"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Allahumma ajirni fi musibati".

Kawai Inna ta shiga mai-maitawa.

Inna zatai magana Ma'u ta faɗo parlon, turus taja ta tsaya ganinsu a tsaitsaye tare da Sakina rake da jakar kaya a hannunta, lokaci ɗaya zuciyar Ma'u ta bata cewa itama ta dawo gidan nan ne da zama su za'a raina ma wayo a wani ce hutu suke zuwa.

"Hmm Aunty kizo keda Humaira inji Abba".

Tana ƙare maganar ta juya ta fice daga parlon.

"Kinji ko?, to ga abunda nake gudu nan zai faru, sai ki zo muje ai duk ke kika ja koma miye Humaira".

Faɗin Inna ta amshi Ummi tana miƙama Sakina ita suka fice a tare da Humaira suka bar Sakina a cikin duhu, miye yake faru a nan kuma?.

Sakina ke tabbayar kanta a zuci........

*TSANIN ƘADDARA*

*©Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 6

*Unguwar Hayin Ruwa, Dutsanma local government Katsina State Nigeria*

A hankali zata shiga cikin gidan, taji wata Muryar, wani matashi yana tsaida ita.

"Haba Bilkisu tun ɗazo nake tsaida ke amma kina ji kinƙi ki tsaya".

Bilki ta ɗan tsaya gabanta na ɗan faɗuwa kaɗan ta dube sa cikin sanyin jiki ta ce.

"Dan girman Allah Sule kayi hakuri ka dai min magana, yanzu idan wani ya ganni yaje ya sanar da ƴan gidamu kasan miye zai faru da ni kuwa?, kayi hakuri kawai ka daina min magana".

"Nifa Bilkisu auranki nake son nayi".

Wani irin sanyi Bilkisu taji har cikin ranta, dan yanzu ba abunda take buri sai na taga tayi auran itama ta bar wannan gidan na Mahaifinta, gidan da ya zame mata kamar kurkuku, to amma duk wadda zai zo auranta maganar bata kai wajan Babanta sai taga ta nemi saurayin nan ta rasa ya daina kulata ya daina zuwa inda take, tun bata ɗaukar wani abu harta zo ta fara zargin kanta, ko dai bata da hali mai kyau ne?, ko kuwa aljanu ne suka aure ta?, tunda kusan Sule shine na kusan biyar koma fi, Bilkisu tana da kyau na nunawa a sa'a dan kusan kamaninta da Humaira sosai suna kama, sun biyo Inna wacce ta kasance tsatson Fulani ne shi yasa take da wani irin kyau haɗe da diri irin wadda maza suka fi so yafi ɗaukar hankalinsu da tunaninsu a jikin Mace.

"Kinyi shuru Bilkisu?, ki bani dama mana".

Ta ɗago kanta zatai magana kawai kamar ance ta kalli ƙofar gidansu idonta ya faɗa cikin na Binta data wani tsaya ta rungume hannunta a ƙirji, tana jefa mata wani irin kallo na tsana da wani irin jin zafin ta.

"Kai Sule wadda na daɗe ina burin ace ya so ni?, shine wancar baƙar dagar zata shiga ta fita yazo har ƙofar gidan nan yana mata magiyar ta soshi?, Sulen dana sani da girman kai baya kula ƴan matan unguwar sai ƴan gayu wadda suke ji da kansu".

Binta ta faɗa a fili zuciyarta na wani irin tururi na baƙin ciki da wani irin zallar kishin Bilkisu daya gama rufe mata zuciya.

Ba ƙarya ta faɗa ba Sule irin samarin nan ne masu mutuƙar tsafta da gayu da kame kansu ga faɗawa harkar kowacce Mace, sana gashi da kyansa shima dai-dai misali tunda bazaka taɓa kallonsa kai tsaye kace mummuna bane.

Binta bata ce komai ba ta juya tayi cikin gida haɗe da sakin kwafa.

Ba abunda ƙirjin Bilkisu yake sai bugawa tana faman zare ido waje wani irin miyau ta haɗe, sai zufa data shiga keto mata a jiki, sai ka ce marar gaskiyar da aka kama.

Gaba tayi tana jin yadda Sule ke mata magiyar ta tsaya ta basa amsa, amma kwata-kwata hankalinta da tunaninta yana gidansu, akan abunda zata je ta iske.

"Na rantse da Ubangijin sammai da ƙassai Inna idan na yarda Bilkisu ta auri Sule Allah ya tsine min".

"Wai mi kike cewa ne Binta wacce Bilkisun ma shin kike faɗa?".

"Ta nan gidan mana muna da wata Bilkisu ne bayan ita?, shegiya munafuka".

Tashi tsaye Inna tayi ba shiri da a dubi Binta cike da mamakin maganarta ta ce.

"Lallai wuyanta ya isa yanka ita harta kai ta rinƙa tsayawa da samari a ƙofar gidan nan ko shakka babu da tsoro?, to sha kumurinki Binta zata zo ta iske

5 / 40