Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
kuma harda Yaran da aka haifa ba tare da aure ba, harda ma wani shigar cikin a lokacin data gano gaskiyar, ƙwaƙwalwarta ta kasa yarda ta kasa ɗaukar abun, shi yasa har ciwon damuwa ya so kama mata Ƴa, da kyar da suɓin goshi aka samu Mansura ta dawo hayyacinta, sai kuma ace duk wannan bai isa ba abunda akai mata ba?, sai an ƙara mata da wani baƙin cikin kuma?.
Har suka isa gidan ita da Abbu da driver gidan nasu ya kawo su bata ƙara magana ba, dan baƙin ciki ma ya isheta ita kam.
************
Tashi yayi a hankali yana ɗaukar wayarsa ya danna number Ammi bayan minti kaɗan ta ɗauka.
"Ki haɗo min coffee yanzu ina jira".
Ya faɗi hakan yana yanke kiran.
Yana yanke kiran yaji sallamar su Abbu da sauri ya ɗago kansa yana kallon ƙofar parlon nasa.
Su ɗin ne suka shigo da Ummu dake biye dashi a bayansa.
Da sauri Abbi yaje inda Abbu yake suka gaisa a mutumci kamin ya nuna masa wajan zama ya zauna sai fara'a yake, dan akwai wani sabo mai tsananin gaske dake a tsakaninsu ciki harda na kasuwancin su.
Abbi a ƙasa ya zauna dan yana bashi girma sosai fiye da tsammani, Ummu ma a ƙasan ta zauna kanta na ƙasa amma a ƙasa-ƙasan tana bankama Abbi harara tana jin wani bala'in haushinsa na kamata.
Bayan sun sake gaisawa Abbu yayi gyaran murya ya ce.
"Sai naga Yarinyar nan kawai taje min gida da wata magana ta daban, shin kaine ka ce mata taho gida ko kuwa na kasa gane abun naku?, na tabbaye ta ita ta ƙi bani amsar da nake son ji".
Ɗagowa Abbi yayi yana kallon Ummu data ɗago itama, ganin kallon da take masa yasa shi sakin murmurshi kaɗan yana dawo da dubansa akan Abbu a nitse ya ce.
"To gaskiya Abbu ko kaɗan ma bansan ta tafi gida ba, bada yawu na ba, ni bance ta tafi ko ina ba".
Abbu ya dawo da dubansa akan Ummu da kanta ke a ƙasa ya ce.
"Kinji abunda ya ce, haka ne?".
Ɗaga kanta kawai Ummu tayi tana jin kamar tayi bindiga tsabar yadda ranta ke mata zafi.
"To mi yasa zaki kwaso ƙafa ki taho gida kuma Mijinki bai sani ba?, wato ku dai Mata na yarda ƙaramin tunani ne daku. Ni tazo min da wata maganar dana kasa fahimtar ta, so nake ka ƙara min jawabi da bakin ka naji".
Gyara zama Abbi yayi ya fara gaya gaya masa duk abubuwan da suka rinƙa faruwa har kawo yanzu tun farkon zuwa ta kawo masa maganar haɗa auran Maryam da Hammad, dace mata da yayi shima ga haɗinsa na haɗa Intee da Hammad ɗin.
"To duk naji bayaninka, kuma na gamsu, babu abun aibu ko abunƙi a nan ciki, dan haka ni kaina na baka goyan baya ɗari bisa ɗari".
"Amma Abbu amin adalci kenan?, shi ya daɗe yana cin zalina amma ba'a taɓa ganin laifinsa ba sai ni tsakani da Allah?".
Ummu ta ƙare maganar tana sakin wani irin kuka mai cin rai.
Abbu cikin kakkausar murya ya ce.
"Karna sake jin muryarki a nan Mansuraaaa, wato mijin naki kike faɗama haka?, kuma a gaba na?, haka muka koya miki ne?".
Da sauri ta shiga girgiza kanta tana jan majina saboda har lokacin hawaye take tana shashshakar kuka ranta a jagule.
"To daga yau karna sake jin haka a bakinki, karna sake jin cewa mijinki yana faɗa kina faɗa kinji na gaya miki wallahi?. Sana idan har Muhammad bazai auri Intee ba to kema babu dalilin da zai yarda da zabinki na haɗasa aure da Maryam".
Muryarta na rawa ta ce.
"A'a Abbu ayi hakuri na amince".
"Da dai yafi miki kyau, kuma ni babu abunda kikai min gashi nan Mijinki shine zaki bawa hakuri amma bani ba".
Abbu ya faɗa yana tashi tsaye yayi sallama da Abbi a gaggauce ya wuce ko kallon inda Ummu take baiyi ba, har waje ya rakasa ya tafi kamin ya dawo parlon ya iske Ummu tana kuka kamar wadda aka ce ma mutuwa zatai.
Suna haka saiga Ammi ta shigo Parlon ganin Ummu na kuka yasa ta jikinta yayi mugun sanyi, tana aje Coffee ɗin zata juya ta fice taji saukar Muryar Ummu na faɗin.
"Saiki tsaya ai burinki ya gama cika Nuratu".
Ummu ta faɗa tana tashi tsaye idonta jawur tana kallon Ammi ido cikin ido data tsaya zuciyarta na bugawa sosai.
"Mansuraaaa!".
Abbi ya kira sunanta cikin kakkausar murya.
Bata san lokacin data ɗaga masa hannu ba ta ce.
"Alhaji ka barni dan Allah".
Ta faɗa tana sake duban Ammi dake tsaye kawai.
"Na ce burinki ya cika Nuratu zaki idasa mallake min Ɗana da kuma mijina, amma ki sani gaskiya fere take bata ƴaƴa, kuma nida ke mu zuba mu gani".
Tana faɗar haka ta juya fuuuu kamar zata bangaje Ammi ta fice daga parlon.
Tana fita Ammi ta shiga sauke lumfashi kaɗan-kaɗan kamar wacce tayi gudu zuciyarta na bugawa sosai, ta dubi Abbi dake tsaye shima yana bin inda Ummu tabi da kallo kawai.
"Abbin Yara ka gani ko?, kaga abunda nake gudu ba?".
"Ba abunda zai faru Nuratu sai alkhairi".
"Amma Abbin Yara shi kansa Mahaifin Intee mi ya kamata?, ya kamata aje neman aurenta ne a wajansa ko ya ka gani?, ni wallahi kwata-kwata abun ne ya gama fice min a rai".
"Babu inda za'aje neman auran Intee, ko kin manta abunda ya ce a baya ne?, da bakinsa yake faɗin cewar Intee ya sallamata ga duniya ba Ƴarsa ba ce yanzu, Ƴata ce dan haka ni ne wadda zai aurar da ita..........
Chapter 27
*SAKINA POV*
Yau tunda ta tashi jikinta a mugun sanyaye yake ta rasa dalili, ga Sadeeq dake ƙara manne mata a jiki, dan yau da safe ma sai da ya matsa mata yayi abunda ta ɗauka shikenan bazai ƙara nema ba, ta rasa dalili kuma ta basa kanta lokacin da bata shirya hakan ba, sai da komai ya lafa ta tasa shi gaba tana masa kuka, yana tayata da share hawaye shima yana yin kamar zaiyi mata kukan.
Rungume yake da ita tun safen da abun ya faru bayan sunyi wanka ko kaɗan basa son matsawa daga inda suke manne da juna.
Motsin da taji ne a Parlo yasa ta miƙewa ba shiri zuciyarta na tsalle a ƙirjinta dan haka kawai take mugun fargabar dawowar su Mome ɗin Part ɗin.
"Kina ina wai?".
Faɗin Huda dake shirin shigowa bedroom ɗin.
Da wani irin sauri Sakina ta tarbeta tana faɗin.
"Gani nan ranki ya daɗe abinci ne na gama bawa Ƴallaɓai Sadeeq".
Wani kallo ta jefa mata tana ƙare mata kallo sosai kamin ta wani juyo zata koma zuwa parlon ta ce.
"Saiki fito ai ga Doctor Halisa ta iso zata gwada ki sai ki shirya".
Gaban Sakina ne ya ƙara yankewa ya faɗi bata san lokacin data sa hannunta tana dafe saitin zuciyarta ba, ido waje take tabbayar kanta.
"Mi yasa tun jiya bata ɗauki wani mataki na ƙare kanta bane?, yanzu idan akayi Awo aka gane tana da shigar ciki fa?, zubar fa dashi zasu sa ayi ko?".
Da wani irin sauri ta shiga girgiza kanta hawayen da bata shirya zubowarsu ba suka shiga zubo mata, zuciyarta na tsintsitsinkewa ta fara taka ƙafarta zata nufi Parlon sai kuma ta tsaya tana waigowa inda tabar Sadeeq sai taga bacci ne ya fizgesa.
Wata ajiyar zuciya ta sauke tana sake zuba masa ido sosai take kallonsa kallo irin wadda bata taɓa yi masa shi ba.
A hankali taji hawaye na sake turowa a cikin idonta suna zubowa a kumatunta, da sauri tasa hannunta ta ɗauke su tana juyowa ta yi hanyar barin bedroom ɗin tana nufar parlon.
"Ke uwar mi kike a bedroom ɗin nan da har Huda zata je kiran ki sai kinga dama kike fito?".
Faɗin Mome dake tsaye da har zata je zuwa cikin bedroom ɗin dan sunga shuru bata fito ɗin ba sai kuma gata ta fito a wani irin yanayi na zallar fargaba da tsinkewar zuciya, kwata-kwata bata wani gane komai zuwa yanzu neman mafita kawai take ita.
"Ba magana ake miki ba ne?, ko akwai abunda kika taka ne Sakina ban sani ba?, Ohh ko dai da gasken ne ciki kika bari wannan nakasashshen ya ɗirka miki shine har kike ganin kin isa zaki fara gogawa damu koba haka ba?".
Da wani irin sauri ta girgiza kanta tana yin ƙasa da kanta bakinta na rawa ta ce.
"Na rantse da Allah abunda kuke zargi ba haka bane?".
"Dalla yimin shuru ai yanzu gaskiya zatai halinta idan ma kina da itan ai za'a gani ne".
Faɗin Huda dake mata wani banzan kallo itama.
Mome ta dubi Doctor Halisa dake haɗa wani abu a cikin kwalba tana aikin tana ƙare ma Sakina kallo sosai dan ita kanta tun kan ta auna ɗin ta riga da ta gama gano yarinyar nada shigar ciki ƙarami wadda ƙila bai wuce wata huɗu ma.
"Doctor Halisa gata nan ya kamata ayi mai yiwuwa".
Amsawa da kai kawai Doctor Halisa tayi tana aje komai ta dawo da dubanta inda Sakina take tsaye wacce ke faman share wata uwar zufa jikinta har rawa yake na zallar tashin hankali da fargabar abunda zai iya faruwa.
Zamu shiga daga ciki zata yo fisari ta bani na fara auna dashi kamin na ɗebi jininta shima.
"Kiyi abunda ya dace kawai ba sai kin gaya mana ba ai aikin ki ne".
Faɗin Mome tana nuna mata hanyar bedroom ɗin. Saboda sunyi bala'in yarda da ita dama ta sani, shi yasa kawai ya ɗauki duk wasu kayan aikin da zatai amfani dasu zuwa bedroom ɗin.
Gaba tayi Sakina na tsaye hankalinta a tashe bata da ma kwarin gwaiwar bin bayan nata, yasa Huda ta watsa mata wani irin kallo yasa Sakina ɗan zabura tana juyowa tabi bayan Doctor Halisa zuwa bedroom ɗin domin zuwa toilet tayo fisarin.
Tana binta tana sake-sake neman mafita addu'a kowacce iri ce yowa take a zuciyarta da domin Allah ya rufa mata asiri kawai.
Suna shiga Bedroom ɗin Doctor Halisa taga Sadeeq dake kwance saman gado har lokacin baccinsa kawai yake hankali kwance zata dawo da dubanta akan Sakina kawai taga Sakina ta zube a ƙasa tana kamo ƙafafunta hawaye kwance akan fuskarta ta ce.
"Dan girman Allah Doctor ki rufa min asiri ki ce masu banda wani ciki a jikina, wallahi Allah na sani tun kan ki auna ni zaki iya gane cewar ke ina da shigar cikin, tunda ke aikin ki ne, Allah ina son cikin nan ko shi na tsira dashi ina son Uban cikin nan, amma nasan da wuya na iya mallakar shi gaba ɗaya, to gara na tsira da koda jininsa ne zan iya rayuwa a haka cikin farin ciki koda Y Sadeeq baya tare dani, amma yanzu idan aka ce za'a rabani da Ya Sadeeq da kuma wannan gudan jinin nasa dake a jikina wallahi Doctor mutuwa kawai zanyi, ki rufa min asiri kamar yadda Allah ya rufa miki".
Wani kalar tausayi ne ya rufe Doctor Halisa ganin yadda Sakina ke roƙonta tana kuka mai tsuma zuciya.
Bata san lokacin data saka hannunta ta ɗagota ba tana zaunar da ita akan gado itama ta zauna daga gefenta tana kallonta ta ce.
"Ko baki roƙe ni ba dama bazan nuna masu cewar kina da shigar ciki ba, da wannan ƙudurin na zo gidan nan dama yau. Burinsu shine idan har na auna ki na gano dimi-dimin kina da shigar ciki to nayi miki allurar zubar dashi a nan take ya zube ba sai anje ko ina ba, nasha yi masu aiki irin wannan mai matuƙar hatsari amma yanzu na tuba bazan sake basu haɗin kai ba. To amma fa akwai matsala gaskiya".
Da wani irin sauri har bakin Sakina na kyarma wajan furta.
"Matsala kuma tami ce dan Allah?".
"Hmmm".
Kawai Doctor ta ce kamin ta sake kallon Sakina sosai a hankali maganarta kamar wacce ke yi mata raɗa ta ce.
"Idan har zaki zauna a cikin gidan nan to tabbas kin san dole wata rana su gane kina da ciki na gasken-gaske, tunda shi ciki ɗan duma ne fitowa yake ba'a iya ɓoye shi".
"Amma Doctor ni dama guduwa nake son nayi, tun kan yayi girman da zasu iya ganewa".
"Idan kin gudun kije ina?".
"Zan tafi wajan Mahaifiyata mana ai basu san inda nake ba".
Girgiza kanta Doctor tayi tana sake riƙe hannun Sakina ta ce.
"Idan har zaki gudu ki zauna cikin ƙasar nan to duk inda kike dole ne ma wata rana su gano inda kike. Sana ba naji labarin wata ƙanwar Mahaifiyarki bace tayi miki hanyar zuwanki gidan nan bane?".
Ɗaga kai tayi tana bata amsa da kai, zuciyarta na sake shiga halin tsoro ina zata je idan ba nan ba?, duniya sata shiga ne?, ina zata fara nufa idan ma ta shiga duniyar?, ina taga kuɗin barin ƙasar nan?.
Abunda take tabbayar kanta kenan a zuci, maganar zucin ce ta katse jin maganar Doctor na sake faɗin.
"To tunda kuwa sun san wacce tayi dalilin kawo ki nan to a ta kanta zasu fara, bawai zasuyi mata barazana bane a'a, kuɗi ne zasuyi mata tayinsu masu mugun yawan da mutum mai ƙarfin imani ne kawai idan yaji su zai iya tsalle ke su, amma mudun mutum mai bala'in son kudin ne to tabbas nan take jiki na rawa zai amshe kuɗin ya faɗa masu dukkan abunda suke son ji daga gare sa, a lokacin dama bai san ya faɗa ba. Mutanen nan da kike gani idan na ce zan baki labarinsu yanzu zamu iya ɗaukar lokaci mai tsawo ne, ki bari sai mun samu lokaci zaki ji tarihin gidan nan gaba ɗaya. Amma fa tabbas zan yi duk yadda zanyi inga kin sake dawowa a cikin gidan nan a matsayin Matar Sadeeq kuma wacce yake mugun so a cikin hayyacinsa".
"Amma Doctor ta yaya duk hakan zai faru. Kuma Aunty Sakina tabbas idan har suka nemo ta, suka bata wasu ƴan kuɗaɗe babu abunda zai hanata nuna masu inda nake?".
"Zan ɗauke ki daga cikin gidan kowa bai sani ba, kinga yanzu zan auna ki na ce baki da shigar ciki ƙarami, washe gari cikin dare nasan duk wata hanya da zan shigo gidan nan domin na ɗauke ki ta hanyar da babu mahaluƙin da zai san ni ce na ɗauke ki, sai dai su tashi suga bakya nan. Zan tafi dake inda babu ɗan Adam ɗin da zuciyarsa ko tunaninsa zai iya bashi kina tare dani ne a wajan, zan riƙe ki har sai kin raini cikin nan kin haifesa Yaron ko yarinyar sunyi girma kamin mu fara shirin tunkararsu da jinin da suke ganin kamar shine tonuwar asirinsu. Sana kinga kin ce Auntyn nan taki Sakina nada son kuɗi to zata iya jefa ku a halaka dage ke har mahaifiyarki dake can zaune ƙalau".
Ba abunda zuciyar Sakina take sai bugawa a ƙirjinta, a hankali ta waiga tana kallon fuskar Sadeeq ɗin da taga yayi mata wani irin bala'in haske kyan nan nasa kamar sake ƙara masa shi ake.
Muryar Doctor Halisa ce ta sake ji tana cewa.
"Tabbas idan har ya tashi yaga bakya nan, ya neme ki yaga baki nan a ko ina, to komai na iya faruwa, ban san dai abunda zai farun ba, saboda irin sabon da kukai dashi to zaiyi wahala komai nasa bai dawo baya ba".
"Doctor komai fa kika ce?".
"Tabbas komai, dan a yanzu naga alamar yana samun sauƙi sosai ba kamar da ba, da nake zuwa na iske shi a cikin halin ƙazanta da ɗauɗana haɗe da ciwo kamar sake ƙaro masa shi ake".
Da wani irin sauri Sakina ta shiga girgiza kanta tana faɗin.
"Doctor bazan iya tafiya na barshi a cikin Wannan halin ba".
"Dole ne idan har kina son gudan jininsa ya rayu tare da ke wata rana ki nuna masa shi ki ce ga gudan jininsa ga ɗansa wadda kuka samu tare, to dole sai kin matsa daga inda yake hakan kaɗai zata sa gudan jininsa kasancewa a raye".
Wasu kalar hawaye masu zafi suka shiga zarya akan fuskar Sakina kallon fuskarshi kawai take.
Da sauri Sakina taga Doctor ta miƙe tana faɗin.
"Mun daɗe a bedroom ɗin nan ya kamata muje na gaya masu abunda muka shirya faɗa masun, kar kuma su fara zargin daɗewar tamu shi yasa ma na shigo da kayan aikin a nan, cewa zanyi masu aunawar na tsaya ne ya ɓata mana lokaci".
Itama Sakinar miƙewa tayi jiki a sanyaye tana bin Doctor Halisa da kallo, Doctor Halisa harta fara tafiya zata nufi Parlon ta ɗan tsaya ta ce.
"Ki tabbatar kin haɗa kayanki da duk abunda kike buƙata zuwa dare, zan riƙe ki ne kawai domin Allah, zan kuma taimaka miki ne saboda na goge laifin dana daɗe ina aikatawa, ko hakan zaisa Allah ya dube ni ya yafe min, duk dai Allah baya yafe cutar da wani har sai shi wanin ya yafe makan. Sana karki sake kiyi abunda zasu iya fahimtar wani abun kike shiryawa, domin wa'innan mutanen da kike ganinsu suna da wani irin haɗarin da zakiyi mamakinsu ne a lokacin da na baki labarinsu gaba ɗaya, ke dai kawai sai an samu zama zaki sha labari".
Tana faɗar haka tayi saurin wucewa zuwa parlon.
Tana fita Sakina ta zube a ƙasa tana sakin wani irin kuka mai sanyi tana kallon fuskar Sadeeq shi kawai take tausayi a yanzu, shi kawai take ji a yanzu, mi zai faru bayan tafiyarta?, mi zai iya kasancewa dashi bayan bata nan tare dashi?, idan ya dawo cikin hankalinsa zai tuna da ita ne?, wacce irin rayuwa zata je tayi tare da Doctor Halisa ne?, mi zata gaya ma abunda zata haifa?. Hawaye ne suka sake zubo mata masu zafi tana tausayinsa da ita kanta da kuma abunda zata haifa ɗin.
"Doctor yaya dai naga fa kun jima a bedroom ɗin?, ko gardama tayi miki ne?".
Doctor ta wani maze tana zama akan kujera ta ce.
"Ko kaɗan babu gaddama kawai fitsarin ne da