Tsanin Kaddara Complele Book Zahra Star.docx

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   26 / 40

75K to 78K   out of 118.4K words

irin jiri ne ya fara gani yana gani dishi-dishi nan take kamin su tsaida matsayar tsaidashi daga abunda yake yi ɗin har ya sume.

Da gudu su duka suka nufi inda yake jiki na rawa Mome ta shiga lalubar wayarta tana danna number Doctor Halisa, sai dai a kashe take ta gwada ya kai sau nawa amma dai a kashe, jiki na rawa ta canza akalar kiran da wani Doctor da suke gani dama domin ciwon Sadeeq ɗin amma a baya suka gujesa saboda irin magungunan da yake basa yana ɗan samun sauƙi suka canza Doctor dan kar ma ya ci gaba da ɗorasa akan magani ya warke shine ita Momen taje aka bata wasu magunguna marassa tushe masu ƙara rikita ƙwaƙwalwar mutum take basa a matsayin magani, shi yasa ƙwaƙwalwarsa take ƙara rikicewa sosai a rasa gane kansa, wadda bai san abunda ke faruwa na sai ya rantse da Allah ko aikin asiri ne akai ma Sadeeq ɗin.

Tana kiransa ya ɗauka yana mamakin kiran nata dan tunda suka raba jaha dashi akan sun canzama Sadeeq Doctor mai kula dashi basu sake nemansa ba.

Bakinta na rawa ta shiga sanar dashi abunda ke faruwa harda su shirga masa ƙaryar da Sadeeq ɗin ya warke amma yau kusan wata ɗaya ciwon nasa ya tashi shine yau suka tashi yana buga kanshi da bango likitar dake kula dashi ce basu sami wayarta ba shine taga bari ta kira shi kar Sadeeq ɗin ya shiga wani hali.

Shima hankalinsa tashe ya amsa da cewar gasu nan zuwa gidan yanzu nan dan sosai yake ganin mutumcin gidan da ma mai gidan wadda har lokacin baya ƙasar bai kuma san abunda ke wakana a cikin gidan nashi ba, kuma hakan ya samo asali ne wajan Mome dake binsa har inda yake shi yasa idan ta ya tabbayeta akwai matsala take ce masa babu wata matsala a gidan, ga ƙarin an kauda hankalinsa daga Yaron da yake ma so ada can baya kamar ransa, anyi masa wani irin mugun abu da kwata-kwata baya ma ko tunosa dai-dai da rana ɗaya sai idan an samu wata ran ya tabbayeshi daga nan sai a shafe lokaci bai sake tabbayar tashi ba......

Chapter 31

*INTEE POV*

"Subhalallahi Intee ki zauna a hankali neman faɗowa fa kike?".

Faɗin Ammi data yi saurin tarbo Intee a jikinta a yanayin yadda ta shigo mata parlon ya tabbatar da akwai wani abu a ƙasa.

Zama Intee tayi a kusa da Ammi sosai tana sake shigewa jikinta tana sauke lumfashi akai-akai zuciyarta na wani irin zafi tana sake tunano yadda daga shigowarta gidan ta ci ƙaro da Ummu na gaf shigewa Part nata ta tsaida ita tana cewa.

"Ke dakata ƴar marassa kunya dangin masu nacin tsiya wa'inda suka gado naci".

Dakatawa Intee tayi kanta a ƙasa tana shirin gaida Ummu ɗin tayi saurin dakatar da ita wajan faɗin.

"Riƙe gaisuwarki Malama. Gaya miki zanyi duk wani asirin da uwarki keyi akan Ɗana da mijina na ɗan lokaci ne, amma fa ki sani zaki auri Ɗana ne kawai amma bazan taɓa sonki ba, bazan taɓa sama auran nan naku albarka ba bada yawu ba, anfi ƙarfina ne amma baccin haka wallahi tallahi ke baki isa auranmin Ɗa ba, amma gaki ga shi nan".

Tana faɗar haka ta juya kamar zata shige sai kuma ta dawo baya kaɗan tana sake kallon Intee kallo irin na zallar wulaƙanci ta ce.

"Idan baccin naci da son asani ba sai ki ba uwar taki shawarar cewa auran Ɗana bai dace dake ba?, amma da yake kema kamar uwar taki ce kamar mayu idan kuka shigo rayuwar mutane sai kunyi masu babban tabo tukunna zaku ji daɗi. Ai ni Alhaji ya kashe ni shida Abbu da har suka dage sai kin auri Ɗana jini na mai asali, kefa babu wadda yasan dangin mahaifinki uban naki ma ana raɗe-raɗin Ɗan Giya ne, aikin banza kawai, mi akai akai da mai shan Giya ai anyi mugun iri dai har abada ba'a canza ma tuwo suna".

Tana ƙare maganar tana juya tana sakin wani dogon tsaki tabar Intee da wani irin mugun tabon daya daɗe da dishashewa a cikin rayuwarta, amma yau ta taɓo mata wannan taɓon, zuciyarta zafi take mata idonta ya kaɗa yayi jawur, ba abunda take sai haɗiyar zuciya wani kalar jiri take gani dan haka a hankali a daddafe ta fara takawa tana jan ƙafa zuwa Part nasu tana ganin wani mugun jiri.

"Kinyi shuru Intee mike faruwa ne sai magana nake miki kinyi shuru?, lafiya mike faruwa?, wani abu ya faru ne?, kin fa fara sani cikin damuwa".

Girgiza kanta kawai Intee ta shiga yi hawaye masu zafi suka shiga zubo mata tana cewa.

"Ammi why da Abbana zaiyi min haka?, mi yasa zaima rayuwata babban taɓon da har zuwa yau yake bibiyar rayuwata?, mi yasa mutane da dama suke jifata da mugun lafazi akan abunda Mahaifina ya akaita ne a baya?, shin Ammi ni na aikata laifin ne?, da har mutane zasu rinƙa jifata da mugun lafazi duk akan abunda shi ya aikata?, Ammi zuciyata zafi take min Abba ya cutar da rayuwata".

Da sauri Ammi ta toshe bakin Intee tana girgiza mata kai idonta sunyi jawur itama, tama kasa magana jawo Intee ɗin kawai tayi ta sake rungumeta a jikinta, babu wacce taja mata duk wannan a cikin rayuwarta data Ƴarta sai Mahaifiyarta wacce ta kawo ta duniya, tana jin wasu zafafan hawaye na sakko mata, ɗaga kanta tayi sama tana kallon rufin parlon tana hasko rayuwar da sukai a baya wacce ta kasa gogewa har yau a cikin ƙundin ƙaddararta..

*WAIWAYE, SHEKARATA 1990*



*Sabuwar Abuja Rimaye, Kankia Local government Katsina State Nigeria*

"Inna dan Allah ki daina mitar nan haka, komai fa hakuri ake yi a rayuwar nan".

"Idan kike sake kika sake samin baki Sadiya na rantse da Ubangiji sai na zo na faffasa miki baki yanzun nan".

Da sauri Sadiya ta toshe bakinta tana tashi daga inda Inna take ta koma kusa da Nuratu dake duƙe a ƙasa tana hawaye, rungumeta tayi tana ɗan bubbuga bayanta.

Inna ta waigo inda suke tana faɗin.

"Aikin banza kawai, idan ma zaki fitar da miji ki fitar tun muna mu biyu, domin wallahi daga ke har ƴar uwarki na gaji da ciyar da ku wallahi na gaji da riƙe kun da nake yi, kamata yayi ace izuwa yanzu na fara hutawa nima, kamar kowacce uwa data samu ƴaƴa a duniya, amma ku duka baƙin jinin Mahaifinku da baƙin talaucinsa ya shafe ku, ya mutu ya barni daku da ɗaunayi daku, dan haka wallahi na gaji, idan har baki samo miji a cikin wannan lokacin ba to duk wadda na samo miki ko mutuwa zakiyi saifa kin aure sa".

Wani irin baƙin ciki ne ya cika zuciyar Nuratu da Sadiya a tare suka ɗago suna kallon Inna dake masifa tana yi har bakinta na kunfa sai mai-maita abu ɗaya take tana mita, ba tun yau take damunsu da irin wannan zantukan nata ba, sosai abun ke damunsu dan har ya fara tasiri a cikin ransu, kwata-kwata zama da Innar ya fara gundirar su, dan ita kanta Nuratun ji take koma waye ya fito zata iya auransa kota tashi daga wajan Innar abun ya fara damunta sosai dan har yana son sakata ta fara kamuwa da ciwon damuwa.

Wasu irin hawaye masu raɗaɗi ne suka shiga sake zuboma Nuratu tana shashshakar kuka tama kasa cewa komai sai Sadiya da tayi ƙarfin halin cewa.

"Haba Inna kina yin abu sai kace ba kece kika kawo mu duniya ba, Inna kifa san......

Bata lura da tashin da Innar tayi ba sai dai taji an wanketa da wani irin kyakkyawan mari mai shiga jiki, da wani irin mahaukacin sauri ta saki Nuratu dake jikinta tana dafe kumatunta tana bin Inna da kallo dake tsaye akanta tana wani irin huci kamar Zakanya.

"Na kusa dawowa ta kanki ne ai Sadiya, idan baki daina samin baki ba zan zubar miki da haƙora wallahi na faffasa miki bakin nan na rashin kunya. Nayi danasanin auran ubanku mai ƙashin tsiya wallahi".

Zata sake magana Nuratu tayi saurin rufe mata baki tana girgiza mata kai da sauri taja ta ɗaki suna bar mata wajan.

"Kibarta mana ta ci gaba da gayan magana marar kunyar banza".

Basu tsaya jin sauran faɗan nata da baya ƙarewa ba suka idasa shigewa ɗakin nasu.

Suna shiga Nuratu tasa hannunta tana share hawayen dake zubo mata tana cewa.

"Haba Sadiya kin san abunda kike ƙoƙarin yi kuwa?".

"Amma....."

"Kinga Sadiya koma miye tayi mana bai kamata ki tsaya kina sa'insa da ita ba, ko banza ita ɗin Mahaifiyarmu ce, ita ce ta kawomu duniya, kinga ko ta gama mana komai, ke koda saka wuƙa tayi akan wuyanmu ta yanka bai kamata ki ɗaga kai kiyi mata magana ba, ta rigada ta gama damu tunda har ta haifemu, iyaye sun wuce komai da kike tunani, kawai mu Allah ne ya jarabce mu da samun uwa irin Inna wacce kwata-kwata bata da godiyar Allah a duk irin halin data tsinci kanta a ciki, a haka zamuyi hakuri mu rungumi ƙaddararmu wata rana komai zai shige".

Wasu hawaye ne Sadiya taji suna zubo mata itama ta ce.

"Amma Aunty Nuratu anya Inna ita ce asalin wacce ta haife mu kuwa?, yaya za'ai ace uwa ce kema ƴaƴan cikinta haka nan".

Murmurshin daya fi kuka ciwo Nuratu ta saki tana faɗin.

"Har yanzu Sadiya akwai sauran yarinta a tattare dake, amma Inna da kike gani ita dai ce Mahaifiyarmu da kike ganinta gata nan, kawai na ce miki mu jarabawarmu a nan Allah ya jarabce mu ta samun uwa wacce bata ganin abunda Allah yayi mata ni'ima ce, samun mu da tayi ma da ace wata ce zata gane ba ƙaramar ni'ima Allah yayi mata ba, amma ita gani take kamar mu ɗin wani nauyi ne da aka tafi aka barta Mahaif.......

Saurin yin shuru Nuratu tayi jin tashin maganar Inna tana cewa.

"To ƴan ɗaki wadda ɗaki ya aura, Maza-maza ku fito ga wanki nan makwabta sun kawo a fito ayi masu wanki, dan na rantse na gaji da ciyar daku da nake yi gara na fara neman sana'a daku, tunda baƙin jini dai an gama kwaso shi wajan gyatumi".

"Kinji abunda take cewa ko Aunty Nuratu, Inna idan wani ya ga yadda take mana cewa zaiyi kishiyar Mahaifiyarmu ce fa, dan Allah miye mu kaima Inna ne a duniyar nan data tsane mu haka muda Mahaifinmu?".

"Kinga tashi muje karma ta jiyo ki, komai fa zai wuce Sadiya".

"Haka dai kullum kike ta faɗa Aunty Nuratu amma kamar komai ɗin bazai wuce ba".

Ɗan tsayawa Nuratu tayi tana ƙaƙalo murmurshin dole tasa hannunta akan kumatun Sadiya ta ce.

"Ki daina faɗar haka Ƙanwata kinji, komai na rayuwa da kike gani ba madauwami bane, Mutum ma da kansa yake goshewa a daina jin labarinsa bare abunda ke faruwa a tsakanin mutanen, wata rana zaki ce na faɗa miki komi da kike gani nan zai wuce ne kiga sai tashin zance".

"Wai baza ku fito bane?, ko sai na zo da kaina na fito daku?".

A tare sukai saurin fita tsakar gidan nasu.

Wani kallo ta fara jefa masu kamin ta ce.

"Wato kun raina ni ko?".

"A'a Inna kiyi hakuri".

Zama kawai Sadiya tayi tana turo baki dan ita bata jin zata bada hakuri da Nuratun ke yawan badawa.

"Ke dama ai baki da kunya a cikin gidan nan, da ace ke ce uwata buguna ma zaki rinƙa yi ko Sadiya?".

Shuru Sadiya tayi ta fara jawo kayan wankin da aka kawo masu yawan gaske dama sun saba wani lokacin ana kawo ma Innar irin wannan aikin a biyata kuɗi wani lokacin su taru suyi tare wani lokacin idan ƴan masifar naka su zasuyi shi tana mitar itafa ta fara gajiya da aikin wahala tana ciyar dasu, kusan ko da yaushe sun saba da irin wannan mitar tata, amma basa jure irin yadda take yada maganganu akan Mahaifinsu wadda ya riga da kwanta dama.

"Ai dole ki juya min ƙeya mana marar kunyar wofi, ai Allah Sadiya sai nayi maganinki a cikin gidan nan, zanne ki zanyi wata rana na daka bakin rashin kunyar nan naki".

Ƙunƙuni Sadiya ta farayi ƙasa-ƙasa take cewa.

"To Inna basai ki daka bakin nawa ba mu gani"....

"Mi kike cewa ne?".

"Inna kinji nayi magana ne dama?".

"A'a ban sani ba marar kunya mai ido tsakar ka".

Sake turo baki tayi gaba tana ci gaba da wankinta.

Nuratu ta girgiza kai kawai tana jawo wasu kayan a roba ta fara wankin itama, dan idan sabo ta saba ganin irin haka daga wajan Sadiya da Innar, da wuya Sadiya bakinta yayi shuru haka nan shi yasa kullum take shan duka a wajan Innar tasu........

Chapter 32

Wani duba tayi mata tana sake kallonta sosai Nuratu tayi ƙasa da kanta tana riƙe abunda ke hannun nata tana kallon Innar itama hankalinta a ɗan tashe saboda irin kallon da Innar ke jefa mata.

"Wato ke dai baza ki taɓa jin maganata ba ko?".

"Inna.....".

"Dalla can rufe mini baki ni, shin baki ji Sagir yayi sallama dake bane a waje tun ɗazu?, ko baki san shine na zaɓa miki a matsayin Miji ba?, shine zaki aura, kuma auran nan ba daɗewa ba za'ayi shi".

"Inna mi naji kina faɗa ne?".

Faɗin Sadiya da tayi wuf ta fito waje har tana tuntuɓe tsabar firgice da razani.

"Ubanki na ce kinji ko?".

Sake tamƙe fuska tayi haɗe da turo baki tana duban Nuratu data sanƙare waje ɗaya tana ma Inna wani irin kallo jikinta na rawa saboda lafazin auren da take shiri yi mata da Sagir ɗin da take faɗi.

"Inna yaya za'ai ki ce wai Sagir ne zata aura?, kin manta waye Sagir ne Inna hala?".

"Uban miye yake dashi ba zata iya auransa ba, ita baki ga yadda take bane?, akwai wani galihu da ubanku ya mutu ya bari da za rinƙa wani tanƙaho baza ku auri mutum irin Sagir ba?, ai tama gode Allah tunda shi har ya yarda ya amince zai aure ta".

"Inna shin wai ko kin manta da cewa Sagir Mashayin Giya ne?, harfa Taba yake sha da wiwi, yana zama wajan da ake Caca, gidan da yake zaune irin gidan Gala ne fa gidan Karuwai, sana duk cikin auran da yake yi babu wacce ke iya zama dashi, kowacce Mace neman saki take nema saboda mugun halayar shi, amma Inna ki runtse ido ki ce sai Ƴarki zaki bawa auran mutum kamar Sagir?".

"Sadiya!! Sadiya!!!, kinji na kira sunanki sau biyu ko, ki fita ido na rufe na rantse da Allah, tun kamin na sassaɓa miki kamanni ki fita daga ido, na ce shi zata aura idan akwai ubanda ya isa ya hana hakan ta faru sai na gani ai".

"Wallahi Inna bazata auri mutum irin Sagir ba, kiyi mata adalci mana, kifa sani ƴaƴanta baza su taɓa yafe mata ba, mudun ta auri mutum irin Sagir, zasu tuhumeta ne ta hanyar da yasa bata zaɓa masu Uba na gari ba, miye kike so ta faɗa masu a lokacin da suka tsare ta da tabbayar nan?, mi.......

Tassssss tassssss tatatassssss.

Ƙarar marin da Inna ta wanke Sadiya dashi yasa Nuratu zabura tana toshe bakinta haɗe da runtse idonta da ƙarfi.

Zuciyarta na bugawa da masifar ƙarfi hawaye masu zafi suka wanke mata fuska, ƙirjinta har sama da ƙasa yake na tsabar razanin da tayi.

"Inna dan Allah kiyi hakuri".

Nuratu ta faɗa tana saurin matsawa inda Inna take tsaye akan Sadiya data riƙe ƙuncinta hawaye na zubar mata kallon Innar kawai take ido waje tana hawaye itama zuciyarta na tsalle a ƙirjinta tana haɗiyar zuciya kamar wacce tayi gudun tsere.

"Inna dan kawai na faɗi gaskiya shine na cancanci haka?, Inna.....

"Sadiyaaaaaa!, karna sake jin bakinki a nan wajan kinji na gaya miki?, kina da hankali kuwa Sadiya?, ko kin manta cewa Mahaifiyarmu ce ita?, ki dawo cikin hankalinki mana".

Wani irin kuka Sadiya ta saki tana rugawa da gudu tayi ɗakinsu tana jin muryar Inna na faɗin.

"Eh ai da yake ke tana jin maganarki da ganin mutumcinki ai gashi daga yi mata magana taji, da kin barta wallahi yau da sai na nuna mata Allah ɗaya ne wallahi, saina dawo da ita cikin hayyacin nata, idanma bata cikin hankalin nata. Kuma na yanke hukunci na rantse da Allah sai ki auri Sagir ɗin sai dai ki mutu idan ƴar uwar taki ta auri maƙiyin naki kinji ko?".

Inna ƙare maganar tana ɗaga murya sosai ta yadda Sadiya zata jiyo ta sosai.

Inna ta sake dawowa da dubanta inda Nuratu take tsaye tana goge hawaye idonta sunyi ja sosai, Inna ta ɗan harareta tana faɗin.

"Ki wuce kije maza nasan yana can kofar gida yana zaman jiranki, saura idan kinje kiyi masa halin naki".

Nuratu bata ce komai ba tayi tsaye zuciyarta na tsintsitsinkewa da al'amarin Innar tasu na son zuciya da ƙin gaskiya tana ganinta kuma tasan gaskiyar ce take danne sani tana yin son zuciyarta kawai.

"Zaki wuce ki tafi ne ko sai na ɓata miki rai kema yanzu nan?".

Girgiza kanta Nuratu tayi kawai tana saurin ficewa daga gidan.

Nuratu na fita taja wani irin birki da wani irin bala'in sauri zuciyarta na bugawa da mugun gudu ta dafe saitin zuciyarta tana kallon Sagir da yake tsaye yana layi a bigensa yake ma daga gani yasha ne yayi maƙis abunsa.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Sagir?".

"Nan....nan nn...na'am masoyiya, kikki....kikkinsan fa ina sossonki sosai, dan hakkka zan aure ki".

"Na shiga uku Sagir miye haka kake yi?".

Wata irin ƴar iskar dariya ya saki yana sake lumshe idonsa irin wadda ya bugu sosai na mashayin giya, yana yarfa hannunsa yana layi sosai kamar wadda ke shirin faɗa mata a jiki.

Ja da baya Nuratu ke yi tana kallonsa cike da wani irin bala'in tsoro zuciyarta na bugawa.

"Kikki.. ki matso mannna... Masoyiya ninni ne fa masoyinki".

Da wani irin gudu Nuratu ta juyo ta faɗo cikin gidan nasu tana banko kofar gidan nasu, dan gani tayi yana

26 / 40