Tsanin Kaddara Complele Book Zahra Star.docx

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   4 / 40

9K to 12K   out of 118.4K words

ɗauke Bilkisu da wani marin tana huci ta kamo kwalar rigarta da ƙarfi ji kake keeeet ta yaga rigar gida biyu.

Dama kuma baƙin ciki ne ya cika Binta ganinta da sababbin kaya masu kyau a jikinta.

Bilkisu ta duƙe ƙasa tana sakin wani irin kuka.......

*TSANIN ƘADDARA*



*© Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 4

*House No: 17 Aurora Wrestling Estate Kaduna Nigeria*

Ɗan juyowa Ammi tayi tana kallon Intee dake zaune ta dubi su Hassan dake tsaye suna jiran Ammi domin Abbi ne ya kira yana son ganinsu gaba ɗaya har Intee ɗin.

"Wai Intee ba cewa nayi kisa Hijab ba Abbi ne ke son ganinmu gaba ɗaya ba?".

Intee ta miƙe haɗe da turo baki gaba, itafa wallahi bata so ana sakata duk wata harka ta cikin gidan, amma da tsiya Abbi ke son sakata yana nuna kamar itama tsatson gidan ce, duk da irin wulaƙancin Ummu keyi akanta duk dan ta tuna mata cewar fa bata da gado a cikin gidan.

Bata ce ƙala ba ta je ta saka Hijab tabi bayan su Ammi da suka riga suka fice daga parlon.

Tunda ta fita tsakar gidan masu aiki dake shawagi a harabar gidan suke binta da kallo.

"Ni wai Lare mi ake nufi da wannan yarinyar ne?".

"Kamar ya fa Laure?".

"A'ato baki gani ba Alhaji ke son ganin iyalansa zasuyi Mitin irin na family dake cikin gidan nan gaba ɗaya, amma kinga fa harda su Kaza a cin danƙo".

Lare ta taɓe baki tana kallon yadda Intee ke tafiya cike da natsuwarta wadda suke ganin haka kamar yanga ce take.

"Ai kinga sai wani yanga take tana ɗaukar kanta kamar kowa a gidan nan".

"A'ato tunda uwarta Matar gidan ce dole ta ɗauki kanta wata ce mana".

Wata dattijuwa ce mai ma Ummu goge-goge tazo gifta su Lare ta ɗan tsaya tana kallonsu ganin yadda suka maida hankali gaba ɗaya wajan gulmar Intee da Mahaifiyarta, ta dube su cike da takaici ta ce.

"Ku dai kunji kunya wallahi ace baku da aiki sai gulmar baiwar Allahn can Mace mai kirki da sanin ya kamata?, kufa sani kune da faɗuwa tunda naman jikinta kuke ci, kuma ranar lahira sai kunyi hisabi a gaban Allah, wallahi rashin aikinyi kesa mutum ya zauna ya rinƙa gulmar waninsa, kuyi abunda ke gabanku yafi ku zauna kuna gulmar wani tunda zunubi ne kuke ƙara dafkama kanku akan naku zunubin dake danƙare akan ku".

Sosa ƙeya Laure da Lare suka kama yi cike da borin kunya suka kalleta Lare ta ce.

"To Inna Abu gulma kika ji muna yi ne?, sana ai da aikin yin yinmu kika same mu muna yi ai ko?, dan Allah a daina shiga abunda ba'a saka mutum ba".

Ta ƙare maganar tana taɓe baki, Inna Abu ta murmusa tana ɗan kallonsu kamar zata sake magana sai kuma ta girgiza kai tana barin inda suke, bin bayanta sukai da harara ƙasa-ƙasa Laure ta ce.

"Kaji Mata da shiga sharra ba shanu?".

"Dalla can rabu da ita, sa ido ne yanzu muka fara inda har Haj Mansura tana bamu kuɗin har dubu ɗari idan muka kawo mata rahoto to kuwa yanzu muka fara, ke ni fa akan kuɗin nan da take bamu zan iya bin Inteen can har Bedroom ɗin Ƴallaɓai Hammad idan naga da rata duk sadda naga alamar zata je Part nashi, saina tabbatar na tarwatsa rayuwar Intee ɗin can, ke ni fa zan iya sakawa Hammad yayi lalata da ita wal......

"Lare mi kike ƙoƙarin cewa ne haka?".

Faɗin Laure ido waje.

Yafutu hannunta Lare tayi ta raɗa mata wani abu a kunanta a hankali, wata shegiyar shewa suka saki suna tafa hannu, Laure ta dubi Lare cike da alfahari ta ce.

"Ke Ƙawata akwai ki akwai kawo wuta fa, ai mu kai masu wannan gagarumin abun har abada ta gama zama gidan nan daga ita har uwarta ko uwar tata bata bar gidan ba ita kam nasan har abada ta gama zamansa".

Tunda Intee ta shiga parlon idon Ummu ya faɗa akanta wani irin malolan baƙin ciki ne ya rufe Ummu ta dubi Abbi dake zaune akan kujera yana ƴan rubuce-rubucensa ta ɗaga kai sosai tana kallonsa kamin ta ce.

"Wai Alhaji miye na kiran su Agola a wajan nan?".

Sarai Abbi yaji ta amma yayi kamar ma bai san abunda take faɗa ba, Ammi dake zaune kusa da ita itama ko ci kanki bata ce ba.

Su Hassan dake zaune ƙasa suma dai sunji kusan abunda take faɗa ɗin, wacce akai dominta ma taji amma ta shanye ta samu waje zata zauna haɗe da gaida Abbi ɗin cike da girmamawa.

Sai lokacin Abbi ya ɗago daga abunda yake yi ɗin ya dubi Intee cike da son yarinyar ya ce.

"Zo nan Ƴata ki zauna kusa dani".

Murmurshi kaɗan Intee ta saki cike da son wannan bawan Allahn ta matsa sosai inda yake ta zauna kusa da ƙafafunsa a ƙasa.

Takaici da baƙin ciki da wani irin tsananin haushi ne ya rufe Ummu har wata ajiyar zuciya take a bayyane.

Ji take da, da dama saita kama Intee tayi mata shegen dukan da zata kasa moruwa.

Sai da Abbi ya gama a tsanake kamin ya dubi su gaba ɗaya bayan yayi gyaran murya ya fara da cewa.

"Ba wani abu bane yasa na taraku sai na shaida maku na naɗa Intee P'A a Companyn da Hammad ke shugabantarsa gaba ɗaya, ita ce zata maye gurbin P'A nasa da muka rasa shi kwanakin baya da suka wuce, tunda dama kin riga da kin gama karatunki gaba ɗaya, kuma dama kusan abunda kika karanta shine Kasuwanci, sai kuma su Hassan suma ɗayan Campany na daga gobe Monday ta kama zasu fara shiga Office su fara jagorantar Campanyn da izinin Allah".

Ido waje hankali a mugun-mugun tashe Ummu ke duban Abbi bakinta na kyarma take faɗin.

"Alhaji ban fahimci abunda kike ƙoƙarin faɗi bafa?".

Abbi ya dube ta cike da ƙosawa da al'amuranta ya ce.

"Sarai nasan kinji abunda na ce ai, to ba sai na tsaya na sake faɗa miki ba".

Ammi ce ta ɗan ɗuka ƙasa ta ce.

"Abbin Yara an gode Ubangiji ya ƙara girma, amma wannan shugabanci da aka bawa Intee anya ba.......

Dakatar da ita Ummu tayi cike da hassada da jin zafinta ta ce.

"Dalla can daka ta baƙar munafuka, zaki wani zo kina masa ƙaramar murya wai shugabancin da aka bawa wannan shafaffa da mai ɗin Agola kafi ɗan gida, dama ba haka kike so bane iye?"

"Mansuraaaa!!".

Abbi ya kira sunanta a kaushashe yana kallonta babu wasa.

"Uhmmm wallahi Alhaji ai dole ka mini tsawa mana, ai an riga da an gama da kai, to ni dai na rantse da Ubangiji ba'a isa ba, nan gani nan bari. Kuma wa'innan Yaran daka wani ɗauka ka ɗora su a saman dukiyar ka, ko mutuwa kayi basu da gadonka kafi kowa sanin haka, har uwar tasu idan ma ta manta bari yanzu na tuna miki".

Ummu ta ƙare maganar tana wani jefama Ammi mugun kallo.

Ammi ta runtse idonta cike da wani irin bala'in bugawar zuciya da yanzu ya risketa ta dafe saitin zuciyarta tana sakin wani nishi kaɗan.

Lura da hakan yasa Intee tashi daga inda take ta matsa jikin Ammi cike da tashin hankali ta kamo hannun tana cewa.

"Ammi lafiya?, tashi mubar parlon nan dan Allah, ku su Hassan ku tashi mu tafi kuma".

Ummu zata sake magana Abbi ya daka mata wata irin tsawar data kaɗa ƴan hanjin cikinta, ba ita kaɗai tsawar ta tsorata ba hatta su Intee sai da tsawar ta tsorata su.

"Mansura idan kika sake kika ƙara magana a wajan nan zan nuna miki ainafin kalata, zan miki abunda ko tunani bai zata ba. Sana daga yau ki shaida Campanyn dana ɗora su Hassan halak malak na basu shi har abada, ga takardu nan yanzun zan saka hannu"

Da wani irin tashin hankali take kallon Abbi ganin yadda fuskarsa ta nuna tsantsar ɓacin rai haɗe da jaddada abun yake faɗa ɗin zai iya aiwatarwa da gaske.

Yasa ta haɗiyar miyau kawai ta miƙe cike da jin zafi zata fice daga parlon tana jan dogon tsaki. Abbi ya ce.

"Ki tsaya mana ki shaida"

Dakatawa tayi tana ɗan juyowa zuciyarta na zullo na tsananin tashin hankali da wani irin baƙin ciki dake danƙare da ƙirjinta har wani nauyi yake mata, tana kallo ya saka hannu a wasu takardu masu yawa ya miƙa ma su Hassan hardama wasu wadda bata san na miye ba.

Juyawa Ummu tayi da sassarfa ta fice daga parlon har tana haɗe hanya.

Bin bayanta Abbi yayi da kallon takaici kamin ya dawo da dubansa akan Ammi ya kalli su Intee ya ce.

"Ja ƙannanki kuje kawai ina son magana da Ammi, kuma ki shirya kema ranar Monday zaki fara shiga Office Saboda munyi magana da Muhammad an riga da an gama komai naki a Office da zaki fara aiki".

Abbi ya faɗa, danshi baya kiransa da wani Hammad Muhammad kawai yake faɗa sai idan ana cikin wasa da dariya ne yake faɗin Hammad ɗin, amma idan magana mai mahimmanci ce zai kira cikakken sunansa Muhammad.

Da to kawai Intee ta amsa jiki a sanyaye suka fice daga parlon Hassan sarkin zuciya sai haɗiyar zuciya yake suna fita ya fara ɗin.

"Wai miye Ummu ta ɗauki Ammi ne?, wallahi na tsani Matar can bana sonta yanzu".

Hussain ya dube sa shima yana faɗin.

"Wata rana zan iya mata abunda kowa bai taɓa tunaninsa ba".

Dan shima yadda yake shanye takaicinta cike yake da haushinta a ransa kallonta kawai yake a matsayin maƙiyiyarsu.

Intee ta dube su tana dakatawa da tafiyar da suke, suma suka ja suka tsaya ta ce.

"Daga yau karna sake jin irin wa'innan zantukan daga bakin ku".

"Amma Aunty Intee....

"Shhhh bana son jin komai, kunji abunda na ce dai ko?".

"Eh munji Aunty Intee".

"Yawwa good".

Ta ƙare maganar suka ci gaba da nufar Part ɗinsu.

A wajan Ammi su Intee na fita Abbi ya miƙe ya matsa har inda Ammi take zaune ya zauna a kusa da ita, yana zama ya jawota jikinsa kamar jira take ta ƙanƙamesa tana sauke lumfashi kaɗan zuciyarta na bugwa da ƙarfi.

A hankali ya shiga shafa bayanta alamar lallashi kamin ya ce.

"Haƙika Nuratu ke alheri ce a cikin zuri'ata, Nuratu kin cika mai tsananin hakurin gaske, shi yasa nake son sake haɗa jini dake ta hanyar haɗa Muhammad aure da Intee ba tun yau ba kin san maganar kin san buri na kenan".

Ɗan tashi kaɗan Ammi tayi tana duban Abbi kaɗan tana sauke ajiyar zuciya kamin ta ce.

"Abbin Yara, wannan haɗin inaga kamar bazai yiwu ba"

"Mi yasa bazai yiwu ba?".

"Ka fini sanin miye yasa, Mahaifiyar Hammad baza taɓa bari ba, a yadda ta tsane ni nida Intee babu yadda za'ai ta taɓa yarda da haɗin, kuma Intee dama yanzu ba jituwa suke da Hammad ba na rasa miye yasa, ada baya can yadda suka kasance ban taɓa ɗauka yanzu abun zai canza ba".

"Nuratu ni ne Mahaifin Muhammad dan haka Mansura bata isa ta hanani na yanke abunda nayi niya akan Muhammad ba, kuma maganar rashin jituwa yanzu ai sai dai idan ba'ai masu auran ba suka kasance a inuwa ɗaya ba dole duk wannan shirmen dole zasu daina su fuskanci abunda ke gabansu".

"Banƙi ta taka ba Abbin Yara amma ka sani idan har Ummu bata saka albarka a auran ba, babu inda zaije za'aita samun matsala a cikinsa, ita bata bari sun huta ba ni bata bari na huta ba, nasan wacece Mansura, ka duba fa ka gani abubuwan da suka faru shekaru kusan nawa da suka wuce ta kasa mancewa a kullum cikin goranta mana take nida Ƴaƴana, inaga wannan wadda kullum cikin gargaɗi take mu kiyaye Hammad ba sa'an Intee bane, yadda kasan fa tana hangen abunda kake son ƙullawa".

Wani dogon lumfashi ya saki ya sake cewa.

"Nuratu ina nan akan bakana bazan taɓa janyewa ba, kema naga kamar ba son haɗa zuri'a kike da ni ba".

Abbin ya faɗa rai a ɗan ɓace.

Da sauri Ammi ta riƙe hannunsa tana girgiza masa kai kamin ta ce.

"Ya za'ai ka faɗi haka, baccin yanzu ma cikin zuri'arka nake, nafi kowa farin cikin ace yau Intee ce ta auri Hammad saboda shima kanshi Yaron ya bada mahimmiyar gudunmawa a cikin rayuwar Intee, idan akwai wadda yafi dacewa da auranta to kuwa baya wuce Hammad ɗin, dan Allah kama daina faɗin haka, Mahaifiyarsa ce kawai idan har bata aminta ba nake ganin komai bazai tafi yadda ake so ba, komai zai caɓe ne, ɓacin rai ya ƙara ɓarkewa da rashin jituwarmu zata sake hauhawa ne, abunda ni kuma ba so nake ba, a kullum so nake Mansura ta fahimce ni ta amshe ni mu dawo zaman lafiya kamar ko wanne gida".

Shuru kawai Abbi yayi ya jawota ya sake rungumeta bai sake cewa komai ba, kawai dai yayi alƙawarin bazai fasa bawa Hammad auran Intee ba idan har ya isa.

*Ummu Pov*

"Aikin banza aikin wofi wallahi Mansura da ni kike zancan, mu zuba mu gani shege ka fasa ɗan halak sai yanka".

"Ummu lafiya dai kin shigo parlo kina magana ke ɗaya?".

Da sauri Ummu ta kai dubanta inda taji maganar, sauke ajiyar zuciya tayi ganin Maryam ce Ɗiyar Ƙanwarta wacce ke aure a Funtua ta ce.

"Ah ah Maryam saukar yaushe?".

Tashi Maryam tayi tana murmurshi ta ce.

"Wallahi Ummu yanzun nan na shigo gidan nan naga bakya nan ƴan aiki suka ce kina can Part ɗin Abbi".

"Masha Allah yasu Maami ɗin taki kwana biyu ma bamuyi waya da Sha'awar ba?, shine bata gaya min zaki zo ba?".

"Eh Ummu ta ce zakuyi waya wai".

"To ai shikenan kije ɗakinki ki ɗan huta ina zuwa, raina a ɓace yake ne akan Matar can".

"Hala abokiyar zamanki ko Ummu?, to gida ma abunda na baro kenan Maami na fama dashi kenan kusan matsalarku ɗaya suna kamanni da juna".

"Ai wallahi Maryam kishiya batai ba, bare wacce taje ta gama haihuwa tazo maka da Agololi a cikin gida".

"To ai Ummu gara nan nake gani, mufa gida dana baro suna can kusan su Uku ko wacce data zo ta koma sai wancan ta sake zuwa, kullum cikin sintiri suke zuwa wajan uwarsu sun cika mana gida".

Ummu zatai magana wayarta dake can akan kujera data bari a parlon tun ɗazo ta dubi Maryam ta ce.

"Kije ki huta ƙila ma Maamin taki ce".

Amsawa Maryam tayi tana murmurshi tana son tabbayar Ummu Y Hammad amma ganin hankalin Ummu ɗin ya koma ga wayarta saita shanye tabbayar, Allah ya sani danshi kawai take zuwa gidan, tun kan tasan kanta take son Y Hammad shi ɗin ƙarshe ne.

Sai da Ummu ta zauna kamin ta ɗauki wayar ganin Sha'awar ce kuwa take kira, sai da ta tsinke kamin ta bi kiran.

Sai da suka gaisa kamin Maami daga cikin wayar ta ce.

"Aunty Mansura ga Maryam nan zatai hutu Allah aunty so nake Hammad da Maryam su saba ko munyi maganar auransu, amma abun sake taɓarɓarewa yake, duk hutu ko duk bayan wasu Watanni saita zo amma har yanzu baya kallonta da so ko kallon arziƙi fa Maryam ta ce bata samu a wajansa".

Ummu ta ja lumfashi kamin ta ce.

"Ai Sha'awa ko bai amince ba ko baya sonta dole dan ubansa ya auri Maryam, dan tsaf ina ganin take-taken Mahaifinsa so yake ya haɗasa da Agolar gidan nan, abunda kuma ko sama da ƙasa zata haɗe bazan taɓa amincewa ba wallahi".

"Tabɗi jam Aunty ashe dama kema kina nan kina fama da Agololi cikin gida?, da ƴan gaba da fatihan nan suna nan?, koda yake gara kema a ni nan karki ga irin wannan abu, da wata tazo ta tafi sai wata ta sake zuwa, ai ni Aunty Huran baya ma ƙasar bare ace ɗanshi ake wannan sintiri, tunda Yaran nata duk kusan Mata ne dan haihuwar datai a gidan nan ma Mace ta haifa fa, ace Mata ko ina kika je sai kin wage gindi kin haihu, kamar wata Jaka".

"Uhmmm ai ko Sha'awa sai kin dage kin saka ido kema dan duk ranar da Harun ya dawo ƙasar gaba ɗaya to haka zaki ga ana masa kwarkwasa duk dan ya samu Mata ɗaya daga cikinsu ya aura".

"Ai wallahi Aunty uban kuturu yayi kaɗan bare na makaho, tabɗi jam ai bazai taɓa saɓuwa ba wai bindiga a ruwa, ita kanta Nanar ta san ni wacece tasan ni ba sa'ar yinta bace, wacce take min aiki ina biyanta ai tasan nisa tayi ma Yaro nisa".

"Hhhhhhh ke Sha'awa wai da gaske ƴar aiki kika maida ita?".

Ummu ta faɗa cike da Mamaki.

"Hhh aunty kenan kware kuwa haka ta zama ƴar aiki".

"To ai ke da sauƙi cewa zakiyi ba kishiya aka kawo miki ba ƴar aiki kawai aka kawo miki, nifa kinga yadda Alhaji yake rawar ƙafa akanta, harya fara ɗora ƴanƴanta akan dukiyarsa".

"Tabɗi jam lallai kuma Aunty kike zaune a haka?".

"Ai babu uwar data isa tayi min, Muhammad shine Ɗa na farko a cikin gidan nan komai na hannunsa duk abunda za'a yanke na dukiyar Alhaji sai dole an sako sa idan har ya amince, dan haka ni hankali na a kwance kawai yake, ina mata habaici ne dan tayi ta ƙusan baƙin ciki da ɓacin rai a kullum kinga idan ciwon zuciya ya kamata ta mutu ba shikenan ba".

Dariya da shewarsu kawai ke tashi a parlon yadda kasan ba waya suke ba, saika rantse kamar zaune waje ɗaya suke maganar.........

*TSANIN ƘADDARA*

*©Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 5

*House No 19, Tudun Yola Kano Nigeria*

"Yawwa tunda kin gama cin abincin sai ki zo ki faɗa min miya kawo ki Kano da yammar nan haka Sakina?".

Sakina ta haɗe miyau tana duban Aunty Sakina wacce suka fito ciki ɗaya da Mahaifiyarta ta ce.

"Aunty wallahi jiya da aka kira ki baki zo gida ba shine yasa baki ji duk abunda ya

4 / 40