Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
*TSANIN ƘADDARA*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
Chapter 1
TSOKACI
Kowacce ƙaddara ta rayuwa akwai mafarinta da kuma ƙarshenta, Tsani-Tsani ce kuma kala-kala ce, akwai mai daɗi akwai kuma akasin hakan, wadda Allah ne kawai ke jarabtar bayinsa dan kawai gawada imaninsu. A wannan book na TSANIN ƘADDARA akwai labari kala-kala haɗe da ƙaddararo na rayuwa masu wuyar cinyewa, shin wannan ƙaddarorin zasu iya cinye su?, wai ma wane irin Tsanin ƙaddara ne haka?, mi zai faru?, su waye wa'inda zasu fi shiga Tsanin ƙaddara?, shin miye ma Tsanin ƙaddarar?.
Duk amsoshin wa'innan tabbayoyin suna cikin book ɗinga mai suna Tsanin ƙaddara, ko biyo ni sannu a hankali zan warware maku duk wata chakwakiya dake a cikinsa.......
*House No: 19 Mando Estate Kaduna Nigeria*
Da mugun gudu ta fito daga toilet ɗin har tana bange Wacce ke kusa da ita, hankali a tashe ta riƙe ta tana kallonta cike da mamaki, sai kuma ta dubi ƙofar toilet ɗin jikinta na rawa itama tana dubanta bakinta na kyarma ta ce.
"Nuratu ba dai abunda muke zargi bane zai tabbata?, dan Allah ki ce min ba haka bane?".
Jikin Nuratu na rawa hawaye na mata zuba na tsananin ruɗani da razani, ƙirjinta na ɗagawa ta dubi Sadeeya dake riƙe da ita da kyar ta iya fisgo magana a bakinta ta ce.
"Na shiga uku na Sadiya wallahi ciki ne dani, wadda babu aure aka same shi, Sadiya na bani na shiga uku".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Nuratu cikinne dai da muke zargi?, yaya za'ai ace Mace ta samu ciki namiji bai kusance ta ba?, saboda nasan halinki baza taɓa iya aikata ɓarna mafi muni irin wannan ba".
Girgiza kai Nuratu tayi tana haɗe wani zazzafan maiyau daya tarar mata a maƙoshi ta ce.
"Cikin nan na mai gidan nan ne Sadiya, ko na rantse bazan kaffara baaaaaaa".
Sadiya ji tai kanta na neman tarwatsewa wata muguwar hajijiya ta rinƙa ji tana neman kayar da ita, wani irin sauri Sadiya ta rufe ma Nuratu baki da tafin hannunta tana girgiza mata kai hankali a tashe ta dube ta tana zare ido waje ta ce.
"Nuratu mi kike ƙoƙarin cewa ne wai?, kin san illar furucin da kike faɗa kuwa?, kin san illar da zakiyi ma rayuwarki mudun Matar gidan nan taji kina ikirarin ƙaƙabama mijinta cikin shege, mijin da take mugun kishinsa da sonshi kamar ya zautata, matar da kin kalli yanayin yadda take mahaukacin kishin mijin nan nata zaki san babu abunda bazata iyayi ba akansa, kin manta wacece Haj Mansura ne Nuratu wai?. Tayaya, tayayama za'a ce shine yayi miki ciki?, mutunan dake da takatsantsan da duk wani al'amarin Mata, saboda yasan halin Matarshi da bala'in zafin kishi. Bazan taɓa yarda da wannan shirmen naki ba Nuratu ki san waye yayi miki cikin nan dake a jikinki".
Nuratu kanta a ƙasa tana duban abunda tayi awan cikin dashi yadda ya nuna tabbas shigar ciki ne da ita, shi yasa kuma a kwanaki biyun take fama da rashin lafiya iri-iri, rashin lafiyar kuma zam irinta masu shigar ciki ƙarami da suke fama da ita ce, shi yasa hankalinsu ita da Sadiya yayi mummunan tashi har suka je kyamis mafi kusa suka sayo abun awan ciki a gida Nuratu ta ɗebe jininta kuma tabbas ya nuna shigar ciki ne da ita.
Jan majina Nuratu tayi tana ɗago kanta hawaye na mata zuba har lokacin ta dubi Sadiya, sai kuma ta saki ƴar robar awan dake hannunta ta kamo hannun Sadiya da har lokacin take cikin zallar mamaki kamar zai karta, Nuratu cikin muryar kuka ta ce.
"Wallahi Allah Ƙanwata Sadiya ba ƙarya nake ba. Akwai abunda ya faru cikin wani dare wadda bazan taɓa mancewa dashi ba, tabbas Alhaji Ahmed bai kusance ni ba, amma tabbas al'aurarshi ta taba farje na, yana goga min al'aurarshi a farje na, kuma naji wani wa'azi ance shi Maniyi gudu yake kamar ruwa, ciki zai shigar Mace mudun shi namiji yana wasa da al'aurarshi a cikin farjen Mace ba tare da ya shige ta ba, a wannan daren Allah ne ya ƙaddara bazai kasance ni ba, saboda da kyar na kwace kaina daga hannunsa, tabbas akwai abunda akai ma Alhaji Ahmed har ya shiga wannan mummunan yanayin. Banji haushinsa ba saboda kwata-kwata baya cikin yaccinsa, Sadiya amma tabbas yasan abunda ya faru tunda safiyar washe gari na lura yana bina da wani kallo wadda na kasa gasgata na miye ne?, har lokacin dana fara ciwon nan na laulayi ban farga ba ke ce kika fara rurar dani cewa rashin lafiyar da nake yi kamar ta masu sabon shigar ciki ƙarami, lokacin hankalina ya tashi kinfi kowa sani, na rasa a ina na samu shigar ciki sai da jiya na saurari wa'azin Malama Juwairiya naji komai tabbas sai lokacin nasan zan iya ɗaukar ciki saboda abunda ya rinƙa min"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, wacce irin ƙaddara ce wannan?, yaya zamuyi da cikin nan, kin san ko karan hauka ya cije mu bazamu taɓa fitowa fili mu ce wannan cikin na mai gidan nan bane kin sani, munfi kowa sanin Haj Mansura zata iya sakawa a ɓatar damu a daina jin ɗuriyarmu a duniyar nan mudun tasan abunda ke faruwa".
Wata irin haɗiyar zuciya Nuratu tayi tana sake kallon Sadiya hawayen tausayin kanta da na Ɗiyarta data baro a can gidansu na rufe mata jiki.
"Sadiya Intee nake tausayi batai sa'ar uba ba, sai gashi nima ina son jefa rayuwarta cikin wani garari, Sadiya gidan aikin nan kawai ya rage mana inda muke ci muke sha, Sadiya dole zan bar gidan aikin nan namu na tafi can Rimaye gida".
Da wani irin sauri Sadiya ta dubi Nuratu ido waje ta ce.
"Yaya zakiyi da cikin nan a Rimaye iyee Nuratu?, kin san kuwa illar hakan da kike sonyi, mi yasa bazamu zubar dashi a nan ba, ba sai kowa yaji ba?".
Da sauri Nuratu ta shiga girgiza kanta wasu hawaye masu zafi na sake zubo mata, bayan hannunta tasa ta ɗan share hawayen kamin ta ce.
"Bazan iya zubar da cikin nan ba Sadiya da ubanshi a raye, kina ganin yadda suke neman haihuwa tunda suka haifi Hammad basu sake samunta ba, nasan zuciyar mai gidan nan yana son haihuwa sosai, Matarshi ce taƙi yarda ya je yayi wani auran wata ƙila rabon haihuwar na wajan wata, amma taƙi gane hakan, waya sani ma rabon wannan cikin yana gaf kusa da zuwa duniya ne shi yasa wannan abun ya faru da ni".
"Nuratu wai kin san abunda kike faɗa kuwa?, so kike ki lalata rayuwarki data ƴarki ki ɓata gobenki dana Intee?, mi yasa baza'a zubar dashi ba tunda dama ba'a same shi ta hanyar aure ba".
"Amma ai bisa tsautsayi da ƙaddara aka sameshi, bamu da laifi gaba ɗayanmu daga ni har Alhaji Ahmed ɗin, mai babban laifin ma ita ce Matarshi, data bari yaje yayi wani auran da duk hakan bata faru ba"
Nuratu ta ƙare maganar a ɗan tsawace haɗe da sakin kuka daga ƙarshen maganar, domin wani irin zafi take ji a zuciyarta idan Sadiya na furta a zubar da cikin dake jikinta.
Lumfashi mai zafi Sadiya ta saki tana jin haushin Nuratu sosai akan maganar gani take kamar neman suna take da kuma neman ta jazama masu gaba ɗaya a ɗaure su har igiya tayi tsawo.
"Kinga Nuratu kije koma miye kiyi amma ni na baki shawari ne kawai bana son a nan gaba kiyi nadamar da bata da amfani"....
*
****************
Ƙofar Sauri katsina State Nigeria*
****Wani irin duba tayi ma Kawunan tana tana kuka mai sauti sosai jikinta duk ciwuka ne, janye take da akwatin ta zata fice daga cikin gidan tana wani irin kuka mai ban tausayi, ta tsaya dai-dai inda suke suna wani mata kallon zaki ce uwarki ne, ta ce.
"Ku sani zan tafi na bar gidan nan amma duk wadda yasan yaci zalina a bisa radin kansa yaje shida Ubangiji. Kuma wannan gidan dai ku ji da kyau akwai haƙƙin uwata a ciki, ɗan kawai tayi aure wani wajan ta barmu a gidansu ba shi yake nuna mun rasa gata ba".
Tana faɗar haka ta fice daga gidan.
Kawu Ismail ne ya mike a zafafe yana nuna inda tabi yana faɗin.
"Kaga ƴar iskar yarinyar nan Humaira mu zata tsaya tana gaya ma magana son ranta, wallahi da an barni saina barta kwance, daga maganar yarinya ta fito da miji mu zata maida shashashu ƙananun mutane?".
Kawu Saminu ya kamo hannun Kawu Ismail dake zafga faɗa kamar wadda Humairar ce a gabansa yana duban wajan data bi shima ya ce.
"Rabu da ita ai ta tafi wajan uwarta daga yau kuma daga ita har Nanar sai dai su nemi inda zata kai yaran nata".
"Keee Sakina kina ina kema zo ki wuce ki bi ƴar uwar nan taki maza-maza daga yanzu ai gidan nan ba gidan Ubanku bane ba dai ko?, to daga yanzu kun gama zama a gidan nan wallahi".
Sakina dake raƙuɓe a ɗakin Kakarsu wacce tana zaune bata iya komai bata iya cewa komai ta kalleta tana hawaye tasa hannunta ta ɗakko ƴar jakar kayanta itama tana kuka zata fice daga ɗakin sai kuma ta tsaya tana shashshakar kuka ta dubi Kakarsu ta ce.
"Dan kawai kin haifi duk Mata a cikin gidan nan ba shi yake nuna kin gama wulaƙanta ba Kaka, kiyi hakuri komai zai wuce, amma tabbas ki sani su Aunty Hadiza basu da wani anfani, a gabansu su Kawu Ismail suka kama Humaira sukai mata dukan kawo wuƙa amma a cikinsu aka rasa wadda zaice zai tafi damu gidanta, Kaka kin riga kin san inda Innarmu take aure baya taɓa son ƴanƴan daba nasa ba, a hakama yaya ake rayuwar bare munje mun ƙara mata nauyi".
Tashi Kaka tayi tana hawaye ta kamo hannun Sakina cikin yanayin tsufa ta ce.
"Sakina kuyi hakuri dan Allah, amma banda fawa a cikin gidan nan Talatu ita da ƴaƴanta suke juya gidan nan yadda ransu ke su. Dan Allah Sakina ƙarku je mata ku duka a can Funtuar, ke ki tafi Kano gidan mahaifinku ita kuma Humairar taje wajan Innar taku Nana".
Jiki a mugun sanyaye Sakina ta waigo tana duban Kaka ta ce.
"Kaka kin san gidan Mahaifinmu kamar kurkuku yake a gare mu, ko kaɗan kunfi kowa sanin baya sonmu yafi son mutuwarshi akanmu, Matarshi Inna Safara'u ta tsane mu ita ce musabbabin fitowar Innarmu daga gidan mahaifinmu mun zauna azaba da wahala tasa dole muka dawo gare ku, yanzu sai ace na nufi gidansa dan Allah".
Sakina ta ƙare maganar kuka na sarke ta.
Hankalin Kaka ya soma tashi ta buɗe baki ta ce.
"Ya kike so nayi ne Sakina, kiyi abunda na ce kawai kinga mahaifin nan naku fa shine dolenku, rayuwar nan da muke ciki bana jin wani zai iya riƙe ɗan wani, itama na tabbatar Humairar zamanta a can ba bai ɗurewa bane".
Sakina bata ce komai ba taja jakar kayanta ta fice daga gidan.
Koda ta fita bata iske Humaira ba da alama tayi nisa zuwa tashar garin, dan haka itama tasher kawai ta nufa tana yanke cewa gara ta tafi gidan ƴar uwar Mamarta Inna Sakina wacce taci sunanta.
****************
Shekarar ta 2014
*House No: 17 Aurora Wrestling Estate Kaduna Nigeria*
A hankali tasa hannunta ta murɗa ƙofar bedroom ɗin ta fito tana jin wani irin bala'in haushinsa.
Turo ɗan ƙaramin bakinta tayi tana komawa ɗayan part ɗin dake kusa da wadda ta fito.
Tunda ta fito a harabar gidan ma'aikatan gidan suke binta da kallo ganin shigar ƙananun kayan dake a jikinta kuma ta fito a hargitse.
"Ke Laure kinga abunda na gani kuwa?".
Wasu masu aiki dake can gefe suna duban matashiyar data fito daga ɗayan part ɗin.
Wacce aka kira da Laure ta ce.
"Ni ko na gani Lare, Agola da ita ta zo gidan nan tana neman gaje komai, nema fa take ta rinƙa shigema Ƴallabai Hammad".
Laure ta taɓe baki ta ce.
"Hmm kar dai tarihi ya maimaita kansa fa?".
"Tabɗi jam ai ko wallahi Haj Mansura bazata taɓa bari ɗanta ya auri jinin Nuratu ba koda sama da ƙasa zata haɗe, koda soyayya zatai masu mugun kamu, baki ga komai na Hammad ɗin ba take kaffa-kaffa dashi ba, taƙi jinin duk wani abu da zai fito daga wajan Haj Nuratu ba?, bare wancar yarinyar Tata Intee mai kama da aljanu yarinya sai kyau kamar dangin ifiritai, yo bama dole Hammad ɗin ya rinƙa shiga harkarta ba, shima da shishshigin tsiya yasan uwarsa bata so amma yana ƙara shige masu. Ke nifa ma sai na kaima Haj Mansura wannan Jaridar dana samu wallahi wata ƙila na samu ƙarin albashi".
Wani duban baki isa ba Lare tayi ma Laure tana yin gaba ta nufi part ɗin Haj Mansura tana faɗin.
"Kaji ƴar baƙin ciki ai ko wallahi sai dai ayi mana ƙarin albashin a tare, tunda ai bake kaɗai kika ga fitowar tata a shashin Ƴallaɓai Hammad ɗin ba, sai dai mukai Jaridar nan tare".
Da sauri Laure ta take ma Lare baya tana jin wani irin haushin Lare dake shige mata hanci a ƙudundune.
Shigarta part ɗin tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba mai ɗauke da wani irin jan laɓe, ta ɗan taunashi kamar mai shan alawa tana tuno abunda wancar Hammad ɗin Mugu yayi mata. Saka hannunta tayi tana taɓa leben nata jin yadda yake mata zafi saboda yadda Hammad ɗin ya kamashi ya matse da hannunsa tsabar muguntar shi har hawaye sai da tayi masa, dan kawai ta ce masa mugu, kuma ya hanata faɗa, ita ko tsabar ta saba faɗa masa hakan yasa ta faɗa bata sani bama, shine ya kama mata baki ya murɗe.
Murguɗa baki tayi can taji saukara muryar Ammi dake dubanta zaune a babban parlon gidan sai su Hassan da Hussaini dake zaune a ƙasa suna home work books ɗin school ɗin sube a tsakar parlon, sai kuma Hanan da Ameera dake wasansu suma a gefensu wadda baza su wuce Shekara Biyar ba sai Hassan da Hussaini da zasu kai shekaru sha Uku zuwa sha huɗu.
Suna ganinta suka tashi suna faɗin.
"Aunty Intee kinga na ce Y Hassan yayi min Home work an bamu a school amma yaƙi wai sai dai muyi da kanmu".
Shafa kansu tayi tana faɗin.
"Sorry kinji Hananuwa ta, ni zan miki karki damu, kinga su Y Hassan suma home work ɗin suke".
Hanan tayi murmurshi tana jawo hannun Ameera da bata da yawan maganar Hanan ɗin suka ci gaba da wasansu da Books ɗin dake a gabansu.
"Ammi"
"Uhmmm ta gidan Ammi miye akai kuma?".
"Ammi ba wannan Y Hammad ɗin bane daga zuwa na kai masa abincin da kika sa naje ya kai masa part nashi shine y.....
"Kinga ba'a shiga tsakaninku can ku kuka sani, tunda bakwai gajiya da yin rigima a tsakaninku koda yaushe sai kace wasu ƙananun Yara haba dan Allah, ni kinfa fara isa ta".
"Amma Ammi..."
Ammi kallon data wurga mata ne yasa ta yin shuru. Ganin kallon da take bin jikinta dashi ne yasa Intee shan jinin jikinta, cike da takaici Ammi ta sake dubanta ta ce.
"Hala a haka kika fita kika je part ɗin nashi?, wai mi yasa Intee kece zaki rinƙa saka ni magana a cikin gidan nan ne?, kin san irin munafukai dake a gidan nan kuwa?, wani ma zai iya zuwa ya ce ya ganki babu kaya kin shige part ɗin Hammad, kinfi kowa sanin kaɗan ake jira damu a cikin gidan nan ko?, kinfi kowa sanin bana son irin wannan shigar da kike a gidan nan Intee, Intee kifa sani babu muharraminki a cikin gidan nan".
Idon Intee ne yayi jawur kyakkyawar fuskarta tayi ɗan ja kaɗan taɓe baki tayi kaɗan tana girgiza ma Ammi kai ta ce.
"Ammi kiyi hakuri wallahi na manta ne amma bazan ƙara ba".
"Yafi miki dai dan bana son abun magana".
Kamar jira ake Ammin ta rufe baki suka ji an bango ƙofar parlon an shigo bako sallama.
Har sai da gaban Ammi ya faɗi jin saukar maganar Haj Mansura.
"Ai ko ku ke da abun magana a gindinku Nuratu".
Tashi Ammi tayi tana duban Yaran ta ce.
"Kuje ciki Intee ke da ƙannanki".
"Ina zasu je kuma munafuka?"
Da wani irin sauri Hassan ya miƙe zuciyarsa na kaiwa wuya, su duka sun gaji da irin cin kashin da ake ma mahaifiyarsu a gabansu amma ba damar su tanka sai Ammi ta hana ko ma ta make ka.
"Ummu Ammi ce munafuka?".
"Kaiii ɗan gaba da fatiha ba da kai nake yi ba da uwar data kawo ka duniya nake, ni nafi ƙarfin nayi da kai wallahi".
"Hassannnnn na ƙara jin bakin ka a nan wallahi sai nayi mugun saɓa maka, ku wuce kubar parlon na ce ko".
Tashi sukai jiki a mugun sanyaye suka shige daga ciki.
Intee ce kawai taja ta tsaya tana jin wata irin tsanar Ummu har cikin zuciyarta.
"Kefa mi kike a nan da baki wuce kinbi Ƙannanki ba?".
"Ahh ahh ai ba sai ta tafi ba Nuratu domin saboda da ita nazo nan. Kiyi ma Ƴarki gargadi daga rana irinta yau karna sake na sake jin an ganta da Ɗana, domin Yaro na ba sa'an yinta bane, duk wata maita taku can ta kare maku. Ina so ki sani cewa Ɗana bazai taɓa zama kamar Mahaifinsa ba da akaje aka kai wajan Bokaye da Malamai domin kawai ya aureki, to a wannan lokacin Hammad ki sani yafi ƙarfin duk wani makircinki, na faɗa na ƙara faɗa ayi nesa da Yaro na tunda dai nina haifi kayana kuma jini Alhaji Ahmed ne da auran sunna na haifi ɗana, ba kamar sauran Yaran dake a gidan nan ba, da wai suke amsa sunan Ƴanƴan Alhaji Ahmed wadda aka riga da aka haife su tun kamin a shafa fatiha, dan haka wallahi a kiyaye ni a kiyaye shiga gona ta, ke kin san baccin na amince da wallahi