Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
gaba kuna hantararsu ba"
Shiru kawai sukai dan sun san dama Baba idan ka zo masa da magana idan har baya sonta, to duk yadda ka ɓullo masa saifa ya kawo maka wani dalilin da dole ma ka sallama masa kayi shiru........
PAGE 17
*Ƙauyen Karaɗuwa, Kankia LGA, Katsina state Nigeria*
"Inna ina wannan yarinyar ne?, tunda na shigo ban ganta ba"
Inna ta aje abunda ke hannunta ta ce.
"Wai fa aiken ta nayi taje nan bayanmu ta sayo min manja da zan soya aci dambun nan da nake daf da gamawa"
Zama Umar yayi yana jiran dawowarta.
************Tafe take tana ɗan tsalle kamar wacce ke wasa.
Batai aune ba taga an tare gabanta.
Ƙafafuwan mutane har uku ta gani daga ƙasa, bata san lokacin data ɗago gaba ɗaya ba tana binsu da kallo.
Wani shegen kallo suke binta dashi, suna riƙe ƙugunsu haɗe da ɓalla mata hararara kamar idonsu zai faɗu ƙasa.
"Ku matsa min hanya Malamai"
"Ke har kin isa ki taɓa Hasiya ki zauna lafiya?"
Riƙe ƙugunta Sadiya tayi tana ƙare masu kallo ɗaya bayan ɗaya, can ta hango Hasiya tana mata kallon banza. Wata dariya ta saki tana cewa.
"Wai ku nan ɗaukar mata fansa kuka zo yi?"
"Kware kuwa kuma daga kanta bazaki ƙara tare wata ki ce zaki daka ba"
"Wato idan na gane harda ma kune aka haɗa kai aka min dariya a makarantar, kuka taho kan hanya kuma kuna gulmata"
"Mu ɗin ne, sai akai yaya?, ko akwai uwar da kika isa kiyi?"
Wata marar kunya mai baki ta faɗa ba alamar tsoro akan fuskarta.
Murmushin gefen baki Sadiya ta saki tana jinjina kai, so take taga mima zata ma yaran nan ne?.
Wani tunani ne ya faɗo mata da wani irin sauri kamar wata Aljana suka ta duƙa ƙasa sai dai kawai suka ji an shammacesu an watsa masu ƙasa akan fuskokinsu, sai a cikin idanuwansu gaba ɗaya.
Ihu suka saki a tare suna rufe idonsu. Lokaci ɗaya idonta suka hango mata wata bulala ta ɗauketa ta zafgegiyar bulala ta fara ɗagata sama sai dai kawai suka fara jinta a bayansu.
Yadda kasan ta samu ƴaƴanta haka ta zane su tass suna ihu, gashi dama wajan da suka tare ta babu yawan jama'a a wajan, sai ihu suke gashi basa ganinta ma kwata-kwata bare su iya kare kansu.
Ga zafin da idonsu ke masu na watsa ƙasar data masu, ga radaɗin bulalar da suke jinta a jikinsu.
Tana sauke lumfashi ta dube su ɗaya bayan ɗaya ta ce.
"Gobe ma ku ƙara tare ni a hanya dan Allah, domin dai-dai nake daku wallahi, ina da rashin mutumci kwando-kwando dana tanadar maku"
Tana ƙare maganar ta bar wajan.
Saida ta kusa isa gida kamin ta tuna da cewa Manjan da Inna ta aike ta sayowa ta yada shi a can wajan faɗan.
"Innalillahi ƙilama ya fashe"
Ta faɗa a zabure.
"Ki koma kawai ki ce tuntuɓe kikai ya faɗi ya zube"
Wata zuciyar ta faɗa mata.
Riƙe baki tayi tana tunanin mafita.
Ɗaga kanta kawai tayi tana nufar cikin gidan dan kawai ta yanke hukuncin gara ta ce tuntuɓen tayi ya zube.
Sai dai tana shiga gidan gabanta yayi wata irin mahaukaciyar Guguwa ganin dodon nata zaune akan kujera suna fira shida Inna.
Inna na ganinta ta miƙe tana cewa.
"Ina kika je kika tsaya ne haka kika daɗe?"
Shiru tayi a tsaye gefe kamar wacce aka dasa, ta zubama Ya Umar ido kamar zata hango wani abu a jikin nasa.
"A'a ina aiken da nayi miki?. Ko babu ne naga kin dawo hannu babu komai?"
Inna ta faɗa tana bin hannunta da kallo.
"Ba magana ake miki ba?, kin tsare mutane da ido"
Firgigit maganarsa ta dawo da ita duniyar data tafi, tana ɗanja da bawa kaɗan cike da tsoro ta ce.
"Wallahi Allah Inna ina gaf isowa gida wani dutse ya taɓiye ni na faɗi sai manjan ya faɗi a hannuna ya zube a ƙasa"
Sake da baki Inna ke kallon Sadiya tana ƙare mata kallo sosai ganin yadda take kame-kame yasa Inna sakin murmurshin gefen baki ta ce.
"Ki dai faɗi gaskiya yarinya, akwai rashin gaskiyar da kika je kika aikata, ni dama nasan wannan daɗewar taki ba'a banza ba wallahi"
"Zoo nan Sadiya"
Ya Umar ya faɗa yana danna wayarsa sai taji kamar ba shine ya faɗa ba.
Shiru tayi na tsawon lokaci, wai so take taji ko dai kunnanta ne baiji bane?.
Sai kuma ta sake jin wannan muryar tasa mai kusan sata fitsarin tsaye ya ce.
"Ba dake nake magana bane?"
"Waw...wi....wai dani kake Ya Umar?"
"Ban sani ba"
Ya faɗa kai tsaye.
Wani maiyau ta haɗe tana matsowa a kusa dashi sosai ta duƙa ƙasa gwaiwowinta a ƙasa jikinta sai rawa yake bakinta na kyarma ta ce.
"Gagg...ga....gani Ya Umar, amma dan Allah kayi hakurii"
Ɗagowa yayi yana zuba mata idon nan nasa mai mugun tasiri a jikin mutum, haba ai sai jikin Sadiya ya ƙara ƙaimin kyarma.
"Gaya min gaskiya mi ya tsayar dake akan hanya har kika zubar da aiken da Inna tayi miki?"
Rufe bakinta tayi da tafin hannunta dan tasan yanzu ƙarya take ta iya kallon tsabar idonsa tayi masa ƙarya, ai bazata iya bama.
"Oya ina jinki. Kika sake baki gaya min gaskiya ba zan gane ne, kin sani kuma, sana kuma naji kinyi wani abun daban hmmm"
Kawai ya faɗa yana jinjina kansa.
Ai sai ƴan hanjin cikinta suka soma yin ƙara, baki na rawa ta ce.
"Wallahi Allah Ya Umar sune suka fara jana, tunda na tafi babu wadda naja faɗa da kaina Allah kuwan sune suka fara jana"
"Su suwa kenan?"
Ya faɗa yana saka wayarsa a aljihunsa, dama yasan za'a rina ne, da wahala ta fita bata jawo magana ba.
"Su Hasiya ne da ƙawayanta suka tare ni akan hanya wai zasu dake ni, shi...sh.... shine ni kuma.....
Sai kuma tayi shiru tana in'ina.
"Shine ke kuma marar hankali kika tsaya kika biye masu ko?"
Kuka ta saki tana cewa.
"To ni Ya Umar kawai saina tsaya su dake ni ban rama ba?"
"Rufe min baki ko na fasa miki shi yanzun nan"
Da sauri tasa tafin hannunta tana rufe bakin nata hawaye na zubo mata.
"Kayi hakurii dan Allah to"
Inna ta girgiza kai tana cewa.
"Ni ai wannan yarinya Allah dai ya shirya ki, ni tsoro na ma kar Allah yasa ba wani abu taje tayi masu ba, azo a rinƙa sallama a ƙofar gidan nan, ke shikenan kullum cikin kawo ƙarar ki ake a gidan nan?"
Ai da rufe bakin Inna kamar ana jira ta faɗa ne aka kwaɗa sallama da murya har biyu a ƙofar gidan, saiga wasu Mata har biyu sun shigo gidan riƙe da wasu yara su huɗu biye dasu, kowacce ido sunyi jawur sun ƙunbura sai shashshekar kuka suke.
"Bayin Allah lafiya?"
Inna ta faɗa tana hasashen faɗan da Sadiya taje ta jawo ne.
Ai ko kamar yadda tayi hasashen hakane, kai tsaye suka fara gaya mata abunda Sadiya tayima yaran nasu.
"Yanzu kunce sai an biya kuɗin magani da asarar data masu ko?"
Ya Umar ya faɗa yana binsu da ido.
Ɗaya daga cikin ce ta ce.
"Kware kuwa"
Saka hannunsa yayi ya ɗebo kuɗi ya miƙama kowaccensu yana nuna masu hanyar fita.
Ɗaya daga ciki ce ta buɗe baki ta sake cewa.
"Kuma sana tsakani da Allah ku rinƙa jama ƴarku kunne akan rigimar da take jawowa, bazai yiwu ta hana ƴaƴanmu sakewa ba a gari yawwa"
"Why not ba an biya ku ba?. Miye na tsayawa wannan dogon gargaɗin Malamai?. Kuma ku tsaya kuji kuma kuja ma ƴaƴan naku kunne, daga rana irinta yau karsu sake ganin Sadiya akan hanya su ce zasu jata faɗa, idan ba haka ba kuma koma miye yaje ya dawo babu ruwanmu"
Ya Umar ya faɗa da muryar nan tasa wacce babu wasa.
Ai sai suka sha jinin jikinsu kowacce ta kama ƴaƴanta suka ƙara gaba yana iya jin yadda suke yada ƙananun maganganu akan gidan nasu da rashin jin Sadiyar ya jawo masu.......
PAGE 18
"Tsallan kwaɗi zaki fara yanzun nan"
Ido waje Sadiya ke kallon Ya Umar da yayi maganar kamar bashi ba.
"Ya Umar tsallan kwaɗi kuma?, na shiga Uku"
"Baki ga ka shiga ukun ba ai yarinya"
Ya faɗa yana tsare ta da idonsa.
Ƙasa tayi da kanta tana jin kaifin idonsa akanta.
"Oya tashi ki fara"
Kuka ta saki tana kallon Inna zatai magana Inna ta ɗaga mata hannu ta ce.
"Karma ki fara ce min komai ni"
Ƙara ɓare baki tayi tana kuka ta miƙe tsaye ta kama kunnan nata ta fara tsallan kwaɗin.
Duka guda biyu kawai tayi ta fara jin ƙafafuwan na neman sagewa sun fara mata zafi.
Sosai take shashshekar kuka tana ƙara bama Ya Umar haƙuri.
Saima taga ya koma ma Inna wata maganar yana cewa.
"Inna tunda na dawo banji kinyi maganar Inna Asma'u ba?"
Taɓe baki Inna tayi tana jin zuciyarta babu daɗi akan ƙanwar Mahaifiyarsu Umar ɗin wacce ke aure a cikin Rimaye can gaba dasu, kwata-kwata bata da zumunci sai ankai ruwa rana take leƙo su.
"Hmm ai Asma'u bata da kirki wallahi, ace yanzu har mun kusa rufe shekara bata taku inda muke ba. Hatta ƴarta Safiya rabo na da ita wallahi Umar na mance, nama manta kamaninta, wata ƙila za su zo shekara ɗaya, kota girmeta da kaɗan ne, domin kwata-kwata fa duk sadda zata tako garin nan bata ma zuwa da ita"
"To ai Inna kamata yayi ke kuje keda wannan marar kunyar"
"Nifa Umar da cewa nayi kawai muyi waje mu aje ta, tunda ta nuna bata yi da mu"
"A'a Inna baza'ai haka ba"
"Hmm Umar kana son zumunci kai dai da ƴan uwanka"
"Inna dan haushi nima tabbas ina jin haushin Inna Asma'u, amma wallahi yadda nake ganin kamaninta da Ummanmu ne ke sawa kawai nake sassauta mata, Inna kamarsu Umma tayi yawa ta ɓaci, yadda kasan Umma tayi kaki ta tofar"
"Hhh haka suke kama da juna dama can, wasu ma basa iya gane su, wasu har cewa suke masu ƴan biyu, amma a zahiri Mahaifiyarku ita ce babba ta bata shekara uku ma a duniya"
Girgirza kai yayi yana jin shima yana buƙatar zuwa ya ganta.
"Inna inaga idan zaku je nima zan biku gaskiya"
"To ai shikenan tunda ka matsa za'aje ɗin. Amma nasan dole rayuka ne zasu ɓaci"
"Mi yasa kike ce haka Inna?"
"Hmm Umar kai dai ayi shiru kawai, amma Asma'u bafa data kirki na faɗa na ƙara faɗa, sai dai kuyi haƙuri da abunda na faɗa ɗin, yaya za'ai ta iya shafe kusan shekara bata leƙo inda muke ba?, dole idan naje sai nayi mata wulaƙancin wallahi"
"Inna a dai bi komai a hankali, wata rana zata gane abunda take ba dai-dai bane ai"
"Har sai yaushe ne zata san dai-daita ne iye Umar?, shekararta nawa a duniyar nan?, ai kamata yayi ace yanzu ita ce zata rinƙa gaya ma wani gaskiya idan yayi ba dai-dai ba, ba wai ita da take babba ba kuma uwa"
Kukan Sadiya ne ya katse masu firar da suke akan Inna Asma'u.
"Mtsww ki tashi kar na zo na iskeki a ƙawancen nan a ƙasa wallahi, zan ɓata miki rai ne"
Ya Umar ya faɗa yana kallon yadda ta wani zube a ƙasa tana rusa kuka.
Tashi tayi da sauri zaune jikinta gaba ɗaya rawa yake na wahala.
"Inna ruwa zan sha dan Allah taimako min"
Ta faɗa gwanin tausayi.
Kamar zaiyi dariya yadda tayi maganar sai kuma ya maze yana miƙewa tsaye ganin har lokacin sallar ƙarfe huɗu yayi yana duban agogon hannunsa yana cewa.
"Inna ni zan tafi sallah saina dawo. Idan Sule ya shigo gidan ki bashi kuɗi gasu ya sake sayo manjan da wannan yarinyar marar hankali ta zubar dashi"
Ya ƙare maganar yana ficewa daga gidan.
Bin bayansa Sadiya tayi da hararara tana hawaye haɗe da jan majina ta ce.
"Mugu kawai Allah dai ya saka min wallahi. Ace duk wata kalar mugunta ya iya ta?"
"Dole zaki ce haka man, kinga ai ya fita bakinki shine ya samu ratar buɗewa"
Turo baki tayi gaba tana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa zuwa can ta ce.
"To ni Inna naga alamar yanzu ma baki so na, wancan baƙin mugun kawai kike so"
"Ki ci gaba dai da ce masa wannan sunan, wata rana ya jiki, ki gane Allah ɗaya ne wallahi"
Rufe bakin tayi da tafin hannunta tana fiddo ido waje, ta saki bakin tana sauke lumfashi kaɗan ta ce.
"Inna fisbilillahi yada wannan mugun fatan kuma?, inshallah bazai ji ba har duniya ta tashi"
"Allah dai ya shirya ki"
Inna ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa Sadiya ta ce.
"Inna naji kamar kuna maganar zuwa Rimaye ko wajan Inna Asma'u?"
"Haka Yayanki Umar yake so muje"
"Inna nima ina son zuwa na gano Aunty Safiya"
Sadiya ta faɗa da murna akan fuskarta.
Ɗan tsayawa Inna tayi tana dubanta sai kuma ta girgiza kai. Allah mai iko babu wadda yake fushi da Asma'u sai ita, su duk murnar ganinta ma suke, hmm lallai jini ɗaya ba wasa bane, amma ita Asma'un ta rasa gane miye ya shiga kanta da har ta mance da danginta?.
Ya Sule ya shigo ɗauke da leda baƙa har biyu a hannunsa.
Cike da garaje Sadiya ta miƙe zata nufi Ya Sule taji cinyoyinta sunyi mata wani irin nauyi sun amsa kamar ana yankan naman wajan.
Ai saita koma ta rashe a ƙasa tana matse hawaye haɗe da cewa.
"Wallahi Allah Inna cinyoyina zafi suke min, kamar ana daddatsa min su ta ciki wayyo Allah nah"
"Subhallahi Inna mi ya same ta a cinyoyin kuma?"
Ya Sule ya faɗa yana saurin ƙarasawa inda take zaune.
Taɓe baki Inna tayi ta ce.
"Ai dai kasan ita zata jawo ma kanta ko?. To faɗan data saba taje ta jawo, aka kawo ƙararta gida, lokaci Umar na nan shine ya hukuntata da tsallan kwaɗo"
"Haba haba Inna, mi yasa Ya Umar yake hukuntata da irin wannan horon?, bafa aso mata suna irin wannan wahalar a jikinsu"
"To ɗan na iya, ai sai ka bari idan ya shigo gidan ka tare shi da maganar, ba wai ka tsaya kana rufe ni da faɗa ba an taɓa ƴar gwal ɗinka ai ko?"
"Nifa Inna ba haka nake nufi ba"
"To idan ba haka bane yaya ne Sule?. Ka riga kasan yarinyar nan bafa jin magana take ba, a haka ma danfa Umar ɗin na garin nan, da abun nata ai kasan sai yafi hakan, ai ni wallahi Umar ɗin zamansa shine dai-dai ya saita min zamanta"
"Dama Inna haka kika tsane ni ne ban sani ba?"
"Kya faɗi haka mana ƴar nema"
Inna ta faɗa tana watsa mata wani kallo.
Kuka ta saki wadda ba hawaye tana cewa.
"Wallahi dama na sani Ya Sule ne kawai yake sona a gidan nan, ke da wancan mugun baku ƙi na mutu ba, kuma wallahi bazan mutun ba, ina nan daram, sai naga tattaɓa kunne na"
Wata dariya ce ta kama Inna ta dara tana kallon Sadiya ta ce.
"Ke za'a bari kiyi gadin duniya ai Sadiya"
Girgiza kansa Ya Sule yayi yana murmushin rigimar Innar da Sadiya bata ƙarewa a kullum.
"Yanzu dai kiyi hakuri, amma ki daina yawan jan faɗa dan Allah. Ga wannan ki ci dama ke na kawomawa"
Da sauri ta amshi ledar tana washe haƙora, ai ganin masoyin nata ne wato biredi da ƙosai yasa ta ƙara sakin dariya tana cewa.
"Kai wallahi Allah Ya Sule na gode Allah dai ya baka Mace ta gari"
Dariya ya saki shima yana kallon Inna ya ce.
"Inna ga manajan data zubar, akan hanya muka ci ƙaro da Ya Umar ya faɗa min na sayo manja na taho dashi gida"
"Au ashe ma kasan laifin da tayi?"
"A'a Inna kawai dai ya ce min na sayo manja. Sai da kika faɗa ne nasan zuwa tayi wajan faɗan ta zubar"
"To shine kuma kake goyan bayanta?"
"Inna zata fa daina duk wannan abun, wata rana ma zaku ce kamar ba Sadiya ba"
"Uhm to Allah ya nuna mana wannan ranar dai"
Inna ta faɗa tana jawo wata ƙaramar tukunya ta zuba manajan ta juyesa a ciki ta yanka albasa a cikin man ta ɗora akan rushin wutar data gama dambu tun ɗazu.
Sule ya miƙe tsaye da sauri ganin lokacin sallah harya wuce ya ce.
"Kash lokaci harya wuce ina nan"
"Au wai dama baka yo sallar ba daga waje?"
"Wallahi Inna, da niyyata fa ina shigowa na miƙa maku sakon nayi alwala na wuce fa, amma na makara bari kawai nayi a gida"
Ya faɗa kwata-kwata baiji daɗin rasa jami'n da yayi ba.
"To ba dole ka makara bama, kana zaune tare da wannan marar jin maganar, ai duk ita ta dauke maka hankali"
"Inna ba ruwanta fa"
"Hmm to ai yayi, tunda dama ba laifinta kake so ba"
Shi dai murmushi yayi yana jawo buta ya fara alwala yana gamawa ya shige ɗakinsu.
Sadiya ta kalli Inna tana turo baki ta ce.
"Wai Inna shikenan kullum ni ce mai laifi a gidan nan?"
"Ke kinga tashi kije ki ɗakko min kwanoni na zubama kowa dambun nan kamin su dawo su iske shi an aje masu komai"
"To nifa Inna naji baki sakawa da ni?"
"Cinyewa zanyi ƴar neman magana, tunda na taɓa abinci na hanaki"
Tashi tayi tana ƙunƙuni ta nufi wani ƙaramin kitchen nasu wadda suke aje kwanoni ta kinkimo su ta kawo ma Innar.
"Yanzu kwano huɗu fa kin san na kowa kuma na ce ki kawo min, amma shine kika kinkimo min kwandon wanke-wanken gaba ɗaya ma ko?"
Zatai magana Inna ta ƙara cewa.
"Kinga ɗauke wa'innan ki mayar dasu"
Ta faɗa bayan ta ɗauki wa'inda zatai amfani dasu ɗin.
Ɗauka tayi tana magana ƙasa-ƙasa.
"Ita Inna yanzu kwata-kwata bana mata abun arziƙi, sai wancan mugun shine ɗan arziƙi kawai a gidan nan yanzu, duk wani abunda yayi shine dai-dai"
Ta ƙare maganar tana murguɗa baki.......
PAGE 19
*SALMA POV*
Tsaye take bakin titi tana tare napep tana ɗan kallon agogon data ɗaura a