Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
nawa Yusura?, ki matsa kawai ta dake nin dan Manzon Allah"
Ummi ta faɗa zuciyarta na ayyana irin abunda zatai ma Aunty Murja, gobe ma bazata ƙara gigin kawo hannu ta ce zata taɓa wani ma ba ita ba.
"Wallahi Allah Yusura idan baki matsa ba a kanki zan sauke wannan abun"
Aunty Murja ta faɗa tana ɗaga ub*an katakon dake riƙe a hannunta.
Ai da sauri Yusura ta matsa ganin da gaske zata rafka mata shi a kai.
Tana matsawa Aunty Murja ta wani taho gadan-gadan inda Ummi take tsaye.
Ummi na murmushin gefen baki, tana zuwa inda take Ummi tasa ƙafarta ta taɓiye Aunty Murja.
Ai sai ga Aunty Murja rikicahh a ƙasa ta faɗi haɗe da gwafje baki a ƙasa, nan da nan bakin Aunty Murja ya fashe ya kuma haye yayi sumtum dashi, jini na zuba.
Ai Ummi ganin yadda bakin Aunty Murja yayi tsini yasa bata san lokacin data kwashe da dariya ba.
Ta duƙa har inda Aunty Murja take ta ce.
"Kin gani ko?, ai taɓa Ummi sai wadda ya shirya, kuma gobe ma ki ce zaki ƙara gigin taɓa ni, wata ƙila ƙafarki ce zata ƙarya, yanzu kin fasa baki dai nan gaba sai ki shirya abunda zai fashe a jikinki"
Tana ƙare maganar tana nufi inda mayafinta yake tasa haɗe ɗaukar jakarta ta kalli Yusura dake ta ɓata fuska, akan abunda Aunty Murja ke jawowa kanta ta ce.
"Kifa yi haƙuri Yusura uwarki ce ke ja ma kanta, tama ci albarkacinki ne da wallahi sai na barta kwance a gidan nan"
"Ai wallahi ub*anki zai dawo sai naji ke yake aure ko kuwa ni?, wallahi sai nasa ya ɗauki mummunar mataki akanki, sai kin gwammace dama baki zo gidan nan ba yau"
Aunty Murja ta faɗa da kyar tana jin yadda bakinta ke mata raɗaɗi.
Dariya ta saki tana cewa.
"Bismillah ai"
Tayi gaba danta rantse bazata ma bari Baba ya zo ya isketa gidan ba.
Yusura zata bi bayanta zuwa waje taji wata uwar tsawa da Aunty Murja ta buga mata, muryar bata fita sosai saboda bakin daya fashe.........
PAGE 30
"Abunda naji kin fara faɗa min a class wai da gaske ne ko kuma dai kawai kin faɗa ne?"
Murmushi kawai Salma tayi tana ɗan shanye ruwan dake gabanta. Sun fito ne bayan sunyi lecture ɗin ƙarfe sha biyu yanzu har biyu da rabi ma ta kusa.
"Shine dai gaskiyar Habiba, ai kin san bama ƴar haka dake"
"Tabɗi ai abun ne da mugun mamaki, wai Mlm Jamilun?"
"Shifa, dan nima kaina mamakin abun har zuwa yanzu bai barni ba"
"To ai dama shi Allah haka yake, wata ƙila sai kama zauna dashi ne sosai zaka iya gane idan baya da girman kai"
"Haka Yusura ta ce ƙanwata, wata ƙila ma yafi haka sauƙin kai a cikin gidansa"
"A'ato kema dai Salma, ya za'ai yayi wannan izzar a gidansa?, mune dai da yake ganin kar a kawo masa raini. Kuma ni wallahi ya burgeni, saboda kinga a hakansa wata ƴar iska bata isa kawo masa shirme ba, duk iyayin mace da feleƙenta bayan idonsa ne, amma da zarar yana waje ƙaryar mace wallahi, bayan idonsa dai ance ana sonsa, ayita maganganunsa amma da zarar kin gansa a gabanki ai wato baki ma san lokacin da zaki shiga taitayinki ba wallahi"
"Hmm bari Habiba nida na zauna a kusa dashi, kinji yadda lumfashi na yake fita kuwa da kyar, kamar wacce ke a gaban dodo"
"Hhhh ai naga ma ƙoƙarinki wallahi, idan da ni ce wata ƙila sai nayi suman wuccin gadi Allah"
Dukan wasa Salma ta kai mata tana dariya ta miƙe daga zaunen da take ta ce.
"Kinga tashi mu shiga aji naga ƴan ajin namu sun fara komawa ciki, bana son zama a baya kuma kin sani"
"Mtsww nifa bana son komawa wallahi lecture ɗin ƙarfe biyun nan zuwa huɗu bana sonta"
"To ai ba lallai ne ma ya zo bafa, kin san bai cika zuwa ba sai anyi sa'a tukunna, nifa danta ƙarfe shidda yasa zan tsaya ta Mlm Hamza, dan kin san baƙin mugu ne shima ace kullum kayi lecture sai ka ɗauki sunayen wa'inda suka halarci lecture ɗinka?"
"Uhm ai ain gaya miki duk masu lecture ɗin huɗu zuwa shidda ɗin nan haka suke mugaye ne, ko dan sun san ba'a wani zama sosai wasu na guduwa shi ne yasa fa suke haka"
Habiba ta ƙare maganar ta miƙewa tsaye a tare suka jera zuwa aji.
Bayan sun zauna a kujerar class ɗin sune kusan na ukun farko-farko.
Habiba ta ɗan karkace tana fuskantar Salma ta ce.
"Allah isa yau ma ki haɗu dashi"
"Na haɗu da waye?"
"A'a shi Mlm Jamilun mana"
Rufe mata baki Salma tayi da sauri tana zaro ido waje ta fara bin wa'inda ke kusa dasu da ido, ganin basu ji abunda Habiba ta ce ba, kowa na harkar gabansa.
"Dan Allah ki rufa min asiri karma wani yaji ki. To ba amin ba, ai yau kona gansa bazan bari shi ya ganni ba wallahi, kuma ma naga kamar yau bai shigo school ɗin nan ba"
Cire hannun Salma Habiba tayi data rufe mata baki dashi ta ɓalla mata hararar wasa ta ce.
"Ban taɓa ganin matsoraciya ba irinki, dalla can miye a ciki to?, ai mu zaki ma kankaroma capacity a cikin school ɗin nan wallahi, aji cewa kuna da alaƙa da Mlm Jamilun"
"Wai bazaki daina kiran sunansa bane haba Habiba?"
"Mtswww naje na kira, ko wani zai zo ya yanka ni ne dan kawai na ce Mlm Jamilu?"
Girgiza kai kawai Salma take tana kallon Habiba da ƙarfin hali, Allah yaso ma class ɗin sai surutu ake kowanne nata harkar gabansa to ba lallai ma aji abunda suke tattaunawa ba, daga Habibar sai ita Salmar.
"Yanzu dai naji abar maganarsa dai haka nan please"
"Ai ko bazan bari ba, ni addu'a ma zanta maku ke da shi"
"Innalillahi addu'a tami kuma?"
Salma ta faɗa tana fiddo ido waje haɗe da dafe ƙirjinta da yayi mata wata irin bugawa, daga Habibar ta faɗi hakan.
"Ai ba sai kinji ba a'ato"
Wata ajiyar zuciya Salma ta shiga saukewa ta rasa dalilin da yasa idan aka haɗata da Mlm Jamilu take jin zuciyarta na bugawa har tana wuce misalin yadda take buga mata a kullum.
Suna zaune har wajan karfe uku da rabi bai zo ba, hakan yasa gaba ɗayansu fita dan ganin ba zuwa ma zaiyi ba.
Sallah kowa yaje yayi kamin a dawo lecture ɗin ƙarfe huɗu zuwa shidda.
Wajan ƙarfe biyar shima ya shigo har wasu sun fara tafiya ma ana cewa ai shima ba zuwa zaiyi ba, sai gashi ya zo ɗin.
Gashi Malamin akwai zuba ya ɗauki lokaci yana masu lecture har wajan shidda da wani abu, ɗalibai sai surutu suke akan lokaci fa tafiya yake ya sallame su haka nan.
Da kyar suka samu ya tattara kayansa ya ƙara gaba kowa lokacin ya jigata sosai kowa gida yake son tafiya.
"Washhh Allah wallahi na gaji kamar zan fadi. Tsakani da Allah wannan Malam Abdullahin ya cika surutu da yawa"
"Ai dole ya daɗe Habiba tunda bai shigo ba sai da aka ci awa ɗaya a cikinta lecture ɗin da zai mana, ai da suna zuwa akan lokaci da yanzu ya sallame mu mun ƙara gaba"
"Hmm bari Salma karki ji yadda na gaji ga yunwa"
"Ai dole muji yunwa tunda abincin safe wajan sha biyu"
Suna tafiya suna magana.
Suna fitowa bakin Get ɗin school ɗin Salma ta tsaya tana duban Habiba ta ce.
"Ki wuce kawai Habiba yau ba sai kin tsaya samar min abun hawa ba, zan samu ne insha Allah"
"Hhhh so kike na tafi kar naga yadda Mlm Jamilu zai rage miki hanya ko?"
"Kin ganki ko?, nifa ba haka nake nufi ba wallahi, kawai dai gara kije kema kina makara, jiya fa kince sai wajan takwas kika je gida, kinga nima wajan bakwai da rabi na isa"
"Ai ke dai bari mu muna shan wahala, kuma kema Allah ne ya kawo Mlm Jamilu ya ɗauke ki ya rage miki hanya, ai da wata ƙilama sai kin fini daɗewa"
"Haka ne yanzu sai gobe ko?"
"Eh ai gobe ƙarfe huɗu zamu koma gida, wallahi nafi son hakan dama"
"Ai yafi duk da dai harda lecture ɗin ƙarfe takwas dai-dai, kin san bana sonta, na tsani duk ranar Monday da laraba wallahi"
"Hmm ai basa ɓata min rai kamar yadda muke kai har ƙarfe shidda Monday da talata da Alhamis, amma kinga ko juma'a da muke kai ƙarfe huɗu duk nafi son su"
"Uhm to gara su kam"
"To shikenan dai sai goben, naji data, please kifa saki jikinki dashi dalla can"
Habiba ta faɗa da zallar zolaya tana dariya ta wuce.
Itama Salma dariyar tayi tana girgirza kai.
Tsallakawa tayi ɓangaren da zata hau napep. Ai tun kamin ta tsallakan taga yadda ake wahalar abun hawa, wasu sai tsaida napep suke amma basa ma tsayawa, dan haka bata wahalar da kanta ba wajan tsayawa tsaida abun hawa a wajan tana tsallakawa ta ci gaba da takawa a ƙafa tana tafiya ita ɗaya.
Tayi tafiya sosai tana tafiya tana ɗan tsayawa ko Allah zaisa ta samu, tunani take ai yau ma kamar bata ga Mlm Jamilu ba, dan bata ga motarsa ba yau a wajan aje motoci na school ɗin.
Wata ajiyar zuciya ta sauke ganin ta tsaida wata napep ta tsaya, saura wajan mutum ɗaya ta cika dama, ta faɗa masa gadon ƙaya zata je, Allah ya so kuntau ya nufa sai ya wuce ta gadon ƙayar, ya ce mata zai aje ta bakin ƙofar gadon ƙayar idan ta yarda, dan ba ciki zai shiga ba wucewa zai yi, ai da sauri Salma ta ce ta yarda, zata iya takawa ma dama da ƙafa ta idasa gida, ai ba wata tafiya bace mai ɗan nisa sosai ba.
Hawa tayi tana cewa, nawa ne zai kaita, mai napep ya ce ɗari uku.
Sai Salma ta ce masa.
"Haba dai Mlm ɗari biyu ce fa nake zuwa nake dawowa fa"
Mai napep ya ce.
"Gaskiya Hajiya ɗari uku ne gaskiya"
Salma ta girgirza kai dan kawai tana son zuwa gida da wuri ne, dama masu napep haka suke masu idan sukaga yamma tayi sai su rinƙa tsawwala masu kuɗi.
"Shikenan Allah ya kaimu lafiya"
"Ameen Hajiya"
Mai napep ɗin ya faɗa yana ci gaba da tuƙinsa........
PAGE 31
*House No 26, Gadon ƙaya, Kano State Nigeria*
Tunda tayi sallama cikin gidan take jin tashin maganar Aunty Murja kamar zata tada gidan dan masifar dake fitowa daga bakinta, a maganganun da take faɗa ne Salma ta tsinci cewa wato Ummi ta zo gidan kenan?, da alama ita ta haddasa wannan faɗan?, dama tasan za'a rina wai an sace zanin mahaukaciya.
"Mlm magana fa nake maka, akan wannan marar kunyar ƴar taka, data zo har gida ta ci mun mutumci, harda su duka na fa tayi, amma naga ka zauna kiyi kunnan uwar shegu dani"
Baba ya aje chokalin da yake cin abinci dashi, wadda Yusura ce da kanta ta jera masa abincin, saboda tunda yasa ƙafa ya shigo gidan ta fara tarbarsa da maganar abunda ya faru, ta inda take shiga bata nan take fita, tama rasa masa bayani yadda zai fahimce ta, sai kame-kame take, daga ta kamo can sai ta kamo nan, dole tasa ya kira Yusura ya shiga tabbayarta abunda ya faru.
Yusura kuwa ta shiga sanar dashi iya abunda ta sani, ai ko nan Aunty Murja ta ta kama Yusura haɗe da kikkifa mata mari, da kyar Baba ya kwaci Yusura, dan bata so Yusura ta faɗi gaskiyar abunda ya wakana ba.
"Mi kike so na ce miki Murja?. Ai tun farko kin riga kin nuna min cewa duk kece kika jawo hakan ta faru dake, nan-nan fa kika kama Yusura da duka akan kawai danta faɗi gaskiya"
"Ohhh ba shakka Mlm, wato ƴarka ta fini a wajenka ma kenan?, ta fini daraja da komai nida nake matarka?"
"Hmm kin mance ita ɗiyata kika ce ai, ke kuma mata ta ce, kinga ana iya canza mata amma ba'a iya canza ƴaƴa"
"Duk wani wulaƙanci da raini wallahi Allah Mlm kaine ka siya min shi a wajan ƴaƴan kishiya gasu nan, amma wallahi tabbas zan fara ɗaukar mataki, bazan ƙara tararka da wata magana akansu ba, ai dai-dai nake dasu, bama suba har iyayen nasu dake can zube a ƙauye dai-dai nake dasu, bare kuma ƴaƴan su"
"Yayi kyau ai dama ko yanzu da ace kina jin magana ta, kuma kina ganin cewa ni mijinki ne kuma shugaba a gidan nan ai bai kamata kiyi duk wannan abun ba, amma can dama baki ganina a matsayin wannan, kiyi duk yadda kike so"
"Yayi kyau Mlm"
Aunty Murja ta faɗa haɗe da miƙewa kamar zata tashi sama.
Saura kaɗan ta bangaje Salma Allah ya so Salma ta matsa da sauri, ta waigo haɗe da watsa mata wani mugun kallo.
"Salma kin dawo?"
Baba ya faɗa yana miƙewa tsaye shima ganin har an fara kiran sallar bangaruba gari ya soma duhu.
"Eh Baba"
"To yayi kyau ki shiga ciki ko?"
"To Baba saika dawo"
Amsa mata yayi yana ficewa daga gidan gaba ɗaya.
Ɗakinsu ta nufa tana sauke ajiyar zuciya tana tunanin Aunty Ummi taja mata wallahi, tasan duk abun nan akanta zai ƙare ta sani wallahi.
"Ah ah Yusura miye kike kuka?"
Shashshekar kuka Yusura take tana haɗiyar zuciya tana share hawayen dake zubo mata ta ce.
"Ba komai Aunty Salma"
Zama Salma tayi a kusa da ita tana girgiza kai ta dafata ta ce.
"Ban yarda ba wallahi, mi yake faruwa ne a gidan nan yau bayan na tafi school miye abunda ya faru?"
"Akan zuwan da Aunty Ummi ne da tayi gidan nan, ba wani abu yaja duk wannan ba Aunty Salma sai Umma duk ita ce silar komai wallahi"
Nan Yusura ta shiga sanar da Salma abunda ya faru daga farko har ƙarshe.
Sauke ajiyar zuciya Salma tayi tana dafe kanta ta ce.
"Kai wayyo ni Aunty Ummi, Aunty Ummi, Aunty Ummi, hmm halinta sai ita wallahi, ai itama harda ita, fisbilillahi miye na tsayawa tayi mata rashin kunyar nan da har haka, ai komin lalacewarta dai tana auren ubanamu ko?, ta ci albarkacinsa ai"
"Uhmm Aunty Salma wallahi ko kaɗan banga laifin Aunty Ummi ba, idan ba'ama Umma haka bazata taɓa gane gaskiya ba, bazata gane abunda take ba dai-dai take yi ba, wallahi duk da mahaifiyata ce bana jin daɗin halinta ko kaɗan wallahi"
"Hakane ai ke halinku ba ɗaya bane, kamar ma ba ita ce ta haife ki ba, idan ba an faɗa ba, duk da dai haka ita uwa ce dole zaki ji ciwo idan akai mata wani abun, dan haka kiyi hakuri kinji?, zan kuma kira ita Aunty Ummi ɗin bata kyauta ba wallahi"
Salma ta faɗa tana miƙewa tsaye ta cire kayan school ɗinta ta fice tsakar gida.
Sai dai tana fita taji gabanta ya ɗan faɗi jin muryar Aunty Murja a waya tana waya tana masifa, sai Salma taji kamar ma da Mama suke wayar.
"Innalillahi kar dai Mama ta kira ta shaida mata abunda Aunty Ummi tayi?"
Salma ta faɗa a fili.
Muryar Aunty Murja ta ƙara ji tana cewa.
"Ni dai na gaya miki, kiyi ma ƴarki gargaɗi ni ba sa'ar yinta ba ce, ke ce dai-dai dani ba ita ba, dan haka ki gaya mata ta kiyaye ni, ta kuma shiga tayi-tayinta, dan wallahi ita ce masha wuya"
Tana ƙare maganar tana datse kiran tana sakin wani dogon tsaki.
Wata sanyayyar ajiyar zuciya Salma ta saki tana girgirza kai, tana wucewa toilet, tana tunanin, yanzu miye abunda Aunty Ummi tayi haka?, gashi suna zaman-zamansu taja ma Mahaifiyarsu an kirata ana faɗa mata magana son rai.
Harta fito daga toilet tana tunanin abunda Aunty Ummi ɗin ta zo gidan ta aikata.
Sai da ta idar da sallar bangaruba tana akan sallaya ta ɗauki wayarta data maƙala a chaji da yake gidan Baba ya saka masu sola ta chaji kawai, saboda rashin nepar da ake yi a Kanon.
Yusura na gefe itama ta idar da tata sallar tana danna wayarta itama tana yi tana murmushi yanzu da alama da masoyinta take chatting ɗin.
"Hello Aunty Ummi"
Daga cikin wayar Ummi ta amsa.
"Amma yanzu fisbilillahi Aunty Ummi haka kika zo gidan nan kika aikata laifin da har kika ja aka kira Mama dage can Rimaye ana faɗa mata magana son rai, kuma duk ke kika jawo haka, hatta nan Baba karki so ganin ɓacin ran da ya shiga fa"
"Kinga Salma, wallahi ba kira ba ko zuwa zatai hakan bazai hana wannan matar ta faɗa min magana ko gobe ne na kyale ta ba. Ai da tayi ba'a tankata ba, amma wallahi Allah banda yanzu, kuma koda ta kira Mama wallahi komi ta gaya mata saina rama nima, ai ina da number ɗin ita Murja ɗin, zata san ta taɓo uwata wallahi"
Ummi ta faɗa a zafafe a cikin wayar.
"Innalillahi Aunty Ummi ina so na gyara lamarin, ke kuma kina neman ƙara dagula shi?, haba Aunty Ummi, dan Allah ki daina wannan abun haka mana"
"Zaki ɓata yawun bakin ki ne Salma dan haka idan wannan abun yasa kika kira ni to sai anjimanmu, dan nasan ni yadda zan ɓilloma abun"
Ta faɗa tana datse kiran.
A zabure Salma tabi wayar da kallo.
Wai anya Aunty Ummi ce kuwa?.
Take tabbayar kanta a zuci.
Duk da tasan dama Aunty Ummi akwai zuciya, idan ta hau wannan dokin zuciyar tofa bata ji bata gani, mai iya saukar da ita sai Baba kaɗai, ko Mama sai tayi da gaske.......
PAGE 32
*SADIYA POV*
Kamar zatai kuka ta kalli Inna data fito zata ɗora sanwar rana ta ce.
"Inna dan Allah ki taimaka min kinga har yanzu banyi rabin wankin nan ba kuma wallahi Allah na gaji hannuna ya fara mini zafi"
Inna kallo ɗaya tayi mata ta ci gaba da yin aikinta kamin ta ce.
"Shi dama marar jin magana ai shike jawo ma kansa koma miye"
"Ni dai