Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   33 / 36

96K to 99K   out of 106.4K words

babu jere saboda tuni Babanku ya tura maza sun wuce da kayan ɗakinku kowacce kayan da yayi mata daga wajan da aka saye su aka wuce dasu kai tsaye gidajan naku, shi yasa kowa idan ya tashi zaije ya gano gidan dole. Ita kuma dangin su Amminku su saida suka bi baya suka je suka ƙara gyara gidan Safiya ɗin, ni dama gaskiya yadda Mlm ɗin yayi ma dai-dai ne, dama daga can Kano na kira Auntynku Sakina ita taje taga gida yayi kyau kam sosai, kuma matar shi Jamilun ta tarbesu da mutumci wallahi kuma naji daɗi, sai santin gidan suke. Part ɗinki daban hakama nata daban akwai ma tazara mai yawa su Sakina suke ce min, hakama part ɗin yaran shi daban na maza dana mata, gidan nashi dai a tsari yasa ayi sa gaskiya, dan ba ƙaramin gida bane"

Jinjina kawai Ummi ke yi tana amsa ma Mama da kai.

Zuwa can Mama ta ce.

"Yaushe kike cewa zaki je ƙunshi ne?. Na ɗauka ma Kano zaki je ƙunshin ai?"

"No Mama kawai zan tsaya nan Iya mai ƙunshi dake nan bayanmu tayi min, na zane amma ja nake so, zan saka Maryam ta taho min da irin lallain su na can Kano, ayo min haɗinsa da komai da komai, sai naje ta zana min kawai, ba sai naje ko ina ba"

"To hakan ma yayi, ai naga yarinyar ta iya ƙunshi sosai ko a birnin iya abunda akeyi kenan ai ko?"

"Tama fi wasu iyawa wallahi Mama"

"To ai hakan ma yafi ki tsaya a nan ɗin, dama ni bana son yawon da amare ke yawan yi. Sana gobe Ladidi mai gyaran jiki zata zo daga Sokoto keda Safiya zata fara yima gyaran jikin insha Allah"

Amsawa Ummi tayi tana kallon wayar ganin kira ne zai shigo ganin haske kiran ne kuwa ya shigo, ganin mai kiran yasa Ummi ɗan miƙewa tana ce ma Mama ina zuwa.

Ɗaki ta shige tana zama a bakin gado sana ta ɗauki wayar.

"Assalamu alaikum"

Daga can ya amsa yana sauke lumfashin daya saka ma Ummi jan ajiyar zuciyar data bata shirya yinta ba.

Magana sukai duk akan shirin bikin da za'a fara nan da kwanaki kaɗan.

Ya nemi ko zatai wani abu na event's ta ƙara tabbatar masa da bata da sha'awar yin komai sai party ɗaya shima kuma a cikin gida ne mata ne kawai zasu halatta ayi a watse sai kuma ranar Al'hamis data ce masa zatai wa'azi shima kuma a cikin gidan nasu za'a shirya sa.

Sosai yaji daɗin hakan dama shi baya da buƙatar zuwa wasu party yana da ƴaƴa manya, koda ma ta shirya hakan shi gaskiya bazai je ba.

To sai gashi ma itama bata da ra'ayin yin wani abu.

Sallama sukai suna gama wayar kawai Ummi taga alert ɗin kuɗi daga garesa har naira dubu ɗari biyar.

Ido waje Ummi ke bin kuɗin da kallo tana mamakin yawansu.

Kasa magana tayi sai kawai ta sake kiransa.

Zata fara ce masa sunyi yawa sai kawai taji ya ce.

"Addu'a zaki yi min Allah ya ƙaro wasu masu albarka kinji matar Jamilu?"

Murmushi ta saki ta shiga kwararo masa Addu'a sosai yana amsawa da jin daɗi.

Suna gama wayar Ummi ta shiga tunanin Salma tana kallon wani waje daban tana cewa a fili.

"Allah sarki Salma, Ubangiji yasa kin huta, yasa iyakar wahalar kenan"

Sai ta saki kuka tana kaiwa ƙarshen maganar.

Ta daɗe a haka kamin ta miƙe ta shiga toilet ɗin nakin ta wanko fuskarta dan kar Mama ta gane tayi kuka.

Parlon ta fito tana zama ta shiga gaya ma Mama kuɗin daya saka mata.

Sosai Mama itama ke faɗan ai sunyi yawa wa'innan iyayen kuɗi haka?.

Ya Muhammed ne ya shigo yaji ana maganar sai ya bawa Mama shawarar kawai ayi amfani dasu wajan ƙara abincin da za'a tarbi baƙin da zasu zo wajan biki ayi komai a wadace.

Shawarar Mama ta ɗauka nan take kuma Ummi ta tura ma Mama dubu ɗari uku ita kuma ta riƙe sauran, harta bawa Ya Muhammed ma dubu hamsin a ciki shima yayi hidimar bikin.

Murmushi yayi cikin jin daɗi ya ce.

"Mrs J kenan, kinga har mun fara dangwalar arziƙi muma. Amma da kina wani botsarewa, ai Salma ba ƙaramin gata ne tayi miki ba wallahi"

Ai sai suka koma firar Salma, amma ganin kamar firar tata na shirin saka Mama cikin wani yanayi marar daɗi yasa Ya Muhammed kamo wata maganar akan bikin.

**************Shirye-shirye ake sosai a gidan gadan-gadan dan sosai Baba ya kashe kuɗi wajan gyaran gidan kansa, dan gaba ɗaya gidan saida aka sake masa fenti, da wasu fasali na cikin gidan.

Shi yasa duk aikin gidan ya haɗe ma su Mama da Ammi.

Mai gyaran jiki ta zo sai cewa Ammi tayi ai wai ita Safiya Kano zata tafi gobe wajan Inna a can za'ayo mata ƙunshi da kitso da kuma gyaran jikin, wai ai tare da Sadiya Inna zata haɗe tayi masu gyaran jikin, saboda su Innar ma a nan zasu taho za'ayi taron bikin harda na Sadiya, kuma Baba ne zai sake amsar auren Sadiya da Umar a sake shaida shi.

Mama bata ji daɗi ba da ta ɗauki nauyin gyaran jikin nasu ne gaba ɗaya, amma sai ta nuna mata ai ba komai duk ɗaya ne ma. Ta kuma saka albarka a taron da aka haɗe da nasu dana Sadiya.

Shi yasa ranar Asabar Safiya ta wuce Kano, ita kuma Ummi Ladidi ta zo tun daga Sokoto dama ƙawar Mama ce ta fara gyara Ummi ciki da waje, sosai jikin Ummi gyara na rana ɗaya ma Ammi taga yadda ya fara wani irin kyau da ɗaukar ido, fatar jikinta har wani shayinin take.

Ai sai kuma Ammi ta fara jin dama Safiyar bata tafi Kano ɗin ba, duk dai itama Innar wata ce ta kira daga cikin garin Kanon zata gyara Safiya ɗin da Sadiya, amma fa tasan gyaran ƴan Sokoto na daban ne, su ɗin sun san takan gyara da magungunan mata sun san sirrin nan sosai.

Ai kamin ranar Laraba idan kaga Ummi baza iya gane ta ba, tsabar yadda gyaran jikin da ake mata ya amshi fatar jikinta sosai, kamar ka sace ta ka gudu.

Suna waya da Maryam dan yau Maryam ɗin zata taho, su Aunty Sakina ma sun iso, inda Aunty Sakinar keta faɗan Aunty Binta bata ƙaraso ba, ubanmi take da har zata ce wai sai Al'hamis zata zo?.

Mama dai tana rarrashin Aunty Sakinar take ce mata ai Anam ce ba lafiya shi yasa.

Ba dan Aunty Sakinar ta yarda ba kawai dai tayi shiru ne.

A ɓangaren su Yusura ma suna waya da Ummi dan su a can zasuyi taron bikinsu, amma duk a nan za'a ɗaura auren harna Yusura ɗin, kawai dai Aunty Murja ɗin a can zatai taron ta, dan duk ƴan uwanta suna can, dama kuma ƴar can ɗin ce, shi yasa ma kawai Baba ya gyara mata gidanta na can yabarta tayi taron ta a can, amma ɗaurin aure a Rimayen za'ayi sa gaba ɗaya.

Ranar da Maryam ta iso ranar anga murna wajan Ummi kamar zata goya Maryam.

Habiba ma ƙawar Salma a ranar suka ganta, sosai Ummi taji daɗin zuwanta, sai nan take da Habiba suna tare duk inda Ummi tayi suna tare da Habiba da Maryam.

Hatta ƙunshi ma tare suka je, dan Maryam ma bata yo ƙunshi ba duk Iya ce tayi masu ana gamama Amarya Ummi suma akai masu.

Sosai ƙunshin yayi bala'in kyau sai ka ce ba'a garin aka yisa ba, su Maryam sai santin lallan Iya suke suna cewa yo ashe haka kuma nan aka iya ƙunshi?.

Lokacin da suka koma gida sun iske har Safiya ta dawo ita da su Inna harda Sadiya ma da itama za'ai taron bakin nata a nan, dan Ammi ce ta bada shawarar a haɗe taron bakin waje ɗaya.

Su duka ba laifi sunsha gyaran jiki da an kyalle su ansan amare ne.

Sai dai lokacin da Safiya taga Ummi yadda fatar ta ke ɗaukar ido ya bata mamaki, harta kasa haƙuri ta shiga tabbayar waye yayi mata gyaran jiki haka?.

Kai tsaye Ummi ta ce mata wacce dai suka ce su basa so ce ta zo tayi mata shi.

Hatta ƙunshin sosai ya ɗauki hankalin Safiya, duk sai taga ma ita nata baiyi kyau ba, sai ta shiga taɓe baki tana koshe ƙunshin su Ummi ɗin tana wasu maganganu.

Ummi bata biye mata ba, sai Maryam ce tana ɗan biye tana maida mata magana cikin hikima.

Sadiya dai na gefe tana mamakin halin Safiya.

Gida fa ya fara cika sosai dan washe garin Laraba su Anam da Mamanta suka iso, da duk wadda ya kamata ranar ya zo.

A ranar aka shirya wa'azi da yamma, sai kuma party da Ummi ta shirya shi wadda su Safiya basu san dashi ba.

Sosai hakan ma ya ƙara baƙanta ran Safiya amma ba yadda ta iya, itama sun shirya wata dinner a za'ayi a cikin wata boarding school dake Rimayen, wacce aka maida ita wajan yin party da event's yanzu.

Kowanne wajan hidimar daya shirya ya tafi, su kam a babban parlon baƙi su Ummi suka shiya nasu partyn aka kira akai masa dakwareshan, sai yayi kamar bashi ba, sai yayi kamar waje aka kama.

Su Maryam dama sunyi wani anko mai azabar kyau gashi su ƴan kaɗan abun ya bada wani irin kyau da ɗaukar hankali.

Aka kira mai camera daga Kankia ya iya pictures sosai ya zo yayi masu.

Koda aka gama kowannen events suka dawo sai Safiya ta rinƙa tsintar pictures ɗin da su Ummi sukai sosai abun nasu ya ɗauki hankalinta, amma sai zuciyarta taƙi yarda ta shiga kushewa, dama duk abunda zasuyi yanzu sai Safiya ta kushe.

Kuma har cikin ranta tasan nasun yafi nata amma baƙar zuciyar nan tata taƙi yarda da hakan.

Su Yusura ma daga can Kano sai shan shagalin biki ake, dan Ummi nashan kallon pictures ta wayarta da Yusura ɗin ke ɗorawa a status nata tana kuma turo mata.

Wa'azi ma Hijab aka saka iri ɗaya aka kira Mlm Sadiya dake garin Rimaye wacce yawanci ita ke yin wa'azi a garin, ta iya wa'azi sosai tasan kuma miye take yi.........

PAGE 60

Washe gari da safe Ummi ta tashi da wata irin kasala da ciwon jiki.

Maryam dake kusa da ita tana latsa waya ta dubeta ta ce.

"Yaya dai Amaryarmu?"

Ɗan yatsine baki tayi tana faɗin.

"Wallahi jikina ciwo yake min, kinji kamar an min dukan tsiya"

Habiba ce ta miƙe zaune itama da yake duka gidan suka zauna basu wani je ko ina ba a ɗakinsu da ita da Marigayiya Salma suka zauna ana hidimar bikin, su Safiya ma a ɗakinsu suka zauna basu wani je ko ina ba.

"Ai tukunna ma wallahi Aunty Ummi saima idan an gama biki an kaiki gajiya ai ba yanzu ba"

"Ai kam dai gaya mata dai Habiba"

Zatai magana Mama ta shigo ɗakin tana cewa.

"Wai dama kun farka?"

Kusan haɗa baki sukai wajan gaida ita ta amsa cike da fara'a.

"Yawwa ke Maryam fito ki ɗaukar maku kayan kalaci, sana ga ruwan zafi can mai yawa na saka maku saboda da wanka, sai ku tsaya a nan ɗakin kuyi naku wankan, dan ban ɗakin waje mutane sunyi yawa"

"Eh Mama dama gaskiya a nan zamu shirya"

Ummi ta faɗa tana sake tashi tsaye ta nufi toilet ɗin.

Mama ta juya ta fice Maryam kuma ta miƙe tsaye tana bin bayan Mamar.

Jim kaɗan ta dawo ɗauke da kayan abinci da kuloli sai farantai a hannunta gaba ɗaya.

Tana ajewa wata yarinya ɗiyar Aunty Sakina ta shigo masu da biredi da kofuna ɗauke da shayi a cikinsu.

Ajewa tayi Habiba na mata sannu.

Sai da Ummi ta fito suka dube ta gaba ɗaya suka sakko ƙasa itama ta zauna suka fara cin abincin suna yi suna mata tsiya.

Suna gamawa Ummi ta miƙe tana hawa gado ta zauna haɗe da kwanciya rufda ciki tana sauke lumfashi ta ce.

"Please Maryam amso mana ruwan wankan nan mana, ko nayi wankan naji ƙarfi-ƙarfin jikina"

Tashi Maryam tayi tana cewa.

"Ban taɓa ganin Amarya mai langwaɓewa irinki ba"

"Bazaki gane ba, wannan hayaniyar ta gidan nan ma data fara yawa ta fara hawan mini kai wallahi, yanzu haka kaina ciwo yake min"

"Dama haka kike ai baki son yawan mutane"

"Uhmm"

Kawai Ummi ta faɗa tana sake gyara kwanciyarta.

"Ni kam Aunty Ummi ɗaurin auren na ƙarfe nawa ne?"

"Kamar sai an sallamo daga masallaci za'a ɗaura gaba ɗaya"

"Ohh hakan ma yayi dan motocin amarya zamu bi daga can zan wuce gida"

"Tabɗi jam ai ko baki isa ba wallahi, sai kin kwana gidan Amarya, ba'a gama biki ba zaki wani ce zaki tafi?"

"To ai Aunty Ummi Kano mu ba'a fa kwana a gidan Amarya"

Ɗan tashi Ummi tayi tana cewa.

"Ai nan ƴar Katsina ya auro, to dole yabar danginta su kwana, haka akeyi, duk ɗan Kano idan har ya auro ƴar Katsina ko ƴar wani garin daban to tabbas ana bari ana kwana, kawai kima shirya kwana gidan Amarya yawwa"

Dariya kawai Habiba ta saki tana girgiza kai, sai ta tuno da Salma tana mata addu'a a zuciyarta. Komai da Ummi ɗin ke mata yadda kasan Salma ɗin na nan, bata taɓa nuna mata wani abubu ba, ɗaukarta take ma kamar itama ɗin ƙawarta ce, dan duk abunda zasuyi da Maryam harda ita a ciki.

Maryam ce ta shigo ɗauke da wani farin bokiti cike da ruwan zafi ta kai toilet tana fitowa ta zauna kusa da Ummi tana ɗan dukan bayanta da wasa ta shiga ce mata.

"Saiki tashi ai kiyi wankan, naga har goma da rabi ma tayi, ya kamata ace amarya ta fara shiga tana fita tun yanzu"

Murmurshi kawai Ummi tayi tana neman tashi tsaye, sai kuma wayarta data aje yanzu ta fara ƙara alamar ki ne ya shigo.

Kallon cikin wayar tayi ganin wadda ke kiran yasa Maryam riƙe baki tana cewa.

"Kambuji, lallai ma Ummi ɗi nan, yanzu ke seving ɗin number nashi ne kika wani saka masa J.S.M kawai?"

"To miye a ciki, ai sunansa ne kawai na ɗan yi...

Ɗaga mata hannu Maryam tayi tana jawo wayar da sauri kamin ma Ummi ɗin ta ɗauka tana tsinkewa ta shiga wajan gyara seving na numbers ta shiga gyara sunan ta goge wadda tasa ita kuma ta saka mata My Nurulhayat da Arabic, da ƴan emojis na love a gaba.

"Waye ya saka ki?"

Ummi ta faɗa tana dariya tana duban sunan data gani wadda Maryam ta saka mata.

"Wallahi baki isa ba, kuma baki isa sake wani sunan ba Allah kuwan. Lallai ma matar nan, yo haka ake yi kawai ki tashi ki wani saka ma ɗan bawan Allah wani sunan da bai dace dashi ba"

"Hhhh kuma fa Aunty Maryam wallahi tana so tana kaiwa kasuwa ne"

Dariya Ummi ta saki tana sakkowa daga gadon tana ce masu.

"Ku dai kuka sani"

Ta shige toilet tana jin yadda suke mata tsiya tayi banza dasu ta shiga toilet.

Tana shiga wani kiran nashi ya shigo, kallon wayar Maryam tayi tana faɗin.

"Kaga masoya fa tunda safe ya kira za'a fara tsinkar fire. Wai ma ka ce Mlm Jamilu ne zai iya haka?"

Wata shewa Habiba ta saki tana tashi daga inda take dan tunda suka gama cin abincin bata tashi ba tana zaune ne tana latsa wayarta ta ce.

"Yo Aunty Maryam ai fiye da hakan ma zaiyi, ke baki san irinsu sunfi iya nuna soyayya mai zafi ba?"

"Hakane fa wallahi"

Maryam ta faɗa suna tafa hannu da ita da Habiba suna dariya.

Koda Ummi ta fito tayi wanka sai uban ƙamshi take data gitta mutum sai ƙamshi kamar wacce ta ɓarar da turare a jikinta.

"Ke angon naki saifa kira yake, so yake yaji yaya lafiyar matarshi take"

Ummi zatai magana sai Habiba ta rigata cewa.

"Ni kam Aunty Ummi ina akai miki gyaran jikin nan?, ga wani ƙamshin humra da kike tayi da kin gifta wallahi sai uban ƙamshi zaki barma mutane tunda na iso nake ta so na tabbaye ki, jikinki yayi kyau wallahi"

"Au ai Aunty Ladidi ce ƙawar Mama ke min gyaran jikin, yanzu hakama tana nan yau ma sai ta zo tamin yanzu ma zaki ganta, ai ita Maryam ta santa, a Sokoto take"

"Wow no wonder ai shi yasa zatai miki gyaran jiki irin nasu na ƴan Sokoto, wallahi suda mutanen Maiduguri sun iya gyaran jiki, gyaran jikinsu na daban ne, ai ko za'a bani number ɗinta na sai wannan humra ɗin mai bala'in ƙamshi da ita da turaren wutar nan na kabbasa da kike turara jikinki dashi, shima akwai ƙamshi na bala'i ma"

"Kai wai na bala'i ma?, wato harma bala'i yake?"

Maryam ta faɗa.

"Ai wallahi Aunty Maryam turaren nata ne akwai riƙe kaya, jifa tun jiya data saka bai saki jikinta ba, har yanzu ƙamshi kawai take"

"Ai turaren wutar ta na kabbasa da humra ɗinta sunyi, dan nima saina saya insha Allah"

Haka sukai ta firar gyaran jikin da akaima Ummi ita kam Ummi Mama ta kira aka kira Ladidin ta zo ta fara gyara Ummi ɗin.

Su Maryam na gani gyara na rana ɗaya idan akai maka yadda kake komawa. Ita kam Ummi sai ta zama kamar wacce aka ɓare a leda.

Sosai Ladidi ta gyarata ta turareta da turaren kabbasa na wuta, da wata Lifaya fara da zata saka aka turareta da uban turare na jiki da kabbasa.

Da kanta ta ɗaura mata Lifayar ba ƙaramin kyau tayi ba ta fito a amaryar tata zam.

Bayan an gama shirya Ummi sai ga aike inji Ammi wai dan Allah Ladidi mai gyaran jiki taje zata ma su Safiya da Sadiya.

Da Ummi harta fara faɗan wallahi ba inda zata je, ai da raina gyaran jikin sukai su duka daga Ammi ɗin har ita Safiyar.

Mama ce ta ce ma Ladidi taje ba matsala, ai dai ko yanzu kafi mutum.

"Nifa ko wallahi mamaki wasu suke bani"

Maryam ta faɗa bayan Ladidi

33 / 36