Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   26 / 36

75K to 78K   out of 106.4K words

munafuka kuna tare fa, ana soyewa shine ko ki ɗan rinƙa bani labari soyayyar taku ma, ko mun ɗan koyi irin salon taku soyayyar"

Dariya Salma ta saki tana shirin magana masu bada tsoron exam's ɗin hall ɗin nasu suka shigo mace ɗaya namiji ɗaya.

Dan haka kusan gaba ɗaya ɗaliban dake cikin hall ɗin suka miƙe.

Macen ce ta fara magana.

"A nan ku kai first semester exam's right?"

Amsawa akai kusan gaba ɗaya ta sake cewa.

"To ai kowa yasan inda ya taɓa zama a wancan time ɗin exam's ɗin?, dan haka kowa ya same waje ya zauna, kuma ayi shiru bama son surutu, duk wadda bai shiryama exam ɗin nan ba yazo kawai ya fice mana daga hall"

Kai daga ganin yadda take maganar da yanayin namijin shima bafa za suyi mutumci ba, dan haka kowa ya shiga hankalinsa, sana kowa ya je inda ya taɓa zama a wancan lokacin.

Habiba bayan sun aje Jakukunansu daga su sai biro ta ce.

"Wa'innan daga gani motsi kaɗan zakai su ce kana satar amsa"

"To ai sai ki natsu idan ba haka ba kija mana ai ko?"

Raba faifar da za'ai exam's ɗin cikinta aka fara hall ɗin ya sake ɗaukar haramin shiru ba abunda kake ji sai ƙarar faifa.

Har wasu sun fara surutu ƙasa-ƙasa bayan an raba komai daya kamata kawai saiga Mlm Jamilu da wani mataimakinsa sun shigo hall ɗin.

Rasssss Salma saida taji gabanta ya yanke ya faɗi, saukar muryarsa da kawai taji, muryar nan mai cike da wata irin izza a cikinta da taushi ga wata irin haiba, muryarsa kaɗai zaka ji kasan mamallakinta baya son wasa ko wargi, ita kanta saita saka mutum ladabtuwa wallahi.

Kasa ɗagowa tayi ta kallesa, ba abunda zuciyarta ke yi sai sun kallon nasa, ga shi sai bugawa take tana wuce misali. Kai bata san lokacin data saki biron da take rubutu dashi ba, tana dafe ƙirjinta haɗe da sakin wani hucin lumfashi tana ci gaba da sauke ajiyar zuciya yadda kasan wacce tayi gudun tsire.

Daki-daki yake bin ɗaliban da kallo haɗe da fara tabbayar number ɗin exam's ɗinka ta school ɗin, ganin kamar a hargitse aka jera ɗaliban yasa ya ce gaba ɗaya a sake jera su, gaba ɗaya kowa ya fice sai an sake jerawa.

Su Habiba suka fita gaba ɗaya da sauran ɗalibai, Allah ya so ba'a fara exam's ɗin ba.

Kiran number aka fara yi ana shigowa ɗaya bayan ɗaya, duk wadda ya kuskure bai amsa number tashi akan lokaci ba, kai tsaye yake ce maka get out kawai.

Wasu ɗaliban na bada haƙuri amma idan kayi sa'a ma ya kalleka to ba ƙaramar sa'a ka taka ba a ranar.

Dole wasu da basu amsa numbers nasu ba suka ja suka tsaya daga gefe suna ƙara bada haƙuri da magiyar yayi haƙuri.

Bayan kowa ya gama shiga wa'inda aka hana shiga suka ja suka tsaya cirko-cirko kamar wasu sojoji.

Yana fita daga hall ɗin sai Salma taji kamar an sauke mata wani gagarumin dutse ne a tsakiyar ƙirjinta, dan har wata iska taji tana shiga hancinta sosai, ai da ji take lumfashinta ma da kyar yake shiga hunhunta.

Wani Malami ne ya zo inda sauran ɗaliban da basu shiga hall ɗin ba yana ce masu.

"Baza kuje ku bashi haƙuri ba right?, maza ku bisa ku basa haƙuri, dama a haka ake bada haƙuri a gidajanku?, har ƙasa zaku kai ku duƙa ku bashi haƙuri, wata ƙila ya tausaya maku"

Kusan a tare suka nufi inda yake.

Su Salma na ɗan hange daga nesa basu san dai ya aka ƙare ba, sai gani sukai gaba ɗaya ɗaliban sun shigo hall ɗin suna ɗan murmushi, da alama an barsu.

Wajan sha ɗaya da rabi Salma kusan ita ce ta farkon badawa sai wasu suka fara tashi suna bada faifar exam ɗin.

Habiba kuwa sai da ta ɓata lokaci har Salma na leƙenta tana mata magana da ido akan dan Allah ta bada haka nan mana.

Da kyar Habiba ta bada faifar nan kamar karta bada.

Tana fitowa Salma ta kai mata dukan wasa tana gocewa ta ce.

"Wai ke dole sai kin cinye exam ɗin nan duka ne?, ke kullum idan aka zo exam's fa haka kike ɓata ma mutane lokaci"

"A'ato wallahi sai na kusa gamawa nake jin wasu abubuwan dana karanta na sake dawo min fa, shi yasa ni kuma bana badawa wallahi saina juye su a faifar exam ɗin tasss, ke nifa wallahi koda babu abunda na karanta daga ƙarshe saifa na juye duka abunda na karanta, dan ni bana karatun banza a'ato"

Murmushi kawai Salma ta saki suna tafiya ta ce.

"Nima ina haka amma sai na gama da wa'inda naga sun fito"

"Ke ba wannan ba, yau baza ku haɗu da Mlm Jamilu ba wai?, naga kun daɗe baku haɗu ba, kuma fa naga sai kallonki yake a hall daya shigo"

"Bana son ƙarya ni Habiba, yaushe ya kalle ni ɗin?"

"Kina jin wasa ko?"

Salma zatai magana sai kuma ta ɗan tsaya tana sauke lumfashi mai wahala, a hankali ta dafa Habiba tana jin jiri kaɗan, tama yi mamaki da tunda ta shigo school ɗin bata ƙara jin wata alamar jiri na ɗibarta ba, sai yanzu da tsayuwar tasu tayi yawa suna magana.

"Miya faru Salma?, kina lafiya dai ko?"

Girgiza kai Salma tayi a hankali ta ce.

"Ina lafiya, kawai ina ɗan ganin jiri ne kaɗan"

"Haba daga gani wallahi dama baki warke ba, duk wadda ma ya ganki yasan baki gama warkewa ba, ko baki daɗe da tashi daga ciwo ba. Yanzu dai muje na kaiki gida, gobe kinga Mlm Jamilun"

Murmushin yaƙe kawai tayi tana ɗaga kafaɗarta, alamar eh, amma tun da safe ta kira wayarsa bai ɗauka ba, bai kuma biyo kiranta ba, kira ɗaya ta masa bata sake ba. Sai kawai taji zuciyarta ta karya jikinta yayi sanyi da al'amarin Mlm Jamilun sosai.

"A'a Habiba ki barshi zan iya tafiya da kaina wallahi"

"A'afa sai na kaiki har gida"

"Kin san Allah zan iya, na gode da kulawa"

"Shikenan to zamuyi waya idan kin isa please ki kira ni"

Da to Salma ta amsa dai-dai wata napep tazo wucewa fitowarsu daga school kenan, mai napep ya ce, shi juyawa zaiyi.

Habiba ta ce eh dama can zasu tsallaka, zai je gadon ƙaya ne please?.

Ya bata amsa da eh amma bazai shiga ciki ba zai wuce ne, sai dai ya aje ta a ƙofar gadon ƙayar.

Salma duk da tasan bazata iya wannan uwar tafiyar ba zuwa cikin gadon ƙaya zuwa gida ta amsa da eh ta sauke ta kawai ta sake hawan wani ya idasa da ita, dama naira hamsin ne ai suke idasa kai ka.

Har sai da Habiba taga ta hau napep ɗin sana ta juya itama ta tafi.

A wajan Salma tana sakin nufarfashi a hankali ta ɗakko wayata zuciyarta na sake azal-azalarta ta ƙara kiransa taji.

Har suka isa gadon ƙaya Salma na faman kiran numbersa amma ba'a ɗauka daga ƙarshe ma da ta fiye kiran nasa sai ta dawo idan ta kira sai taga ance mata kamar ma a kashe take.

Haƙura tayi tana jin jikinta na sake ɗaukar zafi-zafi kamar mai shirin kamuwa da zazzaɓi, hatta miyaun bakinta ji tayi ya ƙafe, sai haɗiyar zuciya take kawai.

Ana sauke ta a ƙofar gadon ƙayar ta ƙara tsaida wata napep ɗin ta shiga, tafiya kaɗan ce aka sauketa tana son idasawa gida tana jin yadda wani irin jiri dole ke son kada ita, yasa da sauri ta samu waje ta zauna tana dafe kanta tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi.

Wani abu ta tuna. Ƙaramar wayarta akwai layin da bai santa dashi ba. Sai zuciyarta ta bata ta kirasa mana da baƙon layi taga zai ɗauka, idan kuwa ya ɗauka ta tabbata dai ita ce baya son ɗaukar kiran nata kenan?.

Zuciyarta na bugawa ta danna number nashi tana kira, a mamakinta sai taji ta shiga, saɓanin number ɗinta daya sani idan ta kira bata ma shiga, duk bugu ɗaya na shigar kiran sai zuciyar Salma ta motsa.

Saida ta kusa tsinkewa taji an ɗauka, da harta fidda rai da zai ɗauka, hankalinta harya fara kwanciya.

Sai dai ganin ya ɗauki kiran yasa Salma sakin baki zuciyarta na duka a ƙirjinta, bata san lokacin da taji hawaye masu masifar zafi nabi mata fuska ba, wani irin raɗaɗin zuci ne ya tokare mata maƙoshi da kyar ta amsa sallamar da yayi mata.

Duk da yaji muryarta sai ya nuna baima san wacece ba, da kyar Salma ta danne abunda ke taso mata tana masa bayanin kanta.

A bayanin ma da kyar ya iya shaida ta.

Ai Salma kawai saita sakar masa kuka mai masifar ciwon da take jinsa a ƙasan ranta.

Daga can tana jin yadda ya wani sauke ajiyar zuciya, ya ɗan fara rarrashinta yana cewa.

"Please Salma, banga kiran ki bane, kiyi haƙuri kinji please ki daina kukan nan?. Ni mutum ne bai busy da yawa banga kiran naki ba kwata-kwata"

Ai ji Salma tayi kamar ta mangaresa amma ta danne tana share hawayen dake zubo mata, Allah ma ya so ta babu jama'a a wajan gidan nasu.

Daɗin baki yayi mata yana cewa zai kira ta inshaa Allah yanzu yana ganawa da wasu baƙi ne.

Kamar dai yadda zuciyar nan tata mai ƙaunarsa hakama wannan lokacin tayi sanyi tana masa uzuri kuma kamar yadda ta saba, jin muryarsa kawai da kuma daɗin bakin daya saba mata shi ya wanke dukkanin laifinsa da ɗan zarginsa data fara yi.

Da ɗan murmushi ta miƙe tana nufar cikin gidan.

Tana jin wata kwarin gwaiwa na zo mata, dan kamar an yaye mata wata damuwa kaso ɗari data taho da ita, jin muryarsa kawai da maganar da sukai ta kore mata wata damuwar.

Sai dai tana gaf shiga ciki gidan kawai taji jini yana fitowa ta hancinta, dama tasan tabbas sai hakan ta kasance bare yau tasha kuka kuma ranta ya ɓaci, tama yi mamaki da bata ji jinin ya zubo mata ba tun ɗazu, amma yau babu tarin nan sai jinin kawai data gani yana zubo mata.

Wani kyalle tasa tana gogewa da sauri dan kar wani tsautsayi yasa wani ya fito ya ganta a halin da take ciki hankalinsu ya ƙara tashi.

Sai dai tana cikin gogewa wani tari kawai ya sarƙe ta, da sauri ta juya tana fita daga zauran gidan kar wani daga cikin gidan yaji tarin nata.

A waje sai da ta gama uban tarin da take jin ƙirjinta kamar ya buɗe, idonta yayi jawur saboda tarin, jini ta gani kaɗan na zubowa ata bakin bayan tarin ya lafa. Miyau ta tattaro tana tofar da jinin daya zubo ta bakin nata haɗe da sakko da jakarta akwai ruwa a ciki ta kuskure bakin nata dashi, tana sauke lumfashi mai zafi, tana ganin wani irin dishi-dishi kamar zata zube ƙasa.........

PAGE 51

*Bayan wasu kwanaki*

*SALMA POV*

Zaune take riƙe da farar takarda a hannunta tana yin rubutu a cikinta.

Shigowar da taji za'ai ne yasa ta ɓoye ta da sauri tana sauke ajiyar zuciya"

"A'a ya na ganki nan a zaune?"

"Nifa Aunty Ummi bazan je wajan Doctor Nura ba, dama kince masa yaje kawai na warke, kuma na gode da kayan daya sayo min"

Zama Ummi tayi tana bin Salma da kallo kawai. Tunda kwanaki ta shigo gidan tana ganin jiri da dishi-dishi bata ganin mutane sosai, duk da irin yadda taso ta ɓoye amma ina, saura kaɗan ta zube a ƙasa. Hankali a mugun tashe Ummi ta tarbota jikinta.

Allah ya so tana da number ɗin Doctor Nuran shi tayi hausar kira ya zo.

Kai tsaye asibitin daya kasance nashi ne suka nufa.

Koda yayi bincike akan abunda ke damunta sosai hankalinsa ya tashi. To tun daga wannan rana shike kula da duk wani al'amarinta idan ciwon nata ya tashi, hatta Baba yasan dashi, sun saba shi yasa ma yanzu da ya zo har gida yake shigowa.

Aunty Murja har lokacin bata wani saduda ba, neman rigima kullum tsakaninta da Ummi ƙara gaba yake, wani lokacin idan suna yin abun kan bawa mutane na kusa dasu dariya.

Idan da sabo sun saba kamar wasu sa'annin juna, kamar suna ganin ƴan hanjin juna.

Shike zuwa dubata duk bayan kwana uku ko fiye da hakan.

Yanzu ma ya zo ne domin dubata sana ya kawo mata kayan graduation. Dan duk yana bin abubuwan da take so, ita kanta bata san ya san yaushe suke graduation ɗin ba, sai yau daya zo mata da uban kayan graduation ɗin da ada ta ce baza tai komai bama.

Saboda tun ranar data dawo suka fara exam's ta farko tayi waya da Jamilu to tun ranar bata ƙaraji daga garesa ba. Zata iya cewa kusan babu ranar banza da bazata kirasa ba amma baya ɗauka. Tun ranar tayi ta jiran kiransa amma bai kira ba, duk da tasan dama da wahala ya kira ta ɗin, amma wannan zuciyar tata na sake masa uzuri, tana kuma jiran kiran nasa, danma kira ɗaya take masa, tana danne damuwar dake cin ranta. Tana yin iya bakin ƙoƙarinta wajan ɓoye abunda ke faruwa a tsakaninta da Jamilu dan kar ta faɗa ma wani ya riƙesa a rai, ita kuma bata ƙaunar wani ya ce ga laifinsa ko ya zagesa ya kushesa.

"Da ke nake magana fa Salma?"

"Uhum Aunty Ummi mi kike cewa ne?"

"Hmmm dole man kiƙi jin abunda nake faɗa, tunda ina magana kin lula duniyar tunanin daya riga ya aureki. Wai mi yasa bazaki mance da Jamilu ba, akansa fa kika kamu da wannan ciwon?, mi yasa bazaki buɗe zuciyar taki ki bawa wani dama ba?. Yanzu dubi uwar hidimar da Doctor Nura ke miki baya ma gajiya da hakan, idan banda shi wallahi na tabbatar yanzu ciwon nan naki ya gama cinye miki komai naki, da yanzu wata maganar ake ba wannan ba"

Shiru Salma tayi tana jin tabbas idan baccin Doctor Nura daya san takan ciwon nata yana kuma iya bakin ƙoƙarinsa wajan zuwa yana duba yanayin jikin nata da lafiyarta da yanzu tabbas wani zancan ake.

Ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani iri ta ce.

"Wallahi Allah Aunty Ummi da zan iya cire son Jamilu da tuni nayi hakan, nima kaina wani lokacin ina jin haushin kaina, ƙaddara ta ce na sani da Allah ya jarabe ni da son Jamilu, na kasa ciresa a raina, duk yadda na so mantawa dashi kasawa nake yi"

Ta ƙare maganar hawaye masu zafi na zubo mata.

Wani abu ta haɗe a maƙoshinta tana saka hannu ta share hawayen kamin ta sauke hannun nata sai ga jini ya taho ata hancinta.

Ido waje Ummi ta ce.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Salmahhhhhh. Dan Allah daina kukan nan haka nan, ki rufa min asiri, yaushe rabon da aka jinin nan ya zubo miki?"

A ruɗe Ummi ke maganar, dan rabon da suka jinin tunda Doctor Nura ya fara dubata. Yau ma ɓacin rai ne ya sakata hakan.

Ummi na shirin fita a ruɗe wai ko ta kira Doctor Nura ya zo ya gani.

Sai Salma ta riƙe mata hannu ta ce.

"Dan Allah karki sanar da kowa, bana so a ɗaga ma Baba hankali dake can gida Rimaye, nasan kuma muddun kika fita sai Aunty Murja ta kirasa ta faɗa masa"

Kamar bazata dawo ta zauna ba, sai kuma ta fasa tana dawowa ta zauna ta ce.

"Tom kiyi shiru haka nan please ki kwantar da hankalinki dan Allah duk abunda Allah yayi dai-dai ne, na tabbatar miki idan har bazaki mutu ba har sai kin aure Jamilu, to tabbas ko yaƙi ko ya so dole ne sai ya aure ki, ni dai abunda nake so dake ki daina wannan damuwar da taƙi ci taƙi cinyewa. Kuma kinƙi bada damar a sanar dashi akansa zaki iya mutuwa, wannan fa ciwon naki duk akan son shi ne da kike yi, shi kuma baya take, ki bari a sanar dasu Baba su suje su sanar dashi, tun kan waje ya ƙure"

"A'a bana so a sanar da kowa Aunty Ummi, akwai lokacin da idan yayi zan baki damar ki sanar dasu ɗin"

"Sai yaushe ne Salma?"

"Yanzu dai muje ki rakani wajan Doctor Nuran nayi masa godiyar kayan nan"

Salma ta faɗa dan tana son kauda tabbayar da Ummi ɗin ta jefo mata.

Girgiza kai kawai Ummi tayi tana binta da kallo ta ce.

"Muje yana parlon Baba na saukar baƙi. Ga Aunty Murja can dama wai kar a ɓata parlon saboda baƙin ƴan kawo lefe da zasu zo. Ta fara bani haushi fa"

Tashi tayi da kyar tana jin juya na neman kayar da ita, da sauri ta tattaro ƙarfin hali dan kar Ummi ta lura da yanayin ta.

Ummi ɗin kamar ta sani ta kamo hannunta suka fice zuwa parlon baƙin.

Salma na sake bawa Aunty Ummi baki akan lamarin Aunty Murja ɗin.

Doctor Nura kallo ɗaya yayi mata ya gane kamar yau ba lau take ba, amma dai ya danne ganinta tana murmushi haɗe da gaida sa tana haɗawa dayi masa godiya.

Tabbayoyi ya fara jefo mata akan yanayin jikin nata, yadda take nuna masa da basa amsa kamar ƙalau take, shi dai badan ya yarda ba kawai ya barta a yadda ta ce masan, dan gani yayi da bata son magana dashi kwata-kwata danma Ummi na zaune a wajan.

"Yaushe ne graduation ɗin?"

Ya faɗa yana kallon Ummi haɗe da kallon agogon hannunsa.

"Gobe ne Doctor"



Ummi ta basa amsa.

"Ohhb Friday zata kama right?"

"Yeah Doctor kuma sun saka ƙarfe kusan biyu da rabi zasu shiga exam ɗin"

"Okey idan sun gama zamu iya zuwa bikin graduation ɗin?"

Sai lokacin Salma ta ɗago tana dubansa ta ce.

"Noo ba sai kunje ba"

"Why?"

Zatai magana Ummi ta rigata cewar.

"Doctor wallahi nima jiya take gaya min wai shugaban School ɗin ya hana iyaye zuwa dama kowa naka, kawai kaine zaka zo ka zana exam a yi ɗan pictures na aje tarihi, suma kar a wuce gona da iri, sana banda shigar

26 / 36