Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
mai dalili ai ko?"
Tashi tayi a hankali tana dafe cinyoyin nata da ƙafafunta da take takasu da kyar tana yamutse fuska.
"Uhm shikenan Inna gara kawai na tafi school ɗin, dana tsaya Ya Umar yaci karo dani a gidan nan. Kuma fa Inna da ɓoyewa zanyi, basai ya ganni ba zai ce banje ba?, Inna ki rufa min asiri mana dan Allah?"
"Lallai Sadiya, to bada ni ba a cikin wannan gagarumar ƙaryar ba"
"Wallahi Inna baki so na yanzu"
"Zaki ce haka man, tunda dama ke dai baki son gaskiya, kuma dama ai karatun ba wani sonshi kike ba, baccin dawowar Umar ɗin shi da kike tsoro da shakka ai ba zuwa Makarantar kike ba, sai an kai ruwa rana, kuma Sule duk shi ke ƙara lalata ki ai"
"Shi kaɗai dai ke so na"
Ta faɗa tana turo baki.
"Hmm ki zauna kita labari dan Allah har ya shigo gidan ya iskoki baki wuce makaranta ba"
Da sauri ta ɗauki kayan Makaranta dake zube akan kujerar da take.
Tana kallon kayan haɗe da masu wani kallon banza, sai ka ce sune Ya Umar ɗin, dan gaskiya ita a rayuwarta bata son makaranta.
Kayan ta shiga sakawa tana yi tana ɓata rai kamar mai shirin kuka.
Tana gamawa taja ta tsaya ta ce.
"Inna a bani kuɗin tara"
Inna bata ce komai ba ta ɗakko naira ɗari biyu ta miƙa mata ta ce.
"Gashi nan ai kinci abincin safe, wannan ta isheki kashewa, nasan dai kayan maƙulashe ne kawai zaki saya da kayan zaƙi"
"To ni Inna....
"Kinga fa ko Sadiya idan har baza je Makarantar nan ba cire kayan nan kiyi zamanki, nifa na gaji da magana da ɓaɓatu haba. Kuma ma duka ba daɗewa zakiyi ba dakin je za'a tashi, tunda yanzu har goma ta wuce har an tashi tara ma"
"Nifa Inna ba wani abu zan ce bafa. Kuma a haka ne bazan daɗe ba?, sai fa ƙarfe biyu da rabi zan dawo, kuma ace wai ba zan daɗe ba, wai karatun nan dole ne ma ya zamar mutum?, tunda mutum yayi islamiyya ya sauke Alqur'ani mai girma, ai ya ishe shi"
"Dole ne kam ya zame miki wallahi, ke bari kiji ma Allah mudun ina raye muka koma Kano da zama Makarantar gaba da sakandarin ɗin zan saka Umar ya ƙara saki, dan so nake ki zama babbar likita, kima ji da kyau, dan haka kima saki ranki da karatu dan wallahi ya zama dole kiyi sa. Kuma islamiyya itama zuwa zakiyi ki koma, duk da saukar da ki kai, ai zata iya zubewa, tunda a nan ɗin yaushe rabon dama ki ɗauki Alqur'ani ki karanta?"
Ai sai Sadiya ta fara hawaye tana yi tana kallon Inna data juya ƙeya tana lilke wasu kayan wanki da tayi.
"Wallahi Inna nasan an shiga tsakaninmu dake, da ai da baki min haka, duk wani abunda nake so shine kike min, amma tun daga dawowar Ya Umar mugu kika wani canza min. Kuma Inna ni karatuna yana nan na Alqur'ani, ai shi bai cika guduwa daga kanka kamar karatun bokon nan ba"
"Nasan duk salon karki je Makarantar ne, shi yasa kika tsaya kina sani magana, kina zaro zance kamar kanyar data lalace, ki zauna dan Allah karki je. Kuma islamiyya hadda ce zaki koma kiyi nama gaya miki"
"Dan Allah Inna ki barni haka ba sai nayi wata hadda ba, naji zan rinƙa karatun Alkur'anin duk asuba ina yin tilawa, kinji Inna ta?"
"To idan ki kai wannan ne zan kyale ni, amma muddun naga kinsa wasa wallahi sai kin koma islamiyya, tunda dama naga yanzu wasa da jan faɗa duk shike ƙara ɗauke miki hankali da tsayawa kiyi karatun"
Jakar Makarantarta ta ɗauka tana sake turo baki sai ƙunƙuni take tana jin haushin zuwa Makarantar nan.
Fita tayi tana cewa.
"Inna na tafi"
Inna bata ce komai ba tana jinta tayi kunnen uwar shegu da ita.
"Inna nafa tafi na ce miki"
Nanma Inna shiru kawai tayi tana girgirza kanta tana kallon ƙofar ɗakin.
Sadiya data gaji da magana ita ɗaya ta fice daga gidan tana tafiya a hankali kamar bata so.
"To ni yanzu da gaske dai Inna take zanyi karatun likitoci?"
Ta faɗa a fili ita ɗaya take tabbayar kanta.
Sai kuma ta girgiza kai ta ƙara faɗin.
"Nifa na tsani karatun nan, Allah bazan yi ba"
Ta faɗa tana ƙara turo bakinta gaba.
Tafiya take tana nufar cikin Makarantar, da yake Akwai tazara makarantar da cikin garin, waje-wajen gari take, kuma dama Sadiya a SS2 take, duk da irin yadda bata son karatu, amma idan exam's ta zo kamar wacce ake ma wahayin karatu tana tsayawa tayi exam's ɗin tsakani da Allah kuma tayi karatu, dan so take tayi-tayi ta gama makarantar wai a cewarta tana gamawa ai dai shikenan za'a barta ta huta, dan ko a Islamiyya shi yasa ta maida hankalinta a wannan shekarar ne aka yayesu akai bikin saukar Alqur'anin da sukai, duk bai wuce mutum biyar ba suka sauke, da yawansu sun koma yin haddar Alqur'ani amma banda Sadiya, dan a cewarta ai ta samu na sallah ba sai dole ta wani hadda ce sa ba, tunda har zata iya ɗaukar Alqur'anin ta gani ta iya karantawa ai ya wadatar, sai kuma yanzu gashi taji Inna na cewa sai an kara kaita wata makarantar ƙaro karatu, ga islamiyya da take faɗi wai zata koma yo hadda.
Harta shiga cikin makarantar bata haɗu da kowa ba, tana shiga ko ina ɗalibai ne keta kai kawo, kowa na sha'anin gabansa.
Wata bishiya ta samu tayi zamanta tana shan iska.
Can taji maganar wata ƴar class ɗinsu A'i.
"Lah wai ke ce a nan Sadiya?"
Ɗan tashi tayi daga gishingiɗan da tayi, tayi ta ce.
"Eh A'i"
"Ashe kinzo yau?, amma ban ganki a class ba kamin a fito break"
Taɓe baki tayi kamin ta bata amsa ta ce.
"Eh sai yanzu na zo ai"
"Haba koda naji. To ki tashi muje cikin class sai ki ɗan kwanta a can kamin a koma class ɗin"
"No ki barni a nan yafi daɗin zama"
"To bari na zauna nima"
Ta faɗa tana samun kusa da ita ta zauna suka fara ɗan labari akan karatun na su.
Suna zaune kawai sukaga wasu ƴan mata kamarsu su biyu sunzo sun tsaya akansu ƙere-ƙere, suna kuma jefa masu wani kallon uku saura kwata.
"Ke Hansai lafiya?"
"Lafiyarce ta kawo haka Sadiya"
"Hmm lallai ma, wai ba Ya Umar yayi maku gargaɗi a kaina bane wai?"
"To anƙi anbi gargaɗin nashi, kuma wallahi kamar yadda kikasa idanuwanmu jinya kema sai mun tabbatar kinyi jinyar jikinki yadda ya kamata wallahi"
"Ai wallahi babu uwar da kuka isa kuyi min"
"Hhhh haka kika ce?"
"Kware kuwa na faɗa"
"To ai zamu gani ne, Mlm Hamisu na kiranki a can Office ɗin Malamai"
Suka faɗa baki wajan faɗa suna jifanta da wani irin murmushi na mugunta.
"Kambuji, au wato ma zuwa kukai kuka haɗa ni da Mlm?, ai na ce dai faɗan da mukai daku dama a school muka yisa ne ban sani ba ni?"
"Waye ma ya sani abu a duhu?"
Suka faɗa cike da rainin wayo, dan sun gama zuwa wajan Mlm Hamisu sunyi mata shirrin da bata isa ta fidda kanta ba.
"Haba dan Allah Hansa'u, ai hakan bai dace ba, tunda kunga ba'a school kukai faɗan nan naku ba, bai kamata ace kuma kun zare kunje wajan Malamai ba kunyi mata shirri ba ai....
Katse mata maganar da take yi sukai Hansai harda ɗaga hannu tana nunata da yatsa ta ce.
"Ke dalla Malama tsaya, dake ake wannan maganar ne?, ko kuwa kinji an saka dake ne?, bana son shiga sharra ba shano yawwa"
Ta ƙare maganar tana ɓallama A'i hararara.
"A'i yi shirunki, ai dai-dai nake da su wallahi. Kuma zanje wajan shi Mlm Hamisun, naji abunda zanmin, ku har kuna tunanin na tsaya ayi min wani hukunci ne?"
"Canta matse miki kuma"
Suka faɗa a tare suna binta da kallo.
Office ɗin Malamai ta nufa suna biye da ita.
Mlm Hamisu na tsaye da bulala yan waya, ganinsu sun taho gaba ɗaya harda mai laifin yasa shi katse kiran.
"Mlm gani ance kana son gani na"
"Ke wato kedai baki da kunya ko?, haka zaki tsaya min wani ƙere-ƙere a saman kai wai Mlm gani?. To duƙa ƙasa na ce marar kunya kawai"
Turo baki Sadiya tayi ta ɗuka ƙasa tana kallonsa.
"Wa'innan suka kawo min ƙararki dama kuma kin saba jan faɗa a school ɗin nan, harma da cikin gari an saba kawo ƙararki. Mi ya kai ki zuwa suna zaune suna cin abinci kisa ƙafa ki ɓarar masu da abinci, ki kuma tashi harda watsa masu ƙasa a jiki?"
Sadiya tsabar mamakin yadda suka ƙulla mata shirrin yasa ta kasa magana kawai. Idonta ta kai akan wasu kuloli da suka aje daga gefe gasu nan duk ƙasa ta ɓata su abincin duk ƙasa ne a jikinsa alamar tabbas ɓarar dashi akai, har kula ɗaya ma ta ɗan fashe.
"Ina magana kina jina?"
Mlm Hamisu ya faɗa yana zuwa inda take duƙe ya zafga mata bulala ɗaya a bayanta, wacce tasa Sadiya dawowa cikin tunaninta. Gantsarewa tayi tana kwaɓe fuska jin bulalar ta shigeta sosai wani irin raɗaɗi ne ya ratsa mata baya.
Ai bata san lokacin data miƙe tsaye ba ganin zai ƙara zafga mata wata bulalar a bayan nata.
"Ke cewa nayi ki tashi tsaye?"
"Nifa gaskiya Mlm bazan zauna a dake ni ba akan kuma laifin da ban san nayi ba"
"Ohh kina nufin ƙarya suke kenan?, su wa'innan kayan da kika zubar masu ub*an waye zaiyi hakan idan ba ke ba?"
"Ni ban san wadda yayi ba, can su suka sani, amma wallahi bazan zauna a dake ni akan abunda banyi ba"
Ta faɗa tana ƙara ja baya, dan taga yadda yake ƙara matsota da bulala ga fuskarsa a ɗaure.
Su Hansai dake gefe sai dariya suke mata a ƙasa-ƙasa, tana kuma sane dasu, ayyanawa take mima ya kamata ta ƙara yima yaran nan ne?, wadda zasu kiyaye ta har abada.
"Ki dawo nan na ce Sadiya"
Mlm Hamisu ya faɗa yana nuna inda ta tashi.
Maƙe kafaɗa tayi alamar wallahi bazata zo ba.
Saima yaga tasa ƙafa ta ruga da mugun gudu ta nufi hanyar barin school ɗin kwata-kwata ko waige bata yi.
Tana gudu tana share hawayen baƙin cikin abunda su Hansai sukai mata.
Kai tsaye gida ta nufa.
Tana shiga ta ja birki ganin Ya Umar a tsakar gidan yana wankin kayan sawarsa.
Tsayawa yayi da wankin yana dubanta sosai, muryar nan tasa taji a kunnuwanta ya ce.
"Ke mi kika dawo yi a irin wannan time ɗin gida?"
Firgigit ta dawo hayyacinta da tayi godon zango da ficewa tunaninta ganin Ya Umar ɗin kaɗai da tayi.
"Ba dake nake magana ba?"
"Wallahi Ya Umar daga can nake, su Hansai ne wa'inda rannan suka zo da iyayensu ka raba faɗana dasu, shine daga zuwana makaranta suka ganni, ashe suna riƙe dani basu haƙura ba, suka je wajan Malamai suka jamin shirri, aka kira ni ana dukana wajan Mlm shine ni kuma na miƙe na gudo gida, tunda nasan ni banyi masu komai ba"
Jinjina kai yayi yana ƙara zuba mata ido ya ce.
"Wato shine ke kuma ki kai masu rashin kunyar nan taki, kika sa ƙafa kika gudo Malami na miki hukunci ko?, ke wai mi yasa baki da hankali ne?, ke baki da bakin da zaki tsaya kiyi ma shi Malamin bayanin komai ya gane?, a'a sai kawai kisa ƙafa ki gudo ko?. To nan ɗin ma ba tsira kikai ba, kuma gobe ni da kaina zan miƙa ki school ɗin a lallasa min ke"
Kuka Sadiya ta saki tana duƙawa ƙasa ta ce.
"Dan Allah Ya Umar kayi hakuri, wallahi ba laifina bane harda laifinsu suma fa"
"Suma ɗin duk zanyi maganinsu ne. Kuma maza ta so ki idasa min wankin kayana, kuma wallahi idan kika sake kikai min wankin iskanci zaki gane kuranki ne"
Inna na daga ɗaki tana jin komai taƙi fitowa, dama tasan wallahi sai makamancin hakan ta faru ta dawo, ita ta rasa mike damun Sadiya a duniyar nan, ace yarinyar ba abunda tafi maida hankali dashi sai jan faɗa da shirme.
Ya Umar na gama faɗa mata haka ya tsame hannunsa daga wankin ya wuce ɗakinsu.
Wani miyau mai zafi ta haɗe, ai ita yanzu da yasa ta wannan ub*an wankin nashi wallahi gara ya sata kamun kunnen akan wannan wahalar, dama gashi hannunta baya son wahala ko kaɗan, duk sadda zatai wankin kayanta hannunta ja jawur suke yi subi su tsatstsage, har jini ke fitowa a hannun nata, yayita mata raɗaɗi, koda kala biyu ne kuwa ta wanke sai hannun nata tayi jinyarsa, shi yasa wani lokacin Inna ke mata wankin ma.
Ita yanzu ta ina zata fara ne?, kuma tasan fa tabbas yasan bata da jumurin wanki, amma shine tsabar yana son hukuntata ya barta da wannan ub*an wankin, ga kayan maza da wahalar wanki.........
PAGE 27
*UMMI POV*
Ummi sai wajan sallar mangaruba tukunna ta tashi bayan tayi sallah ta ce.
"To Maryam nifa zan wuce kar naƙi samun napep"
"A'a zaki samu insha Allahu"
Maryam ta faɗa tana murmushi.
Fitowa sukai a tare Ummi taje tayi ma Umma sallama inda Umma ke cewa.
"Ummi zaki koma?"
"Eh wallahi Umma zan tafi"
"To Ubangiji ya tsare, amma dai zaki ƙara shigowa ko?"
"Insha Allahu Umma zan ƙara zuwa, zama muje da Maryam gidan Aunty Asiya idan na ƙara zuwa ɗin insha Allah"
"Tom shikenan Allah dai yayi albarka"
"Ameen amin Umma"
Ta faɗa suna wucewa waje da Maryam.
"Dan Allah Ummi idan kika je karki yi mata maganar nan"
"Hmm ai kin san halina Maryam wallahi bazan mata magana ba, amma fa a yadda ta tarbe ni to haka zanyi mata nima"
"Uhum Allah dai yasa ta gane gaskiya, amma kam Aunty Binta tana da matsala. Yanzu dai ga wannan gurasar ki tafi da ita, dama na ce idan zaki tafi zan baki ita, idan kinje gida ki jiƙa kici, dan nasan yau yadda kikai mata laifin nan ba lallai ta baki abincinta ki ci ba"
Maryam ta faɗa da tsokana.
"Hmm kefa kin faɗi maganar nan da wasa ko?, to wallahi Allah tsaf ta iya, ai ƙaramin aikinta kenan ma tabɗi. Amma naji daɗin gurasar nan idan ma ba'a bani ba na ci abata, bare yau ban tsaya nayi mata duka abincin ba ai sai yadda na gani yau kam"
"Wai yanzu dan Allah akan wannan ɗan abun saita hanaki abinci da gaske?"
"Kina wasa ma Maryam, ashe har zuwa yanzu baki karanci ma wacece Aunty Binta ba, labarinta kawai kike ji daga nesa, Allah dai ya kyauta kawai Maryam"
Ummi ta faɗa tana girgirza kai.
A tsaye suke bakin titin gidansu Maryam ɗin suna labarin suna tsaida abun hawa.
Wata napep ce ta zo wucewa suka tsaida ita ganin da mutum har biyu yasa Maryam cewa.
"Sheka ƴar kasuwa"
"Okay ku shigo"
"A'a mutum ɗaya ne ma zaka ɗauka"
Jinjina kai yayi Maryam ta sake cewa.
"Nawa ne?"
"Ɗari biyu ne"
"Haba Mlm ɗari ne fa zuwa ƴar kasuwar"
"To ta shigo mu wuce"
Shiga Ummi tayi Maryam ta ce mata.
"To sai munyi waya ki gaida Aunty Binta da Anam please"
"To zasuji nagode Maryam"
Mai napep yaja suka wuce Maryam kuma ta tsallaka titin ta koma gida.
*********Tunda ta shigo parlon gidan taga Aunty Binta zaune a parlon da Anam dake gefenta tana wasa, da yake yarinyar ta iya zama.
Gaida ta tayi tana ce mata ta dawo, bata kalleta ba ta amsa ciki-ciki kamar bata son maganar, fuskar nan kuwa a murtuƙe kamar kunun kanwa, sai turo baki take gaba tsabar yadda ta cika da haushi Ummi ɗin.
Ummi bata damu ba ta taɓe baki tana wucewa ɗakin data sauka.
Tana shiga ta shiga cire kayanta ta shiga toilet ta watsa ruwa ta ƙara yo walwala ta fito ganin har an fara kiran sallar Isha'i tuni.
Sai da ta gama sallar tana zaune tana ɗan latsa wayarta suna chatting da wasu mutane tana ƴar fara'a kaɗan-kaɗan.
Ta daɗe a zaune bata ƙara jin motsin Aunty Binta ba, tana dai jin gwarancin Anam a daga can parlon.
Motsin shigowar Uncle Abdul ne taji gidan, jin muryarsa yana ɗaukar Anam haɗe da mata wasa, ita kuma tana masa sannu da zuwa.
Aje Anam ɗin yayi a kusa da ita yana yin hanyar ɗakinsa.
Da sauri Ummi ta miƙe tana leƙawa tayi masa sannu da zuwa ta gaida shi.
"A'a Ummi baki fitowa parlo sai ki shige ɗaki ke ɗaya?"
"Ba haka bane Uncle kawai na dawo ne na gaji shi yasa"
"Ohh wani waje kika je ne?"
"Eh naje gidan su Maryam ƙawata ne"
"Ohh Allah Sarki"
Ya faɗa yana idasa shigewa bedroom ɗin nasa.
Aunty Binta ta take masa baya.
Ɗan tsayawa Ummi tayi a hankali ta furta.
"Aikin banza karki tanka min ɗin mana. Amma dai ba Anam suka bari ita ɗaya a parlo ba?"
Ta ƙare maganar tana ɗan jiyo gwarancinta a parlon.
Jinjina kai Ummi tayi ta dawo ta zauna tana jinjina ƙarfin halin Aunty Binta.
Sosai ta ƙara mamaki ganin sun shige ɗaki ko motsinsu ba'a ji, ga yarinya sun aje a parlo harta fara kuka sosai.
Tausayin yarinyar Ummi yasa ta miƙe zuwa parlon, ɗakkota tayi tana ɗan mata wasa, dawowa ɗakin tayi ta ajeta kusa da ita.
Amma kamar ance ta ƙara wake baki ta fara kuka, harda su hawaye.
Dole tasa Ummi miƙewa haɗe da jan tsaki, danta tsani rainon yaro wadda keda kuka sosai wallahi.
Rirrigata ta farayi tana mata wasa sosai.
Tun tana mitar kuka harta gaji tayi shiru. Ummi tun tana jiran fitowarsu harta haƙura ta zubama sarautar Allah ido kawai.
Har sai da Anam ɗin ta fara bacci akan kafaɗar Ummi tukunna Aunty Binta ta fito sanye take da kayan bacci yanzu, riƙe take kuma da kayan Anam ɗin na bacci.
"Kawo ta"
Kawai Aunty Binta ta ce mata.
Bata ita tayi tana ɗan matsawa gefe inda wayarta take