Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   15 / 36

42K to 45K   out of 106.4K words

ta ci gaba da dannawa.

Sai da ta gama saka mata kayan kamin ta ce.

"Ki tabbatar kin wanke min kayan wanke-wanke dake kitchen bana son kayan wanke-wanke suna kwanar min"

Tana ƙare maganar ta fice daga ɗakin.

Ummi ta saki baki tana bin bayanta da kallo, cike da izza da isafa take gaya mata maganar.

"Ohh'ni Ummi wai ko dan kazo gidan mutum ne shi yasa harya samu damar yadda ya so da kai?"

Ummi ta faɗa a fili tana riƙe baki.

Tana jin motsinsu a parlo da Uncle Abdul yana cin abinci.

Sai da Ummi taji sun gama da darning table ɗin sun komawa bedroom nasu yasa ta miƙe zuwa kitchen ɗin da wayarta a hannunta ganin kiran Maryam gaf da zata fita zuwa kitchen.

"Hello Maryam"

Ummi ta faɗa dai-dai lokacin data buɗe ƙofar kitchen ɗin ta shiga.

Daga cikin wayar Maryam ta ce.

"Kin isa lafiya?"

"Wallahi Alhamdulillahi Maryam"

"Ba dai wata matsala ko?"

"Hmm babu kam na dawo dai na iske ta kamar yadda na saba fuskar nan ba fara'a, da alama dai rashin dawowar da banyi ba da wuri, kuma taga ban nuna mata Mama ta kira ni ba, shine fa abun inaga ya bata haushi dan ko abincin da kike faɗa yau ba'a ce gashi ba"

"Haba dai Ummi?, yanzu dama sai ta ce miki ga abinci ba zuwa zakiyi ki ɗauka ba?"

"Haba sai ka ce baki saba zuwa gidan Aunty Binta ba Maryam, ai ni koda abinci nayi mata wallahi bana fara ɗiba har sai tazo ta ɗibi nata, idan ta gama duk lokacin data ce naje na ɗiba shine fa nake zuwa nasa nawa na ci, saboda bana so ace nayi ba dai-dai ba a kira Mama a gaya mata"

"Tabɗi jam ai ko kina matuƙar haƙuri da zama a gidanta, ai ni wallahi Allah bazan taɓa iyawa ba lallai"

Sun daɗe suna magana kamin Ummi ta aje wayar tana bin kayan wanke-wanken da aka jifge mata.

Sauke lumfashi kaɗan tayi tana aje wayarta ta fara kiciniyar wanke-wanken.

Ta daɗe tana wanke-wanken har wajan goma na dare bata gama ba.

Sauke ajiyar zuciya tayi bayan ta gama wanke-wanken, ta goge kitchen ɗin.

Firiza ta buɗa zata ɗauki ruwa, ganin sauran abinci ansa a faranti an sakashi a firizar yaba Ummi mamaki sosai. Wato dai bata da kaso a yau na abinci?, shi yasa ma aka saka saura a firirza karma tasa rai kenan?.

Haka nan sai Ummi taji ranta ya sosu, amma sai ta waske ta ɗauki ruwan kaɗai ta haɗa da ɗaukar wani faranti ta fice daga kitchen ɗin.

Tana zuwa bedroom ɗin data sauka ta ɗakko gurasar nan da Maryam ta bata Allah ya so harda ƙuli ta haɗo mata.

Kitchen ta koma ta yanka gurasar ta kunna Gas ta turarata.

A nan ta haɗa komai ta yanka kayan albasa da tumatur a ciki, kamin ta ɗakko ta dawo ɗaki.

A ƙasa ta zauna tana latsa wayarta ta fara cin gurasar tana yi tana kallon cikin wayar ta..........

PAGE 28

*SALMA POV*

A hankali tasa hannunta tana rufe Alkur'anin dake a gabanta bayan ta gama karantawa.

Miƙa hannu tayi ta shiga tashin Yusura tana cewa.

"Yusura kifa tashi Asuba tayi"

Kwaɓe fuska tayi tana miƙewa zaune bacci cike da idonunta.

"Wai har asuba tayi ne?"

Hararar wasa Salma tayi mata tana cewa.

"Tunda jiya kinsha soyayya ai dole kiga asuba ba wahala, jiya fa kece har biyu na dare ina jinki kuma sai kashe murya kike fa"

Dariya Yusura ta saki tana miƙewa da sauri ta ce.

"Kai Aunty Salma, dama duk kina jina wai?"

"Uhm ai banda nauyin bacci ne. Amma dai wannan Abubakar ɗin dashi za'ai ko?"

"Eh Aunty Salma, ai harma ya zo yaga Baba tuni, baki sani ba wai?"

"A'a banda labari gaskiya, kin san ni idan ba saka ni akai cikin abuba ban fiye maida hankali na akai ba"

"Ayyah Aunty Salma kiyi hakuri mancewa nayi wallahi, ai har sun gama fahimtar juna da Baban, dan jiya ma yake gaya min wai nanda sati ɗaya zasu turo manya a tsaida rana"

"Kai Masha Allah, wallahi nayi murna sosai Ubangiji ya kaimu, muna da gagarumin biki gaskiya. Ai ko kinga ƙila a haɗe bikin naku dana Safiya dan itama inaga bikin bai wuce nanda bayan sallah ƙarama ba, kuma kinga azumi bai wuce wata huɗu ba yanzu ko?"

"Hakane fa"

Yusura ta miƙewa tsaye ta nufi waje, tayo alwala ta dawo ta kabbara sallah.

Bayan ta idar ta kalli Salma data koma ta kwanta ta ce.

"Aunty Salma yau baku da lecture safe ne?"

"Eh wallahi sai ma sha ɗaya zan fita, yau ta ƙarfe sha biyu ce, mu dawo ƙarfe shidda kuma ba kamar dai jiya"

"Ai jiya sai kunfi shan wahala, tunfa safe fa?,gara ai yau zaki tsaya a tsanake kamin ki tafi"

"Ai ko dai dan wallahi Yusura na tsani lecture ɗin safen nan ta ƙarfe takwas"

Tashi Yusura tayi tana hawa kan katifarsu kusa da Salma dake kwance ta ce.

"Wai kuma Malaman suna zuwa tunda safen?"

"Hmm ai in gaya miki idan ma kayi sake wani Malamin a class zaka iske shi wallahi"

"Tabɗi jam sunma fiku iya kwaɗa sammako kenan?"

"Ai wani sammakon nasa na mugunta ne"

"Ni kam wai yau Aunty Ummi ta ce zata zo ko?"

"Haka dai ta faɗa, amma da wuya ma mu haɗu"

"Kashh makaranta ko?, amma ai zata iya zuwa kamin ki wuce tunda yau ta sha biyu ce dake, kilama ki dawo ki ƙara isketa a gidan nan, dan wani lokacin sai ta kai sallar mangaruba take tafiya idan ta zo nan"

"Eh zata iya yiwuwa"

Ta faɗa tana rufe idonta dan bacci take ji.

Baccin suka koma sai da gari ya waye sosai rana ta fito kamin Salma ta miƙe a hankali tana niyyar fita saiga Aunty Murja ta sawo kai cikin ɗakin.

"Wai duk abun nan baku tashi ba dama?"

"Ina kwana Aunty Murja?"

"Lafiya. Ke wato ma kina nan kin baje bacci kawai kike?, to ai garin ya waye sai ki miƙe ayi mai yiwuwa. Dama ai dole ki kwanta ki kasa tashi tunda jiya an shafe yini ana yawon iskanci, Namiji duk ya gajiyar dake ai dole"

Ai Salma bata san lokacin data ɗago gaba ɗaya ta zubama Aunty Murja ido ba, da wani maɗaukakin mamakin matar da kullum ke ƙara kasheta.

"Ko ƙarya na faɗa kin wani tsare ni da ido?"

"Tsakani da Allah Umma abunda kike masu Salma yayi yawa fa, tunda safe zaki fara ko Umma?"

"To sannu uwata na ce, wallahi Yusura zanyi maganin wannan rashin kunyar taki, wacce wannan marar kunyar ta koya miki"

Aunty Murja ta ƙare maganar tana nuna Salma da yatsa.

Turo baki tayi tana magana ƙasa-ƙasa.

"Ke kuma ki tabbatar kamin na ƙara zagayowa kin fito duk wani aikin da kika san naki ne a gidan nan kin gamasa"

Da kai kawai Salma ta amsa har lokacin data juya ta fice daga ɗakin tana binta da kallon mamaki.

"Kai jama'a, kai jama'a, wannan wane irin abu ne wai Umma ke yi dan Allah?"

"Uhum kinga tashi muje ki kamamin mu gama da wuri naga har tara da rabi, munsha bacci ne ai muma"

Miƙewa tayi ranta ba daɗi tabi bayan Salma data rigata ficewa.

Yusura ta fara sharar tsakar gida ta gyara ɗakin Aunty Murja ta shiga nasu ta gyaro.

Ita kuma Salma ta shiga toilet ta wankesa ta fito tana duban Yusura dake kwashe sharar data tara ta tsakar gida ta ce.

"Ki tabbayo min Aunty Murja mi za'a dafa da safen nan please, gara na fara da wuri yanzu kinga lokaci yaja"

"Ai inaga kamar wainar gero ce za'ai da ƙuli, sai kunun gyaɗa naga ta aje komai a kitchen ɗin"

"Okay bari na fara shiga wanka to"

"To ki shiga bari ɗora ruwan zafin da za'a dafa kunun dashi"

"Yawwa ƴar uwa rabin jiki na gode fa"

"Haba Aunty Salma ai ba komai duk ɗaya muke fa"

"Ta gidan ub*an waye kuka zama ɗayan iyee?"

Aunty Murja ta faɗa tana ɗaga labulen ɗakinta ta fito.

Ta sake nuna Salma da yanzu tayi ƙasa da kanta tana kallon wani wajan ta haɗe wani miyau mai zafi.

"Kuma kika sake kika taɓa wani aikin bayan wannan uwar sharar da kika taimaka mata, wallahi Allah kinji na rantse ko yau na lahira saiya fiki jin daɗi, domin wallahi saina saɓa miki"

"Amma Umma miye danna taimaka mata?, school fa take zuwa, bafa aikin gida ya kamata ace an bar mata ita ɗaya tana yi ba, tunda karatu ta zo fa"

"Ungo nan Yusura kinji"

Aunty Murja ta faɗa tana danƙarama mata daƙuwa da hannu ta ƙara cewa.

"Ashe ke baki da hankali ban sani ba?, wato kan baiwa ta aje tana zaune sai dai taci tasha kenan kike so ko?, taje daga yawon barbaɗancinta ta dawo sai dai taga abinci kawai?, to ai kuwa bata isa ba wallahi, daga ke har ita baku isa ba, muddun tana cikin gidan nan aikin gidan nan gaba ɗayansa ya wajaba akanta ne wallahi, munga ub*anda ya isa hana hakan ta faru"

"A'a babu wanda ya isa hanawa Aunty Murja kiyi hakuri, kuma zan fito nayi ne ai yanzu, dama can ai bance tayi min ba"

"Ohhh kinyi baki, magana zaki gayan?"

Saurin girgiza kai Salma tayi tana jin yau tayi abunda bata taɓa yi ba, wato yin magana idan Aunty Murja nayin ƴan maganganunta, tunda take abubuwanta, bata taɓa ɗaga kai ta tanka ba, yau ma kawai taji bakinta ya buɗe ne.

"A'ato magana kike shirin gaya min ai naga alama, to dai-dai nake da ƙugun kowacce shegiya wallahi. Ke kuma na gaya miki dai"

Ta faɗa tana kallon Yusura ta juya ɗaki ta shige.

"Aunty Salma da......

"Kinga Yusura kiyi shiru babu komai fa, ke kenan kullum bada haƙuri?, to karki damu ni bana riƙeta a zuciyata, ki manta kawai kamar ba'ayi komai bama"

Kallonta Salma ta ƙara yi ganin kamar zata nufi kitchen da sauri ta tsaida ita ta hanyar cewa.

"Ah ah, ina kuma zaki je ne?"

"Aikin nan zan tayaki mana, ke kije ki shiga wankanki kawai"

"Kashh haba dai Yusura baki ji miye Aunty Murja ta ce miki bane?, karki sake ki taɓa aikin nan Yusura"

"Bafa wani abu Aunty Salma bazata san ni ce nayi bama"

"No a'a wallahi bazan bari ki taɓa aikin nan ba wallahi, dawo ma, kin san furucin uwa kuwa akan ɗanta Yusura?, haba Yusura, sai ka ce wacce bata je Islamiyya ba?"

Jikin Yusura ne yayi sanyi ƙalau a hankali taja ta tsaya tana zama akan wata kujera dake tsakar gidan ajiye tana sauke ajiyar zuciya ranta a dagule ta ce.

"Na tuna Aunty Salma, amma wani lokacin Umma ke sawa ina mancewa da duk abunda ya dace nayi mata, ita ai bata tuna duk wa'innan, ko ance mata ta rinƙa wulaƙanta ku ne a islamiyyar?, ai ko cikin Alqur'ani mai girma, ance duk mai wulaƙanta mutane bazai gama lafiya ba, amma ita fa?"

"Kinga ai ba wasu taje ta wulaƙanta ba ai ko?, mune dai, muma kuma ƴan gida ne, kuma muma akwai dalilinta nayin hakan, saboda haka ki daina wannan maganar, addu'a kawai ya kama ce ki, ki rinƙa yi mata ba dare ba rana, zata daina ne"

Bin Salma da kallo kawai Yusura tayi, ganin zatai magana Salma tayi saurin juyawa tabar wajan.

Ɗaki ta koma ta ɗaura zani ta fito da sosan wanka, shaf-shaf tayo wankan ta shafa mai da turare ta fito tana ta sauri ta ɗora, dan taga har sha ɗaya saura mintina goma.

Kitchen ɗin ta nufa Yusura dake zaune tsakar gidan har lokacin tana latsa wayarta data ɗakko a ɗaki, saita miƙe ta bi bayanta zuwa kitchen ɗin, zama waje ɗaya tayi suna labari Salma na aikinta........

PAGE 29

Zama tayi tana duban Yusura ta ce.

"Wai yanzu ta tafi school ɗin?"

"Eh wallahi Aunty Ummi yanzu ta wuce, ai kinga ƙarfe sha ɗaya da rabi yanzu, inaga ko kunsha banban ne?"

"Sai dai haka gaskiya, dan ni ta can baya na biyo, ita kuma ƙila ta ƙara min titin can ta wuce, shi yasa bazamu haɗu ba"

"Ai amma zaki kai yamma a nan ko?"

"Eh insha Allah sai wajan shidda idan anyi sallah zan wuce"

"Aikin banza, aikin kenan yawo keda ƴar uwar taki, gaki nan shiraf babu mashinshini, ga ƙanwar ƙanwarku nan ma gobe-gobe za'a turo maganar aurenta, amma ku ko ma wani abu bakwaji wai?, ace ƙannanku zasu tsalleku suyi aure ku kuna zaune?"

Wani murmushin gefen baki Ummi ta saki tana juyowa ta fuskanci Aunty Murja dake maganar ta ce.

"Ai da yake suma sune suke bada mijin ko kuma wayonsu ne yasa suka sami mijin shi yasa kike wannan maganar ƙila?"

"Ke ni kika gaya ma magana?"

"Ahhh yo wadda baiji kunyar hawa Jaki ba ai ko Jaki bazaiji kunyar kayar dashi ƙasa ba"

"Keee wallahi zan ci.......

"A'a nan fa ɗaya Murja, wallahi kina zagar min iyaye saina rama, dan kamin ki rufe bakin ma na sauke miki nawa zagin"

"Innalillahi wa'inna alaihir raju'un na shiga Uku, ke Ummi"

Aunty Murja ta faɗa tana dafe ƙirjinta, cike da madaukakin mamakin Ummi, yadda take gaya mata magana kanta tsaye babu tsoro ko shakka.

Ahh lallai wannan yarinyar kanta rawa yake, kila tana da shafar jinnu ne a saman kanta, dan taga yadda take wani juya ido tana masifa.

"Kinga ni ko Umma?, ai dama wata rana zaki ji ma fiye da abunda yafi haka wallahi"

"Dalla gafara can marar zuciya kawai, kina zaune wannan yarinyar take zagin uwar data kawo ki duniya, amma baki tashi kin gurji bakinta ba, ai kinji haushi wallahi"

"Umma mi zan mata?, ai duk abunda akai miki kece kika siya da kuɗinki, dama irinsu Ummi ɗin ne dai-dai zama a gidan nan ai......

Wani kyakkyawan mari ne Aunty Murja ta yarfama Yusura haɗe da tashi tsaye tana nunata da yatsa ta ce.

"Ashe baki da hankali ban sani ba?, ni kike gaya haka?, ni dake waye ya haifi wani ne wai?, ko wa'innan ƴan iskan masu yawon bariki sun fara buɗe miki ido kema kina kallon kowa dai-dai dake har ni dana kawo ki duniya?"

Murmushi kawai Ummi ta saki tana jinjina kai bata ce komai ba, saima Aunty Murja da take kallo tana jefa mata murmurshi mai sanya zuciya jin zafin wadda ake mashi.

"Dole zaki yi murmushi mana makira tsohuwar marar kunya"

"Kinga Murja ni ba danke na zo gidan nan ba yawwa, dan haka karki ƙara sako maganarki dani a ciki, idan kuma ba haka ba duk abunda nayi miki ki kuka da kanki"

"Innalillahi wai Ummi kin san da waye kike magana kuma, Matar ub*an taki kika zauna kina faɗa ma haka?. Ko dai dama ai'koki iyayenki dake can zaune a ƙauye sukai kiyi min rashin kunya?"

"Wannan kuma can miki"

"Ai shikenan bari shi ub*an naki ya dawo saiya gaya min idan ni sa'arki ce a gidan nan"

Wata dariya Ummi ta saki tana basarwa dan bazata taɓa yarda ta kai ma dare a gidan ba, idan ya so Baba ya kirata a waya taƙi ɗauka, dan dama a shirye ta zo, idan ta faɗa mata dubu ta faɗa mata million.

Shigewa ɗaki Aunty Murja tayi tana mazurai kamar zata haɗiyi zuciyata ta mutu haka take ji, dama tasan Ummi bata raga mata ba koda ta zauna a gidan karatu kamin ta gama, bare kuma yanzu da take ganin ba'a gidan nata take zaune ba.

Tana shiga ta ɗauki wayar ta ta kira wata ƙawarta a waya.

"Helloh sister"

"Ina jinki sister lafiya dai naji muryarki a haka?"

"Hmm bari sister, kin san tunda muka haɗu da ke kwanaki nake baki labarin abunda ke faruwa a gidana. Wai yanzu ƴar mijina ce tazo tana gaya min magana son ranta"

"Kumbuh*un ub*nan, mi yasa baki tashi kinyi mata jakin duka ba a wajan?, ta gane ruwa ba sa'an kwando bane, ai barin a huce shike kawo rabon wani in gaya miki, da kin ma jikinta mugun duka ai da yanzu bata isa ta ƙara buɗe baki ta ce zata gaya miki magana ba"

"To yanzu sister saina kama ɗiyar Mijina da duka?"

"A'a baki isa ki dake tan bane?, kaji ai, ai tun farko ma kece kika ja suka raina ki, ai suna miki abu kawo hannu kawai ki ɗauke shegu da mari, gobe Allah bazasu sake ba"

Ai sai Aunty Murja ta riƙe baki tana fara yarda da abunda sabuwar ƙawarta wacce tasa mata sister, duka-duka kwanaki biyu da haɗuwarsu, waccan ƙawar tata tuni sun ɓata da ita, dan ta ce ita bazata bi Boka ba, ita kuma ƙawar bin Bokaye take, ita kam Aunty Murja har a zuciyarta bata yarda da aikin Bokaye na ci ba, sun haɗu da sister ne a napep sun jone, suna bawa juna shawarawarin da duk mai hankali da tunani yaji yasan basu san ciwon kansu ba kwata-kwata.

"Ai ko kin kawo shawara mai kyau zanyi abunda kika ce, kawai sai kin jini"

Ta ƙare maganar tana datse kiran.

"Ki zauna kiyi hakuri Yusura, ai kema kinyi wauta, da tana faɗa kina faɗa, ba'ama Iyaye haka Yusura ki daina kinji?"

"To amma Aunty Ummi ita mi yasa tak.......

Ido waje Yusura ke kallon Aunty Murja data ɗakko wani ƙaton katako tana nufo inda Ummi take zaune.

Ai ganin inda Yusura ke kallo ne yasa Ummi waigowa, ai a mugun zabure ta miƙe tana fiddo ido waje tana kallon Aunty Murja da mamakin daya kusa tsaida lumfashinta.

"Dukahhh?"

Ummi ta faɗa a fili muryarta cike da mamaki.

"Ko bazaki daku bane?"

"Hhhhh ai wallahi ni yanzu mai dukana saiya shirya Murja"

"Ai a shiryen nake marar kunyar wofi"

"To shikenan Bismillah ai gani a tsaye"

Ummi ta faɗa tana aje gyalenta dake rataye a jikinta, dan ko ciresa batai ma dama.

Yusura ta miƙe a zabure tana shiga gaban Aunty Murja ta ce.

"Dan Allah Umma miye kike ƙoƙarinyi ne haka?, dan Allah Umma ki daina, wannan fa abun shike ƙara sawa ana raina ki wallahi"

"Yo raini tun na

15 / 36