Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   7 / 36

18K to 21K   out of 106.4K words

zaki mutu domin tafiyarsa ba yanzu ba inma gaya miki"

Ƙara ɓata fuska tayi zuwa can ta ce.

"Wallahi daya ji ƴan bindigar nan sun shigo a gabansa yana nan to na rantse washe gari bazai kwana a garin nan ba, na sanshi ai da shegen tsoron masifa"

"Kinfi ƙarfina Sadiya, yanzu Umar ɗin ne ke da tsoron masifa?"

"A'ato Inna ƙarya nayi ne, mune nan yake mana mazurai kamar Soja ya kama ɓarawo"

"Kiyi tayi dai gulmarsa har ya zo ya iskoki a nan kin gane kuranki ai ko?"

Miƙewa tayi a hankali tana sake ɓata fuska ta dubi tuwon da Inna ta aje mata tana ƙara ɓata fuska ta ce.

"Haba Inna wai mu shikenan kullum tuwo kullum tuwo dan girman Allah, yaya rayuwa zata tafi da kullum tuwo?"

"Ungo nan Sadiya"

Inna ta faɗa tana mata daƙuwa da hannu.

"To ni Inna gaskiya na gaji da cin tuwon nan wallahi"

Ta faɗa tana zama haɗe da ture kwanan tuwon dake gabanta kamar zata fashe da kuka.

Sake da baki Inna ke kallon ta ganin da gaske bazata ci ba.

Sallamarsu gaba ɗaya da Ya Sule da Ya Umar ne yasa Sadiya miƙewa tsaye tana nufar Ya Sule kamar zata sakar masa kuka ta ce.

"Ya Sule!"

"Miya faru Sadeen Yayanta?"

Sake turo baki tayi a hankali suka zauna tana zama a kusa dashi.

Tana ɗan satar kallon Ya Umar dake ma Inna magana.

"Ya Sule Allah yinwa nake ji, amma ni bazan iya cin tuwon nan ba yau shikenan mu kullum tuwo?"

Ta faɗa kamar mai raɗa dan bata so Ya Umar yaji ta.

Zaiyi magana sukaga Ya Umar ya miƙe haɗe da miƙa mata wata leda.

Sake da baki Sadiya ke kallon ledar ta kasa amsa.

"Amshi mana"

Ya Sule ya faɗa.

Hannunta na rawa tasa ta amsa.

Tana binsa da kallo tana murmushi, dan har ƙamshin tsire da rogo ta fara jiyowa. Harga Allah tana bala'in son Yayyen nata son sonta, matsalarsa ɗaya shi baya dariya ga muguntar da take ganin yana mata, amma duk wata kyautatawa kamar yadda Sule idan ya samo yake mata shima haka ne.

Dariya ta saki tana murna ta kalli Inna itama da ya miƙa mata ledarta daban ta ce.

"Inna ke mi aka kawo miki?"

"Ban sani ba ƴar neman magana"

"To ni Inna daga magana?"

Sule dake dariyar diramar Inna da Sadiya ya tashi tsaye shima yana ɗakko ledar dake riƙe a hannunsa da basu lura da ita ba ya miƙa ma Inna ya ce.

"Inna ga wannan kayan amfanin gobe ne da safe"

"Masha Allah kai Allah yayi maku albarka, ya ƙaro buɗi mai yawa mai amfani kunji, Allah ya albarkaci rayuwarku, ya jiƙan iyayenku kuma"

Inna ta ƙare maganar tana ɗan matse hawaye.

"Ameen ameen Innarmu"

Sule ya faɗa yana ɗan murmushi ya wuce.

"Hmmm Inna kinji daɗin tsiran nan kuwa?"

"Ke tafi can"

Turo baki tayi tana tauna abunda ke bakinta ta haɗewa tana cewa.

"Nifa Inna gaskiya na kusa daina zuwa tallar nan"

"To ƴar iya"

Zatai magana Ya Umar ya fito yana zama akan kujerar daya tashi yana fuskantar Inna ya ce.

"Inna ina so muyi magana akan yarinyar nan"

Gaban Sadiya ne ya yanke ya faɗi, tana ɓalla masa hararara ƙasa-ƙasa.

"To Umar ina jinka miye ya faru?"

"Eh Inna gaskiya akan tallar gwaɗar nan ne, ya kamata a daina saka mata, insha Allah kamin na koma zan baku jari kuja jari amma sana'ar ta kasance ta cikin gida ce kawai ba sai an fita zuwa tallar ba. Sana Inna idan har na koma na kusa kammala karatuna, zan fara sana'a ne a Kano kuma dana samu buɗi mai yawa zan zo na ɗauke ku daga garin nan, dan naji Sule na gaya min cewa har zuwa yanzu ƴan bindigar nan na shigowa sa'i-sa'i, kinga kuwa zaman garin nan akwai haɗari ta wani wajan"

"Hmm banki ta taka ba Umar, amma ni bana son barin garin nan idan ba dole ya zame min ba"

"Inna wani abun dolen ce take sawa haka"

"Kai Alhamdulillah wallahi Ya Umar dama na gaji da garin nan, muma zamu koma birni iyeee"

Ta faɗa kamar zata buga tsalle.

"Ke dalla tashi ki bawa mutane waje, marar kan gado kawai"

Umar ya faɗa yana nuna mata hanyar ɗakin Inna.

Ai bata san lokacin data dawo cikin hayyacinta ba, dan ita kam ta mance da waye ma Ya Umar ɗin a gabanta, baya son shirmen nan da hayaniya tafi kowa sani.

"Allah ya baka haƙuri"

"Naji tashi kije please"

Ya faɗa taga yana ɗan riƙe kansa. Dan tana son fara sa masa ciwon kai daga dawowarsa.

Miƙewa tayi jiki a sanyaye tana waigen bayansa harta shige ɗakin Inna.

Tana shiga ta taɓe baki ta ce.

"Kai jama'a anya Ya Umar ciki ɗaya muka fito dashi kuwa?. To ai kwata-kwata halayyarsa ba irin tamu bace, ace ayo mutum sai shegen girman kai da ɗaukar zafi ga wata izza da isa kamar ɗan gidan Sarki, gashi kuma duk ya so yama fimu kyau fa"

Sadiya ta ƙare maganar tana riƙe baki haɗe da ɗan tashi tana ɗaga labulen dakin Innar tana hango bayansa, mai faɗin gaske ga ƙirar ƙarfi da Allah ya zuba masa, ga wani gashin Fulani irin nasu daya tarasa a saman kansa yasha gyara har yana ƙoƙarin zubo masa a bayansa, hakan ba ƙaramin kyau yayi masa ba.

Ƙara taɓe baki tayi tana ƙara cewa a fili.

"Hmm baccin kawai mu Fulani ne, nima ina da gashin nan to da tabbas sai na ce roƙonsa ake kawai a gidan nan ba namu bane wallahi"

Sai magana take ita ɗaya tana sake leƙensu kamar mai magana da wani a kusa da ita........

PAGE 14

*SALMA POV*

Hasken safiya ne daya dalle mata ido yasa ta ɗan motsawa tana ɓata fuska kaɗan kamin a hankali ta shiga miƙawa zaune tana sakin yamma, jikinta tana jinsa yayi mata bala'in nauyi, kamar wacce akaima dukan tsiya a cikin baccin nata.

Aunty Murja ce ta yaye labulen ɗakin nasu tana tsayawa daga ƙofar ɗakin bata idasa shigowa ba tana riƙe ƙugunta tana kallon Salma sosai da itama ta zuba mata ido kamin ta ce.

"To ƴar hutu safiya tayi ai sai ki fito ki ɗora mana abun kiri, kuma ga aiki nan na jiranki"

Agogan ɗakin nasu ta kalla da sauri ta ware ido tana ganin ƙarfe bakwai da rabi yanzu yasa ta miƙewa tsaye da wani irin sauri tana cewa.

"Wayyo Allah Aunty Murja wallahi na sha'afa yau Monday ina da lectures ƙarfe takwas, kuma wallahi Malamin baida mutumci, idan ya shiga baya bari kowa ya ƙara shiga ƙulle ƙofar aji yake"

Taɓe baki Aunty Murja tayi tana faɗin.

"Ke ni babu ruwana da makarantar da zaki je yawwa, ni dai abunda na sani dole ne kiyi duk aikin dake kanki kamin na barki kisa ƙafa ki fita daga cikin gidan nan nama faɗa miki kiji da kyau"

Yusura dake kwance gefe akan katifar da suke kwana, hayaniyar maganar Aunty Murja yasa ta motsa, tana ɗan miƙewa zaune a hankali ta shiga mursa idonta kamin ta ce.

"Aunty Salma je ki fara shiryawa kawai, ni zan fara tayaki aikin"

"To ƴar neman magana, sarkin tausayi, kuma aikin saita yisa naga ta tsiya"

"Haba Umma dan Allah, School fa zata je kuma kin sani fa"

"Ke dalla can yimin shiru, wallahi Yusura ki fita idona na rufe tom"

Aunty Murja ta faɗa tana yin kwafa ta juya tana ficewa daga ɗakin.

Kallon Salma Yusura tayi tana tashi tsaye itama ta ce.

"Kije ki fara yin wanka, naga lokaci ƙara tafiya yake ma"

"Na gode Yusura"

"Haba mine na godiyar kuma Aunty Salma?"

Girgiza kai tayi tana ƙoƙarin cire rigar baccin dake a jikinta tasa zani ta ɗaura, tana ficewa daga ɗakin dan ita Yusura ta fara fita tabi bayanta.

Tsakar gidan kaca-kaca kamar wadda ke ɗauke da yara ƙana-ƙana, kuma jiya a iya saninta sun gyara shi kamin su kwanta bacci da yamma.

Amma yanayin data tsaya ta kalli tsakar gidan tasan da gayya aka ɓata shi.

"Wai waye ya lalata tsakar gidan nan haka Umma?"

Aunty Murja dake zaune akan kujera ta ɓalla mata hararara haɗe da cewa.

"Ban sani ba"

"Amma Umma ai gani nayi bamu da yara ƙana-ƙana bare har ace gidan yayi saurin lalacewa kamar haka"

"To zakiyi aikin da uwar taki ta saki ne ko kuwa ni zaki zo ki tsare da banzar tabbayar nan taki?, idan bazaki gyara ɗin ba ita shafaffa da mai ɗin ta zo maza ta gyara shi wallahi"

"A'a zan gyara ai ni na ce"

"Mtswww"

Aunty Murja ta saki tana tunanin yadda zatai da Yusura ta daina shige ma Salma bare har taji tausayinta a ranta.

Shaf-shaf Salma tayo wanka ta fito tana shigewa ɗakinsu, tana ganin har lokacin Yusura nata fama da sharar gidan ko abincin karin bata kai ga ɗorawa ba.

Dan haka tasan bata fita daga cikin gidan saita ɗorasa kawai ta sadaƙas bata shiga wannan lecture ɗin ta safe.

Kayan Makaranta tasa dan school ɗin da take yi wacce ake saka yinifam ce.

Kalar wandon data saka ruwan ƙasa sai Hijab ɗinta fara da riga, kayan ba ƙaramin kyau sukai mata ba, tana sauri ta aje Hijab ɗin tata bayanta ɗaura kallabinta ta fito tsakar gidan.

Kitchen ɗin tsakar gidan ta nufa tana ma Yusura sannu dake sharo ɗakin Aunty Murja, ita ko tana zaune tana jin redio a cikin wayarta.

"Aunty Murja mi za'a dafa"

Salma ta faɗa tana ɗan leƙowa daga kitchen ɗin.

Wani kallo ta jefa mata na wasu mintina, har Salma na kiran Innalillahi a zuciyarta, saboda duk ƙara ɓata mata lokaci ne kawai take kuma tasan tana sane take hakan, duk dan ta ɓata mata rai kamin ta tafi school ɗin.

"Ki dama koko, sai kosai anyo markaɗe zaki gansa an ajesa"

"Amma Aunty Murja soya Ƙosai yanzu wallahi wahala zansha kuma ƙara makarar dani zaiyi naga yanzu fa har takwas ɗin tayi ma"

Salma ta faɗa da fuskar tausayi sosai.

"Mtswww ke kika sani, ki tsaya magana zaki ga makara ganin idonki ma kuwa"

Kawai ta faɗa tana juya mata ƙeya alamar bazata ce mata komai ba kuma daga nan"

Juyawa tayi tana kallon kitchen ɗin, sauƙin ta ɗaya Gas ne ba murhu bane, idan Gas ɗin ya ƙare ne ake sanwa da murhu ko Gawayi.

Kunna Gas ɗin tayi tana dora ruwan da zata dama kokon dashi kamin ta sake kunna ɗayan da yake mai biyu ne yasa ta fara haɗa kayan Ƙosan, ta ɗora Mai akan wuta, tana gama saka magi da duk abunda ya dace ta buga ƙullun ƙosan ta fara soyawa.

Tana tsame kasko na biyun ƙarshe taga ruwan dama kokon ya tafasa.

Shigowar Yusura tana sauke lumfashi ne yasa ta ɗan kallonta tana ganin yadda ta gaji sai zufa take yasa Salma cewa.

"Sorry sannu kinji, kinyi aiki yau wallahi sosai"

"Ba komai ai, yanzu dai kawo na dama kokon sai ki idasa soya Ƙosan ko kin samu ki tafi"

"Da kin barsa ma sheƙa kokon kawai zanyi na gama"

"A'a dai kawo na idasa kawai"

Bata tayi tana maida hankalinta wajan soya kaskon ƙarshen.

Ita kuma dandanan ta dama kokon tana juyesa a wani farin bokitin da suke sawa gaba ɗaya.

Bata wani ɓata lokaci ba ta idasa soyar itama, suka fito a tare a tsakar gidan suka aje kayan abincin a gaban Aunty Murja.

Da sauri Salma ta juya ɗaki domin ɗakko sauran kayan Makarantar tata.

Tana cikin saka Hijabinta taji sallamar Yusura ta shigo ɗauke da faranti a hannunta da kuma kofuna guda biyu dake ɗauke da koko a cikisu tana kallonta ta ce.

"Gaskiya bazan iya tsayawa naci abincin nan ba Yusura ƙara makara zanyi idan na ce zan tsaya"

"Ko kaɗan ne ki tsaya kici dan Allah, dan makara ai kin riga kin makara ma yanzu"

"Allah bazan iya tsayawa ba, yana fa ɗaukar duk sunayen da suka halacci lecture shi, wadda babu shi kuma ƙari Over fa yake baka, gara kawai naje ko bai barni na shiga lecture ɗin ba na samu dai sunana ya shiga cikin sunayen da yake ɗauka na wa'inda suka shiga lecture ɗin tashi"

"Wai waye wannan Malamin marar kirki haka?"

"Hmm Yusura kenan, ai yawancinsu duk haka suke, bare shi fa provers ne fa na Hygiene ɗin gaba ɗaya, yake ɗaukarmu lecture shima, Mlm Jamilu kenan Yusura bashi da wasa ko kaɗan bashi kirki kuma, baya sakar ma ɗalibai fuska, kowanne ɗalibi tsoran Mlm Jamilu yake"

Taɓe baki Yusura tayi tana zama akan katifar da Salma ta gyara masu tama gyara ɗakin a tsaitsaye a tsaitsaye.

"Shi dai ya sani nifa shekara mai zuwa idan zan tafi karatun nan bazan iya irin makarantar da kukai keda Aunty Ummi ba, gashi harta gama ta barki ke ɗaya"

"Ai kin san ita shekara biyu ne ni kuma har Uku ce fa"

"Kun kusa kuma ai ko?"

"Da saura gaskiya tunda ko first semester bamuyi ba ga kuma second"

"Haka ne amma duk da hakan kamar gobe ne zaki ga kin gama ai"

"Hakane ni dai nayi nan Yusura sai na dawo"

"Tsaya Aunty Salma dan Allah"

Yusura ta faɗa tana fita da sauri ta dawo ɗauke da wata leda baƙa tasa mata nata a ciki ta buɗe jakarta dake hannunta tasa mata tana kallonta dai kamin taji Yusura ta ce.

"Idan an sami sarari ki ci abincinki dan Allah, ai ba'a taɓa karatu sosai sai anci an ƙoshi, koma miye a duniya sai da ƙoshi ake samu ayisa yadda ya dace. Allah ya tsare hanya"

"Amin sis na gode saina dawo"

Salma ta faɗa tana murmushi haɗe da kallon ta.

Tana fitowa ta iske Aunty Murja na cin nata abincin tana ganinta ta fito Aunty Murja ta taɓe baki tana faɗin.

"Hmm wai karatu, ni na rasa gane karatun Allah da Annabi ake zuwa ayi ne ko kuma yawon iskanci ne Ohhoo?"

Salma bata ce komai ba tayi saurin ficewa daga gidan gaba ɗaya tana jin zuciyarta na bugawa........

PAGE 15

A hankali tasa ɗayan hannunta tana yin filo dashi ta kwanta tana tunanin tafiyar da zatai gobe-gobe. Dan ji take kamar zata je kurkuku ne, kwata-kwata bata farin ciki da zuwanta Kano. A rayuwarta idan akwai garin data fi tsana bai wuce garin Kano bane. Dole za'ai mata uzuri dan tunda tasa ƙafarta a garin Kano da sunan karatu da zaman gidan wasu bata taɓa cin karo da mutanen da suka san darajar mutane ba daga ita har ƴar uwarta Salma, har basa so ace yau zasu koma Kano.

A hankali ta sauke ajiyar zuciya tana ƙara gyara kwanciyarta tana kallon saman silin ɗin ɗakin tana ƙara jefa kanta cikin tunanin rayuwarta baya.

*****************"Wallah Allah Ummi baki da kirki ko kaɗan, ni zaki yarfa a gaban bayin Allahn can masu gani na da daraja?"

Ya Muhmd ya faɗa dai-dai lokacin da suka shigo ɗakin Mama.

Mama dake a tsakar gida da sauri ta biyo su a baya. Ammi na binsu da kallo suna shiga tana jin lokacin da Ya Muhmd ɗin keta ma Ummi faɗa.

Bata san lokacin data saki wata ƴar dariya ba tana girgirza kanta kawai ta ci gaba da abunda take yi.

"Ammi naga kina murmushi mike faruwa ne?"

Safiya ta faɗa tana fitowa daga ɗakinsu tana bin Ammi da kallon ganin Yadda fuskarta ta faɗaɗa murmushi.

"Hmm babu komai mi kika gani?"

"A'a Ammi naga kina ta murmushi ne akan fuskarki"

"Ba wani abu fa wani abu ne ya ɗan bani nishaɗi shine kawai amma ki manta kawai"

Ammi ta faɗa dan so take ta kauda zancan.

"Kai Muhmd miya faru ne fitar taku?. Hala tayi baƙin halin nata ko?"

Mama ta faɗa tana kallonsu gaba ɗaya. Ummi taga yadda Mama ke jefa mata wani irin kallo yasa Ummi saurin shigewa ɗakinsu.

Mama ta kwala mata kira.

"Keeee zo nan na ce"

Dawowa Ummi tayi jiki a sanyaye cike da tsoro kuma.

"Mike faruwa ne gaya min Muhmmd?"

Zama Muhmmd yayi ransa a ɓace yana duban Mama data kai ta zauna itama ya ce.

"Hmm Mama ai komai ma wannan yarinyar tayi shi wallahi"

"Ka tafi kanka tsaye ka gaya min abunda tayi ɗin"

"Wallahi Mama muna zuwa yarinyar nan tana ganinsa, ko gaisawa basu yi ba, ta dai gansa taga ai ba irin Maza ƴan ƙaryar da take son aura bane, saita fara ɗaure masu fuska wallahi Mama, sai gaya masa magana take tana harararsu gaba ɗaya. Koda muka matsa da P'A domin basu waje wallahi a nan ta samu ƙofar gaggaya masa magana son ranta wai ita tafi ƙarfin aurensa, shi ko kunya ma baya ji, ina laifin yanzu ace neman auren ɗansa ya zo yi ba wai nashi ba?, shi kam mima zai yi da aure yana gaɓar mutuwa?"

Mama da tayi shiru tana jinjina kai.

Ummi da kanta ke ƙasa bata san lokacin da Mama ta tashi ta zo inda take ba sai dai kawai suka ji ƙarar wani mari mai ƙarar gaske da Mamar ta ɗauke Ummi dashi. Shi kansa Ya Muhammad a zabure ya miƙe yana kallon Mama, yadda yaga ranta a ɓace zata iya kai mata wani marin.

A mugun zabure Ummi ta miƙe tsaye dafe da kumatunta tana zaro ido waje tana bin Mama dasu.

Wani marin Mama ta ƙara kai mata a ɗayan kumatun nata, ai dandanan Ummi ta fashe da kuka tana kaiwa ƙasa ta kama ƙafafun Mama tana faɗin.

"Mama dan Allah kayi hakurii"

"Ki sake ni na ce Ummi. So kawai kike dama kiga baƙin cikin ki ya kashe ni, to wallahi baki isa ki ɗora min hawan jini ba, bare baƙin cikinki ya kashe ni wallahi baki isa ba. Kije duk abunda kika ga ya dace dake kiyi, amma bazan ƙara cewa wani ya zo neman aurenki ba, akwai ranar da zaki gane gata nake miki ba wai bana sonki bane"

Da sauri Ya Muhmmd ya tashi yana kamo hannun Mama ya zaunar da ita sai sauke ajiyar zuciya take tana ɓallama Ummi wani irin kallo haɗe da harara.

Zaiyi magana sai ga Ammi ta faɗo ɗakin ita

7 / 36