Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   4 / 36

9K to 12K   out of 106.4K words

ɗaukar wannan rainin, jiya ma dan a gaban uwarta ne yasa bata ɗauki mataki akan Safiya ɗin ba, da tai mata rashin kunya.

Wani ub*an ihu Safiya ta saki tana sakin kuka iya ƙarfin tana nuna Ummi da yatsa.

"A'a a'a mi zan gani haka ke Safiya mike faruwa a nan?"

Wani kalar kuka ta ƙara saki tana matsawa inda Ammi take ta ce.

"Ammi wai fa daga na kawo kwanukan nan wadda Baba ya gama cin abinci shine ta ce wai bazata wanke ba, ni kuma na ce mata ai ita ke da aikin waye zai wanke idan ba ita ba?, shine kawai ta ɗaga hannunta ta sharara min mari"

"Gaskiya ne Ummi kin riƙa kin zama riƙaƙƙiyar kuɓewa, har kin isa a kin kai a kawo wani aiki a cikin gidan nan ki ɗaga hannu ki ce zaki mari Safiya. Wai idan kin gaji da aikin mi yasa bazaki fiddo da miji ayi miki Auren ki bar gidan gaba ɗaya bane?, ai shine kawai zaki daina aiki a cikin gidan nan idan kin tafi naki gidan, amma muddun kina zaune a cikin gidan kuwa dole ne kiyi kiyi aiki wallahi, idan fitsari banza ne Kaza tayi mana wai mu gani"

Wani baƙin ciki ne ya turnuƙe Ummi zatai magana sai kuma tayi shiru jin wani irin malolan baƙin ciki daya riƙe mata maƙoshi.

"Kiyi magana mana ai dai-dai nake dake a cikin gidan nan wallahi"

Ammi ta faɗa tana banka mata wani banzan kallo.

Tasan Mama tana jin komai amma bazata taɓa fitowa ta shigar mata ba, ta rasa wane irin hali ne da Mamar tasu.

"Wuce ki tafi kawai kuma dole ko taƙi ko ta so dole ta wanke kayan ub*an wani zaiyi mata aikin ne?"

Wucewa Safiya tayi tana juyowa tayi ma Ummi gwalo, kuma ta gani wani irin murmushin daya fi kuka ciwo kawai ta saki tana duƙawa ta wanke kayan kawai ta tashi bar tsakar gidan da sauri dan bata so wani abu ya ƙara haɗata da su Ammi ɗin.

Tana shiga taga Mama a zaune tana jan carbi, a hankali ta zauna a kusa da ita, tana ƙoƙarin shanye hawayen da ta riƙe tun a waje suka sami nasarar zubowa akan kumatunta, ta riƙe hannun Mama ta ce.

"Wai mi yasa hakan ke faruwa damu ne Mama?, muma fa ba'a son ranmu muka kai har yanzu ba bamuyi auren nan ba, wallahi Allah munfi ku so muyi mu matsa daga kusa daku"

Wani irin kallo Mama ta jefa ma Ummi daya sa Ummi yin ƙasa da kanta.

"Ke har kina da baƙin magana ne Ummi?"

"Amm.....

Ɗaga mata hannu Mama tayi tana sake kallonta sosai ta ce.

"Kin riga kin san babu irin damar dake baki samu ba a rayuwar nan, kin san irin Maza da yawa tun kan ki kai haka yadda suke mugun sonki da son aurenki, amma a can baya kikai ƙimeme kika hana, kika ƙi bawa kowa dama, ni ada can bayan ma na ɗauka ko aljanu ne dake, ashe iskaci ne kawai, ai dama wani lokacin shi Allah zaita baka dama ne kai kuma kana wasa da ita, yanzu ina Mazan suke Ummi?"

Kuka mai sauti kawai Ummi ta saki, domin gaskiya Mama ta faɗa, sosai tayi wasa da damarta, bata jin duk gidansu wani yayi farin jinin Samari irinta, a lokacin da tayi tashen samari baya ita duk gidan nasu, amma ta rasa miye ya shiga kanta tayi ta wasa da damarmakin da Allah yayi ta bata, ta samu dama ba ɗaya ba ba biyu ba.

"Hmm ai idan dai kuka ne Ummi yanzu kika fara ma, amma idan zaki tsaida hankalinki waje ɗaya ki fiddo da miji kamin Babanku ya fara gajiya da ku ya bada ku sadaka wallahi daga ke har Salma ɗin"

"Haba Mama kiyi mana addu'a kawai"

"Ai addu'a yadda nake maku ma ni banawa kaina bari kinji in gaya miki. Na dai gaya miki gobe-goben nan ki shirya zaki wuce Kano karma ki ce ban faɗa miki ba"

"Wai yanzu Mama dole sai naje Kano ɗin nan?, wallahi Allah bana son zuwa gidan nan na Aunty Binta"

"Kyayi da wani"

Mama ta faɗa tana miƙewa ta wuce ta, ta barta a nan.

Jiki a sanyaye Ummi tayi ƙasa da kanta tana ɗan zamewa a hankali ta kwanta a ƙasa tana zurfafawa cikin tunani akan rayuwarsu ta baya tada wuce.

***************"Kinga Aunty Ummi wallahi gayan nan yayi Over a dai yadda Ya Muhmd ke gaya min shi, dan Allah kar ki ce shima baki sonshi"

Gyara tsayuwarta Ummi tayi tana duban Salma ta ce.

"Nifa baiyi min ba Salma, idan har mijin nan nawa ya zo zanji fa ina sonshi amma wannan kam a'a gaskiya baiyi ba"

"Ikon Allah yanzu miye aibun Sadiq Aunty Ummi?"

"Bashi da wani aibu Salma bana son nashi ne kawai shikenan"

"Anya baki da motsi a saman kanki ba kuwa?"

Wani dukan wasa Ummi ta kai ma Salma tana gocewa da sauri ta miƙe daga inda take tana ƴar dariya ta ce.

"Ai gaskiya ce, ya za'ai ke kullum baki son kowa, to ma wai waye zaki so ne?"

Shigowar Mama yasa Ummi yin shiru.

Kallonsu tayi ta ce.

"Shima wannan ɗin da Yayan naku ya haɗaku baiyi miki ba ko?"

Juya ƙeya tayi tana turo baki ta ce.

"Haba Mama kin gansa kuwa da wani ƙaton ciki, ni gaskiya bana sonshi bai min ba"

"Hmm yayi miki kyau ai, amma wallahi ku duka ku sani idan har na gaji zan bar maku gidan ne, sai ku zauna ku tare kuda Mahaifin naku, dan naga shima shike ƙara ɗaure maku gindi ai"

Shiru sukai gaba ɗaya kansu a ƙasa tana gama faɗar haka ta wuce parlo ta barsu a ɗaki daga parlon suna jin yadda take mita tana ƙara cewa.

"Shi dai mutum idan har yayi wasa da damar shi ai zai gane kuransa, wata damar dai sau ɗaya a rayuwa take zuwarma mutum wallahi"

Su duka ba wadda yayi ƙoƙarin ƙara magana dan sun san Mama idan ta kama mitar nan sai Allah kawai.

Shigowar Ya Muhmd ne yasa ta ɗan yin shiru suna iya juyo muryarsa yana cewa.

"Wai yanzu tsakani da Allah Mama haka Ummi tayi ma mutunen wulaƙanci?, wai fa kai tsaye ta nuna masa bata ra'ayinsa fa"

"Yo ai Muhmd kamar baka son yaran nan ba ai basu da hankali da tunani, garama Salma, amma kaga Ummi, kwata-kwata bata iya tafiyar da mutum ba, ai ko baka son mutum ba ka sanar dashi a nan take ba, sai ka lallaɓasa ku rabu lafiya, amma da yake bata da wayo duk bata iya wannan ba ita"

Daga can cikin ɗaki Ummi ta kumbura fuska kamar zata saki kuka ta ce.

"To ni Mama kawai sai nayi ta yaudarar mutum da soyayyar ƙarya?, gara kawai na gaya masa a nan take karma yasa ka ran son nashi nake"

"Dalla gafara can rufe min baki, shashasha marar wayo, ai kinyi ma kanki wallahi"

"Hmm ai Mama wallahi ba ƙaramar asara tayi mana ba, Abuja fa zai aje ta Mama, harfa alƙawari aiki yayi min da anyi bikin nasu zai bani aikin, amma yanzu tayi mana baƙin ciki"

"Ai tayi ma kanta, ni wallahi dama ba ita ya ce yana so ba dama Salma ya ce yana so"

"Tabɗi jam ai wallahi itama haka zata ce masa, duk fa halinsu ɗaya Mama"

"Ai gara Salma nasan ita bazata gaya masa kai tsaye bata sonshi ba, zata lallaɓasa ne koda bata son nashi su dai rabu lafiya, amma fa ita Ummi kowaye ya ce yana sonta kai tsaye take sanar dashi itafa bata ra'ayinsa, wai a haukanta sai dai kawai a rinƙa gaisawa, ko suyi abota da shi, baccin kina hauka wata rana ma hatta mai abotar zaki nema ne ki rasa muddun bazaki shiga hankalinki ba wallahi"

Daga cikin ɗaki Ummi ta taɓe baki tana kamo hannun Salma ta ce.

"Ke yanzu nan sai ki yarda a ƙaƙaba miki wannan mutunan?"

"To Aunty Ummi miye ne dashi na abun ƙi wai?"

"Hmm lallai to in gaya miki duk yadda Ya Muhmd ke faɗa miki shi ba haka yake bafa. Wai kin gansa da wani ƙaton ciki gashi ance har aure garesa da ƴaƴa manya, ina zan kaisa ni?, inaaa wallahi bazan iya ba"

Jikin Salma ne yayi wani irin sanyi itama sai taji bazata iya auren nasa ba.

Suna iya juyo yadda Mama keta ruwan masifa Ya Muhmd na ƙara zuga ta......

*Wannan book ɗin na kuɗi ne Free pages zai tsaya daga na 10 insha Allah, zaki iya saka kuɗinki a turo miki complete nasa akan Naira ɗari biyar kacal #500*

Account number 8130479973 Fatima Rabi'u Opay Bank.

Shaidar biya 08130479973

*MUGUN ICCE*

*Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSO........*

PAGE 8

*UMMI POV*

"Wai Ummi baku shirya ba har yanzu?"

Da sauri Ummi ta shiga ɗaure kallabinta da yayi saura, tana ƙoƙarin saka gyale, tayi kyau sosai ta dubi Salma dake saka takalmi tana cewa.

"Wallahi fa Mama tun ɗazu ita nake jira"

"To ni nayi gaba ku iske ni bakin hanya, kuyi sauri kuma"

Mama ta faɗa tana ficewa daga ɗakin.

"Kiyi sauri dan Allah Aunty Ummi"

"Muje karki cinye ni ɗanya. Nifa da Mama ta biye min baza ni wani biki ba ni wallahi"

"Wai mi yasa ke baki son mutane ne?, komai akai miki ba'a iya ba"

"To ƴar iya, baki ji jiya ƙawar Mama ta kira ta ba suna maganar bikin nan na ɗiyar ƙawarsu a Kankia?. Harda gaya mata matsala ta, wai ta ce mata ta rinƙa tahowa damu wai ko za'a dace a wajan biki mu samu miji, jifa wata magana dan Allah?, nifa ko bana son haka wallahi, ita kuma Mama ta wani biye mata"

"To Aunty Ummi miye a ciki kika sani ma rabon samun mijin zai kai ki bikin nan, kin san wata ko wani a bikin wasu suke samun nasu abokan zaman ai"

Taɓe baki Ummi tayi suna idasa fitowa daga cikin ɗakin nasu. Suna fitowa suka iske Ammi da Safiya a tsakar gidan suna zaune.

Sunyi ma Ammi sallama a sama-sama ta amsa tana binsu da wani kallo, basu damu ba suka yi gaba dan sun saba da irin hakan daga gare ta dama.

"To wai su nan ina zasu je ne Ammi?"

Faɗin Safiya tana bin bayansu da kallo har suka ɓace ma ganinsu.

"Yo waye ma ya sanar masu ne?"

"Daga ganin wannan gayun dai ƙila biki ne zasu je"

"Hhhh to ikon Allah yanzu kuma ita Nadiya ta fara zuwa da ƴaƴanta biki kenan?, ko duk neman mashinshinin ne haka?"

"Lahh ai ko shine ma Ammi neman mijin aure aka tafi"

Faɗin Safiya tana riƙe baki.

"Hmmm ayi mu gani dai"

Kawai Ammi ta ce tana sakin wani maƙirin murmushi na gefen baki.

"Wai tunda muka fito baki ga Ammi yadda take jefa mana kallon banza bane Aunty Ummi?"

"To sai miye?, na gani man, tayi da wadda zata yi ai. Matar can fa munafuka ce, a gaban Mama karki so ganin yadda take mana, bata taɓa nuna komai sai ta rinƙa nunawa kamar ita ce ta haifemu, tana wani nunawa kamar duk ɗaya muke da Safiya a wajanta"

"Ni na san hakan kuwa Aunty Ummi, ai gida ɗaya fa muke zaune da ita, kinga ita da Aunty Murja na rasa gane waye yafi wani iya munafurci"

"Lallai ai ita Aunty Murja ƴar kai tsaye ce, nan take, take faɗar abunda ke cin ranta, itafa wannan baka taɓa gane inda ta dosa fa"

"Allah dai ya shiga tsakanin na gari da mugu wallahi"

Faɗin Salma dai-dai lokacin da suka ƙaraso bakin hanya inda Mama take tsaye da Ya Muhmd dake son tare masu Mota.

"Mi kuka tsaya yi ne a gidan?, shiru kunje kinyi wani zamanku Allah da an sami Motar da sai da kuji Mama ta tafi tabar ku"

Turo baki Ummi tayi tana magana ƙasa-ƙasa.

"Dama an samu ɗin wallahi kamin isowar tamu, da an hutar dani nikam"

Ta ƙare maganar tana wani juya ƙeya baya.

Girgiza kanta kawai Mama tayi dan tsaf taga bakin Ummi na motsi ta san kuma magana ce zata faɗa. Allah dai ya shirya mata Ummi, dama tunda ta nuna mata son zuwa bikin nan zata yi abunda yafi haka ne, bata son hayaniya kwata-kwata shi yasa sai baƙin rai take.

"Ya Muhmd mun ɗan tsaya sallama da Ammi ne"

Salma ta faɗa.

"To yayi"

Ya faɗa dai-dai wata Mota ta zo giftawa ya tsaida ita, anyi sa'a kuwa har Katsina Motar hayar ta nufa dan haka Ya Muhmd ya ce Kankia za'a kaisu. Suka hau gaba ɗaya kamin ya wuce ya tafi wajan aikinsa, dama kuma daga can ya fito shan iska ya hango Mama a bakin hanyar shine ya tako ya zo yana tsaida masu Mota.

Har suka isa Kankia Mamar na ɗan basu labarin ƙawar tata wacce sukai Makaranta a tare Salma ta gane ta, ita ko Ummi tana dai jinsu ne a sama-sama.

Basu wani ja lokaci ba suka isa Kankia, ana sauke su suka gangara da yake gidan kusa da bakin hanya ne.

Sun samu tarba ta mutumici sosai ƙawar Mama ɗin uwar bikin kenan sai nan take da su sosai taji daɗin ganin Mama da ƴan matanta.

Dandanan aka cika gabansu da kayan ciye-ciye.

Mama dake zaune da ƙawarta uwar bikin ta ce.

"Ni kam sister wa'innan duk yaranmu ne suka girma haka?"

Mama ta kallesu tana murmushi ta ce.

"Wallahi fa kin dai gansu nan"

"Ai ko tubarkallah sun girma wallahi Masha Allah. Amma fa gaskiya babbar can Ummi sunanta ko?"

"Haba Salamatu harkin manta sunan ƴar taki, kin san sunan mahaifiyar Babansu taci Bilkisu shine ake ce mata Ummi, ita kuma ƙanwar ai nasan bakin mance da sunan nata ba tunda takwararki ce ai"

Dariya suka saki a tare Salamatu ta ce.

"Ya za'ai na mance da takwara ta kuwa?. Kinga ba wannan bama wallahi na fara sha'awar haɗa Ummi da ɗan waje na Al'mustapha, kin san har yanzu baida aure. To da can ya samo Mata a can Kano ni kuma gaskiya ban aminta da yarinyar ba, shine yasa ma ya ɗan takatar da maganar tata, ni kuma yanzu tunda naga Ummi naga kamar zasu dace da juna"

Wani irin daɗi ne ya rufe Mama zuciyarta kamar an mata albishir da aljanna haka taji tana murmushi ta ƙara maida hankalinta ga Salamatu ta ce.

"Kina ganin shi zai so ta ne?"

"Haba ai duk abunda na ce ma Al'mustapha ina so to tabbas shi zaiyi, karki wani damu, kawai ita a sanar da ita, ai dai nasan bazata ƙi jini na ba"

Ɗan shiru Mama tayi, mita tuna kuma ta saki murmushi kawai tana cewa.

"Karki damu insha Allah kawai Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, ki bani number nashi saina bata ko kuma shi idan kuka gama magana sai ki bashi number ta, idan ya so da mun koma gida zanyi mata maganar insha Allah"

"Yawwa sister shi yasa nake yi dake, ai ni yaron na ya sami kamar Ummi ai abun alfahiri na ne wallahi"

"Amma dai bata da wadda take so a yanzu ko?, ba wadda ya fito neman aurenta?"

Salamatu ta ƙara faɗa tana kallon Mama sosai.

Girgirza kai Mama tayi ta ce.

"Gaskiya babu kowa a yanzu, kuma ma koda akwai bai shigo gida ba, kinga kuwa ai ba an bawa na dawa na gida bai ƙoshi ba"

Dariya suka saki a tare harda tafa hannu.

Sun daɗe suna tattaunawa akan haɗa Ummi da Al'mustapha ɗin yadda zasu ɓillo ma al'amarin, bare Mama da take ganin sai ta miƙe tsaye sosai akan Ummi idan ba haka ba zata iya rusa mata komai, to ya zama dole a wannan lokacin sai tayi mata jan ido tukunna zasu shirya da ita......

*Wannan book ɗin na kuɗi ne Free pages zai tsaya daga na 10 insha Allah, zaki iya saka kuɗinki a turo miki complete nasa akan Naira ɗari biyar kacal #500*

Account number 8130479973 Fatima Rabi'u Opay Bank.

Shaidar biya 08130479973

*MUGUN ICCE*

*©Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSO.....*

PAGE 9

A hankali ta ɗago ta kalle ta tana cewa.

"Ki zauna magana zamuyi dake"

Zama Ummi tayi tana mamakin wacce magana ce haka da zasuyi daga Mamar sai ita kuma haka?.

"Ki buɗe kunnanki da kyau ki jini"

"Tom Mama ina jinki"

Ummi ta faɗa jiki a sanyaye.

"Bikin da muka je jiya a Kankia na ɗiyar ƙawata Salamatu, to ta ganki kuma tana son ɗanta ya aure ki, dan yanzu haka sunyi magana da ɗan nata ta bashi number wayarki zaiyi miki magana na sani. To wallahi Allah ki sani idan har kikai masa wulaƙancin nan naki da kika saba to tabbas zaki ga ɓacin raina da baki taɓa gani ba a rayuwarki, dan nasan ba wayo ne ya ishe ki ba"

"Kaiii Mama mai aikin nan a hukumar custom Al'mustapha ko?"

Faɗin Ya Muhmd dake cikin ɗakin Mama ya faɗa yana fitowa gaba ɗaya.

"Ai ko yarinya da kinyi sa'a wallahi custom ne fa"

Wani tsaki Ummi ta saki a cikin zuciyarta tana ɓallama Ya Muhmd wata hararara ƙasa-ƙasa.

"Ni dai na gaya miki zaki iya tashi ki bani waje"

Miƙewa kawai Ummi tayi tana shigewa ɗayan ɗakin wadda yake nasu ita da Salma.

Tana shigewa Ya Muhmd ya dubi Mama ya ce.

"Mama mi yasa da yawan mutane ke cewa wannan yarinyar suke so ne?, dama Salma ce take samun damarmaki haka da yanzu wallahi tayi aurenta, bata da baƙar zuciya da kafiya irin na Ummi"

"Hmmm Muhmd kenan itama tana da nata farin jinin, kawai dama ce bata cika samu kamar yadda ƴar uwarta Ummi take samu ba, ni dai fatana Allah isa karta yi halin nan nata akan wannan ɗin shima"

"To amin dai kam amma kaɗan daga al'amarinta ta rusa abun"

"Za kuwa taga ɓacin rai na wallahi, dan naga alamar sai an tashi tsaye a kan wannan yarinyar"

Ummi najin duk abunda suke faɗa daga ɗakin tana duban Salma data miƙe

4 / 36