Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   23 / 36

66K to 69K   out of 106.4K words

son wannan bawan Allahn, ni dai yanzu kimin alƙawari cewar su Mama basu taɓa sani ba, sana dashi kansa Jamilu bana so yasan halin da nake ciki akan sonshi"

"To mi yasa?, ai kamata yayi yasan irin halin da kike ciki, tunda baida tausayi shi, bazai iya tausaya maki ya aure ki ba"

Ummi ta faɗa ranta a mugun ɓace.

"A'a Aunty Ummi ki rinƙa masa uzuri, wata ƙila fa ko ayyuka ne sukai masa yawa shi yasa bai neme ni ba"

"Dalla can kafara can, wallahi azim Salma ki shiga hankalinki. Wai kuwa kin san mi Doctor ya ce akan rashin lafiyar nan taki?, cewa fa yayi zuciyarki ce ta fara kunbura saboda damuwa da halin tsoro da kike shiga ne yake shirin jawo maki kunburin zuciya, kuma ya ce idan har bazaki cire damuwa ba to zuciyarki zata iya bugawa ki mutu a banza, kinga idan kika mutu ai shi baida asara, ƙilama ko gaisuwa bazai zo ba taki, mune yayi ma asara"

Hawaye ne masu zafi suka shiga zuboma Salma ta ce.

"Nasan koma miye zai sami zuciyata Aunty Ummi ni kaɗai nasan yadda nake jin ciwo da radaɗin rashin Mlm Jamilu a kusa dani, ni kaɗai nasan ciwo idan na kirasa baya dauka kuma idan yaga kiran baya kira na, ko messages masu fahimci nawa baya dawo min da amsa, ni kaɗai nasan yadda nake tsintar kaina idan hakan ta faru"

"To kuma sai ki ce kar ayi magana akan rashin kyautawar da yake maki?. Ba wani uzurin daya kamata ayi masa, ai duk wadda ya ce yana sonka wallahi ya wuce wulaƙanci. Kuma yasan bazai aure ki ba miye na faɗa miki cewar wai zai aureki?, harda cewa da yanzu kin daɗe da zama matarsa da ace tun shigowarmu school ɗin kuka haɗu, yasan ba gaskiya yake faɗa yasan ba aure zaiyi danmi zaisa zuciyarki ta yarda?, danmi zai saka miki rai?"



Aunty Ummi ta ƙarasa maganar ranta na sosuwa.

"Ai Aunty Ummi adai masa uzurin, wata ƙila baya son aure ne yanzu ko dan kar ya tarwatsa gidansa, ko matarsa ce yadda zata ɗauki abun yake gudu, ni ina kallon abun ta fuskar hakan"

"Ahhh to sai mine?, ba sai ya yatsa tsayin daka ba ya fuskanci gidansa, idan ba'a auren wasu matan zasu mutu ne a gida ai, sana ba'a aure ita aka aureta?. Shin wai ba Allah ne ya ce ayi ba fiye da ɗaya ba?, to akan mi abunda Allah ya ce ke wata can banza zaki zo ki ce ba'a isa ayi ba?. Kinga ko nifa Salma shi yasa duk runtse bazan iya auren mai mata ba, saboda bazan iya da wannan ciwon kan na wasu matan ba, da haukan kishi da suke ɗorama kansu ba, akan kawai za'ayo masu kishiya. Kuma babu wani uzuri ni da zan masa, idan ma aikin ne yayi masa yawa yasan kina kiransa ai kuma yana ganin messages naki, mi yasa idan ya samu time bazai kira kin ba?, mi yasa hakan?. Wai mi yasa wasu mazan idan sukaga mace na mugun sonsu suke amfani da wannan damar wajan wulaƙantata ne?"

"Ni Aunty Ummi bazai taɓa wulaƙanta ni ba"

Sake da baki Ummi ke duban Salma, ai sai ta shiga girgiza kanta tana cewa.

"Ahh lallai wallahi Allah Salma kin hauka ce da son Jamilu, Allah ya yaye maki. Amma ki sani idan baki rage damuwa dashi ba zaki mutu ne a banza, shi dai baida asara wallahi, sana kuma idan baki rage wannan damuwa da zakwaɗin akansa ba na rantse maki saina gaya ma su Mama da Baba, dan shi Baba ya ɗauka ko irin abunda Aunty Murja dasu Mama ke mana ne na munƙi fitar da miji ne yasa ki cikin damuwa irin haka, basu gane ainafin abunda ke damunki ba, to idan baki shiga hankalinki ba zan sanar dasu ainafin abunda ke faruwa"

Salma zatai magana su Mama suka buɗe ƙofar ɗakin suka shigo. Da sauri Salma ta share hawayen dake zubo mata Ummi na tayata sharewa.

Murmushi yaƙe suka saki a tare Ummi ta miƙe daga inda take ta ce.

"Yawwa Mama ta farka yanzu, da yanzu nake shirin fita na kirawo Doctor ma ya ƙara dubata"

Hamdala Mama tayi tana ɗan sakin fuskarta sosai ta matsa kusa da Salma Ammi tuni taje ta zauna a kusa da ita inda Ummi ta tashi ta ce.

"Ya jikin naki Salma?"

"Da sauƙi Ammi"

Mama ta riƙe hannunta ta ce.

"Ke yanzu Salma akan wannan ƴar maganar ce da nake maku akan fitar da miji ce tasa ki haka?. To da yardar Allah ki kwantar da hankalinki na daina faɗar haka, amma abunda nake so daku shine dan Allah ku natsu ku fitar da miji, gidan miji shine mutumcin mace, mace bazata gane tana da gata da ƴanci ba har sai tayi aure, kunji ƴan albarka"

Murmushi Salma ta saki tana ɗaga kanta alamar insha Allah.

Fita Ummi tayi itama tana murmushi tana so itama dai ta fitar da mijin nan kota farantama Mama rai, har tausayi Mamar ke bata wani lokacin......

PAGE 45

"Insha Allahu za'a iya sallamarta zuwa goben jikinta ba laifi. Amma dole fa saita kiyaye saka damuwa a ranta"

"Insha Allahu Likita za'a kiyaye saka ta cikin damuwa"

Ammi ta faɗa tana kallon Doctor.

Fita yayi bayan ya bada umarnin a bata magungunan.

Zama Ummi tayi tana kallon yadda Ammi keta irin wannan abu sai ka ce Safiya ce ke kwance a gadon asibitin, tana ganin yadda Ammi ke ɓalle magungunan tana bata da kanta, itafa Allah ya gani wannan abun da Ammi keyi haushi yake bata, kuma gani take duk son asani ne da ƙara shigema Mama ta yarda da ita.

Washe gari tunda safe aka sallamesu.

Su Baba na zuwa suka shiga Motar Baba daya zo da ita yau. Tunda suka shiga Ammi ke waya da Inna.

"Eh wallahi kwananmu biyu a asibiti, bama cikin kwanciyar hankali shi yasa ban ɗauki wayar taki ba jiyan"

Daga cikin wayar Inna ta ce.

"Subhallahi Allah ya bata lafiya. Dama kira ne nayi na gaya miki yanzu haka mun koma Kano"

"Masha Allah Inna yaushe kuka koma?"

"Mun kwana biyu yau da komawa, dan har anje an biya ma Sadiya kuɗin jarabawar nan da ake wucewa ta gaba da sakandiri"

Ummi dake gefen Ammi abun ya bata dariya, yadda Inna ke faɗan secondary.

"Inna insha Allah zan zo Kanon idan na samu dama"

Ammi ta kauda maganar Sadiya, dan bata ƙaunar maganar yarinyar ko misƙala zarratin.

Inna duk da tasan tayi hakan ne dan kawai bata son maganar data kawo mata ta Sadiya sai Inna ta biye mata itama ta ce.

"Tom shikenan ki gaida mai jiki, Allah ya sawwaƙa"

Sauke wayar Ammi tayi tana ɗan taɓe baki, dan ranta ma sosai ya ɓaci akan maganar Sadiya da Inna ta kawo mata.

Ummi duk na ankare da motsinta.

Itama girgiza kai tayi haɗe da maganar zuci.

Shi dai mutum idan munafurci ne ya iyasa ga kowa ma, har dangin naki wadda kuka fi kusa ma baki kyale ba ashe?.

Ta faɗa a zuci tana ƙara jefama Ammi wani kallo.

Suna komawa gida Ummi ta kamo Salma suka shige ɗaki.

Kwanciya Salma tayi tana jin ƴar tafiyar da tayi daga waje zuwa cikin gida harta gaji zuciyarta sai duka take kamar wacce tayi gudun tsire, da alama tana buƙatar hutu da gaske.

"Sannu kin gaji ko?, naga sai nishi kike daga ƴar tafiyar nan"

Gyara kwanciya Salma tayi tana sauke lumfashi ta ce.

"Wallahi kuwa Aunty Ummi kinji yadda ƙirjina ke duka kamar wacce tayi wata muguwar tafiya"

"Sannu gaskiya ki daure ki cire damuwa a ranki please"

"Aunty Ummi ina wayoyinmu ne?"

"Gasu can kusa dake akan gado, ai tunda muka tafi jiya a nan muka barsu, a ruɗe muka tafi shi yasa banma bi ta kansu ba, Allah yasa basu mutu ba rashin chaji"

Ɗaukar wayarta Salma tayi tana zumuɗin ko zataga kiran Mlm Jamilu.

Sai dai tana buɗe wayar ba laifi akwai sauran chaji a jikinta bata kai ga daukewa ba.

Akwai kira da akai mata kusan sau uku, amma duk ciki babu na Jamilu. Jikinta ne yayi wani irin sanyi ƙlau. Anya kuwa ba ita kaɗai ke haukanta ba kuwa?, akan son bawan Allahn nan?, anya shi yana sonta har cikin ransa kuwa?.

"Miya faru kuma Salma?"

Ummi ta faɗa tana saurin zama kusa da Salma ganin yadda tayi shiru tana ƙurama waje ɗaya ido a cikin wayar tata.

"Wai minene dan Allah?, kinga fa yau kika dawo daga asibiti"

Sauke wani lumfashi Salma tayi ta ɗago tana duban Ummi ta ce.

"Ba komai fa Aunty Ummi"

"Ƙarya kike wallahi"

Ummi ta faɗa tana amshe wayar Salma dake hannunta.

Ganin inda take kallo wajan jerin numbers miss call na Doctor Nura ne kawai take kallo a wajan, sai kuma WhatsApp data ga ta buɗe data shima tana binsu da kallo. Lokaci ɗaya ta harbo jirgin Salma da abunda yasa ta damuwa yanzu ɗin.

"Akan Jamilu ne ba?. Kinga dai kin kwanta a asibiti bai ma sani ba, sana yaga kwana biyu duk messages ɗin da kike tura masa kina damunsa da kira bai gani a kwana biyu ba, amma bai neme ki ba, sana ke kuma ki zauna kina damuwa da hakan. Wai mi yasa bazaki fitar da Mlm Jamilu a ranki ba, wallahi baya sonki Salma"

Hawaye ne Ummi taga Salma nayi wadda ita kanta bata san lokacin da suke zubowa ba.

Hankali a tashe Ummi tasa hannu ta riƙe hannun Salma ta ce.

"Kuka kuma?. Shin kin mance da abunda Doctor ya ce maki ne?. Idan kika zo kika kashe kanki mune da asara bashi bafa Salma"

Girgiza kai Salma tayi tana cewa.

"Na rantse da Allah Aunty Ummi ko yanzu bana ganin laifinsa, zuciyata taƙi ta bashi laifi, ina sonshi ina ƙaunar Mlm Jamilu, ji nake duk irin ƙunci da azabar da zan shiga ni dai zan auresa, ni dai burina kawai na auri Mlm Jamilu, koda ace ranar auren bayan an daura ne Allah ya ɗauki rayuwata Aunty Ummi"

"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un. Salma kanki ɗaya kuwa, shin ko dai asiri Mlm Jamilu yayi maki ne?, yo wani irin so ne wannan haka kike ma Mlm Jamilu?, zai fara zama hauka fa Salma ki shiga hankalinki fa, ki dawo cikin hayyacinki fa, ki daina ganin ina biye maki Salma zan je kawai na sanar dasu Baba, su zasu iya maki magana ki ji, tunda ni kinga ina gaya maki gaskiya baki ji"

"Wallahi Allah Aunty Ummi ba haka bane, babu abunda yayi min, kawai sonshi nake daga Allah shine ya saka min, kuma nasan jarabawa ce ta Allah"

"To ki mance dashi, sana zan ɗauki waya na kira shi na sanar dashi halin da kike ciki"

"A'a A'a Aunty Ummi bana so yasan irin halin da nake ciki dan Allah karki kirasa"

"To ki ciresa a ranki mana, tunda har baki so yasan kina so ki kashe kanki akansa. Miye kike yi haka wai Salma akan Namiji?, ban taɓa tunanin hakan daga gareki ba haba Salma, shi yasa fa ni ban cika saka lamarin soyayya ba a raina, shi yasa gani nan babu abunda ke hanani bacci"

Sauke lumfashi mai zafi Salma tayi ta koma a hankali ta kwanta tana share hawayen dake zubo mata tana jin jikinta a sanyaye. Lamarin Jamilu na ƙara sakata cikin mamaki da sanyar mata da gwaiwa sosai, amma duk da hakan ji take koma wane ƙalubale ne zata iya juresa indai zata sami Jamilu a matsayin Miji.

"Dan Allah Salma ki kwantar da hankalinki indai Mlm Jamilu ne zaki same shi da yardar Allah ki dage da addu'a dai kawai"

Ummi ta faɗa danta lura idan ta ce mata bazata samu Jamilu ba ko ta rinƙa faɗa mata gaskiyar Jamilu baya sonta da gaske, shike ƙara sakata cikin damuwa mai tsananin gaske, ta fahimci dai ko ƙarya ce indai zata samu Jamilu ne kana yabonsa da kalami masu daɗi shi tafi so.

Yanzu ma sai taga ta ɗaga kai tana ɗan murmushi haɗe da amsawa da kai.

Girgiza kai kawai Ummi tayi tana kallon Salmar cike da tausayinta.

Allah Sarki Salma, da ace Jamilu zaiga irin sonshi da kike yi, da irin yadda kika damu dashi haka, da irin yadda kike masa uzuri baki bari a zage shi ko kushesa, wallahi da bai wantafar dake haka ba.

Ummi ta faɗa a cikin ranta cike da tsananin tausayin ƴar uwar tata......

PAGE 46

*SADIYA POV*

Kallonta Inna tayi tana sake duban Umar da yayi kicin-kicin da fuska zatai magana ya rigata cewa.

"Wallahi Inna kiyi mata gargaɗi, daga zuwa gari bazai yiwu kawai daga fitarta na haɗu da ita da wani ƙato ya tareta a hanya ba, kuma wai da yake ita bata da hankali da tunani ta tsaya dashi, ko ubanmi yake ce mata?"

"Ni fa Ya Umar ba wani abu ya ce min bafa"

"Dalla rufe min baki kona bigesa har sai yayi jini"

Ai da sauri Sadiya tasa hannu tana rufe bakin nata ido waje.

Inna ta sauke ajiyar zuciya ta ce.

"Sadiya kinga ko karatu fa zakiyi, dan haka tsayawa da samari bama naki bane. Bari na fito miki a mutum Sadiya mun riga da munyi maki miji auren kawai ya rage idan lokaci yayi za'a yi sa, dan haka ki kiyaye"

Turo baki Sadiya tana kallon Inna ta ce.

"To ni Inna soyayya kin san ba yinta nake ba, banma taɓa son kowa ba ni kin sani, yanzu ma fa tsaida ni da yayi tabbaya ta fa yake yi, ko nasan wani waje a unguwar nan, shine nima na ce masa baƙuwa ce nima a unguwar"

Inna najin lokacin da Umar ya saki ajiyar zuciya. Ta saki murmurshi kaɗan dan tasan kishi ne yau ya motsa, a haka kuma yake cewa wai baya son auren.

"Shikenan tashi ki bamu waje"

Tashi tayi simi-simi ta shige bedroom ɗin daya kasance tana da Inna, tana sake turo baki tana ma Umar wani kallo, a zuci take faɗin.

Ɗan takura kawai. Kai Shikenan baka da damar yin wani abu sai yayi magana akai?, nifa shi yasa dawowa birnin nan ba wani yimin yayi ba, ace kullum kana gida tunda muka dawo sau ɗaya na fita yau shima ake ne nan baya Inna tamin, gaskiya na fara gajiya da zama waje ɗaya haba.

Ta ƙare maganar zucin haɗe da sakin tsaki kaɗan.

Inna dake can parlo da Umar da ta murmusa ta ce.

"Umar wai ko dai kishin ne ya motsa?"

Ta faɗa cike da zolaya.

Ai sai ya wani waske yana cewa.

"Haba Inna akan wannan abar zanyi kishin?. Kawai dai Inna bai kamata ace da aure na a kanta ba a rinƙa barinta tana yin duk abunda taga dama ba, ya kamata a ɗan rinƙa nuna mata"

"Ikon Allah Umar da tun a can Karaɗuwar bakai duk wannan tsirfe-tsirfen ba sai da aka zo nan?"

Sosa ƙeya yayi yana murmurshi kaɗan. Yama za'ai ya bari ta rinƙa abubuwa kamar suna a can. Nan dai birni ne kuma cike yake da samari masu kyau da naira ga masu rashin ji masu hure ma ƴaƴan mutane kunne ai bazai taɓa bari ba.

"Inna ba haka bane, dole a nan akwai banbanci, idan samarin can ƙauye basu hure mata kunne ba, to nan fa Inna akwai shaiɗanun da zasu iya. Shi yasa Inna kawai idan ta fara school ɗin nan zan rinƙa ɗakkota ina kaita"

"Ai Umar bazata kai ga haka bama, insha Allah tana fara karatun nan da kaɗan zan taraku har ita a sanar da ita duk abunda ke faruwa da rayuwarta, ina ganin hakan sai yafi, dan nima hankalina sai yafi kwanciya wallahi"

Shima Umar ɗin yaji daɗin maganar da Inna ta ce masa, to amma fargaba ɗaya ce yake yi akan Sadiyar, wajan sanar da ita ɗin, yaya zata ɗauki maganar?, bama wannan ba yaya zata ɗauki cewar su ɗin ba danginta bane?, basu haɗa komai da ita ba.

*SALMA POV*

A hankali ta miƙe tana sakkowa daga gadon.

Dare ne sosai tunda aka sallamota a asibiti ta fara sallar dare babu dare babu rana. Yau kusan sati biyu da sallamota kullum addu'arta kenan Allah ya juya da hankalin Jamilu gare ta, amma gani take kamar abun ba wani ci gaba (Ɗan Adam da gaggawa).

Kuma ta hana kanta kiransa da duk wani makusantan ta.

Sunyi waya da Habiba bata dai sanar mata da komai ba.

Yusura ma ta kira ta a ruɗe dan Baba ya sanar da Aunty Murja ta kira ta tana mata sannu ba laifi a sake, Yusura ma ta amsa suka gaisa har tana janta da firar Jamilu, kuma dama abunda take so kenan duk duniya a rinƙa firar Mlm Jamilu har wani daɗi take ji har cikin ranta.

Alwala tayo ta shinfiɗa sallaya ta zo ta fara sallah, tayi raka'a huɗu da kyar saboda yadda zuciyarta ke yin saurin bugawa kamar wacce tayi gudun tsire.

Sallamewa tayi tana ɗaga hannuwanta sama kuka take sosai da hawaye tana ma Allah kirari, duk cikin addu'o'nta mafi yawa ta Mlm Jamilu ce, Ubangiji ya karkato mata da hankalinsa gareta, haɗe da rokon Allah ya bata shi a matsayin miji.

Kuka da take ne wani ɗan tari ya sarƙe ta, a hankali tasa hannunta tana toshe bakinta dan kar ta tayar da Ummi dake kwance.

Sai dai Ummi duk tana jinta.

Tarin data ji ne kaɗan yasa Ummi tashi hankali a ɗan tashe dan tasan ba wata lafiya ce ta ishi Salmar ba, gashi duk ta rame ta ƙare kowa ya kalleta cewa yake ta rame sosai.

Ummi ta tashi tsaye tana haska fitilar wayarta ta dubi Salma ta ce.

"Kukan ya isa haka Salma dan Allah, baki da cikakkiyar lafiya fa kin sani. Naga alamar ke lafiyar taki ma baki damu da ita ba, ta Jamilu kawai kike, mutunan da bai ma damu dake ba, yanzu haka idan aka ce ya mance dake a cikin rayuwarsa ba'a gaddama wallahi. Ke nifa tsakani da Allah Salma kin fara bani haushi fa"

Maganganun da Ummi ta faɗa ne

23 / 36