Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   10 / 36

27K to 30K   out of 106.4K words

hannunta ganin har takwas da rabi yasa Salma yin tsaki tana ƙara tare wata data zo wucewa amma bata tsaya ba.

A hankali ta dafe kanta tana cewa a fili.

"Wayyo Allah, ya rabb kasa na samu abun hawan nan yanzu ka taimake ni"

Ta faɗa kamar zatai kuka.

Zata ƙara tare wata napep ɗin taga wata Mota kamar ta santa ta ɗan dawo baya, bayan ta wuce ta kaɗan.

Tsayawa tayi saitin da take, Salma na ɗan mamaki sai taga an zage gilas ɗin Motar.

Murmushi ta saki tana kallon na cikin Motar ta gaida shi a takaice sai ya ce.

"Ki shigo ciki sai kiji daɗin gaida ni ɗin ai ko?"

Girgirza kai tayi da sauri ta ce.

"A'a Doctor wallahi na gode ba sai na wahalar da kai ba"

"No ba wani wahala a nan, kawai ki shigo na sauke ki, kinga time na ƙara tafiya karki makara"

A hankali ta a sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya tana zagayawa ta gefensa ta buɗe murfin Motar ta shiga, tana jin idonun jama'ar dake wajan na yawo a kanta bata damu ba ta rufe murfin Motar bayan ta shiga.

Wani sanyin Ac ne kamar dai shigarta ta farko taji ya ratsa mata jiki ga ƙamshin daɗin data taɓa jinsa a cikin Motar mai kwantar da hankalin mai shaƙarsa.

"Mlm Salma!"

Ɗan kallonsa tayi tana murmushi kaɗan ta ɗan gyara zamanta duk da jinta take a takure ta ce.

"Ina kwana fatan kana lafiya?"

"Alhamdullah Salma. Ni koma sunan nawa ba'a sani ba ko?"

Murmushi ta sakar masa tana ɗan kallon titi.

"To sunana Nura"

"Uhm Masha Allah"

Kawai Salma ta ce.

"Sai jiya na zo aka ce min baki nan, wai baki kwana a gida ba, amma dai ban yarda ba gaskiya"

"Uhm hakane jiya Aunty Murja ta ce ka zo ka kawo min magungunan dana mance dasu ranar daka kawo ni gida, nagode sosai fa"

"Ba komai ai"

Daga nan kowa yayi shiru. Sai shi daya ji shirun yayi yawa ya ce.

"School of hygiene kike yi night?"

"Yeah ita ce"

"Masha Allah. Amma wane department kike"

"Environmental health"

"Wow Masha Allah abu ne mai kyau. Kune ƴan duba gari ba naji ana faɗa?"

Dariya ce ta kama Salma dan yadda ya faɗi maganar cike da jan faɗa da tsokana.

Shima murmushi ya saki mai haɗe da dariya ya ce.

"Yes koba haka bane?"

"Hakane amma ai kasan a environmental aka ɗibi wasu department ɗin ko?, ko public health a cikin environment aka fitar dashi, but environmental abu ne mai kyau ai"

"Yeah yeah abu ne mai kyau gaskiya. Ashe kina surutu haka?, ko dan na taɓa abunda kike karanta shi yasa baki ya buɗe sosai haka?"

Murmushi ta saki kawai tana girgirza kanta.

Basu daɗe ba suka isa har bakin ƙofar shiga hygiene ɗin ya tsayar da Motar.

Yawanci ɗalibai ne keta shigewa cikin school ɗin wasu kuma na ɗan fitowa daga waje suna sayan wasu abubuwa da ake saidawa a wajen makarantar.

Tunda Motar ta tsaya wasu ke binta da kallo hatta masu gadin Get ɗin makarantar ma sai da Motar ta ɗauki hankalinsu.

Ɗaukar Jakarta Salma tayi dake akan cinyarta tana masa godiya zata buɗe ƙofar Motar ta fita taji ya ce.

"Ƙarfe nawa kuke tashi ne?"

"No karka damu mu ko wanne lokaci ma muna iya kaiwa"

"Hmm baki so dai na dawo na ce zan maida ke gida ko?"

"A'a wallahi ba haka bane Doctor"

"To amma ai kin san unguwar ku da tamu ba nisa night?"

"Yeah hakane"

"To danna rage miki hanya banyi laifi ba"

"Eh Doctor duk da haka dai bazai yiwu na rinƙa saka wahala ba, idan an tashi kawai zan tare napep na koma gida karka damu"

"Uhum ai shikenan. Amma muyi ɗan wani alƙawari dake mana"

Ɗan kallonsa tayi tana jinjina kai ya ce.

"Idan har na ganki da safe zaki tafi school ni ne wadda zan rinƙa kawo ki, kin yarda?"

Shiru tayi na ƴan wasu lokuta, ganin tayi shiru da yawa ta time nata tafiya yasa ya ce.

"Mlm Salma kinyi shiru?"

"Shikenan na gode"

"Kin amince kenan ba?"

Ɗaga kanta kawai tayi tana murmushi.

Miƙa mata wasu kuɗi yayi. Ai sai Salma ta saki baki tana girgirza kai da sauri ta ɓalle murfin Motar ta fita.

Tana jinsa yana kiran sunanta ko waigowa bata yi ba.

Murmushi ya saki haka kawai sai yaji ta ƙara birgesa. Amma mi yasa matar nan ke mata shaidar wacce ba nitsatstsa ba?.

Ya tabbayi kansa, yana kallonta harta shige cikin school kamin ya ɗaga kafaɗarsa yana murmurshi ya tayar da motar yayi gaba.

Tunda Salma ta fito daga Motar taga yadda idanuwan Mutane ke yawo a kanta.

Shi yasa da sauri ta idasa shiga cikin makarantar.

Tunda ta shigo take baza ido ta inda zata hango wani ɗan department ɗin nasu, amma ganin babu a tsakiyar school ɗin yasa tasan yanzu suna class ana lecture, dan tasan Mlm Jamilu sai goma na safe zai fito daga lecture ɗin tasa.

Jiki a sanyaye ta nufi class ɗin da suke lecture ɗin tashi.

Tana zuwa ƙofar class ɗin taja ta tsaya tana jin gabanta na faɗuwa sosai ganin ita ce kaɗai a waje ga ajin ya cika maƙil da mutane.

Ta window ɗin ajin ta hangi Habiba ƙawarta wacce suke mutumci da ita duk makarantar ita ce kaɗai sukai sabo da ita.

A hankali Habiba dake ciki ta ɗaga mata hannu tana mata alama da hannu akan ta shigo babu abunda zai faru.

Gaban Salma ne ya ƙara faɗuwa ta ɗage kafaɗarta alamar wallahi bazata iya shiga ba.

Dan ita wallahi a hakama da take hangosa tsoronsa ƙara shigarta yake, bare ace ta nufi ajin ita ɗaya, dama ace suna da yawa sai su shiga a tare.

Tana nan tsaye tana saƙa da warwara ta ƙara ɗaga kanta sai taga Habiba na nuno mata wata farar takarda alamar atandas yake ɗauka kuma kowacce nata take rubutawa ta miƙa masa.

Ai sai Salma taji ƴan cikinta na kuka, ita yanzu yaya zata yi ne ma?.

Nuno mata wata takarda tayi alamar wai zata gwada yi mata.

Addu'a ta farayi Allah yasa kar a samu matsala.

Har sun fara murna ganin yadda mutane ke zuwa suna kaiwa harda na kusa da kai zaka iya amsa ka kai, yasa Habiba yima Salma ta kai takardar a tare, wani ɗalibi na amsa dage gefen Mlm Jamilu shi kuma yana ta danna wayarsa a zaune akan wata kujera.

Kowa na gama kowa tasa suka ji Mlm Jamilu ya bada umarnin a fara kiran sunayen takardar kowanne aka kira ya zai amsa sana ya fita waje, kuma yana kallon kowanne ɗaya bayan ɗaya aka fara fita ana kiran sunaye.

Sosai gaban Habiba ya faɗi ganin mutane da yawa ba'a gansu ba, wato dai wasu da yawa ba ita kaɗai bace tayi ma wasu atandas ɗin ba.

Sauƙin su ɗaya ba'a gane wadda yayi maka.

Amma dai sunga yadda shi da kansa ya riƙe takardun masu sunayen da ba'a gani ba.

Habiba na fita waje ta kamo Salma suka nufi wani waje suka zauna..........

PAGE 20

"Habiba ya zanyi?. Gashi kinsa sunana ya kuma riƙe takardun fa"

Lumfashi mai zafi Habiba ta sauke tana cewa.

"Bafa abunda zai faru, kawai nasan zai yaga takardun ne"

"Amma ai kin san zai bani kari Over ko?"

"Tabbas da wuya ki tsallake exam's ɗin shi, amma dai ai akwai Allah kiyi ta addu'a shine kawai"

Sosai fuskar Salma ta nuna damuwa akanta kamar zata saki kuka, Habiba ta saki murmushin gefen baki tana dafa kafaɗarta ta ce.

"Haba sisi nah, miye na damuwar wai?, insha Allah zamu tsalla ke ne karki damu"

"Tom Allah yasa. Ai mun kusa fara exam's ɗin ko?"

Tashi Habiba tayi tana kallon wani waje ta ce.

"Eh naji ana cewa nan da wata ɗaya ko ɗaya da rabi haka dai. Tashi muje muci abinci dan yinwa nake ji ni"

Tashi Salma tayi tana cewa.

"Nima banci komai ba na taho fa, sai gashi ma duk saurin nawa saida na makara"

"Ai dama nasan zaki makara ne wannan gidan naku ana sane ma za'a makarar dake ɗin ai"

"Hmm ke dai bari ai ni na fara gajiya da Kano, so kawai nake ayi hutu na koma Rimaye wallahi na gaji kwata-kwata Kano bata min daɗi"

"Hhh kefa baki jin kunyar kushe Kano a gaba na, insha Allah a nan zaki yi aure munga ta tsiya a wajanki"

"Ai Habiba idan aure nayi ai da sauƙi, nawa gidan ne babu wanda ya isa ya zo ya ce zai wulaƙanta ni"

"Kware kuwa haka ne"

Habiba ta ƙare maganar dai-dai sun iso wajan da ake saida abinci kala-kala gashi nan, da yake an gyara school ɗin harda wajan zama aci abinci da runfa mai kyau ga kujeru masu kyau.

Zama su kai Habiba ta aje jakarta tana niyyar zuwa domin sayo abincin taji Salma ta ce.

"Ina kuma zaki je ne?"

"Wai wainar fulawa zan sayo mana"

"A'a zauna na taho mana da ƙosai zai ishe mu, sai dai ko ki sayo mana ruwa da kunun aya kawai"

"Okay tom bari naje na sayo"

"Ga kuɗin nawa"

Ta miƙa mata ɗari biyar.

"A'a wallahi akwai kuɗi a hannu na ki barshi zai isa"

"Amma....

Kamin ma ta ƙare maganar Habiba tayi gaba tana murmushi.

Bata daɗe ba ta dawo masu da ruwa da kunun ayar ta aje masu akan table ɗin dake gabansu tana cewa.

"Idan banda abunki kawai saina amshi kuɗinki?. Sau nawa kina biya min irin wannan"

Salma dai murmushi kawai tayi tana kwance ledar da ƙosan ke ciki, dandanan ƙamshinsa ya rufe wajan, da zafinsa har lokacin.

Da murmushi Habiba tasa hannunta tana ɗaukar ɗaya tasa a baki tana faɗin.

"Uhmm amma yayi daɗi sosai wallahi, da alamar ke ce kika yisa ko?"

Ɗaga kanta kawai Salma tayi bayan tasa ɗaya a baki itama.

Sai da suga kama cin abincin gaba ɗaya suna shan kunun ayar daya rage Habiba ta ce.

"Wallahi Salma Mlm Jamilu da gaske kowa na tsoron wannan bawan Allahn"

Taɓe baki Salma tayi tana wata addu'a a zuciyarta kamin ta ce.

"Nifa haushi yake bani ma wallahi"

"Hhhh lallai ai bake kaɗai yake bawa haushin ba yarinya. Abu ɗaya yake ɓata min rai dashi shine izza da isar daya fi nunawa, koda yake a jininsa take, dan ko yana tafiya kamar baya so haka yake yinta, ke yadda kika san ɗan Sarki wallahi jinin sarauta"

"Uhum na gani kam ai, yaji dashi dai"

"Ke ni kasan mima nake tunani?"

"Sai kin faɗa"

Salma ta faɗa dai-dai lokacin da suka miƙe a tare suna ɗaukar kayan su, suka bar wajan suna tafiya a hankali ta ce.

"Nifa tunani yau mu tafi gida da wuri, domin wallahi yau har shidda fa zamu kai, gashi ana wahalar abun hawa idan har yamma tayi, hakafa wancan satin da baki zo ba ranar Monday wallahi sai dare na isa gida"

"To ya zamuyi Habiba?, sune Malaman basu kyautawa ace lectures harta ƙarfe shidda?"

"Wallahi nima tana bani haushi, haka fa ranar Friday ma muke kaiwa shidda ɗin nan. Gara ma ke gadon ƙaya baku wahalar napep, amma ni da nake can zoo road hmm wallahi muna wahalar napep ko da safe ne wajan zuwa"

"Wallahi Habiba muna yi, ke dai kawai Allah ya kyauta, ni abunda nake iskewa ma gida idan na koma shine yake ƙara dagula min lissafi, bare ace idan nayi dare na kai yamma hmm"

Dafata Habiba tayi ta ce.

"Kin taɓa gaya min Salma, amma ai Allah yasan ba yawan iskanci kike yi ba, kuma kema kisan ba abu marar kyau kike yi ba, dan wata can ta ce miki haka ai kar ya dame ki kinji?"

Girgiza kai Salma tayi. Habiba bazata gane yadda zuciyarta ke mata zafi ba idan har Aunty Murja ta fara jinfanta da kalamominta masu zafi da taɓa zuciyar wadda ake ma su ba.

Zatai magana suka ga wasu ƴan mata sun wani rugo da gudu suna rungume juna ana shewa haɗe da canza harshe, suna turanci na zallar iyayi irin anyi farin cikin ganin junan nan.

Taɓe baki sukai kusan a tare Habiba na nuna ma Salma su tana cewa.

"Wai kin san duk dan waye suke wannan haukan da rashin hankali?"

"Can su suka sani, kawai dai ni irin wa'innan mamaki suke bani ma, yanzu dan Allah miye abun birgewa a abunda sukai?"

"Su ja hankalin mutane mana. Kuma ga dan wadda suke yi nan a zaune"

Ɗagowa Salma tayi tana kallon inda Habiba ta nuna, ai ko sai akai sa'a shima ya ɗan ɗago a lokacin suka haɗa ido da Salma, wata wawar bugawar zuciya ce ta samu Salma har jinin jikinta na gudu sosai, wata irin ajiyar zuciya ta sauke bayan ta sadda kanta ƙasa jikinta taji na rawa kaɗan ta kamo hannun Habiba da sauri suka bar wajan.

"Wallahi Salma danshi suke wannan haukan. Kin san fa ƴan Matan school ɗin nan dama na waje suna haukan son wannan bawan Allahn, gashi dai ba wani kyan azo a gani yake dashi ba, amma ka rasa uwar da suke gani a jikinsa suke manne masa haka?. Koda yake ko kallonsu ma baiyi ba, bare yasan iskar data kwaso su, yama za'ai ya kalle sun yana ji da izzar nan tashi?"

Salma najin Habiba har suka koma class ɗin da zasu shiga lecture ɗin ƙarfe goma zuwa sha biyu, dan har sha ɗaya ma ta kusa Malamin bai shigo ba, ƴan department ɗin duk sun dawo class ɗin ana jiran shigowarsa.

Samin kujera sukai suka zauna ɗan baya kaɗan ganin basu dawo da wuri ba gashi duk an zaune kujerun na farko-farkon.

"Bana son zama a ƙarshen nan saboda ba'a wani ji sosai ko ganin abunda ake rubutawa a allo ba'a yi sosai"

Salma ta faɗa tana son kauda maganar da Habiba ta isheta da ita.

"Wai ina baki labarin Mlm Jamilu da ƴan mata ke mahaukacin so, kin wani banza dani"

"To suje suyi tayi mana Habiba, su suka ji zasu iya ne. Idan banda abunsu yaje ya aje Matar a gida amma su wani zo suna hauka akansa?. Mutunen da kin kallesa kin san ya fara tsufa hutun da yake ciki ne baya nuna hakan, ai ke da kin kallesa kin san ya aje ƴaƴa manya irinmu wallahi. Kuma daɗi na dashi ɗaya baya kallon kowacce shegiya duk iyayinta da feleƙenta, ko yanzu ɗin na lura ko iskar data kwaso su bai kalla ba bare su"

"Ahh kware kuwa yana da ƴaƴa manya, ni nama san ɗansa namiji Fu'at da wata ƴarsa Hanan wallahi. Kinga Hanan ɗin nan dan taga ubanta mai kuɗi ne karki so ganin yadda take rayuwar ƙarya da kuma zuwa social media kamar su tik tok tana posting videos ɗinta, aje nan aje can, karki so kiga ƙaton gidansu. Garama shi Fu'at ɗin miskili ne kamar dai babansa. Kuma wallahi Salma matarshi ɗaya"

Tunda Habiba ta fara bada labarin Salma taji jikinta na yin sanyi haka kawai bata san dalili ba.

"Hmm to duk ke a ina kika san su ma wai?"

"Ahh yo zasu ɓoya ne?"

"Ai nake ganin basa kawo ƴaƴansu school ɗin da suke koyawa ko aiki a cikinta, sai suje can wata uwa duniya su samar masu Makaranta"

"Eh hakane, duk cikin ƴaƴansa gaskiya babu wadda ya taɓa yin Makarantar nan, amma Hanan kamar ma a Katsina tayi tata school ɗin, dan a lokacin da Aunty Ummi sukai graduation suma naga tana posting a TikTok sunyi kuma naga sunan school ɗin a Katsina take. Shi kuma ɗansa a ƙasar waje India a can yayo nashi karatun, duk da dai nasan akwai wasu yaran nasa da ban sani ba"

"Ohh Katsina hmm?"

"Eh a garinku"

Habiba ta faɗa tana dariya.

"Ai kin san dama Katsina gaskiya tafi kyan makarantu, Katsina anfi tsayawa aba boko fahimmanci sosai, dan gaskiya mu a can irin Makaranta nan sosai suke kada yara idan basa maida hankali, kinga da ace a can ne muke karatun nan a department an ɗauki kamar mutum ɗari biyar haka, to babu lallai mutum ɗari su haye"

Riƙe baki Habiba tayi ta ce.

"Wai da gaske haka suke zubar da yaran mutane?"

"Kware kuwa ai gara kije kiyi NCE da ace kiyi irin wannan Makaranta ta karatun kiwan lafiya a Katsina. Nasan shi yasa kawai ya kaita"

"To ke mi yasa kika tsalle taku kika zo nan?"

"Haba Habiba, shifa karatu sa'a ne, idan har kana da ƙwaƙwalwa to ko ina kaje za'a dama da kaine, ni bana jin duk inda zani yo karatu kin ganni nan, kawai duk inda ka tsinci kanka ka maida hankali shine kawai, kuma harda ƙaddara ma ke sawa kaje koma ina ne da kuma rabon zaka haɗu da wasu Mutanen, kema harda rabon zamu haɗu dake"

Salma ta faɗa tana dungure mata kai tana murmushi.

Itama murmushi ta saki tana cewa.

"Kuma fa haka ne ko miye ya same ka dama can rubutacce ne a littafinka na ƙaddarar da dole saita faru da kai a cikin rayuwarka...........

PAGE 21

*UMMI POV*

Ta sauke numfashi yafi a ƙirga tana ɗukar da kanta ƙasa saboda gajiyar da tayi a Mota.

Tana tsaye ne a ƙofar wani babban gida tana kwankwasawa.

Tsaki tayi a fili tana ƙara jin haushin zuwanta wannan ƙuntattacen gidan.

Wayarta ta jawo tana tuna sai fa an kira su kamin azo a buɗe maka gidan.

Number ɗin Aunty Binta ta kira sai data kira ya kai sau biyu bata ɗauka ba, zata sake na uku ne wata zuciyarta ta ce mata ta kira Mama.

Mama ta kira bugu ɗaya Mama ta ɗauka.

"Hello Ummi harkin isa ne?"

"Eh Mama yanzu na iso ƙofar gidan Aunty Bintar, amma na kira wayar ta bata ɗauka ba, ko zaki kira min ita please"

"To bari na kira ta ƙila bata kusa ne"

Ummi sai bata ƙara magana ba ta yanke wayar dan kowa ma yanzu haushi yake bata ita.

Minti kaɗan taji an buɗe gidan an buɗe ƙofar, Aunty Binta ce ta buɗe riƙe da wata baby girl a hannunta

10 / 36