Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   13 / 36

36K to 39K   out of 106.4K words

da za'asha shayi"

Da to kawai ta amsa tana miƙewa tsaye, miƙewar da zatai kawai taji kanta ya sara mata sosai, ɗan dafe kan tayi tana jan lumfashi.

Kitchen ɗin ta nufa bayan ta ɗakko wani gyalenta ta yafa.

Kamar yadda ta ce ruwan zafi biyu ta haɗa, ruwan shayin ta haɗa duk abunda ake so, sai tashin ƙamshi yake.

Komawa tayi ɗakin saita iske ta tana cire ma Anam ɗin kaya, wasu kaya a gefenta tasan ana mata wankan za'a saka mata su.

Yarinyar a yanzu sai wasanta take kamar ba ita ce jiya take masu ihun kuka ba.

"Kula da ita ina zuwa"

Cewar Aunty Binta tana ƙare maganar ta fice zuwa kitchen ɗin.

Ummi na lura da Anam ɗin dake da kazar-kazar, dan irin yaran nan ne sai ana kula dasu, da ace babu kowa ma da sai ta faɗo daga kan gadon.

Ganin ta kusa kaiwa bakin gadon yasa Ummi saka hannu ta maido da ita tsakiyar gadon.

Tana jin motsin Aunty Binta tayi can tayi nan.

Jin ta shiga ɗakin Uncle Abdul ta ɗan jima a ciki kamin ta aji ƙarar buɗe ƙofa ta fito.

Ta ƙara buɗe wani toilet dake jikin tsakiyar dakunan guda biyu, dama kuma gidan toilet a wadace yake kusan toilet uku ne a gidan.

Wata robar wankan Anam ta ɗakko ta wucewa kitchen ɗin ta haɗo ruwan wankan Anam ɗin tayo ɗakin dashi.

Tana zuwa ta dubi Ummi bayan ta ɗauki Anam ɗin ta ce.

"Kije ga biredi can akan darning table ki ɗauka naki ne, tunda dama baki shan shayi ke"

Ɗaga kanta kawai Ummi tayi tana miƙewa tana jin kwata-kwata babu daɗi gidan, saboda kwata-kwata Aunty Binta har lokaci babu sakin fuska bare murmushi, shi yasa kwata-kwata Ummi ta ƙara jin a takure ma take a gidan.

Ganin ta fito parlo, kuma parlon kaca-kaca dashi, can filo can an zubar da toshu.

Sauke ajiyar zuciya tayi tana riƙe ƙugunta, dan tasan duk wannan ub*an aikin na gyaran parlon ita ce zata yi shi, idan ma batai ba ta bani ta shiga uku, dan idan Aunty Bintar ta fara murtuƙe-murtuƙe har Mama dake can Rimaye sai an kirata an gaya mata cewar bata yin komai ta zo ne kawai daga ta ci saita kwanta ta sani, domin ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba ana mata hakan, dan akwai ranar da suka zo da Salma, daga Salma na karatun exam's bata aikin gidan sosai amma dai tana yi, shine tana school aka kira Mama a waya aka gaya mata ƙarya da gaskiya, lokacin Ummi ma na zuwa school ɗin, suna cikin Makaranta Mama ta kira sai bala'i take danmi za'a ce Salma ta zauna bata taya su aikin komai sai ta bar Ummi da aiki kawai da kuma ita Aunty Bintar?.

A ranar sosai Salma tayi kuka kamar mi, bata wuce sati biyu ba tana gama exam's ɗin ta kwashe kayanta ta koma Rimaye, ai ko Ummi ma ta ce wallahi tafiya zatai itama, a tare suka koma gida, suna komawa kuma Mama ta dasa da mita, wai idan sun dawo nan ɗin uwar mi zasuyi?, ga cikin birni can inda zasu zauna ko sun sami mijin aure a can.

Katse tunanin tayi kawai ta shiga share parlon, sai da ta share shi tsaf kamin ta haɗa ruwa da abun ƙamshi ciki ta zo da moper ta fara goge ƙasan tayis ɗin.

Sosai bayanta taji ya amsa a lokacin data gama goge ub*an parlon.

Goge darning table tayi da wani tsumma ta gyarasa sosai kamin taje wajan Tv itama ta goge ta da sauran kayan kallon.

Sai ta koma kitchen shima ta share ta gogesa.

Parlo ta ƙara dawowa ta shiga fesa masa turaren ɗaki ko ina sai yayi kyau gwanin sha'awa.

Zata juya ta koma kitchen ɗin taji muryar Aunty Binta ta a fito.

Bin parlon tayi da kallo, sai Ummi taga ta ɗan saki fuska ganin an gyara mata parlo yayi kyau.

"Sannu da aiki. Dan Allah ɗan goya min Anam nasan bacci zatai, naje na haɗa ma Abbinta abunda zai karya kamin ya wuce wajan aiki"

Ummi bata ce komai ba tasa hannu ta amshi Anam da zanin gayon, Aunty Binta ta taimaka mata ta goya Anam ɗin.

Juyawa tayi ta shige ɗakin nasu tabar Ummi sake da baki.

"Ohhh yanzu duk aikin nan da nayi har sai an haɗa da bani yarinya goyo?"

Ummi ta faɗa ranta a mugun ɓace.

Bayanta ne sosai taji yana mata ciwo, gashi dama Anam ɗin irin yaran nan ne masu ƙiba sosai haka take.

Kitchen ta koma tana ɗakko wata chocolate a firiza wacce zata haɗa taci biredin da ita.

Biredin data gani akan darning table ta ɗauka tana komawa ɗaki.

Ajesa tayi akan gado tana shiga toilet ta wanke bakinta kamin ta fito ta ɗan zauna jin Anam ɗin tuni tayi bacci a bayanta.........

PAGE 25

*House No 11, Sheka Titin Ƴar Kasuwa, Kano state Nigeria*

"Ki ɗora min abinci da wuri naji kin ce zaki je gidansu Maryam"

"Eh Aunty Binta da yanzu ma nake shiri wallahi, ina so ne naje na yini"

"Hmm yayi kyau ki tabbatar dai kin ɗora min abincin zan idasa kawai"

Ta faɗa tana taɓe baki ta juya ta ɗauke Anam dake akan cinyar Ummi ɗin.

Taɓe baki itama Ummi tayi tana bin bayanta da hararara a fili ta ce.

"Ƴar baƙin ciki, duk abunda zaki yi dai sai naje indai gidan su Maryam ne wallahi baki isa kin raba mu ba"

Ta faɗa tana miƙewa tsaye dan dama da shirinta ta isketa tayi wanka tana zaune ne tana danna waya, dama tunda safe ta sanar da ita zuwan da zatai gidansu Maryam ɗin dake Sheka titin aci lafiya.

Ba wani nisa ne daga gidan Aunty Bintar ba dan naira ɗari kawai take biya akai ta zuwa gidansu Maryam ɗin.

Kitchen ta nufa tana ganin Aunty Binta a parlo ta wuce ko kallonta Aunty Binta batai ba, dan Ummi ɗin duk tana lura da ita sai wani cika take tana batsewa, kuma tasan duk akan zuwan da zatai gidansu Maryam ne.

Bata damu ba dan idan da sabo ta saba.

Kamar yadda ta gaya mata za'ai shinkafa dafaduka da kayan lambu a cikinta da kuma kaza daban da za'a soya sai ƴar miya da za'ai ta jajjage asa kazar a ciki, sai latas da za'a yanka daban shima.

Aikin ta fara rage mata ta ɗora komai ta fito bayan ta yanka mata har latas ɗin ta koma ɗakin, bata isketa parlon ba sai ta iske ta a ɗakin.

"Yawwa Aunty na ɗora ni zan tafi yanzu"

"Yayi kyau Allah ya tsare"

Ta faɗa tana sakama Anam nono da take bata.

Ummi bata ƙara magana ba ta saka mayafinta da yake Abaya ta saka baƙa irin ƴar dubai ɗin nan, sosai kuma Abayar tayi mata kyau.

Jakarta ta ɗauka tasa wayarta ta a sagala ta fice daga gidan.

Tana fita rana ta haske mata fuska rana ake sosai, tana tafiya a hankali harta isa bakin titi inda zata hau napep.

Tana tsaye ta fara tare napep wasu idan suka ji inda zata ji sai su girgirza kai, da alama basa son zuwa aci lafiyar.

Kwaɓe fuska tayi tana saka hannunta ta ƙare ranar data haske mata fuska.

"Ya rabb kasa na samu da wuri, ana rana wallahi"

Ummi ta faɗa a fili.

Ta ɗauki kusan minti ashirin a wajan kamin Allah ya kawo mata wata napep babu kowa a ciki tana tsaida shi ta gaya masa inda zai kaita ya ce ta shiga.

Kamin ta shiga ta ci.

"Nawa zaka kai ni ne?"

"Hajiya nawa kike biya?"

"Uhm naira ɗari nake biya"

"Haba Hajiya ɗari da hamsin ne fa"

"A'a gaskiya ɗari nake biya, ai ba yau na fara zuwa ba ko Mlm?"

"Shikenan zaki iya shigowa"

Shiga tayi tana sauke ajiyar zuciya a hankali.

Tafiya mai ƴar tazara ce ta kawosu aci lafiya dogon layi.

Ana zuwa dai-dai inda zata gangara ga gidan su Maryam ɗin nan tana ma hangensa.

Sauka tayi ta miƙa ma mai napep ɗin kuɗinsa, ta juya ta nufi gidansu Maryam.

Da sallama ta shiga.

Umman Maryam ta iske a tsakar gidan tana ɗaura alwalar sallar la'asar.

"A'a Ummi ce a gidan namu?"

Umma ta faɗa ɗauke da murmushi akan fuskarta.

Murmushi mai sauti Ummi ta saki tana kaiwa har ƙasa ta gaida Umman tana cewa.

"Wallahi kuwa Umma mune"

"Kai Masha Allah, anzo lafiya?. Ina ita Salma ɗin kika baro ta?"

"Wallahi Umma tana can gadon ƙaya"

"Ohh ke ce kaɗai a nan ɗin kenan?"

"Eh Umma"

"Tom Masha Allah. Ki shiga Maryam ɗin na nan bari na kira miki ita yanzu ta shiga ɗaki"

Umma ta faɗa tana nufar wani ɗaki.

Ita kuma Ummi ta shige parlon nasu.

Zama tayi akan kujerar parlon tana sauke lumfashi kaɗan ta aje jakarta dake rataye a hannunta.

Jim kaɗan sai ga Maryam ta shigo parlon.

Murmushi ta saki tana zama a kusa da Ummi ta ce.

"Wallahi na ɗauka ba yanzu ba zuwan naki?"

"A'a ai dama na ce miki da wuri zan zo ai Maryam"

"Ai kin san gidan Auntyn nan taki ne nasan zata iya tsaida ke, koma ta ce baki zuwa"

"Hmm ai wallahi bata isa ba, na barta dai sai baƙin ran data saba take"

"Allah dai ya yaye ma Aunty Binta abunda ke damunta, ni ban taɓa ganin ƴar uwa irinta ba. Gaskiya ni ba haka muke da Yaya Asiya ba"

Maryam ta faɗa tana tashi tsaye ta kira Iliham ƙanwarta tana miƙa mata kuɗi tana cewa.

"Jeki ki sayo min ruwan sanyi dan Allah kiyi sauri kuma"

Amsa yarinyar tayi tana fita.

"Ai ke daban ai Yaya Asiya ma daban, nifa tunda nake ban taɓa ganin mai hali irin na Aunty Binta ba. Ko dan ba'a hannun Mama ta girma ba, a hannun Kakarmu ta tashi, sai da Kakar tamu ta rasu ne ta dawo gidanmu da zama bata kuma daɗe ba akai auranta, wata ƙila dan bamuyi sabo bane"

"Wata ƙila to, amma dai ai abun nata yayi yawa ne"

"Haka fa take, yanzu kuna zaune ƙalau da ita kuna raha yanzu zaki iya ganin ta birkice miki tana murtuƙe maki fuska, abun nata sai ka ce mai shafar jinnu"

Dariya kawai Maryam tayi tana tashi ta fita jim kaɗan ta dawo da faranti samansa a rufe.

Ajewa tayi kusa da Ummi kamin Iliham ta dawo da ruwa a leda.

Shima aje mata akai.

"Please ki ci abinci bari nayo sallah"

"Nima bari na fara sallar"

"To bari nasa Iliham ta zuba miki ruwa a buta"

"No ina da alwala ta ma na fito"

"Okay to ga Hijabi nan da abun sallah"

Maryam ta faɗa tana nuna mata abun sallar dake shifiɗe a ƙasa da Hijabi akansa.

Amsa tayi da kai tana miƙewa ta saka Hijabin ta kabbara sallah.

Tana idarwa ta shafa addu'a ta tashi haɗe da cire Hijab ɗin ta ƙara komawa kan kujera.

Wayarta ta a ɗakko ta fara danne-danne har Maryam ɗin ta dawo ta same ta.

"Wai miye haka ne Ummi?, ki aje dan Allah ki ci abincin nan"

Dariya Ummi ta saki tana aje wayar ta ce.

"To muci tare mana?"

"A'a danke fa nayi sa"

Buɗe faranti tayi ganin gurasa ce, kuma taji kayan lambu irinsu albasa da tumatur, an turarata ga ub*an ƙuli tasha, da man gyaɗa sai ƙamshi ke tashi.

Ai Ummi bata san lokacin da miyan bakinta ya tsinke ba.

"Kai amma wallahi kamar kin san ita nake sonci tunda na zo Kano"

"Ai na sanki da gurasa ko a school kinfi sayenta, shi ne yasa kina faɗa min yau zaki zo nasa aka sayo min ita nan bayan layinmu na haɗa miki ita"

"Kai wallahi na gode"

Ummi ta faɗa tana fara cin gurasar.

Suna yi suna taɓa fira, wata akan school ɗinsu wata akan rayuwar yau da gobe.

"Yaushe zaki je gidan Yaya Asiya ne?"

"Ai ni kullum ma zan iya zuwa, kin san bamu da nisa sosai, ko zuwa zakiyi muje tare ne?"

"Eh haka nake so gaskiya, kin san tunda akai bikinta sau ɗaya fa na taɓa zuwa gashi kuma harta haihu ko sunan banje ba"

"Ai ko dai Hanan ɗinta tayi wayo ma"

"Insha Allah zan ƙara zuwa nan da dai kamin na koma gida sai muje tare"

"Yaushe zaki koma ne?"

"Gaskiya sati biyu zanyi Maryam"

"Kai dan Allah Ummi wane irin sati biyu kuma?, ki bari kiyi mana ko wata ɗaya ne haka mana?"

"Hmm lallai Maryam ɗin nan ma, ashe kin manta irin uwar wahalar da nake gurza a gidan Aunty Binta?, ai bazan iya zama ba Maryam, gara na koma gidan ubana saiya fiye min kwanciyar hankali, koda a bukka muke koda kullum muna cin tuwo to gara zama a gidanmu wallahi duk halin da muke ciki"

"Haka ne kam Ummi gaskiyarki, kina da hujjar komawa gida wallahi, ai ni idan da ni ce ma bazan iya irin haƙurin da kike yi ba na zama tare da irinsu Aunty Binta ba. Wai ina Salma ne, ai itama basa jituwa da ita fa"

"Ai ko basa zama inuwa ɗaya da Salma, tana can gadon ƙaya gidan Babanmu, kin san yana da Mata a nan daya aje"

"Haka ne kin taɓa gaya min, amma itama ai ba wani jin daɗin zama take a can ɗin ba"

"Hakane kam dan wani lokacin gara zama da Aunty Bintar, saboda ita duk abunta ƴar uwa ce ta jini, bata isa ta gaya mana wasu maganganu marassa daɗi ba, amma kinga Aunty Murja hmm, matar nan fa bata jin kunyar Baba a gaban idonsa take ce mana ƴan iska masu bin Maza"

"Kai jama'a kudai kuna ganin rayuwa wallahi, daga zuwa karatu kuma duk hakan take faruwa daku"

"Hmm bari Maryam, ai zama gidan wani baiyi ba, dama ace school ɗinmu akwai hostel mai girma da ɗalibai zasu kama ai kin san wallahi Allah ba gidan ub*anda zan zauna bare harya samu ratar da zai rinƙa gaya mana magana son ransa, to matsala ɗaya aka samu hostel ɗinmu bai da kyau"

"Hakane wallahi ai gara zaman hostel dama akan zama gidan wasu"

Wayar Ummi ɗince kira ya shigo, miƙa hannu tayi ta ɗauki wayar bayan ta aje ruwan da take sha, dan har ta gama cin gurasar tana shan ruwa suna firar.

"Mama ce ma"

"Assalamu alaikum Mama"

Daga can Mama ta amsa tana cewa.

"Wai kina ina ne Ummi?"

"A'a Mama ina gidansu Maryam mana"

"Wai yanzu Binta ta kira ni ta ce kin fice tun safe kin barta da aikin gida, kuma ma baki tashi gaya mata cewar zaki je gidan ƙawarki ba sai yau da safen nan"

"Innalillahi wallahi Allah Mama ba haka bane, wai mi yasa Aunty Binta ke min haka ne?,ace duk lokacin da zan fita saita kira ki ta haɗani dake, sai ka ce tana jira na dama?"

"Kinga ba wannan na kira naji ba ni, ki tabbatar kin koma da wuri, kinyi mata duk wani abunda ya dace, dan kin san bana son abun ɓacin rai"

"Uhm shikenan Mama naji"

Ummi ta faɗa tana sauke wayar.

Shiru tayi ranta na mugun soya da irin halin Aunty Binta.

Dafata Maryam tayi tana sauke lumfashi ta ce.

"Naji komai amma kiyi hakuri, ita uwa ce kuyi mata biyayya kinji Ummi"

"Ai wallahi Maryam tasan ita Aunty Bintar darajar Mama take ci, amma baccin ita bata isa na ƙara zuwa inda take ba wallahi, amma akwai ranar da wallahi bata isa ta ganni inda take bama"

"Haka ne kware da gaske ma kuwa, ai komai lokaci ne Ummi kiyi hakuri. Yanzu to zaki tafi ne yanzu?"

Girgiza kai tayi idonta jawur kamar zata saki kuka ta ce.

"Wallahi ba inda zanje har sai nayi sallar mangaruba zan tafi, idan ya so idan na koma tasa kaina gabas ta yanka"

"Amm.....

"Kinga Maryam karma ki ɓata yawun bakin ki, dan wallahi ba inda zanje yanzu, baki ji abunda taje ta ce ma Mama bane wai?, canza fa magana tayi, wai ban tashi gaya mata cewar ga inda zani ba sai yau da safe dana shirya, kinji fa wani shirri?, ita da yake bata tsoron Allah"

"Mi yake faruwa ne haka Ummi?"

Umma ta faɗa jin muryar Ummi ɗin da kuka take fitowa, dan lokacin harta fara zubar da ruwan hawaye, muryarta na fitowa ne da kyarmar kuka.

"Wallahi Umma ita da Auntyn nan tata ce Aunty Binta, kin san nasha gaya miki bata da kirki ko kaɗan a tsakaninta dasu Ummi"

"Kiyi hakuri kinji Ummi, ai wata rana ma bazata ganki ba wallahi, kuma ki rinƙa kai zuciya nesa ki daina saurin kukan nan haka nan, ita kuma Allah ya shirya ta yasa ta gane gaskiyar wulaƙanta ɗan uwa ba abu bane mai kyau"

"Shikenan Umma na daina, amma abun ne da ciwo"

"Na sani tabbas amma a ki ƙara haƙuri, ai shi mai haƙuri daban yake ko a wajan Ubangiji, sana Allah yana masa sakayya kinji"

Umman ta faɗa tana fita tabar masu ɗakin tana ƙara rarrashin Ummi ɗin da har lokacin ke share hawaye........

PAGE 26

*Ƙauyen Karaɗuwa, Kankia LGA, Katsina state Nigeria*

"Wai Sadiya Makarantar ce bazaki ba ko mine kike nufi?"

Kwaɓe fuska tayi tana ƙara bajewa ta ce.

"Nifa gaskiya Inna bazan iya wani zuwa school ba yau. Wallahi cinyoyina ciwo suke min, kuma duk wancan mugun ne yaja. Na rantse karki ji yadda idan na miƙe suke min ciwo, kwata-kwata jikina ma ciwon yake min duk yayi tsami"

Jinjina kai Inna tayi tana faɗin.

"To ai shikenan. Amma ki tabbatar idan ya dawo ya tabbaye ki kina da amsar da zaki basa wacce ta hanaki zuwa Makarantar, dan ni babu ruwana, karma ki matso inda nake na gaya miki"

Kamar zata saki kuka ta ce.

"Haba Inna yanzu so kike na shirya na tafi makaranta bayan kin san na makara ma?"

"To ai koma miye ki ce kika ja ma kanki, ni dai na gaya miki, ki tanadi abunda zaki faɗa masa, idan kuma ya ƙara baki wani horon mai tsanani kinga ai cinyoyin sai suyi ciwon

13 / 36