Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
tashi badan ta gama bada amsar komai ba a exam ɗin taje ta bada ita ta fice tana sakin ajiyar zuciya kawai.
Habiba ko kamar yadda ta saba ne sai da kowa ya kusan fita kamin taje ta bayar da tata.
Tana fitowa suka wuce can cikin school ɗin domin sake kaya su saka kayan graduation.
"Mun fito lafiya, Alhamdulillah. Amma naga ke baki farin ciki ma, ko ɗan ƙorafin nan na daɗe a ciki baki yi min ba yau?"
Murmurshin yaƙe Salma ta saki tana cewa.
"Kinga muje can naga kamar a can Mata ke zuwa suna sake kaya muma sai mu sauya namu ko a can?"
"Eh muje ɗin"
Suka nufi wajan.
Mata ne sosai sai hayaniya ake, wasu na bada labarin cewar wai Mlm Jamilu ya hana a sake kaya miye da miye, maganganu iri da iri kake ji gasu nan.
Ita dai da Habiba sake kayansu kawai sukai.
Salma tasa dogowar riga Abaya ƴar dubai kalar Ja, sai ta ɗora rigar da sukai ta graduation nasu, sai wata hula data saka a saman kanta, sosai kayan sukai mata bala'in kyau kamar ba ita ba, duk ma ramar data yi hakan bai hana kyanta fitowa ba sosai, dan sai Habiba taga yau tayi mata wani irin haske a ido, ga rigar data saka ta ƙara fiddo mata da hasken fatarta sosai.
Ita kuma Habiba wando ne tasaka falazo da wata riga iya gwaiwarta, sai ta ɗora rigar graduation itama haɗe da hula itama, saita yafa wani gyale fari, da yake kayan nata baƙaƙe ne ita.
Suna gama shiryawa suka fice daga wajan, dan hayaniya tayi yawa sosai mata sai shewa ake.
Duk da irin gargaɗin da Mlm Jamilu yayi akan baya so yaga ansa matsatstsun kayan amma wasu dan rashin ji saida suka saka, wata ma ƙarewa siket ne tasa iya gwaiwarta, sai wata safa data saka dogowa ita ce ta rufe mata sauran jikin nata, ke kowacce dai da irin shigar data yi.
Pictures kawai ake yi duk inda ka waiga photo ne ake yi.
Dan haka su Habiba ma samun waje sukai aka fara kashe pictures.
Duk da dai Salma ƙarfin hali ne kawai take.
An daɗe ana abu ɗaya har Salma sai da ta gaji ta samu waje ta zauna, dan Habiba bata gaji ba ci gaba da yin pictures kawai take ita da wasu ƴan department ɗinsu da suka zo dan Allah tayi masu da IPhone ɗin da suka gani a hannunta.
Tunda Salma ta saɓe ta zauna ta fara kiran Mlm Jamilu a waya, dan so take karta tafi bata basa wannan saƙon nasa data kawo masa ba.
Sai dai tayi masa kira ya kai babu daɗi ma, amma baya ɗauka harta gama ringing ɗinta ta katse.
Ƙarshe ma sai taji kamar yayi blacked ɗinta ne.
Duk layikanta guda biyu idan ta kira number nashi bata tafiya.
Wani iri taji har cikin ranta tana jin babu daɗi sosai taji ta muzanta ma, ta ƙara tabbatar ma kanta Jamilu koda can alfarma yake mata ashe baya sonta.
Wani kalar tari ne ya sarƙe ta ba wadda ya lura dan Habiba tana can sai pictures take ɗaukar wasu.
Sosai take tarin har yana janye lumfashinta da kyar take iya jan lumfashi, saboda tarin daya ci ƙarfinta.
Toshe bakinta tayi da hancinta da wani kyalle da take yawo dashi dama gudun irin haka, tana jin yadda jini tabbas ke zubo mata da sauri ta miƙe tana barin wajan. Ruwa ta sayo tana matsawa gefe ɗaya duk da yadda take ganin mutane dishi-dishi ta shiga wanke uban jinin daya zubo mata, ita kanta tayi mamakin yawan jinin yau daya zubo mata.
Da sauri ta idasa wankewa tana dawowa inda su Habiba suke tajawo hannun Habiba ta ce.
"Please Habiba dan riƙe ni bana gani sosai"
Habiba ai sai ta maida wayar a jaka tana riƙe Salma sosai hankalinta tashe sai tabbayarta take lafiya take kuwa?, miya same ta?.
Salma ba bakin magana dan ita kaɗai tasan miye take ji a jikinta.
"Kinga muje gida kawai naga baki cikin hayyacinki ma"
Girgiza kai Salma tayi tana ƙara riƙe Habiba suka fara takawa Habiba na riƙe da sauran kayansu ta ce.
"A'a ki sani a napep kawai zan iya komawa da kaina"
"A'a bazan barki ki tafi ke ɗaya ba gas......
Amsar da Habiba ke bata ce taji ta daina shiga kunnen ta, domin ɗaga kan da zatai kawai idonta ya gane mata Mlm Jamilu ya fito daga Office nashi tare da wata Mace. Fuskarta a rufe sanye da liƙabi, suna tafe a tare sun jero suna magana sai murmurshi yake mata, har kusa da Motar shi suka tsaya suna sake magana da budurwar da fuskarta ke rufe.
Ai ji Salma tayi duk wani jinta da ganinta yana shirin barin gangar jikinta, zuciyarta na masifar bugawa.
Da kyar ta jawo magana a bakinta dan kwata-kwata yanzu bata ma ganin komai a cikin idonta sai wani farin abu da take gani.
"Habiba bana iya ganinku, please ki ɗauki wayata ki kira Doctor Nura, zaki ga ansa Doctor Nura"
Da kyar ta kare maganar saboda wani irin tari daya sarƙeta.
Yawan jama'ar dake ta kai kawo a school ɗin yau shi ya hana fahimtar halin da suke ciki.
Ganin hayaniya na ƙara hargitse jikin Salma yasa Habiba fita da ita daga school ɗin baki ɗaya. Ita kanta Habiba zuwa yanzu hawaye kawai take bata sani ba.
Jikinta na rawa ta ɗauki wayar Salma tama ruɗe, da kyar ta iya lalubo number ɗin Doctor Nura.
Da kyar ta iya tsaida hankalinta ta shiga masa baya ni. Bawan Allah a ruɗe shima ya ce mata gashi nan zuwa karta sake kiran kowa.
Abunda ya ƙara tada hankalin Habiba shine yadda Salma ke ce mata bata gani wallahi kwata-kwata ga zuciyarta dake mata zafi, ga tarin daya ƙi tsaya mata, ga jinin daya fara zuboma Salmar, dan tunda Habiba take bata taɓa ganin haka ba daga wajan Salma ɗin, tunda ɓoye mata take, iya saninta cewa take mata zazzaɓi ne kawai ke damunta, shi yasa yanzu da take ganin yanayin jikin nata ke ƙara sakata cikin damuwa da tashin hankali, sai hawaye take tana jijjiga Salma.......
PAGE 53
Kuka dai kam Habiba tun tana yi da hawaye har ta fara da ƙarfi.
Tunda Doctor Nura ya zo suka wuce asibiti da Salma aka shiga da ita emergency Habiba keta kuka dan sosai Salma jikinta yayi mugun rikicewa, bare ita da take ganin yadda take aman jini ta baki ta hanci.
Dole ganin hankalinta yaƙi kwanciya gashi babu kowa a cikin ƴan uwan Salma yasa kawai ta kira gida number ɗin Aunty Ummi ta shiga sanar da ita.
Zan iya cewa Aunty Ummi baccin Yusura dake kusa da ita da zubewa zatayi a ƙasa tsabar kiɗimar data shiga, Yusura ce tayi namijin ƙoƙarin tarbota jikinta ta shiga tabbayarta lafiya kuwa mi ya faru?.
Sauke ajiyar zuciya Ummi ta shiga yi tana jin ƙirjinta na mata nauyi.
A ruɗe take neman number ɗin Baba, dan zuwa yanzu zuciyar Ummi ta yanke shawarar kawai ta sanar da su Baban abunda yake damun ƴar uwarta ko Allah zaisa su samo mata abunda zuciyarta ke so, baza ta bari ta rasa ranta a banza ba.
"Dan Allah Aunty Ummi ki natsu miye ke faruwa ne?"
Hawaye Ummi keyi tana kallon cikin wayarta ta ce.
"Salma ce wai ta faɗi a makaranta yanzu haka suna asibitin Doctor Nura emergency aka shiga da ita"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Aunty Salma?"
Itama Yusura ta faɗa ƙirjinta na bugawa.
Ai Baba yana ɗaukar wayar Ummi ta shiga kora masa jawabin Salma ba lafiya yanzu haka suna asibiti dan Allah su taho kawai.
Tana yin maganar tana kuka.
A ruɗe ta kashe wayar tana neman Hijab ɗinta.
Jakar kayanta ta shiga laluba sai dai tana ɗakko Hijab ɗin wata farar takarda ta faɗo daga cikin kayan nata.
Da mamaki tabi takardar da kallo.
Har zata share saboda a ruɗe take sosai, ba komai take ganewa ba a lokacin, sai kuma wata zuciya ta ce mata ta buɗa ta gani, tunda iya saninta bata aje wani abu mai kama da wannan ba a jakarta. To waye ya saka mata?.
Jiki na rawa ta buɗe takardar tana bin rubutun da kallo kawai.
"Wannan ai rubutun Salma ne, Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, mi wannan yarinyar ke nufi ne?"
Ummi ta faɗa jiki na rawa ta fara bin rubutun tana karantawa.
Harta idasa karantawa jikinta na kyarma, ga wata uwar zufa data wanke mata fuska.
"Na shiga uku na Yusura, wai wasiyya fa ce ta barmin Ya salam"
Jikin Yusura na rawa ta amshi takardar itama tana karantawa.
"Wai dama Aunty Salma duk wannan ciwon na Mlm Jamilu ne?. To dama bai san yadda take sonshi bane wai?"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, wai fa cewa take dan Allah na tabbatar koda ta mutu an ɗaura aurenta da Jamilu, na taimake ta na cika mata burinta na auren Jamilu ta mutu da aurensa akanta. Wannan wacce irin wasiyya ce haka?"
Jiki na rawa ta sanya Hijab ɗin Yusura ma ta take mata baya riƙe da takardar a hannunta.
Suna fitowa waje Aunty Murja ta jefa masu tabbayar lafiya?, ta gansu a ruɗe haka daga ita har Yusura ɗin.
Yusura ce ta shiga sanar da ita a ruɗe.
Ai sai itama ta sanyo Hijab suna barin gidan a tare.
Da yake Ummi tasan asibitin Doctor Nuran kai tsaye can suka nufa.
Suna ƙarasawa ta kira Habiba da kyar Habiba ta iya zuwa ta taho dasu.
Yadda suka ga Habiba na kuka ya ƙara tayar masu da hankali sosai ba kaɗan ba.
Doctor Nura na ciki ba damar ganinsa dan har lokacin Doctors ɗin basu fito daga duba Salma ɗin ba.
Ba abunda Ummi ke yi sai kiran Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un.
Kwata-kwata Ummi a ruɗe take hawayen ma sun kafe tsabar tashin hankali.
Su Baba wani irin gudu sukai sai gasu a Kano dandanan sun iso, suka kira Ummi, Ummi kasa ɗaukar wayar tayi sai dai Yusura ta ɗauka tana masu bayanin inda suke.
Aunty Murja na tsaye tana kallon Ikon Allah.
Koda su Baba suka ƙaraso kai da ka kalli Mama kasan taci kuka tun akan hanya, dan duk tayi zuru-zuru idonta sunyi ja sosai.
Ya Muhammed duk da yana namiji amma daka kallesa shima kamar wadda yayi kuka.
Baba kuwa ai ɓata baki ne ma bayanin irin halin da yake ciki, dan tabbayoyin duniya ya shiga jefoma Ummi da zuwan nasu yasa ta fashe da kukan da take ta riƙesa tun ɗazu, dan abun duniya ya taru yayi mata yawa.
Bata da zaɓi sai na sanar dasu Baba ainafin abunda ke faruwa.
Ai ji Baba yayi kamar ya gaura ma Ummi mari. Faɗa sosai ya shiga mata ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, yana cewa mi yasa tun farkon abun bata sanar dashi abunda ke damun Salma ɗin ba tuni?, sai da abu ya zo ya ƙure.
Ta barsu cikin duhu, sun ɗaukar wata damuwarce daban ba wannan ba. Ashe abunda ke damunta nata mai girma ne irin haka?.
Faɗi yake koma waye wadda take so ɗin zai je da kansa ya roƙesa alfarma, miye a ciki idan yaje?, ai ceton ƴarsa zaiyi.
Sosai yake faɗa, kamar zai rufe Ummi da duka, su Ammi na basa baki, suma suna mamakin wacce irin soyayya ce haka ta kama Salma. Da suna jin ana cewa soyayya na iya kashe mutum, ko kuma suna kallo a films, ai da wasa kawai suke kallonta, sai gashi yanzu a zahiri suke ganin abun, a kuma kusa dasu yana faruwa.
Kai tsaye Baba ya ce Ummi da Ya Muhammed suje har school ɗin a tare dashi ko kuma a basa Numbers ɗin shi Jamilun ya kirasa.
Ummi na kuka ta shiga bashi number ɗin Jamilu, dan wayar Salma da aka amsa a hannun Habiba, dama babu key a jikin wayar. Habiba ko datai tsamo-tsamo itama tana mamakin dama ciwon Salma na son Jamilu ne duk yasa ta ƙare haka?.
Wani irin tausayi taba duk jama'ar wajan da duk wani mai imani. Kai jama'a dama haka ƙarfin so yake?.
Habiba take tabbayar kanta tana mamakin ƙarfin son da Salma kema Jamilu gashi har saboda dashi tana shirin rasa rayuwarta.
Suna gaf yanke shawarar tafiya har school zuwa wajan Jamilu Doctors suka buɗe ƙofa.
Ai kusan zuga akai ana yayyaɓe Doctor Nura, tabbayoyi ne kowa ke jero masa.
Shi kam zufa kawai yake gogewa hankalinsa shima kansa a tashe yake.
Ganin irin halin da yake ciki shima, sai ya ƙara tayar masu da hankali ainun.
Mama ce tayi ƙarfin halin ƙara jefo masa tabbaya.
"Doctor ka sanar dani yaya jikin ƴata yake?"
Wani miyau ya haɗe yana cewa.
"Muje Office amma daga Baba sai Mama sai kuma Ummi su biyo ni, su kawai nake da buƙatar gani"
Ai jin haka yasa Baba da Mama bin bayansa kawai basu ma tsaya cewa komai ba, Ummi ma take masu baya tayi tana jin hankalinta na ƙara tashi.
Wani bayani ya fara masu kamar nasiha haka, ai Mama najin haka ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu zuciyarta na bugawa ta ce.
"Kaga Doctor fitowa kawai zakai fili shin Salma ta mutu ne?, kake ta mana wani kauce-kauce da wani wa'azi naka?"
Mama ta ƙare maganar kamar a faɗace.
Haƙuri ya shiga bata yana cewa.
"Mama kiyi hakuri Salma bata mutu ba, amma gaskiya da wahala ta tsallake yau, dan munyi iya bakin ƙoƙari wajan saita bugun da zuciyarta ke mata amma ina, ga jini da take zubarwa, kuma kwata-kwata taƙi bamu damar dubata ma yadda ya dace, yanzu sosai zuciyar tata ke ƙara kunbura. Akwai wani buri nata da take ƙarfafa kanta cikawa da kuma burin taga ta cinmasa shine ma yake bata kwarin gwaiwar lumfashi danta rayu. Yanzu dai mun saka mata abun taimakawar lumfashi, tana neman ganin Ummi da kuma Baba"
Mama ta dafe kanta idan baccin a zaune take da tabbas tasan zubewa zatai a ƙasa, dan wani irin dummmm taji har tsakiyar kanta.
Ganin yanayin da take yasa Doctor Nura fara bata taimako, jininta ne ya hau nan take sosai, dan tsaf da ace a tsaye take ta faɗi za'a iya samun matsala babba ma kuwa.
Baba shine mai ƙarfin hali, amma shima da za'a duba tabbas jininsa ya hau shima.
Ummi ce kawai mai ƙarfin hali itama dan tana kuka ne shine ke rage mata abunda take ji a cikin ranta.
Baba ne ya miƙe da kyar yana ficewa daga office ɗin, a nan aka kwantar da Mama dan akwai gado a Office ɗin, na duba marassa lafiya, office akwai girma sosai. Mama ko tashi bata jin zata iya sosai take ganin juwa a zaunen da take ma.
Sun ɗauki lokaci a Office ɗin kusan awa nawa kamin Mama ta ɗan dawo dai-dai.
Mama najin ta fara dawowa dai-dai. Ita ta matsama Ummi ta kamata ta kaita wajan Salma, karta mutu basu gana ba.
Ummi na kuka take ce mata Mama, dan Allah ta daina faɗar mutuwar nan.
Basu san ya akai ba, ko yadda akai ba, su Mama na fita da Ummi suka ci karo da Mlm Jamilu na fitowa daga ɗakin da aka kwantar da Salma.
Daka kalli yanayinsa shima hankalinsa yayi mugun tashi. Dan duk ɗaukarsa shifa ya ɗauka soyayyar da Salma ɗin ke masa ba wata ba ce, kuma baida ra'ayin ƙara aure a cikin tsarin rayuwarsa, shi yasa ma yake mata haka, yana ɗan kakkaucewa kodan wai ta mance dashi, ashe ita wannan abun da yake mata ba ƙaramar illa yayi mata ba. Tabbas kallo ɗaya zakai masa kasan yayi kuka shima.
Ummi bata san lokacin data saki Mama ba, kai tsaye sai dai aka ga taje inda Mlm Jamilu yake.
Bata taɓa tunanin zata iya gaggaya masa maganganu masu zafi irin wadda ta shiga yaɓa masa ba a yanzu ba, dan sosai take jin tsanarsa har cikin ranta, tana yi tana nunatsa da yasa.
Shi kam tunda ta fara yake binta da kallo, kawai, kwata-kwata baiji haushinta ba, sai jarumantar data nuna harta iya tsayawa a gabansa tana faɗa masa magana kamar haka, ya ɗauki hankalinsa gare ta.
Baccin abunda ke faruwa da Salma yasha masa kai ba abunda zai hana ya ɗaga hannu ya mareta, amma sai ya kasa.
Ya Muhammed ne ya zo ya janye Ummi dake masifa kamar zata ari baki.
Baba ne ya zo har wajan yana janye Jamilu wajan.
Kuka kawai Ummi ta ƙara saki, jin wai cewa an ɗaura auren Jamilu da Salma a yanzu a masallacin dake cikin asibitin, mutane ƙalilan ne suka shaida, dan shi cikin ƴan uwansa ma mutum ɗaya ne ya sani.
Kuka take tana baƙin cikin wannan aure da aka ɗaura shi babu son rai, da alama ma Jamilun ya yarda ne badan yana so ba.
Ita kanta Mama badan ta yarda dashi ba ko tayi farin ciki kawai dan cika burin ƴarta ne da aka sanar da auren ma kasa cewa komai tayi.
Duk da Doctor Nura na son Salma amma bai nuna komai ba, dan dashi aka shaida auren ma, yana mamakin son da take ma Jamilun.
Dan kwata-kwata ɗazu ƙin yarda tayi a duba ta yadda ya kamata, amma yanzu suna shiga da sauran Doctors sai yaga tana sakin murmurshi mai haɗe da hawaye.
Kai tsaye muryarta da bata fita ta ce ma Doctor Nura, kai suyi mata komai ita kam ai yanzu tata ta ƙare, karma su ɓata lokacinsu wajan ceton ranta.
Fur taƙi basu damar dubata dan har ana shirin shiga da ita aiki ma, amma taƙi.
Kawai dai a kira mata Ummi.
Kai tsaye da aka sanar da Baba sai ya bada umarnin a kira Jamilu ya fara shiga.
Dan kai tsaye shima Baba yaba Salma mutuwa haka kawai jikinsa ya basa, shi yasa komai cikin sanyin jiki yake yinsa.
Jamilu daya shiga, kawai jawota yayi jikinsa ya rungume, a mamakin Salma kuka ya sakar mata kamar ƙaramin yaro.
Salma farin cikin da take ciki ko iya haka ne ma ya isheta.
Itama tana hawaye zatai magana tarin