Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   18 / 36

51K to 54K   out of 106.4K words

tun lokacin da Aunty Ummi ta zo gidan nan, dan haka ni bance ki taimaka min ki saɓama mahaifiyarki ba, please ki barsa kawai zanyi fa"

Kamar Yusura zatai kuka ta sakar mata tsintsinyar sharar ta koma gefe tana binta da kallo.

Da sauri Salma ke yin aikin, tana gama sharar tsakar gidan ta nufi kitchen, dan ma sauƙinta ɗaya indomi ce zata dafa da safen ba wani abu mai wahala bane.

Dan haka a gurguje ta idasa dafawa ta soya kwai ta zuba ma kowa tasa da kwan a sama. Kusan sati biyu kenan da komawar Baba Rimaye, kuma tunda ya tafi Aunty Murja ta ƙara matsa mata number da taƙura a cikin gidan, Aunty Ummi ma satinta ɗaya da wucewa Rimaye, kuma jiya ne suka fara, jarabawa ta first semester level 3.

"Ki kawo na kai mata kije ki yi wankan"

"Yawwa ki kai matan, namu ma ki miƙa mana ɗaki ina zuwa"

Ta faɗa tana ficewa daga kitchen ɗin ta shiga toilet, shima a gurguje tayo wankan ta fito, lokacin har Yusura ta kai masu abincin nasu ɗaki.

Shiryawa tayi da sauri da sauri dan ganin tara har tayi, gashi tara da rabi suke shiga jarabawar ta yau.

"Aunty ki fara zama mu ci abincin, tunda shiryawar bata da wahala"

"Ai da wuya na iya cin abincin nan Yusura, kawai ki aje min nawa, ai da wuri zan dawo ana fitowa daga jarabawa"

"Amma ba naji kince Ya Muhammed ya kira ki jiya ba ya ce ki tsaya wajan Mlm Jamilu, har ya turo miki number tashi, saboda jarabawar da bakiyi ba jiya"

Tunowa da haka yasa Salma sauke ajiyar zuciya, tana tunanin ta inda zata fara kiran Mlm Jamilu, duk da dai jiya tayi namijin ƙoƙari wajan yi masa magana ta chatting.

Tayi mamakin data gaya ma Ya Muhammed ɗin jiya bata samu an barta ta shiga jarabawa ba, saboda yadda Aunty Murja ta matsa mata da aiki yi wannan yi wannan, har sai da taga ta makara sana ta barta, Salma harda kukanta, data je school aka hanata shiga, saboda lokacin data isa har an fara jarabawar, Habiba kuwa zagi dai tayi ma Aunty Murja shi a ranar, tana ja mata Allah ya isa.

Sosai tayi mamakin lokacin da Ya Muhammed ya turo number ɗin Mlm Jamilun ya ce taje wajansa insha Allah zai taimake ta zai san yadda za'ai da jarabawar da bata yi ba, ya ce mata ɗan uwan ogansa ne wajan aiki, ba tun yau yasan hakan ba, dama kuma Ya Muhammed ɗin ne ya bada shawarar a samar masu school of hygiene ɗin, ashe ta hanyar Mlm Jamilun suka shigo school ɗin, kawai dai shi Ya Muhammed bai taɓa faɗa bane, sai jiya, kuma sunyi magana da shi Mlm Jamilun da Ya Muhammed akan cewa ƙanwarsa nada matsala kaza zata zo ta same sa, kuma ya amsa.

"Bari kawai naje Yusura idan na ce zan tsaya zanyi irin ta jiya ne, so nake idan muka fito daga exam ɗin naje na sami Mlm Jamilun. Kawai saina dawo dai"

"Tom Allah ya tsare ya bada sa'a kuma"

Da amin ta amsa tana ficewa daga ɗakin.

Tsaye take bakin titin ƙofar gadon ƙaya, sosai take addu'ar Allah yasa ta samu abun hawa, dama jiya irin haka ne yasa ta ƙara makara.

Tana rufe baki ta hangi kamar wata Mota data sani.

Saida ta zo inda take ta tsaya akai parking a inda take ne Salma ta shaida Doctor Nura ne.

Lokacin daya zage gilas ɗin Motar fuskarsa ta bayyana yasa Salma sakin ɗan murmushi.

Zatai magana yasa hannunsa a tsayansa alamar tayi shiru kawai ta shigo daga ciki tayi maganar.

Bata da zaɓi saina kawai ta shigan, dan lokaci sai ƙara tafiya yake, dan har tara da minti goma sha biyar tayi.

Bayan ta shiga ta rufo murfin Motar, ya tayar da Motar suka fara tafiya ta gaidasa a hankali tana kallon titi.

"Lafiya lau. jarabawa ku ke ba?"

"Uhm ya akai ka san exams make?"

Murmushi kaɗan ya saki yana murza sitiyarin Mota ya ce.

"Duk wani halin da kike ciki ai na sani Hajiyata. Yanzu dai koma ki tabbaye ni kwanaki da dama baki jini ba?"

Kunya ce ta ɗan kama Salma, ya kamata dama ta fara tabbayar lafiya?, tunda ya ɗauke ta da daɗewa ya kaita school bata sake ganinsa ba.

"Ina so na tabbaya ne fa"

Salma ta faɗa tana turo baki, yadda tayi maganar yasa Doctor Nura sakin murmurshi sosai dan ba ƙaramin kashesa da salon da tayi maganar yayi ba.

"Okey okay naji, yanzu kina son sanin dalilin daya sa baki ƙara gani na ba?"

"Yeah"

Kawai Salma ta faɗa.

"Bana ƙasar ne, munje ne nida Madam ta raka ni yin wani aiki a dubai, sai jiya na dawo"

Wani iri Salma taji, dama yana da aure?.

Take tabbayar kanta, sai kuma tayi saurin girgiza kai, ai dama zaiyi aure, bai ma kamata tayi mamakin jin cewa yana da Mata ba.

"Sorry nasan zaki ce dama ina da aure night?"

"Noo a'a wallahi banyi wani mamaki ba, ai da an ganka anga magidanci dama, tabbayar kuma akan mi zanyi?, banda hurumi gareta ai"

Murmurshi ya saki zaiyi magana suka iso bakin get ɗin school ɗin, gashi waje ya ƙure dan tara da rabi dai-dai suka ƙaraso.

"Sorry zan shiga school time na dab da ƙure min"

"Okey tara da rabi zaku shiga exams?"

Tana ɗaukar jakarta ta ce.

"Yeah thanks"

Ta ƙare maganar tana buɗe ƙofar Motar.

Bata bari ya sake wata magana ba tayi saurin barin jikin Motar ta nufi bakin get ɗin school ɗin...........

PAGE 35

"Yawwa ke nake ta jira wallahi, ina tsaye wajan nan ina addu'ar Allah yasa wannan Auntyn taku karta ƙara ja miki wata matsalar yau ma"

Murmurshi ta saki ta kamo hannun Habiba suka shiga ajin da suke exam's.

Zama su kai a gaba kamin a shigo kowacce ta koma sin nata.

"Wai ya za'ayi da exam ɗin da kika rasa jiya ne?"

"Hmm ke dai bari abunda zan baki labari kenan fa Habiba. Kin san dama na ce miki zan kira Ya Muhammed nayi masa maganar akan exam ɗin. Wallahi karki so jin yadda yayita min faɗan dan mi ban bar mata aikin ba nayi tafiya ta school?, ko dan ba ita ba ce take biya min kuɗin school ɗin ba?, harfa yana shirin gaya ma Baba, ni na hanasa"

"Ahhh ke dalla kin ma bani haushi, akan wane dalilin zaki wani hanasa sanar dashi Baban?, kina da matsala Salma wallahi, zurfin cikinki yayi yawa wallahi, akan mi mata kullum tana ɓata miki amma bazaki iya buɗe baki ki kwaci ƴanci ki ba?, shi yasa fa Aunty Ummi ta fiki ta nan wajan haba"

"Kai Habiba, sai kuma kita min faɗa?, ai kin tsaya kiji ƙarshen maganar ko?"

Salma ta faɗa kamar zatai mata kuka.

"Okey naji, amma ni ba faɗa nayi miki ba, kawai ki rinƙa tsayawa ki kwaci ƴancinki shine kawai, tunda dai ba mutum ci ne da ita ba, bai kamata ana raga mata ba itama"

Salma zatai magana aka shigo ajin masu tsaron exam's ne suka shigo haɗe da wasu Malamai.

Kowa komawa yayi inda yake zama, ajin ya ɗauki wani irin shiru.

Salma na bayan Habiba, kusan numbersu ɗin ɗaya dama ɗaya nabi ma ɗaya.

Rabama kowa faifar exams ɗin sukai ajin ya ɗauki wani irin shiru sosai baka jin komai sai motsin raba faifar exam's da wasu masu tsaron exam's ɗin suke.

Malamai da dama suna shigowa ajin suna ɗan zazzagayawa suna duba ɗalibai, motsi kaɗan mutum zaiyi kaji anja masa worning, ko kuma kaji ance ya fita daga ɗakin jarabawar, mutum na bada haƙuri Allah da Annabi amma ko sauraronsa ma ba'ayi.

Kusan awa ɗaya Salma ta fara fita kusan ita ce ta biyun bada faifar.

Dama kuma exam's ɗin awa biyu ce.

Jim kaɗan itama Habiba taje ta bada ta gama.

"Yawwa ke nake jira muje kiji abunda nake ta so na faɗa miki, sai kuma aka shigo exam"

"Kin san yau so nake na koma da wuri dan zanje wata unguwa ne muje kiyi sauri ki gaya min please"

"Ina zuwa ne yau?"

Salma ta faɗa suna ci gaba da tafiya zuwa can cikin school ɗin suka bar wajan hall ɗin da sukai exam.

"Wallahi zamu je wani suna ne"

Suna tafiya Salma na cewa.

"Ke wata magana ce fa wacce da wuya na iya zuwa wajan wadda Ya Muhammed ya ce naje akan exam ɗin dana rasa banyi ba jiya"

"Waye ya haɗaki dashi?, Malami ne a school ɗin nan?"

"Yeah Habiba"

"To miye a ciki Salma?, kawai kije mana na rakaki yanzu, tunda nasan yasan da zuwan naki ai Okey?"

"Hmm Habiba bazaki gane ba, kin kuwa san waye?"

"Ina zan wani sani idan ba faɗa min kikai ba, waye wai to ma?"

"Hmmmmm"

Salma taja wani lumfashi kamin ta kamo hannun Habiba suka zauna a wani lanbun masoya dake cikin school ɗin, wadda ƴan school ɗin suka saka masa suna lanbun masoya.

"Ina jinki fa waye?, ai dai nasan ya baki number koma wane Malami ne ko?, sana fatan kunyi magana yasan zaki zo yau ki gansa night?"

"Yeah munyi magana, har nake faɗa masa cewar ina tsoran zuwa wajansa, dan kar yayi min faɗa, amma mamakina Habiba, sai ya fara rarrashina kan cewa na zo kawai bazai taɓa min faɗa ba, amma fa har zuwa yanzu mamakinsa nake fa"

"Dalla banza ni ki gaya min waye to?, sai ƙara sakani cikin duhu kike yi fa"

Dariya Salma ta saki duk da irin yadda gabanta ke faɗuwa saboda kawai zata haɗu da Mlm Jamilu ta rasa mi yasa kuma.

"Kinga sorry ai zaki ji ko waye ma"

"To faɗan waye?"

"Hmmm"

"Allah Salma zan tashi na wuce gida, kina fa ji na ce miki unguwa zan wuce dana koma gida"

Habiba ta faɗa kamar mai shirin miƙewa tsaye, da sauri Salma tasa hannu ta dawo da ita tana murmushi kaɗan ta ce.

"Kinga bafa kowa bane Mlm Jamilu ne faaaaa"

Ido Habiba ta zaro waje kamar zasu fito waje tsabar zaro su da tayi waje, baki sake hanci a buɗe Habiba ke kallon Salma kamar ta samu TV.

Har sai da Salma tasa hannunta ta rufe ma Habiba baki da idon data fiddo waje.

Wata ajiyar zuciya Habiba ta saki kamar wacce tayi gudun tsere, zuwa can ta saki wani shegen murmushi ta kamo hannun Salma da sauri tana murmushi kamar bakinta zai zage ta ce.

"Wai dan Allah da gaske kike yanzu Mlm Jamilun zaki je ki gani?, kuma ma dashi kikai magana jiya?"

"Kware ma kuwa, bari ma kiga chatting ɗinmu dashi"

Salma ta kare maganar ta fiddo da wayarta a jaka ta shiga nuna ma Habiba ɗan chatting ɗin da sukai dashi a jiyan.

"Tabɗi jam Salma, dole bawan Allah ya ruɗe kin tashi kin tura masa wannan photon naki, gashi kina masa kamar shagwaɓa, kin fa san su maza haka fa suke, lokacin da zasu saki layi a gaban mace idan tana masu shagwaɓa da kashe murya basu fa sani ba"

"Ke Habiba bana son shirri ni Allah kuwan banga wata shagwaɓa da nayi masa ba"

"Ahh yo dama ke ai kowa ma yima shagwaɓa kike, ba gashi ba yanzu ma nima kina min"

"To ni ai a haka yanayi na yake kin kuma sani ai, bata wata niyya nayi ba"

"Hmm to shi dai kin ruɗasa da salon ki kawai. Amma fa wallahi mamaki nake"

"Yeah nima haka fa Habiba"

"To yanzu ya za'ai Salma?"

"Nima ban sani ba, dan ji nake kamar bazan iya zuwa ba yau wajansa wallahi"

"A'a baza'ai haka ba, tunda kin riga kin gaya masa yau zaki zo wajansa, muka wallahi kinga har ganinsa nayi a can wajan hall ɗin da muka baro inaga yana can wajan, yanzu tashi zakiyi na rigaki amma fa ba zuwa har wajansa zanyi ba, ko kuma ki ɗauki waya ki kirasa kiji ko a Office zaku haɗu"

"Gaskiya a Office ɗin dai yafi ai ko Habiba?, saboda nasan ƴan saka ido, yanzu da an ganni dashi Allah kaɗai yasan mi za'a je ana yaɗawa a school ɗin nan"

"To sai mi?, sun daɗe basu yaɗa ɗin ba, ke tashi muje ma ki kirasa yanzu dai"

Salma ita kaɗai tasan yadda gabanta ke lugudan daka. Kiran number ɗinsa tayi tana jin yadda zuciyarta ke tsalle a ƙirjinta.

Sai da ta kusa tsinkewa aka ɗauka.

Da wannan muryar tasa mai izza da kauri ga taushi dake ɗauke da ita yayi sallama.

Salma saida tayi da gaske ta iya saita kanta, dan muryarsa na bala'in hautsina mata kwanya.

Bayan ta gaida sa, baki na ɗan rawa ta shiga tabbayarsa tana school ina zata zo ta iskesa?.

Da muryar nan tasa mai sa Salma a wani hali ya amsa da cewa.

"Ki zo ina wajan hall ɗin da kuke exam's ina jiranki"

Yana faɗar haka ya katse kiran.

Ai sai Salma ta shiga sauke ajiyar zuciya tana bin wayar da kallo kawai.

"Wai ke lafiya?, kin cika tsoro wallahi"

"Ke bazaki gane mi nake ji bane, na rasa dalilin jin hakan daga garesa wallahi"

"Hmm yanzu dai muje na rakaki ko?"

"Amma dai dan Allah zamu je tare har wajansa please Habiba"

"Bazan miki alƙawari ba, dan nima nan in gaya miki shakkarsa nake ji, mutum sai ka ce yana shan wata addu'a wacce mutane zasu rinƙa ganin kwarjininsa sosai, kai Mlm Jamilu ƙarshe ne wallahi"

A zuciyar Salma ta ce ni ce na san haka Habiba.

Tafiya suka ci gaba da yi zuwa inda ya ce masu yana nan.

Suna zuwa inda sukai exam ɗin tun tahowarsu Salma ta hangersa, jin wayarta na ƙara alamar kira ne ya shigo yasa ta kalli cikin wayar, ganin Mlm Jamilun ne yasa Salma ɗagowa dai-dai shima ya ɗago da idonsa suka sauka a cikin nata, wata wawar bugwar zuciya ce ta sami Salma, waigawar da zatai kuma ta nemi Habiba ta rasa sai ta hangota can nesa da ita, tana mata alamar saita dawo ta nan tana jiranta, ai sai Salma taji kamar zata saki kuka, gashi tunda ta nufi inda yake hankalin ɗalibai da dama suka yo wajanta, tunda inda yake zaune kowanne ɗalibi na tsoron zama a wajan, duk wajan zaman ɗaliban ne, dan dakalin hall ɗin dasu Salma ke yawan yin lectures ne a cikinsa, ganin ita kai tsaye wajan da yake take nufa, gashi haɗa idon da sukai taga ya sakar mata wani murmurshin daya kusa saka Salma mutuwar tsaye, dan tasan shi dai ba amabocinsa bane, haka kowa ya sani, sai gashi ita rana ta farko da taga murmurshinsa, kuma sai taga yayi masa wani irin sahihin kyau.........

PAGE 36

*SALMA POV*

Ba abunda jikinta yake sai kyarma, amma baka taɓa gane hakan saika ƙure mata kallo, jikinta sosai yayi sanyi zama a kusa dashi.

Wasa take da yatsun hannunta tana kallon ƙasa, can ta ƙara jin muryar nan tashi mai cike da isa da wata izza ya ce.

"Uhmm why mi ya faru da har kika bari kika rasa exam's jiya?"

Wani miyau Salma ta haɗe tana ɗan ɗagowa ta kallesa, ai da sauri tayi saurin ƙasa da kanta tana jin yadda zuciyarta ta hautsina da wata irin bugawa, ganin idonsa akanta yake yana binta da kallo.

Zatai magana wani ɗalibi ya zo wucewa ta wajan tsabar gulma sai da ya tsaya ya kai har ƙasa ya gaida Mlm Jamilu, fuska a ɗan sake ya amsa da hannu yana sake zubama Salma ido.

Gaba ɗaya ɗaliban school ɗin rabi da rabi hankalinsu na wajan, shi yasa sosai Salma ke addu'ar Mlm Jamilu ya gama da ita, Allah kaɗai yasan irin yayaton da za'ai mata.

"Kinyi shiru fa? and ina da abunyi"

"Hmm dam....dama...dam....dama Daddy jiyan ne na aka tsare ni da aiki a gida abunda yasa ban iso school ɗin da wuri ba, sana ana wahalar abun hawa Daddy"

A yadda ta kira sunansa da Daddy da yadda tayi maganar sai yasa Mlm Jamilu sakin murmurshi kaɗan ya ce.

"A gidan ba'asan kina exam's bane?"

"An sani Daddy to amma, gidan da nake zaunan ne sai....

Sai kuma tayi shiru tana tunanin ba huruminsa bane yaji irin abunda ke faruwa da ita.

"Ki gaya min komai fa, ta yadda zanga ya kamata na taimake ki ko kuwa?, ki ɗauke a matsayin Daddyn nake, kinga ai ba maganar ɓoye-ɓoye a tsakaninmu night?"

Ɗan murmurshi kaɗan ta saki har kumatunta na lotsawa, kuma sosai hakan ya ɗauki hankalinsa gareta, shi kansa bai san ya akai yake sakin murmurshi ba haka suna tare.

Salma bata da zaɓi saina sanar dashi, kuma haka kawai taji hankalinta ya kwanta da sanar dashi ɗin.

Ɗagowar da zatai ta hangi Habiba nata mata alamar wai har zuwa yanzu basu gama maganar ba, itafa sauri take.

Alama tayi mata da tayi haƙuri sun kusa, maganarsa ta ƙara ji ya ce.

"Uhm mi yasa ba'a kama miki hostel ba?, ai da hostel aka kama miki da duk hakan bata faruwa ma daku ba. And mutane dama sai a hankali zama gida wani ba'a gaban iyayenka ba akwai wahala, duk da naji kince ma gidan Babanku ne"

"Yeah Daddy"

Zai sake magana kenan, saiga wani Mlm ya zo yana miƙa masa gaisuwa, daga nan ya samu waje ya zauna a kusa dashi, yana nuna masa wasu takardu.

Sun daɗe suna magana, ganin maganar kamar ba ƙarewa zatai ba yasa Salma ɗan gyaran murya ta ce.

"To ni Daddy zan wuce, naga kuna wani abu"

"Okey kije kawai zamu sake magana kamin ku gama exam's gaba ɗaya"

"Okey Daddy thanks"

"Okey you're welcome my dear"

Ya faɗa iya laɓɓansa, ta yadda ita kaɗai ce zata ji.

Da sauri Salma tabar wajan tana sauke wata ajiyar zuciya mai ƙarfi, tana mai-maita my dear ɗin daya kirata dashi.

"Wai ke mi kuke tattaunawa ne haka?, kin daɗe fa, Allah baccin ina so naji gulma da tafiya ta fa zanyi"

Habiba ta faɗa tana kamo hannun Salma.

"To zama zamuyi na baki labari ko kuwa tafiya zamuyi na baki a hanya?"

18 / 36