Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
ya ɗaga mata hannu yana duban Yusura data riƙe Salma ya ce.
"Ke kamata ku wuce ciki"
Juyawa sukai suka shiga ciki Ummi na tsaye dai a wajan.
Baba ya dawo da dubansa inda Aunty Murja take ya shiga nuna su gaba ɗaya da yatsa har ita Ummi ɗin ya ce.
"Bari kuji na gaya maku, bazai yiwu ku zauna kuna mana hayaniya a cikin gida ba, ga marar lafiyar da kwata-kawata ke Ummi kin san bata san damuwa yanzu, idan ita bata sani ba ai ke kin sani. Ke kuma Murja dan Allah ki kama girman ki"
"Haba Mlm haba Mlm, miye haka kake min a gaban ƴaƴanka ne?. Yaya za'ai ka tsaya a gaban marar kunyar nan kana tsinkani haka?, wai Mlm mina tarema ƴaƴan nan ne?, ni shikenan duk sadda sukai min abu na rashin dai-dai bazaka taɓa ɗaukar mataki ba, sai dai ma ka ƙara tsinka ni a gabansu?, to wallahi bazai yiwu ba, muddun marar kunyar nan ta ƙara taɓa ni to wallahi ka rubuta ka aje sai dai kazo kayi jinyar ta"
"Haka kika ce ko?. To ai gaki ga Ummi ɗin bismillah, tunda ni ban isa dake ba"
Baba ya faɗa yana sake duban Ummi da kanta ke a ƙasa saboda kasancewar Baba a wajan yasa ma bata ce komai ba.
"Ke kuma wuce daga ciki"
Simi-simi ta wuce ɗakin da suke sauka tana ƙara jin ɓaɓatun Aunty Murja kamar zata ari baki sai faɗa take tana cewa.
"Yo haka kawai yara sun zame min ƙarfen ƙafa, nida gida na amma an hanani zamansa ni ɗaya. Su iyayen nasu dake can zaune ba su kaɗai ne a zaune a can ɗin ba?, ko kuwa an taɓa cewa bari Yusura taje masu koda hutu ne na ƴan kwanaki, ba dai tana nan waje na ba. Sai ni za'a ƙirƙiri wani karatun banza ace za'a zo gidana a zauna, tsabar salon a hanani zama da Mijina lafiya. Ƴaƴa sun zama gaddama-gaddama gasu nan sunma so su fimu jikin girma, suna jerawa damu, dole su zo su taya uwarsu kishi dani mana. Ita wannan marar kunyar Ummi mai ido a buɗe ai gani take ma dai-dai dani take, wannan ko haɗa miji nayi dake ai sai haka"
Ba wadda ya ƙara tanka mata dan su Ummi najin komai Salma ta hana ma Ummi ɗin maida hankalinta ga maganganun Aunty Murja da take ta zaro su kamar mi, sai zuba take kamar kanyar data lalace.
Baba kuwa ficewa yayi daga gidan dan idan ya ce zai zauna tsaf zai mata abunda bata tsammani, gara kawai ya fice dama lokacin sallar mangaruba tayi, dama sun shigo Kano bada wuri ba, wajan ƙarfe shidda suka shigo Kano.
Har Baba ya fice Aunty Murja na tsakar gida tana wasu ƴan kaye-kaye tana mita da surutu ita ɗaya. Itafa baƙin cikinta ɗaya an taho da Ummi, ta riga tasan bata isa saka Ummi abu tayi mata ba, da ace babu Ummi ɗin dole tasa Salma aiki tayi mata, kuma ta faɗa mata magana son rai bazata tanka ba, amma yanzu kam tasan ko Salma ɗin bata isa sakawa aiki Ummi ta bari ba, tasan wacece Ummi ɗin, bare yanzu da take ganin dai-dai take da ita, gani ma tayi ta ƙaro wani sabon iskanci, amma wallahi ta rantse bazata kyale ta haka ba, ai gidanta ta zo dole tayi mata biyayya........
PAGE 49
*SALMA POV*
Shigowa tayi cikin ɗakin tana zama a kusa da ita ta dube ta ce.
"Salma zaki iya tafiya ke ɗaya kuwa?, ko dai na zo na kai ki school ɗin?"
Da sauri Salma ta girgirza ma Ummi kai dan bata so taje ma school ɗin, dan wani abu daban da take tunani ta ce.
"A'a Aunty Ummi Allah zan iya, ai kinga jikin nawa da ƙarfi na tashi yau"
"Shikenan to bari naje na haɗa miki abun kari kamin ki tafi"
Tana binta da kallo ta tashi ta fita, jim kaɗan ta dawo dauke da wainar kwai da shayi sai biredi akai.
Zama tayi tana cewa.
"Ki cinye sai ki rage min nima na ci"
"A'a kisa hannu mu ci tare mana Aunty Ummi"
"A'a wai ina Yusura ne?"
"Yanzu ta tashi tana toilet ɗin tsakar gida, inaga wanka zatayi dan babu daɗewa nake jin tana waya da wadda zai aureta ne zai zo akan kayan lefen da za'a kawo jibi ne naji dai Aunty Murja na waya jiya da dare tana sanar da ƴan uwanta"
"Ohh waifa bikin bayan sallah ne ko?. Gashi har azumi saura ƴan kwanaki ma"
"Ai ko dai abun ba wahala Aunty Ummi"
"Amma gaskiya sun saka maku lokacin exam's da wuri, wasu fa har bayan sallah zasuyi graduation"
"Eh ai kin san masu graduation ɗin da yawa, wasu mafa har sunyi Habiba ke gaya min"
"Ku dai kunyi sa'a da aka saka maku ita da wuri,danmu fa lokacin da zamuyi tamu sai bayan sallah ne da sati kusan uku"
Salma zatai magana tana ɗan cin wainar kwan da Ummi ta soya mata tana korawa da shayin, biredin ma ba wani ci take ba, dan yanzu abincin ma kaɗan take samu taci, bata cin abu mai yaji ko mai tauri haka.
Aunty Murja ce ta ɗaga labulen ɗakin ta shigo tana wani riƙe ƙugunta tana hararar Ummi haɗe da cewa.
"Ohh ba shakka wallahi, har kin miƙe kinje kinyi ma ƴar uwarki abun kari, wato mu ko Ohoo ko?. To wallahi baki isa ba, fitowa zakiyi kije nima ayi min abun kari nida tawa ƴar tunda ba sassaƙa ni kukai ba"
Murmushi mai ciwo Ummi ta saki tana shirin miƙewa tsaye Salma ta kamo hannunta haɗe da girgirza mata kai.
A hankali tasa hannunta ta janye na Salma data roƙo mata nata tana miƙewa tsayen ta ce.
"Mu ai naga sassaƙamun ki kai ai ko?. Sana idan kin mance bari na tunatar dake Murja, bafa bauta ko aiki aka kawo mu muyi miki ba yawwa, na rako ƴar uwata ne domin tayi exam's ba dan haka ba ke kinsan babu uwar.....
"Haba dan Allah Aunty Ummi miye kike yi haka?. Mama fa ta ce ki daina irin haka idan muka zo. Mi yasa wai bazaki sassauta harshenki bane?"
"Ai kawai ki barta ta zage ni, dama ai raini na gidan duniya ta gama min shi, kuma na rantse da Ubangiji baki isa ba, dole ma ki fito kiyi min aiki, ai tunda kika saka ƙafa a gidan nan nawa to aiki ya zame miki dole shashasha kawai marar kunyar wofi"
"Nanfa ɗaya Murja, yafa isheki haka, karki ƙara zagi na, tunda banga abunda nayi miki ba. Aiki ne da kika fito tsakar gida baki ga an gyara gidan bane iye?, ko kuma so kike saina zo ina shelar nayi miki aiki?, tunda ga ƴar aiki kin samu"
Zata buɗe baki tayi magana saiga Yusura ta shigo ɗakin tana cewa.
"Haba Umma dan Allah, tunda sanyin safiya za'a fara jinmu a gidan nan. Nifa na ce mata tayi sharar gida ni zan dafa abincin kari"
"Dalla gafara can ki bani waje, kona mangare ki yanzun nan"
Aunty Murja ta faɗa ganin yadda ta zo ta tsaya mata akai.
Da sauri Yusura ta matsa tana turo baki ta ce.
"To ai Umma.....
Ɗaga mata hannu tayi haɗe da cewa.
"Kimin shiru bada ke nake ba. Kuma da kike cewa wai kece kika raba maku aikin, ya akai naga ita ta shige kitchen tayo ma ƴar uwarta abincin kari gasu nan a tare suna ci?, to wallahi bazai yiwu a rinƙa raba min abincin gida ba, ace a dafa wannan a dafa wancan ba"
"Ai dai nake ganin abinci dai Ubanmu ne ya kawo ya aje ko?, to dan haka wallahi duk abunda naga dama saina dafa shi ida.....
Rufe mata baki Salma tayi tana girgirza mata kai da sauri, duk da haka saida Ummi tasa hannu tana kauda hannun Salma data rufe mata bakin dashi tana ƙarasa maganar data ɗakko.
"To shikenan mu zuba nida ku shege ka fasa, wallahi ke dai-dai nake da iyayenku can da kuka baro, sunyi maku huɗubar zuwa domin dama kuzo ku hanani zaman lafiya ku kashe min aure ko?, to wallahi zama gidan Uban naku zama daram ba fita sai mutuwa, baƙi ciki kuwa sai dai ya kar iyayen naku"
"Mur.....
Tari ne ya sarƙe Salma wadda hakan ya hana Ummi idasa maganar data ɗakko zata maida ma Aunty Murja magana.
"Innalillahi mi ya faru?"
Yusura da Ummi suka faɗa a tare suna nufar inda take kusan a tare suka isa hankalinsu a tashe bare ma Ummi.
Dama tarin wasa ne tayi dan kawai Ummi tayi shiru,sai ta saki ajiyar zuciya tana sauke lumfashi ta ce.
"Ba komai, amma dan Allah kodan lafiyata kiyi shiru ki kyale ta haka nan, wallahi hayaniyar nan ta fara hawa mun kai. Yanzu idan Baba ya shigo ya iske ku a haka ya kike tunanin yadda ransa zai ɓaci?"
"Shikenan na daina sannu kinji, mi kike ji yanzu?, ko dai naje kawai nayi miki exam's ɗin?"
"Noo zan iya zuwa fa Aunty Ummi. Kuma kin san ai school ɗin nan yadda ake bada tsoron exam's, wani bai isa ya shigarma wani ba"
Wani mugun tsaki suka ji anja suka juyo a tare suna bin Aunty Murja data juya ta fice tana sakin tsakin.
"Dan Allah Aunty Ummi daga yau idan zaki dafa abu ki rinƙa dafawa gaba ɗaya, nifa ko kodama can bana son fitina da hayaniya please kin kuma fi kowa sani, shi yasa ma nake mata duk wani abu da take so dan kawai a rabu lafiya"
Salma ta ƙara faɗa.
"A'a wallahi Aunty Salma ni zanyi abinci harku tafi, ai dan ta kula dake aka taho da Aunty Ummi ɗin ba wai haka nan ta biyo ki ba"
"Yanzu dai tashi ki shirya na rakaki inda ake hawa napep can ƙofa"
"Kai Aunty Ummi har can?, ai da kin bari na tafi kawai babu komai fa ina jin sauƙi sosai fa a jikina"
"No kedai ki tashi ki shirya kawai"
Da to ta amsa tana miƙewa duk da ƙarfin hali take yi, dan idan ta miƙe sai taji wani luuuu kamar zata kifa a ƙasa, saita ɗan daɗe da miƙewar sana zata ji ɗan dai-dai, danma tana namijin ƙoƙarin ɓoyewa ba'a gane yadda take ji cikin jikinta, ita kaɗai tasan ya take ji.
Da kyar ta idasa shirin domin ko tsayuwar kirki bata so, idan ta cika tsayuwa jiri ne sosai take gani.
Shiryawa sukai a tare suka fito Yusura ta wuce kitchen tana ɗora abun kari. Aunty Murja na zaune a tsakar gida ta bisu da hararara, suna ji tana cewa.
"Kuma Yusura iya abincin mutum biyu zaki ƙara dafawa, ai su yau sunci nasu abincin safen, sai kuma wata safiyar wallahi"
Basu tanka mata ba suka fice Salma na girgirza kai tana mamakin halin Aunty Murja sosai, bazata taɓa sauyawa ba.
Kamin suje ƙofar gadon ƙaya sosai Salma ta gaji, amma bata nuna ba, har wata zufa take ji tana yanko mata a jiki, tana dai daurewa ne dan kar Ummi ta gane wani abu, dan idan ta lura da wani abu wallahi tasan yau sai dai asan yadda za'ai da exam's ɗin nan tata, dan tasan bazata bari taje ba, bare ma a sanar da Baba shima ba bari zaiyi ba, yanzu ma dan tana nuna masu taji sauƙi sosai shi yasa hankalinsu ya ɗan kwanta da taje exam's ɗin.
Waje ta samu ta ɗan zauna a bakin titi Ummi kuma na ƙoƙarin tare napep.
Wata Mota ce mai kyawun gaske tayi parking a inda suke. Da ɗan mamaki Ummi ke binta da kallo, tana ɗan matsawa kaɗan, ganin kamar tana son ture ta.
Ita ko Salma ganin farko ta shaida Doctor Nura ne. Ɗauke kanta kawai tayi tana jin kwata-kwata yau bata wani ji daɗin ganinsa ba.
Sai da ya zage gilas ɗin Motar sana Ummi ta shaida shi, danta sanshi a photo wajan Salma ɗin. Ɗan sakin fuskarta tayi tana shirin gaida shi, shi ya rigata miƙo gaisuwa, yana tsokarnarta ai shi ya kamata ya fara gaida ita, tana babbar yaya.
Murmushi kawai ta saki tana sake gaida shi ya amsa da murmurshi yana duban mutuniyar tashi yadda ta haɗe fuska.
Sosai ramar daya gani a tare da ita ta basa mamaki har akan fuska ya kasa daurewa ya ce.
"Yayarmu ni kuwa Salma lafiya take?. Naga ko magana bata san yi yanzu"
"Wallahi Doctor bata da ishashshiyar lafiya dama, exam's ɗin nan taso ce ma ta ƙarshe tasa dole sai munzo Kano, amma dai jikin nata da sauƙi ai yanzu ba kamar daba gaskiya"
"Subhallahi mike damunta ne haka?. Amma ni bata taɓa sanar da ni ba, duk da dama idan na kira ta bamu daɗewa a waya, saboda kamar bata son magana kwata-kawata dole take sawa nayi mata sallama"
Taɓe baki Ummi tayi tana jin haushin Salma. Yanzu fisbilillahi ga mai sonta tsakani da Allah sosai yake ƙaunarta, yana bata kulawa, amma ace mutum yaje ya maƙalema wadda kwata-kwata hankalinsa baya gareta.
"Ai da yake kasan rashin lafiyar tata ce ta koya mata rashin son magana"
"Tom Allah ya ƙara lafiya, bari na rage mata hanya ko?, naga har yanzu baku samu napep ba"
"Ai ko damun gode wallahi dama waje nata ƙurewa karta makara"
Kamo hannun Salma tayi tana sakata a gaban Motar ta lura sai turo baki take ita dai Ummi bata damu ba tayi masu bye-bye ta tsallaka tana komawa gida, su kuma yaja mota suka wuce.
Dubanta yayi yana juya sitiyarin Mota ya ce.
"Ranki ya daɗe wai laifi nayi ne?"
"Uhum uhum"
Kawai ta faɗa tana kauda idonta gefe tana kallon hanya.
"Ban yarda ba gaskiya, idan ma nayi ban sani ba to amin afuwa gimbiya"
Murmushi ta ɗan saki yadda yayi maganar harda haɗe hannunsa waje ɗaya.
"Ba abunda kamin fa Allah, kawai bana son yawan magana ne shi yasa ai Aunty Ummi ta sanar da kai"
"Hakane, amma ko zan iya sanin wane irin ciwo ne haka daya ramar mun dake, ko zan iya taimakawa da gudunmuwa ta please"
Sauke ajiyar zuciya tayi, ai ko zatai hauka bazata sanar dashi ainafin abunda ke damunta ba wallahi.
Zata buɗe baki tayi magana suka ƙaraso ƙofar get ɗin shiga makarantar. Wata hamdala ta saki tana cewa.
"Lokaci ya ƙure min ni zan shiga school, amma ciwon da nayi ba wani ciwo bane zazzaɓi ne kawai"
Tana faɗar haka bata jira jiran abunda zai ce ba, tayi saurin ɗaukar Jakarta tana ɓalle murfin Motar ta fice. Tabar Doctor Nura da binta da kallo yana sauke ajiyar zuciya. Tabbas yana son Salma, amma ita ce take ƙin basa damar ya nuna mata irin son da yake mata........
PAGE 50
"Hello kina jina Asma'u?"
Ammi ta ɗan gyara zamanta tana taɓe baki kamin ta ce.
"Inna ina jinki"
"To shine ina magana ki kai banza da ni?"
"To Inna mi zan ce?, nifa gaskiya Inna kiyi hakuri bazan iya ma Muhammed magana ba"
"Ikon Allah, yanzu Asma'u maganar da kawai zakiyi masa ya taimaka ya samarma Sadiya irin Makarantar da su Salma keyi shine bazaki iya ba?"
"To Inna miye haɗina da ita?, dan Allah Inna indai Maganar Sadiya ce a daina kira na, ko a saka ni ciki da Allah"
"Yanzu Asma'u baki ji kunyar faɗa min hakan ba?. Kawai ki ce bazaki masa magana ba, saboda anyi maganar maƙiyiyarki ko?"
"Inna abu ɗaya zan iya maku shine na turo maku number ɗin shi Muhammed ɗin ku kirasa da kanku kuyi masa maganar"
"Shikenan hakanma yayi, ina jiranki"
"Tom shikenan"
Ammi ta faɗa tana kashe wayar.
Safiya dake zaune a kusa da Ammin ta ce.
"Ammi miya faru kuma?"
Ammi ta ƙara kicin-kicin da fuska ta ce.
"Ni da Inna ne mana. Wai akan wannan tsintacciyar aka kira ni, wai nayi ma Muhammed magana tunda shi ya samarma su Ummi makarantar da suke yi, itama dan Allah yayi mata hanya wajan samunta"
"To dole ne ma sai tayi karatun wai, nifa shi yasa gara da Baba bai matsawa idan zakiyi to kanka, idan ma baza kayi ba kanka"
"A'ato su sunce sai tayi, kilbibi ne yanzu haka irin na ita Sadiyar"
Taɓe baki suki Safiya tayi tana ɗaga kafaɗa.
*SALMA POV*
Tunda ta shiga school ɗin take baza ido ta inda zata hango Habiba.
Ganin waje na ƙurewa yasa Salma ɗaukar wayarta dake cikin school back ɗinta ta soma kiran wayarta.
Tana ɗauka sai kuma taji kamar muryarta a kusa da ita. Da sauri ta juya bayanta ganinta gaf da ita yasa Salma sakin murmurshi haɗe da hararar Habiba ta ce.
"Ƴar rainin wayo, kina kusa shine sai kin ɗaukar min kira?"
Habiba ta ɗan saki murmushi tana kamo hannun Salma ta ce.
"Salma kinyi rama da yawa wallahi, wai wane irin ciwo ki kai haka please?"
Habiba ta faɗa tana ƙare mata kallo sosai da mamakin ramar da ke jikinta da kuma tausayinta.
"Wallahi fa zazzaɓi ne kullum dashi nake kwana nake tashi"
"Ikon Allah wane irin zazzaɓi ne haka mai nacin tsiya?. Allah dai yasa ya tafi kenan, ya barki ki idasa exam's ɗin nan ƙalau"
Da amin kawai Salma ta amsa tana canza maganar wajan cewa.
"Wane hall ne muke exam's ɗin wannan karan?"
"Wadda dai mukai a first semester shine wannan ma aka kafe mana a can"
"Mtsww wallahi bana son exam's cikinsa, Malamai sun fiye shigowa ciki, kowanne Malami sai kiga ya lallaɓo fa"
"Ai gani suke yayi ƙarami da yawa hall ɗin, kuma hanya ce idan suka biyo sai su ce dole sai sun shigo"
"Yanzu dai mu tafi hall ɗin naga time ya kusa baifi saura minti biyar bama"
"Eh gaskiya muje kona samu na ɗan ƙara duba karatun da nayi. Wai ni ko ina Mlm Jamilu ne mutunen naki?"
Wata ajiyar zuciya Salma ta saki jin yadda zuciyarta ta motsa kiran sunansa da kawai akai.
"Ina tabbayarki kinyi shiru?"
Habiba ta faɗa dai-dai shigowarsu hall ɗin da suke exam's suka samu waje suka zauna a gaba.
"Mi zan ce miki to ni kam?"
"Hmm