Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   36 / 36

105K to 106.4K   out of 106.4K words

da zasu shiga gaba ɗaya su Fu'at na parlon Mommi basu daɗe da gama breakfast ba suma.

A nan suka shiga gaida Abbey da kuma Ummi. Ummi har ƙasa ta duƙa ta gaida Mommi, kuma hakan da tayi sai ya bawa su Fu'at mamaki, sai kuma suka fara ganin girmanta, tunda har tana girmama Mahaifiyarsu.

A nan ta zauna suka ci gaba da fira, a nan ta ƙara lura da yanayin zamantakewar gidan cike da ilimi da tsantsar wayewa ake rayuwa a gidan, dan yanzu ma zaune yake a tsakiyar su Fu'at suna labari yadda kasan abokin wasansu ne, suna basa labari shima yana biye masu harda su Aftihal a nan kowa idan yana buƙatar wani abu yake gaya masa, nan take kuma zai baka, ana raha ana dariya.

Sai da rana ta take sana Ummi ta koma part ɗinta har Hanan na biyo ta suka nufi part ɗin nata suka ci gaba da firarsu.

Sati ɗaya Mommi tayi tana masu abinci, daga nan kuma Ummi ta fara nata abincin a part ɗinta, sosai suke zaune lafiya kamar ba kishiyoyi ba, sai abunda ba'a rasa ba, wani abun ta ciki na ciki kowanne daga cikinsu na ƙoƙarin dannewa, kuma kullum safiyar duniya sai Ummi taje gaida Mommi. Yadda take sakar ma su Hanan fuska da komai nata yasa Aftihal itama fara shige mata, da sai dai Hanan kaɗai ke zuwa, ita kam sai ta koma gefe kamar mai taya uwarta kishi, amma ganin Ummi ɗin bata da damuwa itama ko kaɗan gashi taga yadda take ma Hanan ai sai itama ta fara zuwa inda take, sosai kuma Ummi tayi farin ciki, dan sai suka koma kamar ƙawayenta.

Zaune Ummi take suna waya da Maryam akan dan Allah ta daure ta zo mata yau man, gashi har sati biyu da aurenta amma ko ƙeyarsu bata sake gani ba.

Har Habiba ma ta kira tana mata tsiyar sunƙi dawowa.

Maryam ta shiga sanar da ita cewar wallahi tayi haƙuri jiya ne aka tsaida ranar aurenta da Mubeen harma yau zasu kawo lefe dan yanzu hakama aiki kawai suke da Umma na tarbar baƙin.

Sosai Ummi taita faɗan bata sanar da ita da wuri ba.

Maryam ta shiga bata baki tana ce mata ita dake amarya ai an barta ta shaƙata ta huta ai ko?.

Nan fa ta rinƙa tsokanarta suna fira cike da wasa da dariya.

Tana gama waya da Maryam ta kira Yusura itama suka sha fira sosai kamar bazasu daina ba.

Tana gama wayar da ita ta fara neman number Safiya itama.

Saida ta kutsa tsinkewa kamin Safiya ɗin ta ɗauka, bata wani sake da Safiya sosai ba, saboda yadda ta fara kamar gaya mata wasu maganganu marassa daɗi yasa Ummi kawai sallama da ita, tana mamakin hali irin na Safiya.

***********A wajan su Sadiya da Ya Umar ma dake can garin Abuja, tun Sadiya na noƙewa taƙi yarda da cewar wai Ya Umar ne mijinta, kai har dai dole ta yarda saboda Ya Umar ganin haka yasa ta dole ta yarda a lokacin daya mayar da ita babbar mace kuma matarshi ta sunna, sosai yake koyar da ita sabon karatun da bata saba dashi ba, wata irin soyayya yake nuna mata wacce tasa Sadiya mancewa da duk wata damuwarta sai shi kawai, kuma a hankali a hankali ta fara sonshi sosai. Ganin yadda hankalinta ya kwanta yasa Umar ɗin fara nemar mata makaranta ta fara karatunta cike da kwanciyar hankali.

A kowanne ɓangare suna zaune lafiya, sai dai wasu hassadarsu ta kasa ɓoyiwa, bare ganin yadda Ummi cikin wata ɗaya da aurenta ta koma kamar wata wacce aka sauya ba Ummin da suka sani ba, dan su Aunty Murja sai da suka tako ƙafa da ƙafa suka zo gidan Ummi suka sha kallo, suka kuma sha abun arziƙi, suka tafi da abun arziƙi da mamaki mai kashe zuciya.

Hatta Ammi dake Rimaye ma ta zo ita da Mama ganin ɗaki sunsha sha tara ta arziƙi a ranar, dan sosai Mommi ta tarbesu ita da Ummi, sosai kuma Mama ke farin cikin yadda taga ƴarta zaune lafiya a gidanta tare da abokiyar zaman nata, ga ƴaƴanta manya data gani sosai ke bawa Ummin girma babu raini a tsakaninsu.

Su Aunty Binta ma an sake zuwa, tun tana jin zafi da haushi a ranta, kai harta saki makaman yaƙinta dan yanzu kam tasan na gaba yayi gaba, dan yadda taga suna tafiyar da rayuwarsu a gidan Ummi ɗin dole ne koma waye ya bashi sha'awa.

Hatta su Aunty Murja tuni aka zubar da makaman yaƙi sai nan-nan ake da Ummi ganinta da abun duniya, abu kaɗan dai an kira Ummi ana neman shawara wajanta ko wani abu, sosai kuma take kyautatama ƴan uwanta daga abunda take samu daga mijinta.

Wata biyu da aurensu Ummi ta samu ciki, zo kuga murna wajan Jamilu dama dukkanin ƴaƴansa bare ma matan su Hanan addu'a suka rinƙa yi Allah yasa a haifar masu mace.

Mommi ma sosai take bata kulawa kamar ƴar cikinta ba kishiya ba.

Su Maryam sun sake zuwa a inda Habiba da zata zo itama ta taho da wata ƴar school tasu a nan fa tasha kallon yadda Ummi ta koma da yadda ake zuba life a gidan Mlm Jamilu, sosai abun yayi mugun birgeta, ai ko ta koma school aka buɗe shafin fira ko ina aka zauna maganar ake.

Ummi kuwa da Mlm Jamilu soyayya ake zubawa ruwa-ruwa kamar ba gobe, kullum ƙara son junansu suke, suna rainon cikin Ummi daya fara wani irin girma sosai har suna mamakin girman nashi.

Ranar da Salma ta cika shekara ɗaya da rasuwa a ranar Ummi ta sauka lafiya ta haifi ƴan biyu duka mata.

A ranar karku so ganin yadda ahalin familyn Jamilu S Muhammed suka shiga farin ciki marar misaltuwa, sosai suke murna da haihuwar da Ummi tayi lafiya.

Sosai kuma aka kashe kuɗi akai abinci na addu'ar da akasa akaima Salma ta shekara da rasuwarta.

Nan take kuma Jamilun yayima yaran huɗuba ɗaya aka saka mata suna Salma, ɗayar kuma aka saka mata sunan Saratu sunan Mommi kenan.

Sosai Mommi ke farin ciki da karar da akayi mata, Ummi ma sai murna take da sunayen daya saka masu.

Amma za'a rinƙa kiransu da sunansu na Hassana da Husaina.

Ranar suna fa su Aunty Murja kwansu da kwarkwatarsu suka taho, hatta Safiya ta zo dake ɗauke itama da ƙaramin ciki, Yusura ce dai cikinta yayi girma sosai dan da kyar take iya komai amma a haka ta zo sunan Ummi.

Su Maryam Iyayen ƴaƴa kuwa ba'a nan ba'a can sai hidima kawai ake ana tarbar jama'a.

Anyi taron suna an gama lafiya. Yaran Ummi rainonsu rabi da rabi su Aftihal ne ke yi mata shi, sosai suke ƙaunar Ƙannan nasu kamar zasu maida su ciki.

Su Fu'at ma ganin yaran masu kyau kuma masu kama dasu gasu tunda Ummi ta fara shayar dasu suka fara tawa ƙiba ƴan kuɓul-ƙuɓul abunsu gwanin sha'awa ga daɗin ɗauka yaran, akwai shiga rai, ko ina aka je dasu har rige-rigen ɗaukarsu ake.

Haka rayuwa ta rinƙa tafiyar masu cike da farin ciki da son juna a family ɗin JAMILU S MUHAMMED........

*END*

*ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH*

*Duka-duka a nan na kawo ƙarshen wannan book nawa, kuskuren da nayi ciki Ubangiji ya yafe min. Darasin dake ciki Ubangiji ya bada Ikon anfanuwa dashi. Abunda na manta ban saka ba a wannan littafi please ayi min uzuri, an san ɗan Adam da mantuwa, kuma sana iya abunda Ubangiji ya hore min rubutawa kenan*

*SADAUKARWA*

*Na sadaukar da wannan book ɗin gare ka JAMILU S MUHAMMED, Alkhairin Allah ya kai maka a duk inda kake, wannan book naka ne kayi yadda ka so dashi. Sai kuma masoya a duk inda masoya suke suma wannan book ɗin sadaukarwa ne gare ku*

*ki biya ko ka biya ka karanta ƴar uwa ko ɗan uwa ɗari biyar ne kacal #500*

*ban yarda ba ban amince a sauya min labari ta kowacce irin siga ba sai da izini na, dan haka a kiyaye*

*ina ƙaunarku a duk inda kuke masoya Zahra Royal Star I LOVE YOU LODI-LODI*

PHONE NUMBER DOMIN ƘARIN BAYANI......08130479973.

36 / 36