Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   5 / 36

12K to 15K   out of 106.4K words

tana cire abunda tasa a kunnanta tana ɗan sauraron karatun Alkur'ani mai girma na Ahmed sulaiman.

"Aunty Ummi lafiya na ganki fuska a murtuƙe?"

Zama Ummi tayi akan gadon tana sauke lumfashi ta dubi Salma haɗe da taɓe baki tana kallon wayarta dake a gefen Salma ta ɗakkota tana jujjuyawa kamin ta kuma ajeta ta ce.

"Ina Kankia da muka je jiya nan?"

"Yeah mi ya faru da muka je ɗin?"

Taɓe baki ta ƙara yi kamin ta kamo hannun Salma ta ce.

"Wai fa matar da muka je ma biki ƙawar Mama ce ta ganni wai tayi ma ɗanta Mata wai ni"

"Kai Masha Allah amma wallahi naji daɗi, saboda naga duk gidan basa da matsala"

Wani kalar kallo Ummi tabi Salma dashi tana sakin hannunta ta ce.

"Ke fa daɗi na dake bakya ganewa wallahi"

"Yanzu Aunty Ummi miye abunda ban gane ɗin ba?"

"To an gaya miki ni zan amince ne na auri wadda ban sani ba?"

"Kashhh Aunty Ummi haba dan Allah ai nasan dole zaku san juna ko?, ku kuma fahimci juna, kamin a dai-daita komai ayi musha biki"

Hararar wasa ta ɓalla mata ta ce.

"Ko kaɗan bana son irin auren haɗin nan wallahi ni, bana ƙaunarsa kwata-kwata kin riga da kin san hakan kuma. Ke zaki iya fahimtata akan Mama, saboda Mama wani lokacin bata son abunda nake so ba da wadda bana ra'ayi, munfi zama dake sosai a waje, kece zaki iya fahimtata sosai. Ni kawai nafi so shi da kansa ya ganni da ra'ayin kansa ya ce yana son nawa ba wai a cusa masa ni ba gaskiya"

"To ai nasan an nuna masa photonki, kuma babu ɗa Namijin da zai ganki yayi saken ki kuɓuce masa"

"Hmm lallai kam Salma baki san so ba, shi ai babu ruwansa da kyau ko wani abu, zaki iya ganin banyi masa ba, ko kuma nima baiyi min ba"

"Hhhh Aunty Ummi kema fa ba so ɗin nan kika sani ba gara ma ni ina soyayya kaɗan-kaɗan, kefa baki san komai game da ita ba wallahi, saboda baki taɓa cewa yau ga wadda kike so ba"

Shiru Ummi tayi tana jawo wayarta dake kusa da ita ta ɗan kwanta tana kunna data ta hau WhatsApp.

Duk da kwana biyu bata hau ɗin ba. Tana hawa kuwa messages suka kama shigowa kamar ana hankaɗosu.

Tsaki ta saki a fili ta furta.

"Aikin banza"

"Da waye ake kuma?"

"Mtswww da mutanen dake min messages ta Whatsapp mana, kinga messages kuwa sunfi gudu ɗari"

"Duk masu dakwan son naki ne, ni ai da zasu ji shawara da sun daina wahal da kansu a banza, dan banga alamar a nan kusa zaki so wani ba"

"Lokaci na zuwa ne yarinya"

"To Allah dai karya kashe ni ya nuna min wannan miji naki"

"Hmm amin to"

Faɗin Ummi tana shiga wani message daya ɗauki hankalinta.

Tana shiga ta karanta message ɗin abunda ya ƙunsa zuwa can da sauri ta ɗan tashi zaune tana sakin ɗan murmushi kaɗan haɗe da girgirza kai.

"Hmm Allah sarki bawan Allah nima wallahi kwata-kwata bakai min ba, gara kaje can ka auri wacce kake so ɗin sai ya fi maka kawai"

"Wai ke da waye Aunty Ummi?"

Aje wayar Ummi tayi haɗe da faɗin.

"Wadda aka bawa number tane Al'mustapha yake koma waye?. Shine naga message nashi wai yana cewa ya ga photo na nayi masa kyau gaskiya, wai harda ba laifi nayi sosai, ni macece son kowanne ɗa Namiji, amma dan Allah dan Annabi naje na ce ma su Mama ban masa ba"

"Kai yo saboda mi?, shi ya turo miki photon nashi ne kin gansa?"

"Eh ya turo min yanzu gaba ɗaya ma. Kawai ya ce min ne shi yana da wacce yake so, wai yarinyar ta kirasa data samu labarin Mahaifiyarsa tayi masa mata sai kuka take masa, shi kuma ya rantse duk duniya ita ce yake so, na taimaka masa ya sami wacce yake so"

"To faaa"

Cewar Salma tana riƙe baki.

"Nifa kinga ko shi yasa bana son irin wannan haɗin na iyaye da suke ma ƴaƴansu, mi yasa baza'a bar mutum ya zaɓi abunda yake so ba kuma yayi masa?. Ki duba ki gani kai tsaye ya ganni ya ce banyi masa ba, shine fa yasa bana son irin haka ni, yanzu gashi anje an haɗa wannan kwamacalar mtswwww"

"Yanzu dai Aunty Ummi muga photon nashi"

Tsaki ta ƙara saki tana miƙa mata wayar bayan ta kamo photon nashi.

Kallon photon Salma tayi tana maida mata wayar akan cinyarta kamin ta ce.

"Na ganshi ba laifi dai kam"

"To ni duk da hakan baiyi min ba, kwata-kwata a tsarin rayuwata bana son namiji mai ƙiba, shi kuma ƙibarsa ma ta so ta fara yawa. Ke koda ya kai na so shi to wallahi zuciyata zanyi iya yina wajan yaƙi da ita akansa, bare dama ni zuciyar tawa bata son daɗin so ba bare zafinsa, dan haka zan sanar da Mama abunda ke faruwa kawai"

"Amma Aunty Ummi sanar da Mam...

Ɗaga mata hannu Ummi tayi tsafff ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin fita sai ga Mamar ta shigo ɗakin suna waya da ƙawar nan tata Salamatu daga jin yadda suke wayar sun san ita ce.

Tsayawa kawai Ummi tayi bayan sun gama wayar Mama ta kalli Ummi ta ce.

"Yanzu muka gama maganarki keda Al'mustapha da Mahaifiyarsa, ta gaya masa komai har number ki ta bashi, kuma a yadda ya ce mata gaskiya kinyi sosai"

"Mama amma abunda ya faɗa mata kenan kawai?"

Wani kallon zargi Mama ta farama Ummi da yasa Ummi ƙasa da kanta, kamin ta sauke ajiyar zuciya ta ce.

"Mama bafa wani abu bane, nima yayi min magana, amma abunda ya ce min ni daban"

"To miye ya ce miki, kar dai kin gama rushe komai muna nan sake da baki?"

Mama ta faɗa ranta na soma ɓaci.

"Kiyi hakuri Mama amma cewa yayi shi yana da wacce yake so, dan Allah na taimakesa na ce maku baiyi min ba, dan yanzu haka yarinyar da yake so ɗin tana kwance a gadon asibiti wai duk saboda taji ance anyi masa mata"

"Shi Al'mustaphan ne ya faɗa miki hakan?"

"Shine Mama kuma ga Salma nan ai ta karanta duk message ɗin daya turo min"

"Ke kuma kika ce masa mi?"

Sosa kanta Ummi tayi cike da ƴar fargaba ta ce.

"To nima Mama ce masa nayi nima ina da wadda nake so, danma karya ɗauka ni ke son nashi, kuma na ce masa zan taimakesan"

Saura kaɗan Mama ta ɗauke Ummi da wani mari tayi saurin tashi daga inda take tana matsawa a zabure.

"Mamaaaa!!"

Salma ta faɗa da mamaki.

Ummi ma ido waje take kallon Mamar.

"Kinyi abunda kike so ba?, kinji kuma daɗi, to ba komai, amma ki sani wallahi na kusa bar maku gidan Ubanku, tunda naga ku duka baku da hankali da tunani. Yaya za'ai nayi ta jerawa daku kun girma kunma so ku fini girman jiki, kun kai milzalin aure amma sai shashashanci kawai da kuka sani da shirmen banza da wofi"

"Amma Mama kina fa ji na ce miki shine ya fara ce min hakan in...

"Dalla gafara can kiyi min shiru na ce. Ai duk kina sane kika lalata komai, saboda dama koda na faɗa miki zancan baki wani nuna farin ciki ba, dama nasan zaki aikata hakan. Ai ita Mace idan ta so wallahi koda namiji ya faɗi haka nan zata saka shi ya canza ra'ayinsa akanta, bare ke kina da kyanki da dirinki tuni zaki canza masa ra'ayi ya mance da duk wata Mace, amma ke da yake shashasha ce baki iya komai ba sai shirme da baƙar zuciya"

Hawaye ne suka fara zubo ma Ummi da sauri Salma ta koma ta tana murza mata hannu alamar tayi shiru.

Mama kuwa ta inda take shiga bata nan take fita ba, sai faɗa take kamar zata cinye Ummi ɗanya, ji Ummi tayi dama bata aikata hakan ba, saboda irin yadda Mama keta faɗa tana ƙara mai-maita abu ɗaya, sai mita take tana ƙarawa kamar baza tai shiru ba........

*Wannan book ɗin na kuɗi ne Free pages zai tsaya daga na 10 insha Allah, zaki iya saka kuɗinki a turo miki complete nasa akan Naira ɗari biyar kacal #500*

Account number 8130479973 Fatima Rabi'u Opay Bank.

Shaidar biya 08130479973

*MUGUN ICCE*

*©Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSO.......*

PAGE 10

"Aunty Ummi dan Allah ki daina kukan nan haka nan please"

Ɗago da idonta tayi tana duban Salma dake lallashinta zaune a kusa da ita ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce.

"Why Mama zata rinƙa min haka ne?, shin su zasu zauna min da ko waye ma?, nifa zan zauna dashi, to mi yasa baza'a kyale ka, ka zaɓi wadda ranka yake so ba?"

"Kinga kiyi shiru dan Allah karta jiki ma"

Girgirza kanta kawai Ummi tayi tana saka bayan hannunta ta shiga share hawayen dake mata zuba, tana sharewar wasu na sake zubo mata, saboda yadda wani malolan baƙin ciki daya tokare mata wuya.

Suna jin Ya Muhmd bayan anyi bangaruba ya shigo gidan, bayan sun gaisa da Mama ta zauna ta fara bashi labarin yadda akai.

Daga can suna jin yadda yake cewa.

"Yanzu tsakani da Allah Mama haka yarinyar nan taje tayi shirme haka?, miye yake damun Ummi ne haka?, anya Mama wannan ƴar taki bata da ɗauke da Aljanu a jikinta kuwa?"

"Uhmm waye ya sanar mata ma, ai dole kuwa na miƙe da addu'a akanta wallahi yarinya sai ka ce wacce iska ta aura"

"Ke Ummi zo nan"

Ya Muhmd ya kwaɗa ma Ummi kira.

Turo baki Ummi tayi tana miƙewa ta nufi parlon fuskar nan a murtuƙe ta ƙaraso tana zama a ƙasa kanta a ƙasa.

"Yanzu abunda kikai ya dace kenan Ummi?, Mata da yawa na so su samu irin damar da Allah yake baki amma basu samu ba, sai ke kin samu shine kike yadda kike so kika ga dama ko?"

"Nifa Ya Muhmd bafa haka bane"

"Dalla gafara nan da anyi mata magana ai dama bakinta baya iya shiru, dole saita sami abunda zata kare kanta dashi, sai shegiyar gardamar tsiya irin wacce sukai gado wajan Mahaifinku da taurin kai"

"Yanzu dai Mama dan Allah kiyi hakuri komai zaiyi dai-dai"

Ya Muhmd ya faɗa dan yaji an fara sako maganar Baba a ciki, shi kam baya son hakan, bawan Allahn da yana can yana neman masu na rufa asiri, baima san halin da ake ciki. Sai dai kamar yadda Mama ta faɗa Baba yana da taurin kai magana ɗaya yake a rayuwarsa komai ya yanke kuma ya yanko, baya taɓa sauya ra'ayinsa sai wani abu daga Allah.

"Mama kiyi hakuri amma shi komai lokaci ne, idan har lokacin aure na yayi dole ne zanyi shi amma kiyi hakuri dan Allah"

"Ni zaki zauna kina faɗa ma aure lokaci ne?, tun kan kizo duniya nasan da cewa lokaci ne bari kiji na gaya miki, ni dai na gama magana ta, idan har baku fitar da Miji ba to tabbas zan bar baku gidan nan, sai ku zauna ku jera da Mahaifin naku"

"Haba Mama kuma mi ya kawo barinki gidan nan?"

"Kaga Muhmd dole ne na ce haka, baka san yadda uwa take ji ba idan har ta buɗe ido taga ƴan mata riɗa-riɗa a gabanta babu miji babu mashinshini, bare su bafa mijin suka rasa ba, kawai tsabar ruwan ido ne da kuma iskanci da wasa da damarsu da suke yi. Wallahi dai na faɗa maku wata damar a rayuwar nan sau ɗaya take zuwarma mutum, kamin taje ta dawo sai mutum yayi danasani Allah ya gama nuna masa kuskurensa kamin ya dawo maka da damar, damar ma da bata kai wancan ta baya daya baka ba wallahi, kuyi ma kanku karatun ta natsu, na dai gaya maku"

Babu abunda Ummi ta iya faɗa dan ita kam yanzu bata da bakin magana idan ta ce zata yi to tabbas ranta ne zai ƙara ɓaci.

Tashi tayi a hankali ta shige ɗaki, tana zuwa ta zube akan gado tana saka hannuwanta biyu tayi tagumi dasu.

Ji tayi an saka hannu an cire mata tagumin da tayi a hankali.

"Ki daina tagumi babu kyau kin sani Aunty Ummi"

"Hmmm abun nan ne na Mama na damuna, banma san nayi ba wallahi. Shin wai Salma mune kaɗai mukaƙi auruwa ne a duniya, duka shekararmu nawa ne ma a yanzu wai?"

"Eh to duka bazamu wuce 25 ne inaga ni ce ma mai 24 ko?"

"Uhm kamar zamu kai. Amma wasu ma ai sun wuce hakan, kuma suna zaune a gidansu babu kyara ko tsangwama, amma sai mu kullum cikin damuwa akan aure kawai haba, wani fa baida ma rabon yayi auren a cikin rayuwarsa"

"Subhallahi Aunty Ummi insha Allah ma zamuyi ma, ai ni rayuwar nan idan babu aure a cikin rayuwarka miye amfanin rayuwar ma, gara mutum kawai ya koma ga Allah shine yafi masa alkhairi. Nifa gaskiya Aunty Ummi ina so nayi aure kamar yadda Mama take so, ni nama fita son muyi auren nan mu tashi daga gidan nan wallahi bata san yadda nake kuka a gaban Allah akan ya fiddo mana da miji ba"

"Uhmm nima wallahi Salma ina so nayi kawai dai duk wadda zan gani sai naga bai dace dani ba, ko kuma sai naga wata matsala a tattare dashi"

Ɗan miƙewa sosai zaune Salma tayi tana runtse idonta kamin ta buɗe su akan Ummi ta dafa Ummi ta ce.

"Ummi a gaskiyar magana kina da matsala kiyi hakuri zan faɗa maki. Kowa aka kawo miki sai naji kince baki so, ni ina mamakin hakan fa, da ace ni ce a matsayin ki da yanzu nayi aure na, kin fini farin jinin samari, amma ke kowa baki so why dan Allah?, ki tsaida hankalinki waje ɗaya dan Allah ki fitar da mutum ɗaya wadda hankalinki ya ɗan kwanta dashi"

"Ai har yanzu Salma babu shi wallahi, babu kwata-kwata har zuwa yanzu banji wani mahaluƙin daya kwanta mini a rai ba bare har na fara jin soyayyarsa a cikin raina, yaya zanyi ne?, ya ake so nayi?, ko so ake naje na fiddo wadda zanyi dana sanin auren gaba ɗaya?"

"Noo ba haka nake nufi ba, ki natsu kawai ki zaɓi ɗaya kiyi addu'ar zaɓin Alkhairi akansa"

Zamewa kawai Ummi tayi ta kwanta akan gadon da suke zaune tana jin wasu zafafan hawaye na bi mata gefen fuska, damuwa ce da wani irin ƙunci suka taru sukai mata dabai bayi, yaya ake so tayi ne dan Allah?........

*To Masoya a nan na kawo ƙarshen Free pages. Ba'a kamo zaren labarin ba, ba'a fiddo da wasu taurarin ba har zuwa yanzu, akwai sauran karatu sosai a nan gaba. Kai dai kasan alƙalamina baya rubutun banza. Shin wai su Salma zasu aure ne kuwa?, idan ma sunyi wacce irin rayuwa ce zasu faɗa bayan auren?. Shin ina labarin Sadiya ne da Babban Yaya Umar?, su ai har yanzu bamu ma san inda labarin nasu ya dosa ba, zan so sanin nima kaina inda book ɗin nan zai zo ƙarshen zan so naga hakan........*

*Wannan book ɗin na kuɗi ne Free pages zai tsaya daga na 10 insha Allah, zaki iya saka kuɗinki a turo miki complete nasa akan Naira ɗari biyar kacal #500*

Account number 8130479973 Fatima Rabi'u Opay Bank.

Shaidar biya 08130479973

PAGE 11

*UMMI POV*

Taɓa tan da akai ne yayi sanadiyar katse tunanin data zurma. Wata ajiyar zuciya ta sauke tana ɗan miƙewa zaune a hankali.

Ganin rana ta take sosai yamma na shirin kutso kai yasa Ummi ɗan mamakin daɗewar da tayi tana wannan tunanin na rayuwarsu ta baya.

"Kina ji ana miki magana wato ki kai banza da Mutane?"

Turo baki tayi tana ɗan yamutse fuska ta ce.

"Yi haƙuri Mama banji bane"

"Yayi kyau ai sai ki tashi ki ɗora tuwon dare ga Amminku can ta shigo ta ce ta gama haɗa miki komai"

Mama na faɗar haka ta gishin giɗa akan kujera tana kallon Ummi ɗin.

Bata ce komai ba ta miƙe jikinta a mace tana ficewa daga ɗakin ta nufi tsakar gidan.

Tana fita ta iske Ammi na ƙoƙarin tankaɗen garin tuwon tana ganinta ta aje haɗe da cewa.

"Kina ina tun ɗazu nake ta faman kwala miki kira?"

Ɓata fuska Ummi tayi ta ce.

"Bacci ne ya ɗauke ni"

"Yayi ƴar hutu, ai kin bari sai kinje naki gidan har kike da ikon kwanciya a tsakiyar ranar nan dake neman faɗuwa sai ki huta a can ɗin, amma nan dai hutu ai ba naki bane yarinya"

Ummi ta rasa mima zata ce ma matar nan, amma sai ta shinye baƙin cikin data ƙunsa mata tana amsar tankaɗen ta ci gaba.

Ganin zata fara mata surutun da zai iya sata ta gaya mata maganar da bata shirya ba yasa ta miƙe ta koma ɗaki haɗe da ɗakko wayarta da abun kunne ta kunna karatun Alkur'ani mai girma ta doɗe dashi bata iya jin komai sai karatun.

Ammi data saki baki tana kallonta zuwa can ta saki murmushi kawai tana miƙewa ta bata waje.

Bin bayanta Ummi tayi da wani kallo tana sakin tsaki ciki-ciki a hankali ta furta.

"Munafuka kawai"

Ta ci gaba da aikin nata.

*House No 26, Gadon ƙaya, Kano State Nigeria*

"Wai ance ana sallama da Salma"

Cewar wani matashin yaro daya shigo gidan.

Wuff Aunty Murja tayo waje daga cikin ɗakinta tana kallon yaron haɗe da kamo hannun yaron kamar zata tambayesa abun kirki ta ce.

"Kai waye yake kiran nata a wajen?"

Ta faɗa a hankali dan bata so ma su Yusura ko Salma suji wani ya fito.

"Wani mutum ne tsaye a jikin wata Mota"

Riƙe ƙugunta Aunty Murja tayi haɗe da riƙe baƙi da ɗayan hannunta tana jinjina kai kamin ta ce.

"Jeka ka ce gata nan zuwa"

Yaro ya juya ya fice.

Ita kuma ta dubi ɗakinsu Salma ɗin kamar zata shiga sai kuma ta fasa tana komawa nata ɗakin haɗe da sanyo Hijabi da sauri ta nufi ƙofar gidan da kanta.

Sakin baki tayi

5 / 36