Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
ta fita zuwa kiran da Ammi tayi.
"Hmm jin zafi ne fa da hassada kawai ke kawo haka Allah dai ya kyauta"
Habiba ta faɗa itama tana miƙewa ta sake cewa.
"Bari nayo wankan muma mu fara shiryawa tunda amarya ta fara ɗaukar nata wankan"
"To shiga ki fito nima na shiga"
Maryam ta ƙare maganar tana duban Ummi dake neman number ɗinsa ta kirasa yanzu.
"Wallahi kinyi kyau kamar a sace ki a gudu"
Murmurshi kawai ta saki tana kallon Maryam zata bata amsa taji ya ɗauki wayar.
Matsawa tayi can ƙarshen gado tana amsa sallamar da yayi mata.
Sun daɗe suna waya kamin suyi sallama lokacin har Maryam ta fito itama daga wankan sun shirya cikin wani leshi kowanne da irin nata sunyi kyau suma sosai.
"Wai har kun shirya, ƴan mata wallahi kunsha kyau"
"Lallai ma matar nan ya za'ai kisan mun shirya dama? Kina ta tsinkar fire keda Ogan naki. Kinma fa cini game wannan matar wai ƴan mata, to ke yanzu ɗin mice ce ma ƴan matan ba ce wai?"
Maryam ta ƙare maganar tana kallon Ummi dake mata dariya ta ce.
"Yo oho dai ai ni yanzu na kusa zama matar aure, kune ƴan mata adon gari yanzu"
Dukan wasa Maryam zata kai mata ta goce tana dariyar ƙeta.
Kwafa Maryam tayi tana cewa.
"Wannan bakin naki zai mutu ne nan da gobe yarinya, sai Mlm Jamilu ya saita miki shi"
Dariya suka saki a tare Habiba na cewa.
"Wallahi lokacin da zamu je gidan nata nan da sati ɗaya ta koma lakwas kamar ba ita, lokacin Mlm Jamilu ya gama koya mata zaman rayuwa dai-dai da iyawarsa"
Wata shewa Maryam da Habiba suka ƙara saki suna tafa hannu, nanfa suka fara mata tsiya tun tana iya biye masu har tayi shiru tana turo masu baki.
Sosai gidan hayaniya tayi yawa ko ta ina mutane ne keta shiga suna fita.
Suna cikin ɗaki Aunty Binta ta shigo tana ce ma su Ummi.
"Ke Ummi ya kamata a ku fito aga amarya ko?, gasu Safiya can harta shirya ta fara fitowa mutane na ganinta, amma ke kun wani zo kun wani lilke a ɗaki"
Ummi bata ce komai sai Maryam ce data ce.
"Ayya Aunty Binta muma gamu nan yanzu zamu fito, da yake yanzu muka gama shirin namu ne"
Bata sake cewa komai ba ta fice daga ɗakin tana sakin tsaki.
Murmurshi kawai Ummi ta saki tana bin bayan Aunty Binta data juya tana sakar masu tsaki tabi da kallo.
"Kai Aunty Binta ita kam halinta sai ita wallahi"
Habiba ta faɗa dan itama ta santa a wajan Salma tana yawan jin labarinta.
"Kema kin san halinta ko?"
Ummi ta faɗa tana duban Habiba.
"Ba dole na santa ba?, ai Allah ya jiƙan Salma na yawan bani labarinta idan muka haɗu a school"
"Hmm ai Allah dai ya kyauta"
Kawai Maryam ta faɗa tana miƙewa tsaye.
"Kinga yanzu mu tashi muje mun dawo karta sake shigowa tana wata mitar"
Maryam ta ƙara faɗa tana duban agogon ɗakin ganin har sha biyu da rabi yanzu ta sake cewa kuma.
"Ƙarfe nawa ne ake tasowa daga masallacin juma'ar a nan?"
"Sai fa wajan ƙarfe biyu da rabi fa suke yin sallar juma'a a nan"
"Ah da saura ma muje dai yanzu"
Suna fita kowa ya fara tsokanar Ummi tana murmushi har wajan Ammi saida suka je. Sosai sukai yawo a cikin gidan kamin ta gaji sosai ta jawo hannun Habiba da Maryam akan su koma ɗaki ta gaji dan lokacin har ɗaya da rabi tayi ma.
Ya Muhammed ne ya shigo gidan yasha wata shadda kalar sararin samaniya sai maiƙo take tana shiƙe.
Kai tsaye ya jawo hannun Ummi yana sanar da ita cewa ana gama ɗaurin aure ita da ƙawayenta zasu nufi wani gida dake bayansu gidan abokinsa ne a can su Mlm Jamilu da abokansa zasu nufa a can za'ai pictures ita dashi na biki, dan shi da kansa Ya Muhammed ya ɗauki nauyin yin pictures ɗin, dan su Safiya ma wani gidan ƙawarta suka samu a can zasu tafi da nasu angonan harda su Ya Umar suma.
Amsa masa tayi tana dawowa inda su Habiba ke jiranta ta shiga sanar dasu.
Sai Maryam ta kamo ta suka koma ɗaki Maryam ta sake fiddo mata wata Lafiyar mai kalar fari itama sai dai ita akwai kalar ruwan ƙasa a jikinta, saɓanin wacce ta cire mai kalar fari da ja.
Nan ma tana ɗaurata ba ƙaramin kyau tayi mata ba, a cikin ɗaya daga cikin akwatunan lefenta Maryam ta buɗa ta ɗakko mata wata sarka da ɗankunne tasa ka mata sai ta fito kamar wata zinariya.
Ai tun a nan Maryam ta fara kashe mata picture da yake wayarta ita da Habiba duk IPhone ce akwai camera shi yasa tun a wajan suka fara mata pictures da video masu azabar kyau, dan ba ƙaramin kyau sukai ba.
Tun a nan suka fara ɗora status bayan suma sun sake kaya sun saka ango a yanzu, angon yayi kyau sosai ya haska su, suma suka fara ɗaukar pictures da amarya suna ɗora a status.
Sadda zasu gama har ƙarfe biyu tayi dai-dai dan haka Maryam da Habiba suka kamo Ummi suna fita waje da ita inda suka sanar da Mama yadda sukai da Ya Muhammed, ce masu tayi ba komai sai sun dawo.
Gidan da yayi masu kwatance suka nufa. Sosai gidan yayi masu Habiba kyau, dan akwai wajan yin pics masu kyau zasu haska sosai ma.
A babban parlon gidan aka ware masu harda yin wata ƴar kwalliya a cikin parlon.
Matar gidan na nan sama suka hau ta tarbesu da fara'a har tana tsokanar Ummi.
Wajan ƙarfe biyu da mintina arba'in su Habiba suka fara jin ƙarar motoci a ƙofar gidan da hayaniyar Maza sosai.
"Tofa wallahi an ɗaura, shikenan kin zama Mrs Jamilu, Ikon Allah kenan"
Maryam ta faɗa tanama Ummi shaƙiyanci.
Ummi kam jikinta yayi sanyi ƙalau kamar zata fara kuka a wajan Habiba ta shiga faɗin, ta rufa masu asiri karta fara kukan nan yanzu ta ɓata kwalliyarta.
Da kyar dai Ummi ta iya maida hawayen nata, amma idonta sunyi ja dan kaɗan take jira zata iya fashewa da kukan, dan haka su Habiba ganin haka yasa sukai shiru suka daina tsokanar tata.
Ya Muhammed ne suka fara shigowa shida wasu abokansa. Sai su Jamilu da nasa abokan suka biyo baya.
Abokan Mlm Jamilu yawanci su Habiba sun san su duk Malamai ne, wasu kam basu sansu ba, kuma su duka da ka gansu hutu ke ɓoye tsofansu, baza ka taɓa kallonsu ba ka ce sunyi shekaru masu yawa a duniya ba. Ai sai mai gayya mai aikin Mlm Jamilu daya sha wata arniyar shadda wacce kallo ɗaya zakai mata kasan mai tsadar gaske ce, bata ƙananun mutane bace, sai shayinin take tana ɗaukar ido, gata fara shar da ita, tayi mugun masa kyau, dama kuma fararan kaya ba ƙaramin masa kyau suke da ɗaukar hankali ba.
Mai camera fa ya fara kashe masu kala tunda Jamilu ya ɗora idonsa ga Ummi ya kasa ɗaukewa.
Wani pictures da sukai ai sai ya rungumeta a jikinsa kawai su Habiba da sauran abokai aka saki wani irin ihu dan abun ya basu kyau sosai.
Sosai mai camera ya rinƙa basu kalar da zasuyi pictures ɗin, sunyi pictures masu masifar kyau da ɗaukar hankalin mai kallo.
Jamilu sosai Ummi ta masa kyau tun a wajan yadda yaji wani masifar ƙamshi da taushin da jikinta yayi sai yaji kamar ya haɗiye ta ko ya huta da irin abunda yake ji yanzu ɗin, ya raɗa mata a kunne cewa tayi kyau sosai, ita kuma ta yi masa wani kallo tana murguɗa masa baki, ai dai-dai nan aka ƙara kashe masu pictures masu kallo su Habiba aka barsu da sakin murmurshi.
Shima murmurshin gefen baki ya saki yana sake raɗa mata cewa zai kamata wannan murguɗa bakin sai yayi maganinsa.
Ummi dai bata iya cewa komai ba, saboda yadda kusancin nasu yayi yawa dan gaba ɗaya a jikinsa take tunda aka fara pictures ɗin, shi yasa sosai jikinta ya sake mutuwa.
Ana gama pictures da amarya da ango sauran mutane suka rinƙa shigowa ana yi da su dasu Habiba suma anyi pictures kamar ba za'a daina ba.
Ana gama yin pictures su Habiba suka fito daga gidan zuwa gida. Suna komawa Mama harda faɗa ta masu wai sun daɗe su Safiya har sun dawo tun ɗazu.
Kai tsaye Mama ta ce ma Aunty Binta ta kama Salma suje parlon Baba su Safiya na can.
Su Habiba kuma Mama ta ce masu su je su shirya dan yanzu za'a wuce da Amaren gaba ɗaya haka Baba ya ce dama ana ɗaura aure za'a wuce da kowacce gidanta.
Haɗa kaya suka fara yi harda na Amaryar wadda ba'a haɗa ba suka haɗa mata komai daya kamata aka fara kaiwa mota, dan wa'inda suka zo ɗaurin aure sune zasu ɗauki Amarya dama.
Lokacin da Ummi zata dawo kuka sosai take yi Aunty Binta na riƙe da ita, ana dawowa da ita ta rungume Mama tana ƙara sakin kuka kamar ba gobe, Mamar ma sai ta fara hawaye tana mata nasiha sosai, lokacin ne kuma rasuwar Salma ta sake dawo masu sabuwa, shi yasa Mama kuka Ummi kuka, da kyar aka samu aka rabasu, har sai da Aunty Sakina ta saka baki tana masu nasiha itama.
Aunty Sakina da kanta taja hannun Ummi ta saka ta a Mota itama ta shiga dan ita ce zata kai Ummi har ɗakin Mijinta.
Su Habiba ma sun samu Mota Maryam kuma na kusa da Ummi dan Mota ɗaya suka shiga.
A ɓangaren su Safiya ma hakan ce ta kasance, su Inna ne da sauran ƴan uwan Ammi suka wuce da ita sai kuma Sadiya Inna suma zasu wuce da ita, amma ita sai zuwa gobe zasu wuce gaba ɗaya, dansu Abuja Umar zai wuce da matarshi da sun koma Kano........
PAGE 61
Komai cikin tsari aka yisa.
Su Habiba sun isa gidan Ummi lafiya, kuma sosai matarshi Haj Saratu (Mommi) ta tarbesu hannu biyu-biyu, dan sai da suka fara shiga part ɗin uwar gida tukunna da kanta tayi masu jagora har izuwa shashin Ummi ɗin.
Sosai fa su Habiba ke mamaki irin danƙareran gidan Mlm Jamilu komai nashi da wani irin tsari mai ƙayatarwa.
Wasu har sun fara ma gidan video ana posting nashi an iso gidan amarya Ummi lafiya.
Su Aunty Binta baki buɗe ake bin gidan da kallo, dan ba ƙaramin tafiya yayi da imaninsu ba.
Kai gida fa yayi sai san barka, sai dai maƙiya ne kawai zai ƙoshi sa.
Dan gida kam videonsa harya kai wajan su Ammi da Aunty Murja ansha kallo kamar ido zai faɗo ƙasa, dan yanzu tabbas sun san Ummi ɗin ta yi dacan miji mai arziƙin daya zarce na ƴaƴan su.
Tofa maganganu akai ta saki wai miye na ɗaukar video salon iyaye ne da ɗaukar magana, miye na video idan ba son asani ba?.
Kai maganganu fa har suka je kunnan Mama, sai tayi kamar ma bata ji miye ake yaɗawa ba tayi kunnen uwar shegu dasu.
Su Maryam kam ba abunda suke sai washe baki suna taya ƙawarsu murna.
Wasu daga cikin ƴan school nasu suna ganin yadda ake posting na pictures na bikin wasu ma harda group na school aka tura pictures, nan fa aka buɗe shafin gulma a group ana maganganu akan auren Mlm Jamilu da Ummi kai harda Salma data rasu sai da aka ɗakko maganarta, magana gata nan har sai da admins suka rufe group ɗin tukunna aka tsahirta da maganar bikin.
Wata kwaryakwayar lifaya Haj Saratu ta haɗa a daren da aka kai Ummi, wacce tabawa mutane mamaki sosai.
Sosai tayi namijin ƙoƙarin nuna komai ba komai bane, ta karrama kishiyar tata Ummi.
Habiba tayi mamakin ganin Hanan ƴar Mlm Jamilu wacce a nesa sai ka rantse zatai wani girman kai sai gashi su basu ma damu ba, harkarsu kawai suke a cikin gidan, ba dai zaka ce wai ko suna murna da auren uban nasu daya ƙara ba, ba kuma zaka ce suna baƙin ciki ba, gara ma Mazan da ba ganinsu ake ba, sai idan kaci sa'a, garama Maryam data ga wata ƴarsa wacce taji ana ce mata Aftihal ita tana da rawar kai sosai dan sosai daka kalleta zaka shaida hakan, amma Hanan kam bata da matsala.
Kwance suke bayan an gama walimar da uwar gida Haj Saratu ta haɗa, sun gaji sosai hatta Amarya na kwance akan gado sai juya take ta gaji sosai ta watsa ruwa. Su Aunty Sakina da Aunty Binta na ɗayan bedroom ɗinta dake ƙasa sun barma su Maryam ɗakin nata dake a sama, da yake part ɗinta bedroom uku ne, na mai gidan daban yake sai nata sai kuma wadda yake a ƙasan kamar na saukar baƙi a nan su Aunty Binta suka zube suna baza fira.
"Ke ni wallahi Hanan taban mamaki, ashe haka take bawar Allah bata da matsala ko kaɗan bare girman kan da aketa tunanin zatai?, gara ma gamai rawar kai nan Aftihal ɗin nan, ita kawai naga tana mana kallon uku saura kwata"
Wata dariya Maryam ta saki tana duban Habiba datai maganar ta ce.
"Yo dai a banza, tunda dai mun zama ƴan gida mun kuma aure Mahaifinsu, dole ne ayi mana biyayya"
Dariya suka saki a tare harda su tafa hannu.
Ummi ta ɗan miƙe zaune tana yamutse fuska ta ce.
"Kunga nifa na gaji sosai ku ɗan rage hayaniya please kunji. Kuma ai ni banga laifinsu ba Habiba, Ubansu fa aka aura, ai naga ƴaƴan nasa ma nada tarbiyya wallahi, Aunty Saratu a tsaye take kansu"
"Hmm gaskiya kam dakin gani kin san an basu cikakkiyar tarbiyyar data dace kam. Dan wallahi nake faɗa miki da wasu ne marassa tarbiyyar ace ubansu bai tashi ƙaro ma uwarsu kishiya ba sai yanzu, wata ƙila da yanzu sunyima amarya dukan kawo wuƙa, kuma su hanata zaman gidan ubansu, cikin ruwan sanyi da kanta zata tattara tabar masu gida wallahi"
Habiba ta faɗa.
"Hakane kam, amma shi gaskiya Mlm Jamilu ya birge ni, dana ga gidansa ma a tsaye yake tsayin daka a cikin gidansa, kamar dai a school wallahi ƙarya kike kiga yarinya wai ta ce ta raina Mlm Jamilu, babu wannan maganar, ko a cikin Malamai masu son mata ƴan iska, ƙarya ne kiji an sako da sunansa, baya ɗaukar raini, gashi ma a gidansa hakane"
Haka dai suka raba dare suna firar yadda gidan Mlm Jamilu yake da tsari, da yadda suke tafiyar da rayuwarsu cike da wayewa da sanin abunda suke yi, kuma daka gani zaka san masu ilimi da wayewa ne ke rayuwa a gidan.
Washe gari suka tashi da ganin an masu breakfast na musamman an aiko masu daga wajan Haj Saratu. Sosai su Aunty Sakina ke godiya suna kuma jin daɗi yadda kishiyar Ummin ta kama girmanta ta nuna tasan kanta, kuma daga gani za'a zauna lafiya a gidan.
Dan dama can ita uwar gida idan ta so tofa za'a zauna lafiya a gida, idan kam bata so ba to tabbas baza'a taɓa zama lafiya ba.
Sunci sunsha daga nan aka hau gyaran part ɗin Amarya, sai da aka tabbatar komai yayi ansa turaren wuta, sana masu shirin komawa Rimaye suka fara.
Aunty Binta dama wucewa gida kawai zatai dan sunyi sallama da Mama tun a can, Aunty Sakina ce kawai zata ƙara komawa Rimaye tayi kwana biyu daga nan ta dawo Kano, daga nan zata taho ma da Ummi da wasu abubuwan da aka manta ba'a ɗakko mata su ba.
Su Habiba kawai aka bari su sai wajan dare zasu tafi. Gidan sai ya kasance sune kaɗai daga Habiba sai Maryam, dan har ansa Mota ta miƙa wa'inda zasu koma Rimaye, Aunty Binta kam sama-sama tayima Ummi ɗin sallama bayan Abban Anam ya zo suka tafi.
Ummi harda kuka ganin duk an fara yayewa an fara barinta.
Su Habiba na zaune suna mata tsiyar saima anjima sun tafi suma lokacin zatai kuka ai banda yanzu.
Shiru ta masu kawai tana jin wani kaɗaici duk ya fara kamata.
"Wai ni kam kinga gidan Yusura ma dake jan bulo shima yayi kyau wallahi, kin gani ta turo miki videon da sukai suma"
Maryam ta faɗa tana kallon cikin wayar Ummi data ɗauka tana danne-danne yanzu ta ci karo da videon.
"Ohh ashe suma sunyi videon gidan nata, shine kuma da ake cewa wai mun cika iyaye zamu fara yin wani videon gida?"
Habiba ta faɗa tana matsowa tana kallon videon gidan, tabbas yayi kyau amma ko kama ƙafar kyan na Ummi baiyi ba, bama za'a taɓa haɗawa ba.
"Yayi kyau kam ai ba laifi zaman gidan mace ɗaya dai. Ai sun san namu ba irin nasu bane wallahi"
Habiba ta ƙare maganar tana kallon Ummi da kwata-kwata ita bata tasu take ba, tana can duniyar tunani.
"Amarsu lafiya dai?"
Maryam ta faɗa tana fuskantar Ummin sosai.
Sai lokacin ta sauke ajiyar zuciya tana cewa.
"Mi kuke cewa ne?"
"Au duk abun nan ina hankalinki yake wai?"
"Hmmmm"
Kawai Ummi ta ce. Su Maryam sai suka fara mata dariya suna cewa.
"Hhh ahaye, yo ai yarinya tukunna ma, anjima kaɗan zaki gane Allah ɗaya ne"
Wata harara ta danƙarama Maryam datai maganar suna tafan hannu da Habiba suna sakin dariya da shewa.
"Kufa ƴan iskan kanku ne wani lokacin idan kuka haɗu sai ka ce wa'inda kuka san juna da daɗewa, ni har mamaki nake ma"
"Yo ai baki sani ba?, ai Habiba akwai daɗin zama dole ne mu jone da ita, dan bikina ma dan Allah Habiba ki zo kinji a baza capacity kawai Mlm"
Dariya Habiba ta saki tana cewa.
"Insha Allahu kuwa zaki ganni, idan lokacin nima ba'a saka ranar tawa ba"
"Au an kusa ne wai dama?"
Cewar Maryam.
"Eh da dai ba'a kusa ba, amma yanzu ya shigo gida. Kuma ba kowa bane sai Doctor Nura wadda ya so Salma a baya, a asibitin da akai jinyar Salma a nan ya ganni shi kuma bai haƙura ba ya biyo