Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
ƴar lukuta Masha Allah yarinyar sai murmurshi take tana kallon Ummi kamar wacce ta gane.
"Aunty Binta inata kira baki ɗauka ba"
Babu wata walwala akan fuskarta sosai ta juya cikin gidan tana cewa.
"Baki da number ta ne"
"Ayyah ai na kira wayar taki fa baki gani bane?"
"Ohh na dai ga kiran Mama kawai"
Taɓe baki Ummi tayi tana bin bayanta a hankali tana jin duk zuciyarta babu daɗi wani ƙunci ne ya mamaye ranta, ganin kwata-kwata Aunty Bintar kamar bata yi farin ciki da ganinta ba, sai wani shan ƙamshi take.
Suna shiga cikin gidan mai ɗauke da parlo ƙato da darning table sai kitchen dake gefen darning table ɗin, sai wata hanya da suka bi ɗaki ne biyu haggu da dama, na haggun ne suka nufa, suna shiga Aunty Binta ta kunna fitar ɗakin da yake akwai solah a gidan.
Akwatin kayanta Ummi ta aje a cikin wata waduruf tana zama akan gado tana sauke lumfashi a hankali ta zare Hijab ɗin dake sanye a jikinta.
Zama Aunty Binta tayi itama tana kallonta ta ce.
"Mutanen Rimaye, ya kika baro Mama?"
"Lafiya lau suke, suna gaida ku"
"Masha Allah"
Ta faɗa tana aje Anam akan gadon tana fita parlo.
Sauke ajiyar zuciya Ummi tayi tana bin bayanta da kallo haɗe da girgirza kai. Sai yanzu fa taga ta ɗan sakar mata fuska, ace shi mutum yayita yin abu kamar mai iska.
Yanzu fa ita kuna zaune da ita saita canza maka fuska, ko kuma ku kwana lafiya da ita washe gari kaga ta canza maka babu wata walwala ko sakin fuska.
Anam ɗin ce ta fara kuka kaɗan da sauri Ummi ta aje wayar ta tana saka hannu ta ɗauke ta tana ɗan mata wasa.
Yarinyar ƙara ɓare baki tayi tana sakin kuka kamar wacce aka mintsina.
Aunty Binta ta shigo ɗakin tana zama akan gadon ta miƙa hannu ta amshe ta tana cewa.
"Yawwa ga shinkafa can da zan ɗora jeki ki ɗora ta, da miya zakiyi mana sai latas na nan a firija shima a yanka sa, akwai Kaza a cikin firizar asa itama, amma kamin asa a fara soyata tukunna"
Tashi tsaye kawai Ummi tayi a sanyaye ta ce.
"To Aunty"
Ta ƙare maganar tana fita haɗe da ɗaukar wayarta.
Tana shiga kitchen ɗin ta sauke lumfashi tana jingina da bango a fili ta ce.
"Kai kenan fa wahala idan kazo gidan nan, can gida baka huta ba a nan ɗin ma, daga zuwa na ko hutawa banyi ba an fara sani aiki kamar jaka. Dama wahalar taka ake so ba wani abu ba mtsww"
Ta ƙare maganar tana kwafa a ranta.
Ɗora ruwan shinkafar tayi a tukunya, haɗe da ɗaukar wata tukunyar ta fidda Kazar data faɗa mata za'ai amfani da ita, tasa a tukunya ta yanka albasa tasa da wasu kayan ƙamshi tasa ɗan ruwa kadan da yake taga ta turawa ce ta ɗora a ɗayan Gas ɗin da yake mai huɗu ne.
Latas ɗin ta ɗauka shima ta shiga gyarashi tana tsaki ciki-ciki tana mita a ranta.
Tana gama yankawa ruwan ya tafasa na shinkafar ta wanke ta zuba, dama ta ganta ta aje mata a gefe.
Kazar ta duba ganin tayi ta sauke ta ɗora mai ta fara soya, tana yi tana ɗan duba shinfakar ganin ta fara dafuwa kaɗan yasa ta saukewa ta ɗaureta tasa wani ɗan ruwa a cikin tunkunyar data sauke shinkafar yana ɗan tafasa ta maida shinkafar a cikinsa tasa marfi ta rufe.
Ta dawo ga naman da take soyawa, bata daɗe ba ta gama soyawar.
Ta buɗe firiza ta ɗakko wasu kayan miya markaɗaɗɗu ta ɗibi dai-dai yadda zatai miyar dashi ta ɗora a tukunya.
Buɗe ƙofar kitchen ɗin akai aka shigo.
"Yawwa kisa ma Abban Anam a kololinsa ai kin san yadda nake masa ma. An ɗibar masa latas ɗin ko?, kin sauke shinkafar ne?"
"A'a Aunty na dai kusa sauke ta so nake ruwan ya idasa tsotsuwa"
"Ohh amma dai ki duba da kinji ta fara ƙas-ƙas ɗin nan to tayi"
Wajan shinkafar ta nufa ta buɗe ta ɗan kanga kunnanta jin ta fara kaɗan yasa kawai ta kashe Gas ɗin tana cewa.
"Yawwa ma Aunty tayi"
"To ki ɗibar masa sana kisa sauran a wannan kolar"
Ta ƙare maganar tana nuna mata wata kula daban.
Amsawa tayi tana yin duk abunda ta ce.
Kayan da tayi amfani dasu ta aje a wajan da ake wanke-wanke.
Tana dawowa ga miyar. Itama komai ta haɗa dandanan ta fara tashin ƙamshi sosai.
Saida miyar taja sosai kamin ta zuba mai, dama tuni ta zuba naman data soya ta motsa miyar tana ɗan rufeta kamin ta kashe ta sauke.
Aunty Binta tuni ta fice jin Anam data baro a parlo tana ɗan kuka kaɗan yasa ta ficewa da sauri.
Tana fita Ummi ta ɗan sauke lumfashi na gajiya sosai tunda ta shigo kitchen ɗin bata fita ba, ba kuma ta zauna ba.
Jin kamar muryar Abban Anam ɗin ne ya dawo yasa Ummi saurin fitowa daga kitchen ɗin tana duƙawa har ƙasa ta shiga gaida shi.
"Ahh su Ummi ne a gidan namu yau?"
"Eh wallahi Uncle Abdul mune"
"Masha Allah, anzo lafiya?, ya so Mama aka baro su?"
"Lafiya lau suke, sunce a gaida ku"
"Tom Masha Allah, amma dai zakiyi mana kwana biyu ko a nan?"
A zuciyar Ummi ta ce anzo wajan.
"Eh to Uncle zanyi dai sati biyu inaga"
"Kai haba Ummi sati biyu ai yayi kaɗan"
"Ai da yake Uncle Baba ne ya ce nayi sati biyun shi ne yasa ma"
"To ai ba laifi Allah ya nuna mana, muda muke so a bamu ma ke a nan har zuwa ranar da zakiyi aure, amma naga ke gudunmu ma kike ko Ummi"
Murmushin yaƙe tayi a ranta ta ce.
"Lokacin ƙila wahala da aikin gidan nan ya kashe ni ko?"
A fili ta saki murmushi tana cewa.
"Uhm a'a wallahi Uncle Abdul"
"To ai shikenan"
Ya faɗa yana idasa shigewa ɗakinsa.
Yana shiga Aunty Binta ta bisa bayan ta ɗauki Anam.
Bin bayanta Ummi tayi da hararara ƙasa-ƙasa a fili ta ce.
"Hmm masu miji manya"
Ka ƙare maganar tana taɓe baki.
Tunowa da miyar data ɗora akan Gas yasa ta juyawa da sauri ta nufi kitchen ɗin, tana zuwa tayi saurin kashewa, tana sauke ajiyar zuciya ganin bata kai ga kamawa ba.
Kamar yadda ta sani haka ta zuba masa komai ta jera akan darning table ɗin dake parlon sauran kuma ta barshi a kitchen ɗin ta fito ta jawo ƙofar ta nufi ɗakin data sauka, tana rage kayan jikinta ganin dare harya fara an fara kiran sallar bangaruba.
Toilet ɗin ɗakin ta nufa ta ɗauro alwala haɗe da watso ruwa ta fito........
PAGE 22
*House No 26, Gadon ƙaya Kano State Nigeria*
Zama tayi tana murmushi ta aje ƙofin ruwan dake hannunta tana faɗin.
"Mlm sai yau muke ganinka?"
"Wallahi sai yau Allah yayi zan zo, shima na zo ne domin wasu kayan lambu na dana kawo kasuwa a nan Kano ɗin"
Taɓe baki tayi tana murmushin yaƙe.
"Wai ni ina wannan yarinyar ne Salma, naga Yusura kawai na gani tunda na zo?"
Taɓe baki ta ƙara yi tana gyara zama ta ce.
"Yo tana fa ina? idan baccin makarantar da take cewa ta tafi, to tana can, gashi dai har dare yayi amma shiru bata dawo ba"
"Wannan wacce irin Makaranta ce haka?, da za'a ce har dare mutum bai dawo ba?"
"Uhum ai Mlm wallahi kusan kullum haka take yi, idan har tasa kai ta fice da sunan wai zuwa Makaranta to sai lokacin da muka ganta kawai"
"To mi yasa kin san hakan na faruwa baki kira kin sanar dani ba haba Murja?"
"A'ato Mlm in kira ka na gaya maka ace shirri nake masu?. Gara dai daka gani da idonka ba wai naje na kira ka ba ace na sauya zance"
Jinjina kai yayi yana ɗan jingina da bango zai ɗauki wayarsa Yusura ta fito daga banɗaki. Sauri take dama ta fito danta ji irin mugun haɗin da Ummar tata ke yima Salma.
"Baba dan Allah karka kira ta"
"Mi yasa Yusura?. Tana ƴa mace ace har zuwa yanzu bata shigo gida ba, kuma ki ce karna kira ta?"
"Baba nasan wallahi wahalar abun hawa ne duk yasa ta tayi daren nan. Dama kuma suna yin lecture ɗin ƙarfe shidda dai-dai wallahi, inaga yau ita ce suka shiga ƙarfe huɗu sai shidda ɗin suke fitowa"
Sai ma yanzu ne Baban ya tuna, tunda shima fa ya taɓa karatun nan yasan yadda yake.
"Kware kuwa Yusura gara da kika tuna min, tabbas ana yin haka. Amma yanzu a wannan zamanin bai kamata ace Malaman nasa masu ta ƙarfe huɗu zuwa shidda ba"
"Ai Baba kasan su babu ruwansu da duk wannan, kawai dai duk abunda suka ga dama sawa suke"
"Ke dalla rufe ma mutane baki, ansa dake ne a ciki uwar iyayin tsiya?. Wallahi Yusura kina shiga hanci saina fyato ki tukunna shashasha kawai"
"A'a Murja miye abunda Yusura tayi a nan?, ai gaskiya ce ta tunatar damu, da yanzu na ɗauki wani mataki idan ta dawo fa wadda bai kamata bafa?"
"Nifa Mlm na kasa gane inda ka dosa fa. Wato ma duk abunda na gaya maka ƙarya nake kenan?, sai abunda ƴarka ta faɗa shine gaskiya da shine ka yarda?"
"Murja na kasa gane abunda kike nufi, ƴaƴan nan dai duk nawa ne, kema ai kamata yayi ace Salma ta zama ƴarki ba wai ki rinƙa yi mata hakan ba, yanzu idan ita Yusurar ce zaki zauna kina mata shaida irin wannan ne?"
"Kaga Mlm ni ƴata ma baza tai wannan karatun bokon ba yawwa, su dai suje suyi ta yi babu ruwan wani dasu canta matse masu"
Girgiza kansa yayi yana mamakin halin Murja sosai.
"Kuma da kake cewa wani Salma ƴata ce, ta ina ta zama tawan?. Yarinyar da ko mutumci na bata gani, ai bata ɗauke ni uwar bane shi yasa nima na ɗauketa ƴar kishiya, taya za'ai ma ƴar kishiya ta zama ƴarka? ai bazai yiwu ba"
"Kinga Murja bana son duk wannan dogon jawabin kin sani bana ɗaukar irin wannan zantukan"
Ƙara taɓe baki tayi tana miƙewa tsaye ta wuce ɗakinsu ta barshi shida Yusura a zaune.
"Yusura mike damun Ummarki ne haka?"
"Wallahi Baba babu wani abunda ke damunta dama can haka take ai"
"To kiyi ta mata addu'a kinji?, wata rana zata daina ne"
"Insha Allah Baba"
****************"Washhh wallahi Habiba na gaji da tsayuwar nan, kawai kije ni zan ɗan fara takawa naga ko zan samu abun hawan a gaba. Ya kamata kema ki wuce inda zaki samu naki abun hawan, kinga kin fini wahalar samu mafa"
"Wallahi na so na fara samar miki kamin ni na wuce can ɓangaren, da zan samu abun hawan a can, ai ni nafi tausayinki yanzu da kin koma gidan nan naku Allah kaɗai yasan irin maganganun da wannan Auntyn taku zata rinƙa faɗa miki, nifa?, babu wadda zai min haka, Ummanmu tasa yadda muke wahala akan karatun nan namu"
"Karki damu ai na saba kije kawai sai mun haɗu goben kawai"
"To ai shikenan bari naje kawai, Allah yasa dai ki samu kinji"
"Ameen, Allah yasa kema ki samu da kinje"
Murmushi ta saki ta amsa da ameen.
Bayan Habiba ta wuce ne ta fara takawa tana tafiya ita kaɗai, tana yi tana yamutse fuska.
Tana tafiyar ne tana ɗan tsaida napep ɗin dake ta wucewa, amma again har zuwa wani lokaci bata samu ba, harta fara nisa da school ɗin tasu ma.
Da yawa ƴan school ɗin ba ita kaɗai bace ke takawa a ƙafa ba, saboda duk yawanci ba'a samu abun hawa ba.
Sosai ta gaji da tafiyar a hankali ta samu wani waje kusa da titi ta zauna tana sauke ajiyar zuciya.
Wayarta ta ɗan ɗakko dake cikin jaka tana ɗan jujjuyawata. Gashi ko number ɗin Doctor Nura bata amsa ba, yanzu da bata hanasa zuwa ɗaukarta ba, ai da yanzu ta koma gida ta sani.
Girgiza kai tayi tana katse wannan hasashen, gara ta rinƙa komawa da kanta sai ya fi mata Alkhairi.
Tashi tayi tsaye tana mayar da wayar dan tasan wajan baka isa ka fiddo waya ba yanzu sai ka haɗu da masu kwacen waya.
A hankali ta fara tsaida napep a wajan data tsaya amma abun kamar haɗin baki basama tsayawa bare suji inda zaka je.
Wani ma idan ya kalli gabas ko kallo baka isheshi ba.
A fili ta furta.
"Wayyo Allah, ka taimake ni"
Ta ƙare faɗar haka kamar zatai kuka.
Wata narkekiyar Mota ce ta biyo ta hanyar da Salma take, tunda ta taho dama Salma ta gane mai Motar, ba kowa bane sai Mlm Jamilu.
Dan haka ma da sauri ta ɗauke kanta daga kallon Motar, dan iya saninta ko mutum zai mutu wannan bawan Allahn ko kallo baka isheshi ba.
A matuƙar mamakinta sai taga Motar ta dawo baya kaɗan inda take tsaye.
Zage gilas ɗin Motar akai fuskar Mlm Jamilu ta bayyana. Sai da Salma taji wata irin buguwar zuciya dan da kyar ta iya haɗe miyau, iskar da take shaƙa ma ji tayi, tayi mata kaɗan.
"Ina zaki je?"
Sai taji kamar bada ita yake ba, bakinta na rawa ta buɗe baki ta ce.
"Gadon ƙaya"
Dan kusan yanzu ita ɗaya ce a hanyar da yawan ɗaliban da basu samu ba tuni sunyi nisa da ƙafa suke tafiya, ita tsayawar da tayi ne yasa har ya fito daga school ɗin ya haɗu da ita. Shi kuma tunda ya hange ta yaga bai dace ya bar ɗan school ɗinshi kuma Mace a wannan wajan da yawanci ƴan daba ke yawan faɗa idan dare yayi ba, gashi tana Mace kuma ita ɗaya.
Jin hanyar da zaibi ce har zuwa Tudun Yola unguwar da gidansa yake yasa kawai yayi mata alamar ta shigo.
Zuciyar Salma ba abunda take a ƙirjinta sai bugawa.
A hankali ta nufi Motar hannu na rawa tasa ta buɗe murfin Motar ta shige gaba kusa dashi dake toƙa motar.
"Ya Allah"
Salma ta faɗa a zuciyarta, tana sauke lumfashi kaɗan, jin wani irin sanyin Ac da ƙamshin turare mai daɗin shaƙa.
Tunda take bata taɓa ganin Motar data haɗu iya haɗuwa ba irin wannan Motar. Har tana tunanin ta Doctor Nura nada kyau sosai ashe ta Mlm Jamilun ma taci ub*an tashi haɗuwa.
Babu wadda yake magana a cikin Motar. Salma kuwa a mugun-mugun takure take, dan ji take kamar zata saki fitsari a wando, tsabar yadda kwarjininsa da girman da Allah ya basa a idon jama'a ya cika mata zuciya da gangar jiki, yayi matuƙar cika mata ido sosai.
Shi kam wannan bawan Allahn yadda mutane ke tsoronsa da shakkarsa anya ba wata addu'a yake ma mutane ba kuwa?, har suke jin hakan daga garesa.
Sun iso dai-dai ƙofar gadon ƙayar taji muryar nan tasa mai zurfi ga taushi, ita kanta Muryar tasa fitowa take da wata irin izza da isa a cikinta, kai muryarsa kaɗai na iya gigita maka tunani.
"Ana shigowa gadon ƙayar ne za'a aje ki?"
Ya faɗa kamar baya so.
Da sauri Salma ta ce.
"A'a akwai ƴar tafiya. Amma idan wucewa zakai Mlm a aje ni a nan ɗin ma na gode"
Da kyar take maganar kamar tana tare da dodo.
Bata ƙara jin ya tanka ba yabi ta cikin ƙofar gadon ƙayar ya fara tafiya akan shatale-talen titin daya miƙa zai iya kaika har Tudun Yola Gwauron Dutse.
Anyi tafiya ba laifi kamin azo dai-daita saitin wani titi daya bi ta cikin wani lungo ta buɗe baki ta ce.
"Mlm nan ma yayi"
Tsaida Motar yayi kawai tasa hannu zata buɗe Motar sai kuma ta ɗan tsaya da ƙarfin hali ta ce.
"Mlm na gode Ubangiji ya saka maka da gidan Aljanna ya tallafi iyalinka"
Tana ƙare faɗar haka ta ɓalle murfin Motar ta fice bata wani tsaya jin abunda zai faɗa ba, saboda Maganar da tayi ma karfin hali ne ta tattaro ta yafa ma kanta harta iya furta masa ita.
Wata wawar ajiyar zuciya ta shiga saukewa a bayyane tana dafe da saitin zuciyarta, tunda ta samo ta fito daga Motarsa take faman sauke ajiyar zuciya kamar bazata daina ba.
"Wayyo Allah, kai jama'a wallahi wannan Mlm Jamilun ƙarshe ne wajan izza da kwarjini, ai ni tunda nake a duniya ban taɓa ganin mutum irin wannan ba"
Salma ta faɗa a fili tana takawa zuwa gida.
Sallamarta ce tasa Yusura miƙewa daga wajan Baba tana murmushi ta nufe ta tana cewa.
"Oyoyo Aunty Salma. Amma kin daɗe yau wallahi, hala abun hawa ne yayi miki wahala ko?"
"Bari Yusura ai inaga yau har kuka nayi tsabar yadda na wahala wajan samun abun hawa, masu napep ɗin nan basa da mutumci ko tausayi wallahi"
Yusura zatai magana Salma ta hangi Baba a zaune. Sakin baki Salma tayi sai ma yanzu ta gansa a hankali ta saki murmushi fuskarta na bayyana farin cikin ganin Baba a gidan yau, ko banza ta tsallake maganganu masu zafi da Aunty Murja ke yaɓa mata, tasan yau dai bazata ji su ba, tunda Baba yana gidan, sai dai idan ya fita.
"Baba wai kaine ka zo yau?"
Murmushi ya saki yana kallonta ya ce.
"Ni ne ƴar albarka, sannu fa kinsha gajiyar Makaranta. Ashe haka kuke wahalar abun hawa idan yamma tayi?. Amma mi yasa baza ki rinƙa haƙura da lecture ɗin yammar nan ba kawai ki taho gida?"
Zama Salma tayi akan kujerar da Yusura ta tashi tana cewa.
"Wallahi Baba idan baka tsaya ba har a exam's ɗinka sai abun ya shafe ka, saboda atandas suke ɗauka na sunayen duk wadda ya tsaya, akwai wa'inda suke guduwa dama, ko yau mu ƴan kaɗan muka tsaya kuma kaga Baba an ɗauki sunayenmu"
"Uhm kuma da wannan fa, ai kun dai kusa gamawa komai ya ƙare, dama shi karatu ya gaji hakan"
"Hakane Baba. Baba ya so Mama da Ammi"
"Lafiya lau suke Salma. Ai ita Ummi tana nan Kano itama yau ta zo"
"Eh Baba ta gaya min ɗazu"
"Masha Allah, kije ki hutu ko?"