Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
suna mugun kama dashi wasu ma kamar yayi kaki ya tofar tsabar kamar da suke da juna.
Ƴaƴansa duka su shidda ne, akwai Maza huɗu mata biyu.
Mazan kusan sune manya, matan ma baza su wuce sa'annin su Salma ɗin ba.
Mazan kuwa zasu kai Ya Muhammed a shekaru.
Danshi kansa Jamilun bafa yaro bane, dan zai kai sa'an Mama a shekaru wata ƙila su zo ɗaya. Kawai yana cikin hutu ne da jin daɗi, dan jikinsa mai kyau ne, fatar jikinsa kamar ki taɓa jini ya fito, fuskar nada ɗan duhu, amma jikinsa saika rantse wani abu yaka shafa masa, fuskar ma tashi daka kalla zaka san eh tabbas yana jin daɗi.
Ƴan school ɗinsu Salma sun zo gaisuwa har gida. Wasu na mamakin wai auren da aka ɗaura mata da Mlm Jamilu. A can makaranta ma haka akai ta yaɗa maganganun iri da iri, wasu sosai mutuwar ta shige su, wasu kuwa shafin gulma ne ta buɗe masu.
Maryam ma taji mutuwar Salma dan tana kuka ta zo ma Ummi gaisuwa kwana kusan bakwai tana zaryar zuwa ita da Ummanta.
Kamar yau ma zaune Ummi take tana kallon photon Salma da suka ɗauka ranar graduation, ranar data zama ranar mutuwarta, ranar kuma aurenta, Ikon Allah kenan, ranar kuma da zata gama makaranta, wannan idan ba tsarin Allah ba na waye?.
Ummi keta tabbayar kanta cikin zuci, tana yi tana kallon photon haɗe da zubar da hawaye.
Zama Mama tayi a kusa da ita, harta zauna Ummin bata sani ba, sai da Mama tasa hannu ta amshi wayar dake hannunta, sai lokacin Ummi ta sauke ajiyar zuciya wacce ta gangaro mata da wasu sabbin hawayen dake zubo mata.
"Wai ke sai yaushe ne zaki daina wannan kukan ne?, yau kusan sati biyu da rasuwar nan har gashi mun dawo gida amma jiya iyau dai? haba Ummi. Addu'a fa take buƙata daga gare mu Ummi"
"Mama wallahi bazan taɓa daina kewar Salma ba, kewarta ke saka ni kuka Mama ba wai mutuwar ba"
"To idan kika tuna hakan Addu'a ta dace kiyi mata. Nima ina kewar Salma, tunda daga cikin jikina ta fito, yadda nake kewarta ma faɗa ɓata baki ne Ummi, ni Mahaifiya ce in....
Maganar Mama ce ta maƙale saboda kukan da itama yaci ƙarfinta.
Da sauri Ummi ta riƙe hannun Mama tana share nata hawayen ta ce.
"Dan Allah Mama ki daina kuka kema, yanzu fa kika gama ce min babu kyau addu'a ce take so, dan Allah kema ki daina"
"Shikenan na daina, amma kema ki daina kukan nan, kukan naki ƙara sani cikin damuwa"
"Na daina Mama"
"Yawwa ko ke fa. Nama manta Babanku ne ya ce kizo shike son ganinki. Naga kamar Jamilu ne ya zo yau"
"Wai Mama shin bazai daina zarya zuwa gidan nan bane?, tunda wacce ta haɗa alaƙalar babu ita?, ya daina zuwar mana gida man. Wallahi Mama na tsane sa, bana son ko ganinsa, shine fa yayi sanadiyar mutuwar...
Ɗaga mata hannu Mama tayi tana cewa.
"Ya isa haka mana Ummi. Amma kin san dai ƴar uwarki harta mutu bata ganin laifinsa, sana kuma ta yafe masa, kuma tana so alaƙalar nan gidan ta ɗore tare dashi, shi yasa ma harta bar wasiyyar cewar ki maye gurbinta a wajansa sabo....
Kuka kawai Ummi ta saki tana cewa.
"Wallahi Allah Mama bazan iya aurensa ba, bana sonshi banzan iya zama dashi ba"
Tashi tsaye Mama tayi ranta ya soma ɗan ɓaci, dan ita har cikin ranta tana son haɗin auren, dan Jamilu mutum ne son kowacce mace, sana daga kallesa zaka san yana da wata irin baiwa da nagartar da dole ma kaji nan take kana ƙaunarsa, gashi Mama taga iyalansa basa da wata matsala, ko a fuska basu nuna wani rashin jin daɗin ko ubansu yayi aure bai gaya masu ba, ko matar tashi baka isa gane wane hali take ciki ba, cike da wayewa tazo masu gaisuwar, a tsaye yake a gidansa sosai daga gani ba sai ma ka tabbaya ba, to Ummin bazata sha wahala wajan Matarshi ba, sai dai abunda ba'a rasa ba.
"Bari kiji Ummi ni ba dole zan miki ba, amma ita kanta Salma Allah yayi mata rahma tasan abunda ta hango a tattare da Jamilu shi yasa ta kasa rabuwa dashi, har kuma take kwaɗayin ke ki maye gurbinta tunda bata a raye. Sana wannan abun da zakiyi mata shi zai sata farin ciki tayi alfahiri da ke ko a can ɗin, kisa ruhinta ya samu salama, ki cika ma ƴar uwarki muradinta Ummi"
Jikin Ummi ne yayi sanyi tana hawaye ta ɗago tana duban Mama ta ce.
"Mama zan auri Jamilu, amma wallahi badan ina sonshi ba, kawai saboda Salma zanyi. Wallahi inama Salma bata bar wannan wasiyyar ba, wallahi bana sonshi kwata-kwata koda da kwayar zarra ne, kullum ji nake idan na tuna yadda Salma tasha wahalar son shi tayi ta dakon ƙaunarsa sai na ƙara jin na tsane shi wallahi"
Sauke lumfashi mai zafi Mama tayi tana komawa ta zauna kusa da Ummi ta ce.
"Ummi kisan abu ɗaya, kuna da laifi daga ke har mariganya Salma. Mi yasa ke kina babba kin san yadda take sonshi da kuma shan wahala baki je kin sanar damu ba?, ai da duk hakan bata faru ba, amma sai kuka ɓoye dake har ita, harshi kansa Jamilu bai san irin son da take masa yayi girman da zata iya rasa rayuwarta akansa ba, na tabbatar daya sani tabbas bazai bari hakan ta faru da ita ba. Sai dai kashhh dama can a haka ƙaddararta ta zo bata isa kuma tsallake ta ba"
Girgiza kai Ummi tayi dan ita ko kaɗan bazata taɓa masa uzuri ba wallahi.
"Mama nifa Jamilu ne yaja ƴar uwata ta rasa rayuwarta, dan haka ko gobe da hakan zan rinƙa kallonsa, kuma Mama hakan bazai taɓa gogewa cikin raina ba"
Mama tayi shiru na ɗan wani lokaci kamin ta ce.
"Yanzu ki tashi kije wajan Babanku na son ganinki"
Miƙewa kawai Ummi tayi ba tare data ƙara magana ba, tasa Hijab ɗinta har ƙasa ta fita wazu parlon Baba.
"Zauna mana Mamana"
Baba ya faɗa yana duban Ummi.
Zama Ummi tayi tana jan lumfashi a hankali ta sake gaida Baban tana sadda kanta ƙasa.
Gyaran murya Baba yayi yana kallon Ummi sosai ya ce.
"Ummi abu ɗaya yasa na kira ki shine, akan wasiyyar da ƴar uwarki ta bari ce, kuma shima kansa Jamilu wasiyyar tata yake son cika mata, saboda ya shaida min cewar yana ganin hakan ne kawai zaiyi ya faranta ma Salma duk da bata raye, kamin Allah ya amshi ranta ta roƙosa alfarma akan ya nemi aurenki, ya maye gurbinta dake. To amma ke ya kike gani?, bazan miki dole ba, sai dai ki kalli wasiyyar da ƴar uwarki marigayiya ta bari"
Jikin Ummi ne ya ƙara yin sanyi murya na rawa ta ce.
"Shikenan Baba na amince zan auresa, idan har kuma kun yarda da hakan"
"Masha Allah Alhamdulillah, ai mu dama amincewar taki kawai muke so, to tunda kuma kin amince ɗin zaki cika ma ƴar uwarki burinta to ba abunda zance sai Ubangiji yasa albarka a ciki, yasa ita kuma tana Aljannah"
Da amin Ummi ta amsa a hankali.
"Tashi kije parlon baƙi Jamilun na nan yana jiranki. Dan Allah Ummi abi komai a sannu, dan wata rana komai ɗin nan zai zo ya wuce kinji?"
Ummi ta amsa a hankali tabbas tasan yayi mata hakan ne dan yasan bata son ko ganin Jamilun.
Yanzu ɗin ba ranta a ɓace ta nufi parlon baƙin, da ƙudirin idan ya ce zai gaya mata magana saita gaya masa maganar da zai kwana tana masa ciwo, danta lura shima ba wani son auren nata yake ba, kawai yana sone saboda wasiyyar da Salma tabar masa.........
PAGE 56
*UMMI POV*
Duk wata rashin kunya data taho da ita zata masa, tana shiga sai duk jikinta yayi sanyi, kuma kwarjininsa ya cika mata ido.
A wancan lokacin ma namijin ƙoƙari tayi bata cikin hayyacinki ne yasa har ta iya kallon tsabar idonsa ta gaggaya masa maganganun, da yanzu idan zaka ce ta mai-maita su zata ce bata san mima ta ce masan ba. Wancan lokacin radaɗin mutuwar Salma ne yasa ta gaya masa maganar da duk tazo bakinta.
A yanzun ɗin ma wata harara ta ɓalle masa tana sadda kanta ƙasa dan idan tana kallonsa babu uwar da zata iya tsinanawa.
"Gani miye zan maka?"
Ummi ta faɗa a gatsine.
Murmurshin gefen baki ya saki wadda ya ƙara masa kyau. Shi zuwa yanzu ƙarfin halinta ma birgesa yake.
Da tana basa haushi ma amma yanzu ya nemi haushin nan ya rasa.
Haka nan idan yana zaune saita rinƙa faɗo masa a rai, da rashin kunyarta, sai ya zauna yana murmurshi shi ɗaya. Tun yana ɗaukar abun wasa har ya zame masa jiki, yanzu ma haka nan ya taso tundaga Kano yazo domin ganinta kawai, zuciyarsa ke so. Saboda idan yana ganin Ummi sai yaga kamanninta da Salma sunsu suyi yawa.
Sosai hakan ke ƙara sashi son ganin nata. Kuma da gaske Ummi da Salma wani lokacin wasu basa gane su, saboda suna tsananin kamanni da juna.
Turo baki tayi tana ɗan satar kallonsa, tana ƙunƙuni ta ce.
"Ayo mutum baida zuc...
Maganar ce ta maƙale ma Ummi jinsa kamar a kusa da ita. Jikinta ne ya soma yin rawa a hankali ta juya da sauri zata fice daga parlon. Taku ɗaya tayi ya cafke mata tsintsinyar hannunta.
Wani irin taushi taji hannunsa daya sauka akan nata hannun, yadda kasan auduka, kamar hannun mace haka Ummi taji.
Shima a wajansa haka ɗin ne.
Batai aune ko gama tunanin data lula ya jawota da ƙarfi saura kaɗan ta faɗa jikinsa, Allah ya so ta tsaya da ƙafafunta gaf dashi, har suna iya juyo lumfashin juna.
"Ni kike ma rashin kunya right?"
Neman maganar tayi ta rasa jin muryarsa sosai a kusa da ita, ga muryar tasa ta saka ta jin wani iri a cikin jikinta. Dama haka Jamilun yake?. Ai da ita ganin nesa-nesa take masa, ashe ya wuce duk yadda take tunani, kai haba dole Salma ke ruɗewa ta kasa sanar dashi wata maganar kai tsaye.
Bata gama tunanin ba ta ƙara jin muryarsa a dodon kunnenta tana mata amsa kuwwa.
Muryar ma tasa sai taji ta cike da isa da taƙama take fitowa, yadda yake komai nasa kamar wani sarki shike ƙara bawa Ummi haushi.
Taɓe baki tayi bata sani ba, sai dai tsaf yaga lokacin data taɓe bakin.
Murmurshi ya saki bata sani ba kawai taji ya saka hannunsa ya kamo ɗan ƙaramin bakinta ya matse sa da hannunsa.
Wata ƴar ƙara ta saki tana ɗagowa da sauri ta kallesa, sai dai da saurinta tayi ƙasa da kanta, saboda yadda ya zuba mata idon nan nasa masu masifar kwarjini ga jama'a.
Duk sai ta kasa sukuni, ga bakinta daya matse yana mata raɗaɗi bata san lokacin data sakar masa wani irin kukan sangarta ba.
Cike da wani irin ɗaukar hankali Ummi na sane ta fara buga ƙafa tana neman shigewa jikinsa. Wani iri ya fara ji da sauri ya sake ta yaja baya kaɗan yana furta auzubillahi.
Wani kalar murmurshi ta saki yana sakinta tasa hannunta tana murja bakin nata dake mata zafi, ta juya da sauri zata fice sai kuma ta tsaya tana juyowa gaba ɗaya ta kallesa tana masa gwalo ta ce.
"Ai na ɗauka zaka tsaya ne. Ka bari a ɗaura ai ko?, sai wani neman taɓa ni kake haka kawai ma, wannan ai neman iskanci ne"
Ta faɗa tana yin saurin wucewa daga parlon.
Ta barsa da mamakinta.
Basarwa yayi yana murmurshi kawai a zuci ya furta.
"Hmm wannan yarinyar ta raina ni fa, amma zanyi maganinta very soon"
Yana fitowa daga parlon shima yana ma su Baba sallama, kwata-kwata ma bata bari sun zanta ba akan abunda ya kawo sa sai shirmenta take masa.
"A'a miye haka zaki shigo ma mutane a guje?"
Sauke lumfashi tayi tana zama akan kujera sai kuma mita tuna saiga hawaye zirrrr kamar wacce aka duka.
"Kashhh kefa daɗi na dake yanzu saurin kuka, tunda ƴar uwarki ta rasu kika koma haka. Wannan yawan kukan fa bashi da amfani Ummi. Miya faru yanzu kuma?"
Share hawaye Ummi tayi da bayan hannunta tana duban Mama dake zaune ƙasa ta idar da sallah ta ce.
"Mama wallahi sai nake jin kamar idan na auri Mlm Jamilu kamar naci amanar ƴar uwata ne fa, sai nake jin yanzu kamar tana kallo na nida shi muna dariya da murmurshi, sai nake ji kamar bazan iya yafe ma kaina ba, idan har na bari na fara son wancan bawan Allahn"
Tofa
Mama ta faɗa a zuci. Dama abunda take gudu ta fara tunani a zuciyarta kenan. Amma sai Mama ta girgirza kai tana murmushi ta ce.
"Haba Ummi, sai ka ce ba wayayya ba, wacce kuma tayi karatun addini ba. Har kin mance ita da kanta marigayiya Salma tabar wasiyyar cewar ki auresa?, ai bake kika ce kina sonshi ba bayan mutuwarta, ita ce da kanta da nemi da ki auresa, kuma idan ma kika fara son nashi kika kwantar da hankalinki nasan koda dawowa tayi zatai farin ciki da hakan. Kima fidda cewa kamar wai cin amana ne, ita ai tafi ki sanin abunda yasa ta ce ki auresa ki maye gurbinta. Daga yau karki ƙara saka ma ranki cewar wai kamar amanarta zaki ci, kunji ko?"
Da kyar ta amsa da kai tana ƙara share hawayen dake zubo mata.
Tashi tayi zata shiga ɗakinsu Mama tayi saurin cewa.
"Koma ki zauna"
"Am Mama kwanciya zanyi fa, kaina ke ɗan ciwo"
"Ai yanzu kam kin gama zama a ɗakin can ke ɗaya. Yanzu kina shiga zaki tasa inda Salma ke yawan kwanciya ko zama kina kukan zuci wadda baya fita, dan haka idan har ina nan tare zamu rinƙa zama, idan ba haka ba kema zaki je ki saka ma kanki wata damuwar ne ta daban, dan haka bazai yiwu ba, ki kwanta a nan akan kujera gata nan"
Ba abunda Ummi ta iya cewa ta koma ta kwanta, tana mamakin yadda yanzu Mama ta sauya ba hantara babu komai.
Mama ta ɗan gyara zamanta tana kallon Ummi ta ce.
"Wai ni kuwa na faɗa miki Binta ta kira ni?, tana faɗa akan wannan haɗin da akai miki da Jamilu"
Ai sai Ummi ta gyara kwanciyarta tana fuskarta Mama ta ce.
"Mama miye ta ce to?"
"Hmm duk na fahimci Binta, kamar tana jin zafin auren Jamilu da zakiyi. Ita ma dai cewa take wai ya za'ai kije ki shige ma mai mata sa'an iyayenki?, miye da miye. Ni kuma tun a nan na dakatar da ita, na ce bana son jin komai, tunda har Salma tabar wasiyyar hakan dole za'a cika mata wasiyyar ta. Shine fa ta dawo kan Salma wai itama rashin hankali ne zata je ta faɗa son tsohon mutum, gashi a banza a wofi ta mutu akansa. To daga nan fa mukai kaca-kaca da ita na kashe wayata"
"Mama wannan fa abun da Aunty Binta ke yi idan bata sani ba kamar hassada ce. Mama ki rinƙa mata wa'azi wallahi, ta nemi kariya daga zuciyarta domin idan ka fara jin haushin abunda mutum ke yi tofa hassada ce zata fara shigowa tsakani, kuma dama ni tuni na fahimce ta"
"Allah dai ya kyauta ya kuma shirya ta kawai, ai taga ɓacin rai na wallahi"
Ummi na shirin magana Ya Muhammed ya shigo ɗakin, bai zauna ba ya ce ma Mama yana kallonta.
"Mama ki zo inji Baba yana parlonsa"
Tashi tayi tana amsawa tabi bayansa aka bar Ummi ita ɗaya.
Mama ta daɗe a parlon Baba ɗin, dan har Ummi wani bacci mai cike da wani irin rikitaccan mafarki ya fara ɗaukarta.
Dawowar da Mama tayi ce ta farkar da ita.
A hankali ta miƙe zaune tana dafe kanta ta ce.
"Mama har kin dawo? kin jima"
Zama Mama tayi akan kujera yanzu wacce ke fuskantar Ummi ɗin ta ce.
"Eh wallahi mun tattauna ne akan aurenku gaba ɗaya aka haɗesa dana su Yusura bayan sallah ƙarama da sati biyu aka tsaida. Dan naki ma shi Jamilun so yayi kamin azumi a ɗaura shi, to sai Baba ya ce masa ayi haƙurin bayan sallar dai, saboda akwai na ƴan uwanki ma, sai a haɗesu a tare, ayi a wace wajan".
Gani Mama tayi Ummi ta faɗa cikin tunani fuskarta ta nuna damuwa.
Mama ta ce.
"Ummi yaya dai?"
"Ba komai Mama, kawai na tuna wani abu ne"
Girgirza kai Mama tayi tana maida hankalinta ga Ya Muhammed daya shigo yana bata labarin cewar kamar gobe ne za'a kawo lefen Safiya, dama abunda ya dakatar da kawo lefen mutuwar Salma ce, to yanzu kuma kusan an kusa arba'in ma da mutuwar tata.
"Amma naji Baba ya ce a bari sai zuwa jibi wai"
Mama tana duban Muhammed ta ce.
"Akan mi za'a bari sai zuwa jibin?"
"Ammi ce man da wata magana, wai gobe ne ake addu'ar arba'in ta Salma, bai kamata a kawo su a ranar ba, a bari sai zuwa jibi, ni nama manta wai ashe har tayi arba'in Mama?. Kai duniyar nan na sauri wallahi"
Mama taji daɗin karar da Ammi ke yi mata ta ce.
"Haka ne nima na sha'afa ne, amma ɗazu ne mafa na bada ayi abincin da za'a raba na sadaka goben"
"Ni ban manta ba Mama"
Ummi ta faɗa tana jin wata kewar Salma har cikin kokon ranta na taso mata.
Basuyi aune ba kawai suka ji Ummi ta fashe da kuka.
"Ohhh God. Haba Ummi, kuka dai?. Tunda Salma ta rasu har zuwa yau kuka kike mata, kuma ba'a son yawan kukan nan"
Ya Muhammed ya faɗa yana kallonta da tausayi.
Mama datai shiru ta girgirza kai kawai, dan ita daurewa kawai tayi, dan mutuwar kamar zata dawo mata sabuwa ne haka take ji itama.
Ummi ba abunda ta tuna sai ranar da zata rasun, take ce mata.
"Aunty Ummi ji nake kamar zan...
Sai ta dakatar da ita.
"Wallahi