Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 36

21K to 24K   out of 106.4K words

da Safiya.

"Subhallahi Maman yara mike faruwa ne naji ihun Ummi?"

Mama ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Ammi ta ce.

"Bari kawai Ammin yara wannan yarinyar gata dai babba a cikin yaran nan amma tana gani kowannensu na fiddo da miji banda ita, ko tsayayya ma itafa babu, ita bata son kowa ya za'ai rayuwa ta tafi a haka kuma?, tana kallo ga ƙanwarta nan Safiya akwai mai zuwa wajanta, hatta Salma tana da saurara samarin nan amma ita banda ita, sai ka ce wacce baƙin Aljani ya aura"

Sai da Ammi ta saki wani murmushi a kafaice kamin ta fara nuna alhini akan fuskarta tana cewa.

"Ayyah ai Maman yara komai lokaci ne, ita da kanta zaman gidan nan akwai ranar da dole ya fara gundurarta, taji duk duniya gidan mijin dai shine gatan kowacce mace, yanzu dai ayi mata hakuri dan Allah"

Ɗagowa Ummi tayi tana hararar Ammi ƙasa-ƙasa tana ƙunƙuni a hankali yadda ba kowa zaiji ba sai ita ɗaya ta furta.

"Munafuka kawai"

Mama ko harga Allah da yarda da amincewar da tayi da Ammi ne ta faɗa mata, tunda, tunda suke da ita wani abun ɓacin rai ko nuna wani halin kishi basu taɓa yi ba, yadda take ma Safiya faɗa idan tayi ba dai-dai ba haka take ma su Ummi ɗin, idan abu ta sayo haka zata raba dai-dai taba su, shi yasa kawai ta yadda da Ammi ɗin sosai. Amma su Salma da Ummi kwata-kwata kamar wa'inda aka shafama Ammi baƙin jini akan fuskarta suke gani, basa ƙaunar Matar ko kaɗan can tashinsu a gidan, ita da Aunty Murja gani suke sune mugun munafakan da suka hana ruwa gudu a gidan.

Mama na ganin lokacin da Ummi ke hararar Ammi tana murguɗa mata baki. Girgiza kai kawai Mama tayi tana nuna Ummi ta ce.

"Tashi ki bawa mutane waje marar kunya kawai"

Tashi Ummi tayi tana turo baki gaba ga hawayen dake zuba mata har lokacin.

Bin bayanta Ammi tayi da kallo tana mata wani irin kallon ƙurulla har sai da Mama tayi mata magana sau biyu kamin ta dawo cikin hayyacinta tana basarwa haɗe da ƙara bawa Mamar haƙuri suka fice ita da Safiya.

"Wallahi Muhmmd wa'innan yaran basu da hankali, amma wata rana zasu gane abunda nake ta gaya masu wallahi"

"Mama kawai addu'a zakiyi ta masu, kamar dai yadda suke faɗa lokaci ne zata daina wallahi"

"Hmm to Allah dai ya shirya min ita"

Suna zaune Salma tayi sallama a ɗakin ta shigo tana binsu da kallo ganin fuskarsu babu walwala, dan ita tun ɗazu ta fice daga gidan zuwa can gidan wata ƙawarta kitso sai yanzu take dawowa.

"Mama miya faru ne?"

"Ke daga dawowarki zaki tsare Mutane da tabbayoyi, to ba'a sani ba ƙara gaba"

"Kai Ya Muhmmd daga tabbaya?"

"To baza'a faɗa ɗin ba"

Ganin fa ran Mamar ma a ɓace yake yasa bata ƙara gigin tabbayarta ba itama ta juya ta nufi ɗakinsu tana turo baki gaba.

Shigarta ɗakin taja ta tsaya ganin Ummi na share hawaye har lokacin fuskarta daka kalla kasan tasha kuka, ga fuskar ta ƙunbura da marin da Mama tayi mata har biyu.

"Subhallahi Aunty Ummi miya faru ne wai?"

Zama Salma tayi tana kallonta sosai haɗe da shafa kan fuskarta tana mamakin ƙunburar fuskarta da tayi da shatin mari.

"Aunty Ummi waye ya mare ki dan Allah?, mi ya faru ne?"

Salma ta ƙara tabbayarta da mamaki da ɗan tashin hankali akan fuskarta.

Ajiyar zuciya Ummi tayi tana kallon Salma ta ce.

"Kin san kin barni da Ya Muhmd akan wannan mutunan da zai zo waje na da sunan yana sona?"

"Eh hakane mi ya faru ne ya zo ɗin?"

"Ya zo Salma, wai kin gansa ma kuwa?, kwata-kwata bai dace da yin aure bama a yanzu, ya tsufa ga wani irin muni da Allah ya bashi, irin Alhazawan nan ne masu ji da kuɗi, yadda kika san irin masu ƙungiyar asirin nan haka wallahi yayi min kama dasu. Ni kuma kawai na gaya masa bana sonshi, ina ma laifin ɗansa ya zo nema ma aure?, amma shi ai abun dai da kunya. Shine fa Ya Muhmmd ya zo ya gaya ma Mama shine ita kuma ta kama ni tana mari, nasan ɓacin rai ne yasa ta hakan"

"Subhallahi Aunty Ummi ke ɗin ce wallahi wani lokacin nima kaina sai naga kamar wacce Aljanu suka shafa. Kowa ke baki so?, dubi fa abunda kika ce wai mummuna ne mutunen. Haka fa kika ce ma Al'mustapha mai ƙiba da ƙaton ciki. To wai ke waye kike so ne?, ke kowa shikenan bai miki ba?. Kuma ma ya akai bai shigo gidan ba kuka tsaya daga waje?"

Harara Ummi ta ɓalla mata tana cewa.

"Na ɗauka ai ke ce zaki fara fahimtata, sai gashi kema kina son juya min baya. Ni babu wasu aljanu dake gare ni yawwa. Kuma shigowa gidan nan ya za'ai dama su shigo gidan nan bayan ba'a sanar da Baba?, ai so sukai na fara amincewa kamin su fara zuwa gidan kai tsaye suga Baba"

"Ba wai na juya miki baya bane, kawai kin fara bani tsoro ne nima"

"A'a dodo na zamar miki ba tsoro ba. Wai tsaya dan Allah Salma, zaki iya auran mutum baki sonshi ne?, ko kuwa ke ana miki haka ne kamar yadda ake min?"

"Ni ai kin san zuciyata mai rauni ce, zata iya son wadda ke ba lallai ne ki so shi ba, ni banda wannan baƙar aƙidar irin taki"

Harararta ta ƙarayi tana taɓe baki ta ce.

"Shi yasa kuma ake yaudarar ki a soyayya ba"

"Hmm ai ni idan zanyi so ina so ne tsakani da Allah, wasu Mazan kuma sona sune kawai dan jin daɗin kansu ba wai dan suna son ka zama Matar su ba, wacce suke so ta zama matar tasu sun ajeta a gefe ne, da yawan Maza haka suke a wannan zamanin"

Salma ta faɗa tana jin wani iri a cikin ranta, dan gaskiya Ummi ta faɗa shi yasa har zuwa yanzu ta kasa fiddo na aure, duk yawanci yaudarata ake yi, saita so mutum kawai taji yayi aure ko kuma ya daina kulata haka kawai, dan har kuka Ummi tasha kama Salma nayi akan soyayya, shi yasa wani lokacin Salma ke kallon Ummi tana cewa inama ita ce Ummi ɗin, saboda so wahala ne ma wani lokacin gara kawai kayi auren idan ka shiga gidan mutum ka so shi sosai daga baya.........

PAGE 16

Zama Mama tayi akan gadon tana kallon Ummi yadda take kallon saman rufin ɗakin, dan bata ma san ta shigo ba harta zauna kusa da ita bata sani ba, tana can tana tunin data ga ya aure ta a ƴan kwanakin nan.

A hankali Mama tasa hannunta tana dafa Ummi haɗe da kiran sunanta.

Saida taɗan firgita kamin ta miƙe zaune tana jin kanta na amsawa sosai ya sara mata. A hankali ta riƙe kan nata tana duban Mama.

"Mama yaushe kika shigo?"

"Hmm ya za'ai kisan yaushe na shigo?, baccin na shigo na iske ki kina wannan banzan tunanin daya aureki a kwanakin nan. Wai shin Ummi mike damunki ne?, mi kike tunani ne kwana biyun nan ne haka?"

Sauke lumfashi kaɗan Ummi tayi kamin ta sadda kanta ƙasa ta ce.

"Mama babu wani abu fa wallahi"

"Uhm idan tayi wari maji ne ai. Yanzu dai ki tashi kije Babanku na parlonsa yana son magana dake, akan tafiyar nan taki da zakiyi gobe zuwa Kano. Ki sake gaya masa tafiyar duk da dai na faɗa masa, amma nasan halinsa zaki iya tashi gobe da tafiya kije sallama dashi ya ce ai baki zo kika gaya masa da kanki ba, to bana son abun ɓacin rai, gara kije ki ƙara gaya masa"

"To Mama zanje"

"A'a tashi fa zakiyi yanzu kije nama gaya miki"

Mama ta faɗa tana miƙewa daga kan gadon ta fice daga ɗakin.

Ummi ta bita da kallo.

A zuciyarta take tunanin, ita dai Mama indai akan Aunty Binta ne to zaku iya samun matsala da ita, koma waye kai kuwa. Sai ka ce tana tsoronta, ta rasa gane mike faruwa da Mamar tasu, iya saninta babu uwar da Aunty Bintan ke mata, saima idan sunje gidan zasu taho ne take ɗan bada taliya guda ɗaya ko biyu ko uku da shinkafa ƴar tiya ɗaya a kawoma Mamar, duk da irin arziƙin da mijinta yake dashi. Wani irin hali ne da Aunty Bintar dan abunda bata so shine tafi badawa. Dan akwai wata sallah da Ummi ɗin taje mata. Yadda tasha aiki da sallar nan kai ka ɗauka Jaka suka samu ko ƴar aikinsu ce, kaca-kaca haka dangin mijin suka zo suka same ta, daga wannan ya ce Ummi ɗakko min kaza sai wannan ya ce ɗakko min wannan, dan wata har cewa tayi, kai ƴar aikin nan kinyi dacen ta, sai da ƙanwar mijin ta ce mata ai ƙanwar mai gidance fa.

Katse tunanin tayi tana sake jin ranta na ɓaci da tafiyar nan, ita kaɗai tasan yadda take ji da wahalar da take sha a gidan Aunty Binta, su Mama baza su gane ba, tunda labari kawai suke ji, kuma da alama Mamar ba wani yadda zatai ba, garama Salma sun taɓa zuwa sunyi sati biyu da ita a gidan taga irin yadda take shan wahala, dan gaba ɗaya aikin gidan Aunty Binta dawowa yake a kanta, hatta ƴarta Anam rainonta saiya dawo kanta, kuma abunda Ummi tafi tsana shine ɗaukar yaro, kwata-kwata ita bata da jumurin wannan, amma haka zata bata ita har sai ta fara kuka, kukan ma sai yarinyar ta kai ga siƙewa tayi fushi tukunna zata zo ta ɗauketa tana mazurai, sai ka ce Ummi ɗin ce ta sata kukan.

Girgiza kai tayi tana sauke ajiyar zuciya a fili ta fice daga ɗakin ta nufi ɗakin Baban nasu dake can gefe guda.

Koda tayi sallama sai taji muryar Ammi na amsawa ita da Baba dake zaune a ƙasa Ammi ɗin na zuba masa abinci.

Tana shiga ta sami waje ta zauna tana kallon ƙasa haɗe da gaida Baban.

"Lafiya lau Ummi"

Ya amsa gaisuwar tata.

Daga nan tayi shiru har sai da Baba ya ƙara mata tabbaya kamin ta ɗago tana bin Ammi data kasa ta tsare a zaune taƙi tashi ta tafi.

Ummi ta ɗan taɓe baki tana kallonta kamin ta maida hankalinta akan Baba ta ce.

"Dama Baba zuwa nayi na gaya maka gobe idan Allah ya kaimu zan tafi Kano gidan Aunty Binta, zanyi mata sati biyu"

Shiru Baba yayi yana cin abincin da Ammi ta zuba masa, har Ummi na tunanin ko baiji bane, sai taga tabbas yaji ɗin.

Turo baki tayi dan dama Baban wani lokacin haka yake, idan kazo tabbayarsa abu sai ya gama baka haushi wani lokacin ma ya ce babu gidan wadda zaka je.

Ita dama zaice bata zuwa ai da gaba ta kaita wallahi.

"Yanzu ke Ummi har gobe ne kuka shirya tafiyar taki, amma sai yau zaki zo ki gaya min?, haka ma uwar taki tazo min da maganar ɗazu nayi dai shiru ne na kyale ta, dan idan na ce zanyi magana rayuka ne zasu ɓaci. To daga yau idan har zakuyi tafiya ta rage saura kwana uku ko ma sati ɗaya azo a rinƙa faɗa min da wuri, bawai a rinƙa min tashi na kama ka ba, kinji abunda na faɗa?"

Da sauri Ummi ta ce.

"Eh Baba naji. Insha Allah za'a kiyaye"

"Tom Madallah"

Ya faɗa yana saka hannunsa a aljihunsa ya zaro naira dubu biyar ya miƙama Ummi ɗin ya ce.

"Ga wannan kiyi kuɗin Mota dashi. Nima inaga jibi zan zo Kano ɗin, kwana biyu ban leƙa su Auntynku ba ta can"

"To Baba na gode Allah ya ƙara buɗi, ya kaika lafiya kuma"

"Ai zaki leƙa can ɗin ko?, ki gano ƴan uwan naki"

"Eh Baba dana samu lokaci kamin na dawo zan je insha Allah"

"To yayi kyau hakan ma"

Ya faɗa yana maida hankalinsa ga abincin da yake ci kaɗan-kaɗan.

Ammi dake zaune sai taɓe baki take tana jin haushin daya ce zaije Kano jibi wajan makirar Matar nan tashi, dan ita tafi jin zafin Aunty Murja akan Mama, dan gani take Aunty Murja yafi so, tunda harya iya kaita Kano cikin birni ya aje ta, amma su ya barsu a wannan gurgurarran gari. Kuma idan wata hidima ta tashi Aunty Murja ɗin ta zo garin sai tayi ta masu wani irin kallo.

Ummi na fita Ammi ta ɗanyi gyaran murya ta ce.

"Wai yanzu Baban yara mu shikenan a nan zamu ƙare kenan?"

"Ban fahimce ki ba Asma'u"

Ya faɗi ainafin sunanta, yana kallonta da mamakin maganar tata.

"Hmm haba Mlm tsakani da Allah mu shikenan muna nan a ƙauye ita kuma Matarka a wani ajeta a birni, ai idan adalci ne muma a maida mu Kano ɗin ko?"

Murmushi ya saki kaɗan haɗe da girgirza kai, ya ɗauki ruwan shan dake gabansa ya sha kamin ya aje ya ce.

"Asma'u sai yaushe ne zaki daina mitar a maida ku Kano kuma ne wai?. Ya kamata zuwa yanzu kin manta da wannan zancan. Na riga na gaya maku bazan iya maida ɗaya daga cikinku Kano ba, saboda harkokina nafi yinsu a nan, ita ma ita ce ta ce taji ta gani a can zata zauna, baki ga sai nayi wata ko sati biyu bama bata ganni ba?, saboda ita ce ta ce ta amince duk sadda ta ganni. Kuma in banda abunki ku bada ga Katsina na ɗakko ku ba?, ita fa ƴar Kano ce dama a can na ganta. Kano idan kinga na shige ta to kayan kasuwancinmu ne na noma suka fara lokacinsu, ko yanzu abunda zai kaini kenan, sai kuma nayi mata ko sati biyu ne na dawo nan. Kuda kuke cikin gata ma kullum kuna gani na ita fa?"

Sai kuma ta saki murmushi tana tunanin ai sune ma ake so, ba wai Aunty Murja ba, tunda har ya iya shafe wata ko satika baije inda take ba, zamansu a nan ɗin ma wata ni'ima ce.

"Kuma rayuwar birni Asma'u sai wadda ya saba da ita fa, saboda idan kuka koma a yanzu baza ku iya zama bama wallahi, rayuwar can tafi ta nan wahala nesa bama kusa ba, gara nan ɗin dai, danni nan ni kaina nafi jin daɗin rayuwar karkara"

"Haka ne kuma Mlm gaskiyarka"

"Yawwa kin gane kenan?"

Ya faɗa yana tashi daga inda zaune ya zauna akan kujera. Zai ɗauki waya Ammi ta ƙara cewa.

"Ni ko na ce Mlm akan yaran nan su Ummi"

Aje wayar yayi yana kallon Ammi ya ce.

"Miya faru akan nasu?"

"A'a ba wani abu bane dama dai cewa nayi bai kamata ace har Safiya zatai aure ba gashi har bikin nata nata matsowa ace kuma kamar Ummi da Salma na zaune a gidan nan ba, ai kamata yayi ace ka zaunar dasu ka basu zaɓi su kawo mijin aure, kaga ba sai a haɗe bikin nasu ba ayi a wuce wajan"

Ɗan murmushi manya ya saki yana kallon Ammi kamin ya ce.

"Asma'u kenan, kuna bani mamaki keda ita uwar yaran, kullum ace ku shikenan hankalinku a tashe akan yaran nan basu fiddo miji ba?. Shifa komai da kuke gani lokaci ne dashi. Dan haka ni Yara na bazan taɓa matsa masu ba, akan wai su kawo mijin aure, idan lokacin auren ya zo dole nasan ina zaune zasu turo su ne waje na, dan haka gaskiya daga ke har ita bana son a ƙara min magana wacce ta danganci wannan akan yara na"

Wani maƙirin murmushi Ammi ta saki a ranta, wani daɗi ne ya lulluɓeta ganin Mama dake ƙofar ɗaki tana jin abunda suke tattaunawa. Kai tsaye Mama ta shigo ɗakin tana jin daɗin yadda Ammi ta ɗauki ƴaƴanta kamar ita ce ta haifesu.

Tana kallon Ammi ta ce.

"Hmm Ammin yara rabu dashi kawai, ai ni harna gaji da tararsa da irin wannan maganar, ai shi bazai gane irin halin da uwa take shiga ba a lokacin da ƴaƴanta Mata suka kai minzalin aure amma shiru babu miji babu labarinsa ba"

Mama ta ƙare maganar tana kaiwa ta zauna a kusa da Ammi dake ɗan nuna damuwa sosai akan fuskarta ta ce.

"Wallahi fa da abunda zance mashi kenan sai gaki kin shigo"

Gyara zama Baba yayi yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya kamin ya ce.

"Miye abun tada hankali a nan?, ni banga abunda zaisa a rinƙa tada hankali akan yara basu samu miji da wuri ba, lokacinsu ne baiyi ba na auren har yanzu, da ace lokacin yayi to tabbas ko kwana ɗaya bazasu ƙara ba zasu yi auren, shifa Aure da mutuwa da arziƙi duk lokaci ne dasu, ko kun manta ne wai?"

"Amma Mlm ai duk abunda kasa ma ranka kana so sai kaga Allah ya taimakeka ka samu, da ace zaka yi masu jan ido ka nuna masu dole su fiddo da mijin ai da yanzu wata maganar ake ba wannan ba Mlm. Kaga Ummi kwata-kwata ita bata bawa kowa damar soyayya bare har takai ga maganar aure"

"Kai amma tayi min kyan kai"

"Mlm ka ce tayi kyan kai?"

Mama da Ammi suka faɗa a tare da mamakin Baba ɗin.

"Eh kware ta birge ni, ai tasan miye take yi ne, idan mijin auren nata ya zo kai tsaye zai zo ya same ni ne, idan sun dai-daita nayi bincike yayi sai ayi auren kawai, ba wai ka zauna kuyita soyayya da mutum yana ɓata maka lokaci ba, kuma yawancin samarin yanzu haka suke ma ƴan mata suna yaudararsu. Kuma kike cewa wai nayi masu dole. Hmm gaskiya ku Mata na yarda ƙaramin tunani ne daku. Yanzu nayi masu dole kawai sai suje su fiddo wadda ma bai dace dasu bafa?, azo ayi auren azo kuma ana wallahi tallahi, to ni yara na bana fatan nayi masu aure su fito, nafi so ace idan suka tafi to sai mutuwa kawai zata fiddo dasu daga gidan Mazajensu. Dan haka yanzu kawai ku taya su addu'a shine abunda ya dace, ba wai ku tasa su a

8 / 36