Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   17 / 36

48K to 51K   out of 106.4K words

Inna ta ki taimaka min kije ki basa haƙuri wallahi hannuna zafi yake"

"Ni zanje ma na basa haƙuri bake ba?, ai ko zaki daɗe yarinya, ai kawai tashi zakiyi kije ki basa haƙuri dan kanki, idan yaga damar haƙura to, idan bai haƙura ba kizo ki ci gaba daga inda kika tsaya dan ko tayaki bazan ba, waye yaja ma kansa?, ai ke ce"

Ɓata fuska Sadiya tayi tana kallon Inna zatai magana Sule yayo sallama a cikin gidan.

Wata hamdala Sadiya tayi a fili tana miƙewa daga inda take tarbi Sule tana cewa.

"Yawwa Ya Sule dan girman Allah ka taimake ni"

"A'a miya faru kuma Sadeeey"

"Uhum uhum Ya Sule ba Ya Umar bane daga dawowata school shine kawai ya saka ni wankin kayansa masu ub*an yawa gasu can, kuma ai dai kasan bana yin wanki mai yawa haka saboda yadda hannu na ke min raɗaɗi duk lokacin da nayi"

"Wanki kuma Inna?, haba Inna ai kamata kina saka baki wajan hanasa sata wani abun"

"Kaga Sule baka san irin abunda take yi bane har yake jawowa ana saka ta aikin ai, dan haka ni bazan saka baki ba, ai dai kasan da ace haka nan ne batai wani abun ba haka kawai bazai saka ta wankin kayansa ba"

"Amma Inna...

"Amma mi?, kaga idan kaine zaka zauna kayi mata wankin a matsayin ita tayi to bismillah ni ba ruwa na, dan muddun bazata daina jan faɗa ba idan har ta fita ta dawo to ni kuma bazan fasa daina ƙin saka baki ba wallahi, dan so nake kamin mu tattara mu koma Kano ta shiga taitayinta, dan bazai yiwu a koma birni da ita ba tana jan faɗa haka ba"

"To ai Inna a birni ba'a duk wannan ai sai a ƙauyen, a birni wama zata gani bare harta jashi faɗa?, ai birni ko fita waje saita zame maka dole ne fa, bare ga mata ma"

"Ai hakan yafi ma wallahi"

Kamo hannunta yayi suka zauna, ya dubeta sosai ya ce.

"Yanzu dai zan tayaki wankin, inayi kina min dauraya kina shanyawa, muyi sauri kamin ya fito, amma idan muka gama zaki gaya min miye kikai yasa ki wannan wankin?"

"Eh..eh..eh zan faɗa maka Ya Sule"

"Okay good tashi oya mu ci gaba da yi"

Da sauri ta miƙe ya fara wankin, tana ɗauraya, suna yi suna labari Inna na binsu da kallo tana girgirza kai.

Zaune suke bayan gama wankin Sule ya ce.

"Ina jinki miye ya faru?"

"Wai fa Ya Sule daga zuwa na school muka haɗu da wa'innan ƴan bakin layinmu wa'inda suka taɓa zuwa nan kawo ƙarata na watsa masu ƙasa a ido?, shine suka kaini wajan Malamai suka ƙullamin shirri wai na same su a makaranta suna zaune suna cin abinci na watsa masu ƙasa a cikin abinci na zubar da abincin harna fasa masu wata kula, sana na ɓata masu kayan Makarantarsu. Kuma Allah wallahi Ya Sule bani ba ce, ban san miya faru dasu ba sharri ne kawai suke min"

"Kai Sadiya anya kuwa bake ba ce ɗin?, zaki fa iya aikata hakan, tunda har zaki iya watsa masu ƙasa a ido"

Inna ta faɗa tana ƙare mata kallo.

Kwaɓe fuska tayi tana matse wasu guntun hawaye ta ce.

"Haba Inna a gabanki fa na tafi school, duka yaushe naje makarantar ma da har zanyi hakan?"

"Ai nasanki ne kamar yinwar cikina wallahi, Allah dai yasa bake ɗin ba ce kawai"

"Inna a yadda ta bada labarin ba ita ɗin ba ce, inaga sunyi mata hakan ne kawai dansu rama irin abunda tayi masu. Ke kuma sai kikai yaya a wajan?"

"To ni Ya Sule kawai cewa nayi ni bani bace nayi masu hakan, amma Mlm Hamisu yaƙi yarda ya fara zuba min bulala a gadon baya na, ni kuma zafin bulalar tasa yasa ni miƙewa tsaye na gudo gida"

"Kashh mi yasa baki tsaya duk kinyi masa bayani yadda zai gane cewar shirri ne suka haɗa miki ba?"

"Haba Ya Sule wallahi a yadda suka je suka haɗa ni da Malamin nan wallahi bazai taɓa yarda cewa ba shirri bane suka haɗa min ba"

"Yayi kyau zamu je school ɗin ai tare dole a ɗauki mataki akansu gaskiya"

"A'a kai ina ruwanka? ai shi Umar ɗin ya ce shi zaije maida ita gobe"

"Amma dai Inna kin san shi Ya Umar idan ya je akwai matsala ko?"

"Ahh babu wata matsala wallahi, kai dai kawai kake ganin hakan"

"Ni dai wallahi bana so Ya Umar yaje kaini school, wallahi sai yasa an ƙara zane ni nima, ni dai Inna ki san yadda zakiyi Ya Sule ya kaini kawai"

"To sannu uwata, ai ko tunda ya amsa shi zaije kin san ban isa na ce kuma Sule ne zai kaiki ba, dan haka keda Sulen kusan yadda zaku yi a goben shi Umar ɗin ya fasa zuwa sai Sule ɗin ya kaiki"

"Haba dai Inna akwai yadda zakiyi fa ki taimaka mana please"

"Hmm Allah ban san yadda zan maku ba, amma dai zan duba"

"Yawwa Innarmu"

Sadiya ta faɗa tana murmushi, Inna ko girgirza kai kawai tayi tana tana kallonta.

Jin motsin Ya Umar na fitowa daga ɗakinsu yasa Sadiya shan jinin jikinta tana natsuwa sosai kamar ba ita ba.

Da alama bacci yasha sosai dan idonsa sun nuna hakan.

"Ya Umar ina wuni?"

Sule ya faɗa yana gaida sa.

"Lafiya ashe ka shigo gidan?"

"Eh wallahi yanzu na dawo ba daɗewa"

"To yayi kyau"

Kawai ya ce masa yana bin kayan wankinsa da kallo sosai yana yi yana taɓa su, ganin sun fita sosai yasa shi kallon Sadiya da tayi ƙasa da kanta ya buɗe baki ya ce.

"Amma ba ke ce kikai wannan wankin duka ba night?"

Turo baki tayi tana cewa a hankali.

"Wallahi ni ce fa Ya Umar"

"Cewa nayi sai kin rantse min?, ai kin gama tona kanki bake kaɗai kikai wannan wanki ba tabbas"

Kamar Sule zaiyi magana sai kuma yaja bakinsa ya tsuke kawai dan idan yayi magana tsaf zai gano wani abu, dan Ya Umar akwai saurin harbo mutum idan baida gaskiya.

"Inna inaga fa gobe zan koma Kano, amma da yiwuwar na turo maku kuɗi ku taho gaba ɗaya, bana jin zan ƙara zuwa garin nan gaskiya"

Ai wani irin mashahurin daɗi ne ya lulluɓe Sadiya bata san lokacin data furta Alhamdulillah ba a fili, sai kuma tayi saurin rufe bakinta tana zaro ido waje, Allah ya sota Sule ne kaɗai yaji hamdalar da tayi.

Duƙawa yayi ƙasa-ƙasa ganin Ya Umar ɗin hankalinsa na wajan Inna suna magana ya ce.

"Kinga ki rufa mana asiri Sadeeey, daya jiki fa, tsaf wallahi ya ce ya fasa tafiyar nan"

"Wallahi Ya Sule banma san lokacin dana ji bakin nawa ya furta Alhamdulillahin ba, daɗi ne ya ishe ni, ai gara ya zo ya tattara ya koma wallahi haba dama na gaji da zamansa wallahi mutum sai muguntar tsiya"

"Hhhh lallai yarinya, baki ji kuma ya ce nanda sati ɗaya zai turo kuɗi mu bisa Kano ɗin ba?, shikenan kuma mun tashi daga garin nan kwata-kwata mun koma kusa dashi ba?"

"Nifa ko bana son mu tashi daga garin nan Allah Ya Sule, amma ita Inna naga sai murna ma take"

"Ai ko ni Sadiya ina murna, tabɗi jam ke waya gaya miki zaman ƙauye nada daɗi, eh to ta wani wajan dai yafi birni daɗi zama da daɗin ma'amala da jama'a, amma birni kam ko Annabi ya ce ayi maka barka duk lokacin daka tashi daga kauye ka koma birni"

"Hakane amma ni wai Inna harda cewa wai sai nayi karatun nan na likitoci idan muka koma"

"Ai ko ni yarinya makaranta zan koma idan muka koma birni, dama tunda na gama secondary ban samu na ci gaba ba, dama a cikinmu Ya Umar ɗin ne kawai ya wuce degree gashi ya kusa haɗa karatunsa, yana shirin ci gaba da wani kuma"

"Kai nan har wani ci gaba zaiyi dama?, ai na ɗauka shi ya gama karatun shikenan kuma"

"Tabɗi jam waya gaya miki ana gama karatu?, ai shi karatu kullum ƙara zurfafa ake a cikinsa in gaya miki"

"Uhum lallai sannunsa, ai ni bazan iya ba, nama samu na taƙarƙara nayi wannan karatun da Inna taci buri akan sai nayisa"

Dariya taba Sule ya dara yana ƙara jadadda mata daɗin karatu da irin yadda duniya zata rinƙa ganinka da daraja a ko ina kuma zaka shiga a dama da kai, ita dai jinsa kawai take tana kuma kasa kunne wajan su Inna dake ta maganar tashin da zasu yi.......

PAGE 33

*UMMI POV*

Ganin kiran Mama ya sake shigowa ne yasa Ummi aje kayan da take wankewa na a kitchen bayan ta gama abinci tana wanke wasu kwanuka da tayi amfani dasu. Kwaɓe fuska tayi, dan tasn zancen gizo baya wuce na ƙoƙi.

"Assalamu alaikum Mama ina kwana?"

Daga can cikin wayar Mama bata amsa sallamarta ba ta fara cewa.

"Wato Ummi abunda kike je kika aikata gidan Babanku kenan ko?"

"Mama ni fa ban gane ba, mi naje na aikata kuma?"

"Ke na ci ubanki wallahi, bana son wasu kauce-kauce na gaya miki, fitowa zakiyi kimin bayanin abunda ya haɗa ki da waccan Matar da har zata kira na tana bigemin worning a kanki, kin san bana shiga harkar wannan matar tunda tun farko ta nuna ba ƙaunarku dama take yi ba"

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce.

"Wallahi Mama dama daga zuwa na gidan fa ta fito ta fara gaya min maganganu masu zafi, dama can ta saba ce mana ƴan iska, wai harda cewa zamu koyama ƴarta iskanci da rashin kunya, shine fa ni kuma na fito fili na faɗa mata cewar mu ba ƴan iska bane, amma wai matar nan Mama saita shige ɗaki jim kaɗan sai gata Mama ta fito da wani ƙaton katako wai zata bige ni dashi, to Mama ni kuma zan tsaya ne ta bige ni haka kawai?"

"Au dama haka akai?"

"Wallahi kuwa Mama kinji dai abunda tayi min duk shi yaja haka"

"To ba komai ai ni kin biya ni ma, gobe ta sake miki hakan bance ki raga mata ba, amma bance kuma ki wuce gona da iri ba, tunda ta ce ita bata da mutumci to a nuna mata wajan ta zo. A da dai tayi maku son ranta, wacce irin wahala ce baku sha bama?, hatta ita Salma nasan Allah kaɗai nasan wahalar da take sha a wajanta"

"Wallahi kuwa Mama Allah kaɗai ya sani, saboda ita Salma haƙurinta yayi yawa, ko ji fa ba'ayi irin abunda take mata, saboda bata taɓa faɗa"

"Ai dai lokaci ya kusa itama ta gama ta bar mata gidan sai taci kanta tasha baƙin ruwa makirar mata kawai. Ai kune nayi-nayi ku fitar da mijin aure amma kun tsaya kuna wasa da damarku, ai ita Mace dama jin daɗinta ace gidan mijinta amma ko gidan uban nata wata rana zamansa sai ya gundire ta wallahi, ku dai zauna Ummi ga bikin ƙannanku nan sai matsowa kusa-kusa yake amma ku kuna a zube ko mutum ɗaya wannan ban gani ba wadda za'a ce gashi ya fara shigowa gida da sunan aurenku yake sonyi, ni na rasa inda kuka kwaso Wannan nauyin jinin"

"Yanzu dai Mama kiyi hakuri indai aure ne muma zamuyi da lokacinmu yayi. Yanzu aiki nake ma Aunty Binta idan na ƙarasa munyi magana"

Ta ƙare maganar suna yin sallama, dan taga Mamar ta fara sako maganar Auren nan itama, to idan batai da gaske ba sukai sallamar tsaf ranta ne zai ɓaci daga ƙarshe.

"Hmm kai jama'a, wai shin mu zamu jawo mazan auren nan da tsiya su fito ne?"

Ummi ta faɗa a fili tana jin babu daɗi a ranta.

"Ni wallahi an fara kaini bango haba, abar mutum da abunda ya damesa ma mana, da wani auren ma ba gara babu shi ba"

Ta ƙara faɗa tana ci gaba da aikinta.

Sai da ta gama aikin ta fice daga kitchen ɗin ta wace bedroom ɗin data sauka ta zauna tana sauke lumfashi ta ɗauki wayarta dake kusa da ita data aje yanzu ta fara kiran number ɗin Maryam, dan ita ce kawai suke tattauna magana irin haka da ita.

Maryam na ɗaukar wayar bayan sun gaisa Ummi ta nisa ta ce.

"Bari Maryam ba jiya na ce miki zanje gadon ƙaya ba gidan Matar Babanmu ba?"

"Eh kin gaya min, kinje ko?"

"Hmm naje fa in gaya miki, ba sai mata ta nemi min akuyanci ba, wai harda ƙoƙarin duka na, saboda ma ta matuƙar ɗaukata shashasha"

"Tabɗi jam duka kuma?"

"Eh fa, ai ko taga ɗanyen kai, dan wallahi sai da na tabbatar ban bar gidan nan ba sai nabar mata tabo a jikinta, ni bata ci nasarar dukan nawa ba, amma ni taji a jikinta, kinga gobe ma tayi gigin cewa zata taɓa ni, dan sai nayi mata fiye da abunda nayi mata a yanzu"

"Innalillahi kai dan Allah Ummi, wai dukanta ki kai ko kuma mi?"

Dariya kaɗan Ummi ta saki kamin ta ce.

"A'a wallahi ba duka bane, kawai ƙaiƙayi ne ya koma kan masheƙiya fa, tana zuwa da sunan zata dakenin nasa ƙafata na taɓiye ta sai gata ƙasa ta faɗi, kuma akai sa'a ta faɗi akan bikinta, baki ya fashe ya haye yayi sumtum in gaya miki, nasha dariya, wai kinga irin borin kunyar data miƙe tana yi, harda su kiran Mama a waya tana farfaɗa mata magana, dan taga ta gaya ma Baba bai ce komai ba, bai kuma kira ni ba har yanzu"

"Lallai Ummi gidanku gidan kallo ne kawai, kuna sha'aninku, Allah ya kyauta"

"Ameen dai, ina Umma?"

"Wallahi Umma tana ɗaki ni ina parlo ne ma"

"Ohh Masha Allah"

"Kinga ni bama wannan ba Ummi, akwai dama wata magana da nake so muyi dake, dama ina so na kira ki sai ga kiranki kuma"

"To ina jinki Allah yasa dai lafiya?"

"A'a lafiya lau fa"

"Yawwa tom ina jinki"

"Yawwa kin san na taɓa baki labarin wani Mubarak dake so na"

"Haka akai tun kamin mu gama hygiene ko?"

"Yawwa kware da gaske, to yanzu shine mu ke magana dashi dai, dan nima kin san ba wasu samari ne dani ba Ummi. To dama kin san wayata ta lalace ce, haka nan dai nake amfani da ita, to munyi magana da Mubarak zai saya min waya, amma wai sai ya shigo gida Iyaye na sun san dashi tukunna zai ɗauki waya ya bani, kuma irin wayar da nake so ce iphone"

"To ke mi kike jira da har baki bashi damar shigowa gida ba har wannan lokacin?, ko dama baki son shi ne wai?"

"A'a gaskiya ina jin sonsa a raina Ummi"

"To kuma jiran mi kike yi?, ai kawai a shawarce Maryam ki ce masa ya shigo gidan kawai, yanzu fa Maryam ba'a wasa da dama irin wannan, mu ba gamu ba Maryam, mijin muke nema, wadda zai kwanta mana a rai muji muna son nashi ba, amma babu shi har yanzu, gashi gida su Yusura sun fitar da mijin an ta so mu gaba nida Salma, dan yanzu haka wallahi maganar da nake miki kamin na kira ki da Mama muka gama waya, sai da tayi min maganar munƙi fitar da miji, mun tsaya ruwan ido"

"Kai amma bana jin daɗin abunda ke faruwa wallahi, shifa aure lokaci ne dashi, karki damu kinji Ummi zakuyi indai aure ne wallahi. Kuma naji daɗin wannan shawarar taki zan kuma gaya masa ya turo ɗin kawai, kuma kema da yardar Allah zaki samu naki Mijin keda Salma insha Allah nan ba daɗewa ba"

"To ameen Maryam, amma Maryam zaka fitar da wadda baka so ne bai kuma kwanta maka ba?, dan Mazan nan akwai su masu sonka, amma wallahi Allah Maryam har zuwa yanzu banga wadda zuciyata take so ba ta kuma aminta dashi ba"

"To wai Ummi ina Mlm Auwal ne?"

Taɓe baki Ummi tayi tana sakin wani tsaki ciki-ciki ta ce.

"Kin fa san bana son lectura a rayuwata, bazan iya auren Malamin nan ba, yana da fa Mata"

"Haba Ummi to miye idan yana da matar?, kuma ai Mlm Auwal ai baida makusa"

"Tabbas baida makusa, amma ni bana son mai Aure wallahi, sai dai idan ya zama dole na auri mai auren, amma bana son na shigar ma wata gida ta rinƙa kallona da cewar na kwace mata miji"

"To Allah dai ya zaɓa mana abunda yafi zama Alkhairi kawai Ummi, amma idan mai sonki ya fito yana matuƙar sonki dan Allah Ummi karki ƙara wasa da damarki please, muddun dai shi yana sonki kamar ransa, dan wallahi sai ma kinfi jin daɗin zama da wadda yake matuƙar sonki akan ace ke kike sonshi, son kuma yafi wadda yake miki"

"Uhm shikenan Maryam insha Allah na gode sai munyi magana"

Sallama sukai bayan Ummi ta sauke wayar sai ta dafe kanta tana sakin wani hucin lumfashi mai zafi tana kallon ƙasa sosai ta zurfafa cikin tunani mai zurfi........

PAGE 34

*SALMA POV*

"A'a ki kawo nayi sharar kawai, karki damu fa Yusura"

"Haba amma fa zaki iya makara, kamar jiya, gashi jiyan har rasa exam ɗinki ɗaya kikai fa"

"Wai zaki bata ne ko kuwa zaki tsaya iyayi da feleken da kika riga kika saba?"

Aunty Murja ta faɗa tana kallonta.

"Amma Umma kina fa ji jiya batai ko baccin kirki ba, saboda jarabawar da suka fara a jiyan, haba Umma, kuma jiyan ma ke kika ja ta rasa exam ɗinta har ɗaya fa"

"Dalla gafara can, ina ruwana da wata jarabawa data fara?, ni dai abunda na sani shine kawai ayi min abinci da gyaran gidan yawwa, idan kuma ba'ai haka ba ba gidan ub*anda mutum zaije yawwa"

"Umma ana jarabawar?"

"Ko jarabawar duniya ce"

Ta faɗa tana shigewa ɗakinta.

"Kije ki shirya Aunty Salma dan Allah, jiya fa kike bani labarin idan aka shiga jarabawa ba'a ƙara bari kowa ya shiga ɗakin jarabawar, sai dai fa kayi asararta kayi C.O kenan fa"

"Hmm, kina ji fa ta ce idan kika ƙara taimaka min da aikin gidan nan bata yafe miki ba,

17 / 36