Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
tana kallon Doctor ɗin data kai Salma wajansa a asibiti ne yake sallama da ita a ƙofar gidan.
"Bawan Allah ina ce dai lafiya?, mima ya kawo ka ƙofar gidan nan?, ina ce dai ai daga ragin hanya shikenan ko, ko akwai wata alaƙa ce data shiga tsakaninku a jiyan bamu da labari?"
Kaiwa ƙasa yayi yana ƙoƙarin gaida ita tayi kicin-kicin da fuska tana ɗaga masa hannu haɗe da furta.
"Kaga bawan Allah Likita, idan ma wani abu ne ya kawo ka wajan wannan ƴar iskar yarinyar to tun wuri kayi ma kanka karatun ta natsu ka rabu da ita. Wai yama da haka ne kai daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaƙi?, an taɓa haka ne dama?, daga ganin mutum sai ka kwaso ƙafa ka wani ce zaka zo har ƙofar gidansu. Kai baka san wacece ita ba ko?, kai baka san daga duniyar da take ba, duka fa jiya ne kuka fara haɗuwa, shine kai har zaka fara wani tunani akanta ko?. To bari na gaya maka gara tun kan waje ya ƙure maka ka kama gabanka shine kawai ya fiye maka Alkhairi yawwa kaji da kyau ma"
Murmushi taga ya saki haɗe da cewa.
"Ayyah Umma ba wani bane yasa na zo wajanta sai dan na kawo mata magungunan data mance dasu a Motata jiyan"
Yana ganin lokacin data saki fuskarta harda sauke ajiyar zuciya tana faɗin.
"Ohho ai da kai baya ni tun wuri ko Likita bokan ture?"
Shi dai girgirza kai kawai ya ɗan yi yana ƙoƙarin miƙa mata ledar magungunan.
Har ya juya zai shiga Mota sai kuma ya fasa yana cewa.
"Umma zan iya ganin ita Salma ɗin idan ba damuwa?"
"A'a gaskiya bata ma gida ai tun jiya data fice cikin dare bamu sake jinta ba, kai baka san yarinya ce marar jin magana ba?, haka fa muke ta fama da ita so ake ma ayi sauri ayi mata aure karta je taja mana abun magana a cikin mutane, saifa tayi kwanaki bamu san gidan uwar data tafi ba, rana ɗaya kuma sai ka ganta ta dawo, ai shi yasa jiyan muka zo da ita na taso ta gaba saboda irin yadda take kwara amai kamar mai laulayin ciki"
"Ohhh shikenan Umma nagode fa"
Ya faɗa da sauri yana shigewa Motarsa ya tayar ya wuce yana barinta tsaye har lokacin tana bin bayan Motar tashi da wani ɗan iskan kallo.
Tsaki ta saki mai ƙarfi tana zafgama bayan Motar hararara harta ɓace ma ganinta.
"Aikin banza ni ce zan bari mutum kamar wannan Salma ki same shi a matsayin masoyi ko miji?. Hmm ina ai sai dai idan ba Murja nake ba wallahi"
Tana gama faɗar haka zata juya taji saukar maganar Abdul.
Juyowar da zatai kuwa tagansa tsaye yana ƙoƙarin gaida ita.
Zatai magana tana sakin wani murmushin tunanin da ƙwaƙwalwarta ta kawo mata wayarsa dake hannunsa ce tayi ƙara.
Ledar dake hannusa ce ya shiga miƙama Aunty Murja dake cike da naman Kaji, hannu na rawa tasa ta amsa tana iya jiyo ƙamshin Kajin da suka ji gashi sai tashin ƙamshi suke.
"Haba Alhaji Haladu ya da haka ne?, wannan wacce irin maganar banza ce?, kasan fa Naira miliyan ɗaya mu kai cinikin abun nan fa da kai yaya kuma zaka dawo min da wata maganar banza wai sai dai a bar maka Naira dubu ɗari takwas?"
Can ya ƙara ɗaga hannu sai ka ce yana magana mutanen a kusa dashi a yadda yake ɗaga muryarsa, muryar har cikin gida kana iya juyo ta tsabar bai iya wayar ba kwata-kwata.
Kashe wayar yayi yana kallon Aunty Murja haɗe da ɗan sakin fuska ya ce.
"Yi haƙuri Umma wallahi wani ne ke ƙoƙarin ɓata min rai"
"A'a ai dama yanayin kasuwa sai haƙuri"
"Yawwa Umma nagode. Ina ita Salma ɗin ayi min sallama da ita"
"Hmm Salma kuma?"
"Eh mana Umma, ko bata cikin gidan ne?"
Abdul ya faɗa da mamakin abunda ta ce ɗin.
"Au na ɗauka kasan halinta ne ai?. To dai bata kwana a gida ba, yanzu ma baka ga wata Mota data bar ƙofar gidan nan ba?, ai ina ce ka ganta ai ko?"
"Eh tabbas Umma na ganta"
"Yawwa to ai abokin shashancin nata ne wai ya zo yaji ta zo gida, dan jiya cikin dare daga wajansa take sun raba dare, shine yanzu ma ya kawo mata ɗankwalinta da sarƙa data mance a wajansa gashi a leda ma, to kuma bata dawo gidan nan ba, wata ƙila sai nan da anjima zaka samu ganin nata. Ni wai idan banda abunka marar kamun kai zaka aura Abdullahi?"
Wani irin baƙin ciki ne ya rufe Abdul baƙin kishi ya rufe masa fuska, sosai yake kallon ledar da Aunty Murja ta ce kayan Salma ne a ciki, da wani ƙato ya kawo mata. Juyawa kawai yiya yana cewa.
"Karki damu Umma ai jahadi zanyi, amma zan san matakin da zan ɗauka akan ta"
"Hmm to ai shikenan, wadda baiji bari ba ai yaji Ohoho"
Ta faɗa haɗe da taɓe baki tana juyowa itama ta shige cikin gida.
Tana shiga ta iske Salma nata fama da aikin gidan ita da Yusura na ɗan kama mata aikin.
"Umma ina kika je ne?. Nifa sai kamar naji muryar Abdul ɗin Salma a waje ko Umma?, dan dai munsa wannan karatun ya hanamu ji sosai"
Wata hamdala Aunty Murja tayi a zuci tana hararar Yusura ta ce.
"To faɗi ba'a tabbayeki ba, ban sani ba"
"Kai Umma"
"Mtswww"
Ta saki wani dogon tsaki tana shigewa ɗaki da ledar dake hannunta.
Zuwa can ta fito tana kallon Salma ta ce.
"Ga wa'innan magungunan abokin iskancin naki ya kawo miki su, dama jiya tsabar lalacewar da kuka tsaya yi ne a cikin Mota yasa kika mance masa da magungunan a Mota, shine ya biyo ki har gida ya kawo miki"
Runtse idonta da ƙarfi Salma tayi tana jin ciwo har cikin ranta, ƙasa miƙa hannu tayi ta amshi ledar magungunan sai Yusura ce data sa ta amsa tana cewa.
"Haba Umma miye haka dan Allah?, yanzu miya kawo wa'innan maganganun kuma?"
"Ke gafara can rufe min baki, bana ce karna ƙara jin ina magana kina kwatse ni ba?"
"Amm.....
"Mina ce miki?, amsa zaki bani kawai?"
Turo baki Yusura tayi tana bata fuska ta ce.
"Ai Umma abunda kike kwata-kwata babu daɗi wallahi"
"Ni zaki gaya ma abunda nake babu daɗi?. Har kin fini sanin abunda ya dace da wadda bai dace ba kenan kike ƙoƙarin cewa?"
"Aunty Murja kiyi hakuri dan Allah"
Cewar Salma, dan ita kam bata so akanta su samu matsala da mahaifiyarta.
Wani kallo ta juyo inda Salma take ta jefa mata tana nuna ta da yatsa ta ce.
"Munafuka ai duk ke ce ke ɗora ta kan hanyar da zata raina ni, amma nasan maganinku daga ke har ita ɗin aikin banza kawai"
Tana faɗar haka ta bar wajan.......
PAGE 12
*UMMI POV*
Mama ta kalli Ummi yadda take cin magani yasa ta girgiza kai tana ƙara dubunta sosai ta ce.
"Naga kina ɗaukar kaya kala kaɗan?"
"Mama nifa ba daɗewa zanje nayi gidan Aunty Binta ba, bazan ma iya ba ni wallahi"
"To ko dai wata ɗaya ko sati Uku ne ai sai kin mata"
Ɓata fuska Ummi ta sake yi dan ita wallahi batai niyyar tayi har wata ɗaya ba, ita niyyarta sati biyu ne zata yi idan ma takai satin biyun.
Ci gaba tayi da haɗa kayanta nata tana yi tana ƙara tunano abunda ya rinƙa faruwa a da ita a baya.
**************"Hello P.A"
Cewar Ya Muhmd dake zaune akan kujerar parlo yana waya da P'A na Office nasu.
"Eh hakane na fahimta"
Sai yayi ɗan shiru yana sake sauraronsa daga cikin wayar kamin zuwa can ya ce.
"Okay na gane insha Allah zamuyi magana. Tom nagode fa"
Yana ƙare faɗar haka ya yanke kiran yana kallon Mama data idar da sallah.
"Miya faru ne Muhmd?"
Mama ta faɗa tana gyara zamanta ta fuskanci Muhmd ɗin.
"Hmm ni abun nan na bani mamaki Mama"
"Wane abu kenan?"
Mama ta faɗa tana sake tsura masa ido da mamaki.
"Na farin jinin samari na wannan yarinyar mana Ummi. Wai fa wayar nan da nake yi da P'A yana sanar dani ne wani uban gidansa dake zaune a Abuja ya ga photon Ummi kuma wallahi da gasken-gasken yake shifa yaga Matar aure"
"Iko sai lillahi, shi ogan nashi da kansa ya ce hakan?"
"Wallahi kuwa Mama kin dai gani"
"To shi kuwa ina yaga photon Ummi har tayi masa haka?"
"Waya sani ma Mama?, can ƙila zai ci karo dashi a wani wajan"
Shiru Mama tayi kamin ta ce.
"Ai gaka ga tana nan, idan anyi sa'arta ta yarda da wannan ɗin to, idan kuma kaima ta watsa maka ƙasa a ido to. Ka dai gani yadda na rasa bakin da zan gaya ma Haj Salamatu yadda akai, sai da kyar na iya cire komai na shiga sanar da ita, saurafa kaɗan su sami matsala da Al'mustaphan da kanshi, sosai ta nuna masa ɓacin rai kuma ta hanasa auran ita yarinyar da yasa ya ce ma Ummi baya ra'ayinta"
"To Mama idan ma tayi ai ita ce tayi ma kanta fa ba wani ba wallahi"
Ya Muhmd ya faɗa yana ƙara gyara zamansa ganin messages da P'A ya tura masa bayan ya karanta yayi ɗan typing ya maida masa ra reply.
"Nifa har na tura masa ma da number nata can taje ita ta sani duk yadda tayi kanta"
"Amma dai ka kira ta yanzu ka sanar da ita, kafa san wacece Ummi"
Sauke lumfashi yayi kamin ya ɗago da kansa yana duban ƙodar ɗakin su Ummi ya ce.
"Ke Ummi zo nan ina son magana dake"
Shiru ba'a amsa ba yasa shi ƙara cewa.
"Wai Ummi bada ke nake ba?"
Da sauri Salma ta fito tana zama a ƙasa ta ce.
"Ya Muhmd bata nan fa ta fita tsakar gida"
"Okay kira min ita"
Tashi Salma tayi a hankali tana ficewa zuwa tsakar gidan nasu.
Fitowarta taga Safiya na shiri zata fita da alama baƙo tayi. Ammi na gefe sai zugata take akan tayi masifar kyau, Ummi kuma na gefe ashe wankin wasu gyalenta take yi, tana kallonsu itama kawai.
"Ohhh Aunty Ummi dama kina nan ne?"
Tana wankin ta ci gaba da maida hankali akan wankin nata kamin ta ce.
"Eh wallahi wasu gyaloluwa na ne naga sunyi dauɗa shine yasa na fiddo ina wankewa"
"Amma banji lokacin da kika fita ba"
"Eh na barki ne kina jin karatu to sai bacci ya fara ɗaukar ki"
"Ohh hakane fa na manta. To yanzu dai Ya Muhmd ne ke son magana dake a ɗaki"
"Magana dani kuma?"
"Haka ya ce dai?"
"To miya faru kuma?"
"Idan kin shigo ma dai zaki jine, dan ni baza'a ji mutuwar sarki a bakina ba"
Salma ta faɗa tana juyawa domin wucewa ɗaki taga wani irin kallo da Ammi ke binsu dashi da wani kalar murmushin da gaban Salma sai da ya yanke ta faɗi.
"Anya matar nan?"
Salma ta faɗa a ranta tana jin zuciyarta na ɗarsa mata wani abu akan Ammi ɗin. Da sauri ta idasa ɗakin tana ƙara jaddada ma Ummi yana fa jiranta.
Miƙewa tayi bayan ta gama wanke na ƙarshe ta shanya da sauri ta kauda komai tana niyyar shigewa ɗakin nasu taji muryar Ammi na ce mata.
"To nan wajan waye kika barmawa ya sharce miki shi?, duk kinyi wanki kin jike wajan da ruwa?"
"Kashhh"
Ummi ta faɗa tana ɗan dawowa baya ta manta ne, bata dai ce mata komai ba ta dawo da sauri ta share wajan tana gamawa ta shigewarta ɗaki da sauri dan karma Ammi ɗin ta ƙara mata wata maganar, dama tasan Ammi da neman abun faɗa.
"Ya Muhmd ance kana son magana dani?"
"Yeah zauna zamuyi magana ne mai mahimmanci"
Zama tayi sosai tana fuskantar shi kanta a ƙasa.
Ya dubeta a tsanake ya ce.
"Ki buɗe kunnanki da kyau kiji ni Ummi, a wannan karon karki sake kiyi wasa da damarki wallahi"
Yayi ɗan shiru yana karantar yanayinta.
Ita kam gabanta ne ya yanke ya faɗi har bata san lokacin data ɗago tana dubansa ba.
"Dama kuma Ya Muhmmd wacce irin dama?"
"P'A na wajan aikina ne ya kira ni ya ce wani Ogansa yaga photonki ya ce yana sonki, dan haka ne ma yasa na tura masa number naki zai kira ki kuyi magana dashi, saura idan kunyi magana koya kira kin kiyi masa wulaƙancin nan naki da kika riga kika saba kuma ya aure ki"
"Ya aure ni kuma"
Ta faɗa tana turo baki, tana jin wani abu ya tsaya mata a wuya. Itafa da zasu gane da sun daina haɗata da wasu samari bata so kwata-kwata, ita tafi so su haɗu da mutum idan yayi mata nan take zata sanar dashi, idan ma baiyi matan ba zata sanar dashi ne, amma wannan kutsa kan bata so wallahi.
"Eh man shi wulaƙancin naki nake nufi mana"
Sadda kanta tayi ƙasa haɗe da cewa.
"Hmmm"
Kawai tana jin zuciyarta na mata zafi-zafi.
"Ni dai na gaya miki, kuma duk abunda kika yanke zanji ne daga wajan P'A"
"To ni Ya Muhmd ba dole sai idan mutum yayi min bane da har zan amince dashi ba?"
"Kaji ko marar wayo marar hankali"
Cewar Mama ta faɗa da sauri kamar zata kaima Ummi duka.
Ummi tsawar da Mama ta buga mata ce tasa ta ɗan matsawa tana kame jikinta da ɗan tsoro.
"Sofa wa'innan yaran na lura sunfi son samari ƴan ƙarya masu ji da kyau shine kawai"
Ya Muhmd ya faɗa yana kallon Mama.
"Ai ka rabu dasu, yanzu auren babban mutum wadda yasan miye ma auren ai shine dai-dai, kuma sunfi bawa Mace kulawa fiye da wa'innan shashashun samarin"
"To dai shima wannan ɗin yana aure harda yara ɗayar matar tashi na Abuja itama ɗayar kuma na Kano, kema ya ce idan har kika amince sai garin da kike so zai aje ki"
Ido waje Ummi ta fiddo tana dafe ƙirjinta bata san lokacin data buɗe baki ta ce.
"Ya Muhmd Mata biyu fa garesa, ni ce zan zo ta uku kenan fa?. Wallahi bazan iya ba, nasan harda manyan ƴaƴa garesa, haba Ya Muhmd ina laifin ma ko ɗaya daga cikin ƴaƴan nasa ne ya ce yana sona ai kamar sai yafi"
"Kaji ba?, tun a nan ta rusa abun, wa'innan yaran ko wallahi basu da mutumci"
"Kashh kyale su Mama. Dan ubanki da ba'ayin haka za'a zo a fara neman auren naki ne, ko an gaya miki haka kawai nake abuna kara zube ne?"
Turo baki Ummi tayi kanta ta sadda ƙasa ta ce.
"Tsakani da Ya Muhmd wallahi Allah bazan iya auren mai Mata har biyu ba, kayi hakurii kawai"
"Ku tashi daga ke har Salma ɗin data zuba mana ido tana kallonmu bata iya cewa ma komai ku bamu waje"
Mama ta faɗa tana nunasu da yatsa tana kuma nuna masu hanyar ɗakinsu.
Tashi sukai da sauri suna jin Mama na ce ma Ya Muhmd.
"Ka rabu da ita kai, ka ce masa idan har ya shirya kawai ya zo gida"
"Amma Mama kin fa san Baba baya ma ƴaƴansa auren dole, sai idan dole sune suke son abu yake basu"
"Kai dai kayi abunda na ce ko?"
Suna shiga ɗaki Ummi ta zube akan gado tana rushewa da kuka, da wani irin sauri Salma ta riƙe mata hannu tana ɗan bugga bayanta ta ce.
"Aunty Ummi kiyi hakuri gaskiya ko ni bance ki yarda ki auri irin wannan mutanen da Ya Muhmd ya kawo miki ba"
"Ai wallahi bazan taɓa yarda ba Salma, kuma zai kira ni ne zaiji magana iya magana wallahi, da ƙafafunsa zai gudu kamar yadda ya zo haka zai koma, ai dai daɗinta Baba baya mana auren dole ko?, hmmm zamu gani ne. Ni na rasa wannan abu irin na Mama da Ya Muhmd ɗin can dake zuge ta, suda basu zasu zauna maka da mutum ba, danmi zasu rinƙa ƙoƙarin tusa maka wadda baka so ne?"
"Hmm"
Kawai Salma ta faɗa tana mamakin ita wannan abubuwan baya faruwa da ita........
PAGE 13
"Wai tunanin miki ke yi ne, har yanzu baki gama haɗa kayan nan ba?"
Sauke lumfashi Ummi tayi tana kallon Mama ta ce.
"Ba komai"
"Ya zaki ce ba komai, bayan kusan awa ɗaya da fitata na barki kina haɗa kayan nan, har na dawo baki gama ba, dole akwai abunda kika sa ma ranki kike tunaninsa har ya ɗauki hankalinki haka"
Idasa haɗa kayan tayi da sauri ta zage ziff ɗin Jakar da zatai tafiya da ita zuwa goben ta ce.
"Mama babu wani abu fa, kawai kaina ke ɗan ciwo ne shine yasa fa"
"Hmm Allah ya kyauta to. Goben zaki bi Baban gidan ne ko kuwa?"
Taɓe baki tayi tana saurin girgiza kanta ta ce.
"Kai Mama gaskiya bazan iya bin Bire ba gaskiya, tafiyar asubar nan bazan iya ta ba, gara kawai na bari sai wajan uku da rabi na tafi, tunda ba'a ranar zan dawo ba"
Mama ta ɗan kalleta a tsanake ta ce.
"Haba Ummi har uku zaki kai baki tafi ba?, ai yamma sai tayi miki, kuma kin san Kano shigarta da yamma wahala mutum ke sha, ki dai tafi a wajan biyu ko ɗaya haka"
"Shikenan Mama sai dai yadda ta yiwu kawai"
Mama bata ƙara magana ba ta barta ta juya ta koma parlo.
"Ohhh wallahi dandai ba yadda zanyi na rusa tafiyar nan, wallahi Allah da ba inda zanje"
Ummi ta faɗa a hankali ranta na ɓaci da tafiyar nan da zata yi.
************** *Ƙauyen Karaɗuwa Kankia LGA, Katsina state Nigeria*
Sadiya ta sake turo baki gaba tana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa.
"Wai Sadiya ba magana nake dake bane?, ko sai Umar ya dawo ne na haɗa ki dashi, shine har zaki tsaya ki ci abincin nan ki wuce tallar gwaɗar?"
"Nifa Inna gaskiya ki daina haɗa ni wannan mugun. Wai dan Allah yaushe ne ma zai zo ya koma inda ya fito ne?"
Sake da baki Inna ke kallon Sadiya ta ce.
"Ai ko