Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   19 / 36

54K to 57K   out of 106.4K words

/>
"Noo ina? kawai mu zauna amma kiyi sauri gaskiya kinga har ƙarfe ɗaya ta kusa ma"

Zama sukai Salma ta saki ɗan murmurshi ta ce.

"Tabbas na yarda da maganar Yusura da take cewa wata ƙila baida girman kai da mutane da dama ke kallonsa dashi, idan har ka ma'amalance sa sosai zaka gane baida matsala sosai. To dai nima zan iya bugun ƙirji a yanzu na ce haka ɗin, saboda wallahi Habiba lafiya lau muke magana dashi, kamar ba Mlm Jamilu dana sani bane, nayi mamakinsa fa, cike da sakin fuska muke magana"

"Hmm ai naga komai Salma, sai murmurshi yake maki harda wasa da dariya fa naga kuna yi"

"Ke Habiba bana son shirri fa"

Dariya Habiba ta saki tana girgiza kai ta ce.

"To naji, amma ai kin san babu wacce ya taɓama haka sai ke ko?, duk wata macen da suke zuwa wajansa, kinga ance uban wanka anzo office nasa, ana iyayi da kashe murya wallahi Allah bai taɓa sakin fuskarsa kamar haka ba"

"Ke ina kika sani?"

"Ba wannan ba dai yanzu ya ake ciki? za'a gyara maki exam's ɗin da kika rasa jiyan?"

"Eh to ya dai ya ce zamu sake magana kamin wai mu gama exam's ɗin nan gaba ɗaya"

"Kai haba?, ai nasan ma gata can an gyara. Wai kinga yadda kuka ɗauki hankalin ɗalibai kuwa?"

"Na gani Habiba, ai na bani da maganar jama'a ni kam"

Salma ta faɗa suna miƙewa a tare suka nufi hanyar get ɗin school ɗin.

Suna fita bakin titi Habiba ta dafa Salma ta ce.

"Please tunda kina da number nashi dan Allah ki ɗauri ki ɗauki hankalinsa ya so ki ya ƙaunace ki mana, ko Allah zaisa ki zama Mamanmu ta hygiene banza"

Habiba ta ƙare maganar tana kai mata dukan wasa.

Ido Salma ta waro tana kallon Habiba da mamaki ta ce.

"Lallai ma Habiba, ni kam bada ni ba"

"Kamar ya bada ke ba?, kefa baki ganewa wani lokacin, dalla can zaki kankaro mana daraja ne a cikin school ɗin nan, ai wallahi akai sa'a ya aure ki, babban bala'in nan, ai nake gaya miki za'ai bikin da ba'a taɓa yinsa ba a garin kano wallahi, dole ne ma a shaida hakan"

"Hmm Habiba mai rai da guri yake, amma ni ban kaita da nan ba. Kefa da kanki kike cewa yana da manyan ƴaƴa kamar ni, kawai sai naje kuma na aure Ubansu?, bazai yiwu ba Habiba"

"Yo dalla miye a ciki?, kanki farau ne hakan data faru?, idan ba'a auran irin hakan ai wasu matan zasu mutu a gida kuwa, ke dai kawai idan har ya nuna yana sonki, dan girman Allah Salma kar kiyi mana baƙin ciki, kiƙi amincewa, dan wallahi Allah kika ƙi amicewa ai baƙin ciki zaki mana gagarumi ma kuwa"

Ita dai Salma bata ce komai ba sukai sallama dan bata ma son maganar sosai. Ita kuma ta tsallaka zuwa inda zara tare napep.

Tana tafiya tana jin yadda zuciyarta yau ke a sake sakayau, kamar ma farin ciki take, ta rasa mi yasa, to ko dan ta haɗu da Mlm Jamilu ne?.

Saurin girgiza kai tayi a fili furta.

"Taya hakan zata yiwu?"

Sai kawai ta ci gaba da tafiya tana son gauda tunanin a zuciyarta kwata-kwata amma ta kasa.

Tsaida mai napep tayi tana tsaidawa tayi sa'ar samu data ce gadon ƙaya, duk dama da rana ba'a wahalar samun ta gadon ƙayar.

Hawa napep tayi tana jin yadda zuciyarta ke ƙara hasko mata yanayin data kasance a tare dashi, murmurshi kawai take saki ita ɗaya tana kallon wani waje daban......

PAGE 37

*SADIYA POV*

"Wato sadiya tunda kiga fahimci Umar zai bar gari kike ta farin ciki ko?"

Turo baki tayi tana duban Inna ta ce.

"Ni dai Inna ban faɗa miki da baki na ba cewar farin ciki nake, karma kaja yaji ya ce ya fasa"

"Hmm ai yama fasan sai zuwa nan dahh....

"Innalillahi Inna mi kika ce ya fasa fa?"

Sadiya tayi saurin katse Inna kamar zatai kuka.

"Eh sai nan da jibi, saboda gobe gaba ɗaya zamu shirya zuwa Rimaye wajan Innarku dake Rimaye ya ce ba zai tafi ba sai yaje ya gaida ita, ni da cewa nayi yayi tafiyarsa gobe kawai ba sai an waje Rimayen ba"

"To Inna amma mi yasa baki so muje Rimaye ne?"

"Hmmm"

Kawai Inna ta faɗa tana saurin girgiza kanta, dan ita tasan muddun suka je Rimaye sai Ammi ta tayar da maganar dake cin ranta tun shekaru da dama da suka wuce akan Sadiya da Umar da kuma ƴarta Safiya akan wani abu data so ƙullawa a tsakaninmu amma a bayan mahaifiyar su Umar ɗin taki amincewa dashi.

"Inna kinyi shiru?"

"Ba komai, idan lokacin jin nasa yayi zaki ji ne ai, yanzu ba hankali kika cika ba bare a sanar dake"

"Haba Inna nifa na girma yanzu, kawai ki sanar dani"

"to yanzu dai hankalin ki ba zai wani ɗauka ba"

Inna ta ƙare maganar tana miƙewa tsaye dan dama tuwon dare ta ɗora ta ci gaba da aikinta.

Kamar yadda Inna ta ce washe gari suka tashi da shirin zuwa Rimaye, Sadiya sai tsallen murna take tana zumuɗin zuwa wajan ƴan uwanta, dan rabon da suje Rimayen ko kuma su mutanen Rimaye su zo harta manta.

*Gwajawa Rimaye, Kankia LGA, Katsina State Nigeria*

"Wallahi wallahi Safiya kika ƙara faɗa min magana irin wannan sai kinyi nadamar faɗarta na gaya miki"

Ummi ta faɗa tana nunata da yatsa ranta a mugun ɓace.

Tunda ta dawo gidan taga Safiya sai wani ƙara tashen rashin kunya take mata, kuma duk Ammi da Mama ne ke ɗaure mata gindi.

"An faɗa ɗin masu nauyin jini, kuma samun mijin idan fitsari banza ne kaza tayi mana mu gani?, kuma shara ce naje na turo, idan kinga dama ki share idan kinga dama ki bar....

Wani kyakykyawan mari mai ƙarar gaske Ummi tasa ka hannu ta kwashe Safiya dashi, tana huci ta sake nuna da yatsa ta ce.

"Wallahil azim zan miki abunda yafi mari kika ƙara buɗe baki a nan wajan, banza kawai marar kunya"

Dafe da kuncinta take tana fiddo ido waje saiga hawayen baƙin ciki na mata zuba kamar an buɗe fanfo.

"Wayyo Allah nahhg Ammiiiiii"

Safiya ta faɗa da ƙarfi kamar wacce ake yankan naman jikinta.

"Subhallahi mi yake faruwa ne?"

Mama ta faɗa tana yin saurin fitowa. Idar da sallar ta kenan tayo waje da sauri dama tun tana sallar take ta jin hayaniyarsu sama-sama.

"Yo Mama mari na fa tayi, daga na turo mata sharar da nayi ta ɗakin Baba shine ta mare ni tana faɗa min magana"

"Ke Ummi miye haka?, dama abunda ya dawo dake gidan nan kenan ki rinƙa saka ni magana ko?"

"Amma Mama ki duba kamar wannan yarinya wacce naba shekaru wai ita keda zarrar tsayawa ina faɗa tana faɗa?"

"Ke ni kimin shiru a nan wajan, ai yanzu ta ƙanwa ta kare tunda gashi har zatai aure ta barki a zube a gida"

Wani irin rasss Ummi taji gabanta ya faɗi, haɗe da wani masifar sanyi jiki lokaci ɗaya.

"Mama yanzu hakama zaki ce kawai?"

"Mtswww ke Safiya wuce ɗaki kiyi hakuri kuma saita share shi wallahi"

Ammi ta fito tana tsaye gefe ta saki wani murmurshi ta ce.

"Haba Maman yara ai kamata yayi ki haɗasu duka kiyi masu faɗan, ba wai ki ware ɗaya ba"

"Ai duk ita ce babbar banza wallahi, da bata biye ba ai da bata tsaya tana gaya mata magana haka ba, ai dama shi babba shike jawa kansa raini"

Wani irin kallo Ummi ta shiga jefa ma Ammi, a zuciyata tana cewa.

"Shegiya munafukar banza kawai, wannan matar anyi baƙar annamimiya wallahi, amma ai wata rana zaki gane Allah ɗaya ne"

Ummi ta ƙare maganar a zuci tana yin wata kwafa kawai zata juya ta ci gaba da sharar suka ji gyaran muryar Baba yayo sallama cikin gidan.

Ganinsu tsaye cirko-cirko yasa Baba kallonsu ya ce.

"Mike faruwa ne a nan?"

Ummi zatai magana Ammi tayi saurin tarar lumfashinta wajan cewa.

"Ah Mlm babu komai fa, kawai mun fito ne shan iska, to kuma sai Ummi ke ta gyara mana gidan"

"Ohh yayi kyau. Amma wai ni tunda na fara lura da wani abu a gidan nan, Ummi kaɗai nake ganin tana ta fama da aikin gidan nan, ita Safiya miye take yi?"

Wata hamdala Ummi ta saki a zuci tana sakin murmurshi, tana kallon yadda Mama da Ammi suka ɗan sauke ajiyar zuciya, Safiya kuwa saita murtuƙe fuska kamar zata saki kuka.

"Ina tabbayarku kunyi shiru?. Ke Ummi miye Safiya ke yi a gidan nan?"

"Haba Mlm ya da haka kuma?, ƴaƴan nan dai duka ɗaya ne, kuma suna yin duk aikin nan tsawon shekaru, to kuma yanzu rana tsaka ka rufe mu da wannan tabbayar?"

Mama ta faɗa tana tarar lumfashin Ummi data buɗe baki zatai magana.

"Zaki bari tayi min bayani da kanta ne ko kuwa?"

Shiru sukai gaba ɗaya kowa na zubama Ummi ido suna son jin miye zata faɗa.

"Baba dam...dama kawai..

"Dama kawai mi?, ki sanar dani karki ji tsoron kowa"

"Haba Mlm Ummi ɗince zata ji tsoron wani a nan cikinmu?"

Ammi ta faɗa tana kallon Baba.

Ɗaga mata hannu yayi yana sake zubama Ummi ido ya ce.

"Ina jinki Ummi"

"Gaskiya Baba ni kaɗai ke yin aikin gidan nan, Safiya tunda aka saka mata ranar biki bata ƙara taɓa komai da sunan aiki ba"

Girgiza kai yayi yana ɗago da idonsa ya sauke akan Safiya data yi ƙasa da kanta, sai kuma ya dubi su Mama da Ammi dake kallon Ummi kamar zasu rufeta da duka.

"Ku duka ku same ni a ɗaki"

Ya faɗa yana wuce su.

Kowa shiru yayi, Ummi kuwa babu nadamar hakan tattare da ita, dan dama ta faɗa wallahi ko Baban bai tabbaya ba ta gaji yau tana da niyyar zuwa har ɗakinsa ta sanar dashi irin rashin kunyar da Safiya ke mata a kwanakin nan, dan yarinya taga zatai aure sai kawai ta rinƙa gaggaya masu magana son ranta?, tana wata ɗagawar banza.......

PAGE 38

"Bana son wata magana, na riga na yanke hukunci, dole ne Safiya tayi aiki a gidan nan, daga yau ita zata rinƙa yin aikin yamma ita kuma ta rinƙa yin na safe Ummi, kuma kar na ƙara jin tayima Ummi rashin kunya, saboda ta bata shekaru kusan biyar, dan haka akwai tazara a tsakaninsu dole ne tayi mata biyayya"

"Amma Mlm kana ganin wannan hukuncin....

Ɗaga mata hannu Baba yayi yana nuna masu hanyar waje ya ce.

"Zaku iya tashi kuje ina da wani abu da zanyi, ina buƙatar a barni ni ɗaya"

Miƙewa sukai kusan a tare suka wuce tsakar gida.

Ummi tana shirin shiga ɗakinsu taji muryar Mama na cewa.

"Ai kinji daɗi ko?, Ubanku dama shike ƙara ɗaure maku gindin zama a cikin gidan nan, amma wallahi ki sani akwai ranar da zan barku da Uban naku, idan har baku natsu kun fitar da miji ba wallahi"

"Haba Maman yara kiyi hakuri mana, zasu fitar ne ai, ko dan ma yadda sunga ƙannan nan nasu bikinsu sai matsowa yake, zasu fitar ne"

Ammi ta faɗa tana dafa kafaɗar Mama dake faɗa kamar zata ari baki.

Ummi da sauri ta shige ɗaki tana jefama Ammi wani kallo.

"Mtswww shi dai munafuki baiji daɗi ba wallahi, Mazajen aure ne zamu fitar da yardar Allah wa'inda ma suka fi na su Safiyar insha Allah, sai dai baƙin cikin hakan ya kusa kashe ki"

Ummi ya faɗa tana idasawa cikin bedroom nasu ta ɗauki wayarta tana neman number ɗin Salma.

Su Mama na tsakar gida suka ji ana kwaɗa sallama.

Da wani irin sauri Ammi ta miƙe tsaye dan ko da gigin bacci ta tashi bazata kasa gane muryar nan dake sallama ba.

Kamin ta ƙara wani tunanin kuwa idonta yayi mata tozali da Innarta a gabanta.

Zuciyar Ammi sai bugawa take sosai.

Ganin irin kallon da Inna ke jefama Ammi yasa Ammi wata kunyar duniya ta rufe ta, bata san lokacin data ɗauke idonta daga kan Innar ba.

Sai dai idonta ne ya faɗa cikin na Sadiya dake riƙe da hannun Innar.

Lokaci ɗaya fuskar Ammi ta sauya zuwa wani irin ɓacin rai, da sauri ta ɗauke dubanta akan Sadiya, da lokaci ɗaya ta fahimci kamar Ammi ɗin bata maraba da ita, duk da ƙarancin shekarunta.

Ta ɗauka Ammi zata fi kowa farin cikin ganinta ne ai, duk da dama bata taɓa ganinta da girmanta ba, tun kan tasan kanta rabon ta da taga Ammi ɗin, sai dai tana yawon jin labarinta a wajan Inna dasu Ya Umar.

"A'a marabanku yau manyan baƙi ne a gidanmu?"

Mama ta faɗa tana katse shirun daya gifta a tsakaninsu.

Ganin kamar Mama zata fahimci wani abu yasa Ammi sakin fuskarta ta tarbesu da fara'ar data ba Inna mamaki.

Kai tsaye ɓangaren Ammi suka shiga.

Suna shiga Ammi ta ƙara ɗaure fuska babu walwala.

"Wai ko dai Asma'u mu tashi mu tafi ne?, wannan baƙin ran duk na ganinmu ne kike ta wannan irin abu?, shi yasa fa ni banso zuwa inda kike ba wallahi, wa'innan yaran ne su Umar suka matsa akan sai munzo inda kike, tunda su sun kasa mancewa dake a matsayin ƙanwar mahaifiyasu, amma ke kin shafe babinsu, akan wani dalilin da bai kai ya kawo ba"

"Haba Inna yanzu akan wannan marar asalin har kike faɗin kin mance da ƴarki ɗaya tilo data rage maki a duniya?. Tun asali waye yaja haka idan ba Yaya Hindatu ba (Mahaifiyarsu Umar kenan)?, da ace bata haɗa aure a tsakanin yaran nan ba ai duk hakan bata faru ba, da ace ta haɗa Umar da Safiya aure kamar yadda naso ƙara ƙulla zumunci da duk hakan bata kasance ba, amma kawai taje ta ɗakko bare wacce aka tsinta a ɓola ta ɗauki ɗanta ta.....

"Kinga Asma'u bana son ƙara jin kin tayar da wannan maganar, bana so bana so na gaya miki, kuma tashi zamuyi mu tafi tunda baki buƙatar ganinmu, idan har zaki tsani Sadiya to kamar kin tsane mu ne muma"

Inna ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa, da sauri Ammi tasa hannu ta riƙe Inna.

Inna na sauke ajiyar zuciya tana gode ma Allah da Sadiya na parlo suna ɗan magana da Safiya, su kuma da Inna da Ammi suna bedroom ɗin Ammi ɗin.

"Kiyi hakuri Inna, amma wallahi zuciyata bazata taɓa son wancan yarinyar ba, ita ce ta rusa min buri na, Inna Umar ba kowanne irin namiji bane da idan mace tayi sa'ar samunsa zata tsaya shashashanci ba, shi ɗin namiji ne son kowacce ɗiya mace, babu macen da bazata ji Umar ya shiga ranta ba, babu ita Inna, Inna kinfi ni sanin waye Umar kinfi ni sanin nagartarsa, dole ne nayi baƙin ciki da ƴata bata same shi ba"

"Amma a can baya mi Hindatu ta ce miki?"

"Cewa tayi dole sai dai ya auri mata biyu. Kuma gaskiya ni Inna banda burin ƴata ta zauna kishiya, bana so bazan kuma a fara ba"

"Hmm kinga ai laifi naki ne, dan haka banga dalilin da zaisa kina wannan abubuwan ba, kuma kishiya da kike maganar ƴarki bazata zauna da ita ba, ke ai ke kaɗai ce zaune a naki gidan nake ganin ko?, ko yanzu ai waje bai ƙure maki ba, wajan samun ƴarki ta auri Umar ba"

Girgiza kai Ammi tayi ta ce.

"Kashhh ai waje ya gama ƙurewa tuni Inna, saboda kin san nasha faɗa miki a can baya dama Safiya ta samu wadda take so, yanzu haka ma ansa ranar aurensu nanda wata uku masu zuwa Inna, kuma kin riga kinsan Mahaifinsu Safiya baya magana biyu, dan haka dole zuciyata bazata taɓa mancewa da irin abunda wannan tsintacciyar taja min ba, da ace yanzu babu ita, bata shigo cikin family ɗinmu ba da yanzu nasan an gama magana akan auren Umar da Safiya, da yanzu nasan ko bata zamo tashi ba ta kusa zama"

Shigowar Safiya bedroom ɗin ne yasa Inna yin shiru.

"Wai Ammi ki zo inji Baba yana parlo"

"Okey gani nan kije"

Safiya na fita Ammi ta miƙe ta ce.

"Ina zuwa Inna"

"Ke ni na mance ma su Umar da Sule fa suna waje, wannan maganar taki da nasan dama bata ƙarewa muddun aka haɗu, ita taja na mance dasu a waje ma wallahi"

"Yi haƙuri Inna bari naje a shigo dasu"

Ta faɗa tana idasa ficewa a ɗakin.

Baba ne a parlo yana ɗanjan Sadiya da fira harda wasa da dariya domin ya santa tun tana ƙaramarta, yanzu kuma yaga ta girma shine yake tsokarnarta.

Fitowar Ammi yasa Baba katse fira da suke da Sadiya ya ce.

"Ya akai aka bar baƙi a ƙofar gida?, wadda kin san ƴan gida ne kuma"

"Wallahi Inna ce bata faɗa min da wuri ba, amma bari nasa a shigo dasu"

"No ai Muhammed ma ya shigo dasu, suna can ɓangarensa, kawai dai a kai masu abinci da abun sha please. Sana ayi min magana da Inna mu gaisa, dan fita zanyi"

"To bari nayi mata magana ka zauna"

Ammi ta faɗa tana komawa ciki.

Sadiya duk sai taji ta taƙura ganin yadda idan suka haɗa ido da Ammi ke jefa mata wani kallon banza, data kasa gane na miye?.

Dawowarsu a tare ne yasa Baba miƙewa ya kai har ƙasa ya shiga gaida Inna.

Inna na murmurshi ta zauna tana amsa gaisuwarsa da sakewa sosai.

Sadiya ce ta taso tana shirin matsowa inda Inna take dan duk ji take a taƙure take.

Wani ɗan iskan kallon gargaɗi da Ammi ta jefa mata ne yasa Sadiya bata san lokacin data koma ta zauna inda take ba, tana haɗe wani miyau gabanta na faɗuwa.

Ba wadda ya lura da hakan sai Baba, duk yana ankare da ita, tun fitowarta ta farko yadda take ma Sadiyar ba sakin fuska sai ɗaure fuska.

Girgiza kai kawai yayi dan ya riga yasan mi yasa Ammi ɗin ke yima Safiya hakan.

Suna gama gaisawa da Inna ya miƙe haɗe da fiddo wasu kuɗi masu yawa ya miƙama Sadiya yana cewa.

"Ƴata ga wannan

19 / 36