Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   32 / 36

93K to 96K   out of 106.4K words

suna Salma. Ita kam wani lokacin har daɗi take ji ana ganin fuskarta a matsayin ta Salma, bata taɓa jin haushi akan hakan ba, saima daɗi da take ji, duk da Salma bata a raye amma mutane da yawa na kallonta a matsayin Salma ɗin, ita hakan ma kaɗai ya isheta farin ciki wallahi.

Daurewa tayi ta sake danna number ɗin tasa ta kira.

Duk shiga ɗaya da wayar zatai sai zuciyarta ta amsa tana bugawa.

Ta ɗauka bazai ɗauka ba, dan yanzu ma da kyar ya ɗauki wayar tana gaf tsinkewa.

Shiru yayi su duka sai lumfashin juna da bugun zuciyar juna da suke iya jiyowa ata cikin wayar.

Da kyar ta iya fisgo magana a bakinta ta furta.

"Assalamu alaikum"

"Amin wa'alaikissallam"

Ya amsa ciki-ciki kamar wadda baya son yin magana. Ummi har sai da ta lumshe ido tana buɗewa a hankali saboda muryar tasa ta fito ne da wani irin rikitaccan sauti mai sa zuciyar wadda akai dominsa motsawa.

"Why da ina kiran ki bazaki ɗauka ba? kin rainani ba?"

Kamar yana gabanta ta sake ɓata fuska da shagwaɓar da bata san tana masa ita ba duk lokacin da zasu kasance da juna ta ce.

"Uhum to ni ai bana kusa ne fa?"

"Okey baki kusa, amma idan kin dawo fa?, shine bazaki iya kiran nawa ba?"

"Yanzu bani na kira ɗin ba?, tom kayi haƙuri kaji pleaseee"

Ummi ta faɗa kamar zata sakar masa kuka.

Shi kam zai iya cewa Ummi nasan ƙara ɗana masa tarkon ƙaunarta ne, dan gaba ɗaya jin yarinyar yake har cikin ransa, ta zauna masa tayi kane-kane, ya rasa wane irin so ne ma ya fara ma yarinyar, bai taɓa ɗauka zai so wata ba a nan kusa, duk ɗaukarsa Matarshi kawai zai so a duniya, amma sai gashi ƙaramar yarinya na son hautsina masa lissafi. Tunda yake a tarihin rayuwarsa bai taɓa ma wani mutum kira ɗaya ya kuma sake kiran nasa ba, sai akanta, sana baya mai-maita magana da wuya wallahi ya mai-maita tata sai idan dole ne, shi ɗin wani irin murɗaɗɗan mutum ne shima kansa ya sani, amma yana mamakin yadda Ummi ke son sauyasa a yadda yake. Wani lokacin kuma idan ya zauna sai yake ganin anya kuwa banda irin abunda yayita ma Salma kamin ta rasu shine Allah yake hukuntasa wajan jarabtarsa ta hanyar saka masa son ƴar uwarta mai tsananin gaske shima, dan sosai yake jinta a ransa, wani abun ma dauriya kawai yake yi, amma yadda yake jin Ummi a ransa abun har basa tsoro yake.

"Kana jiiiii?"

Ummi ta faɗa cike da wani irin salon da bata san tana yi ba ita kam, dan ita tsakani da Allah take masa magana kamar yadda take ma kowa a nata tunanin. Bata san shi kam ƙarasa kashe masa zuciya da begen kasantuwa da ita yake ba.

"Yeah, gobe zan shigo ƙauyen naku"

Ai sai ta zunɓuro baki ta ce.

"To ai kowama ɗan ƙauyen ne"

Murmurshi taji ya saki yana sake cewa.

"A ƙauye kika girma, ki yarda ko karki yarda. Ƴar ƙauye kawai"

Ya faɗa da zolayar da shi kansa mamakin kansa yake yadda yake zama da ƴar cikinsa suna haka da ita.

Wani ɗan ihu ta sakar masa da kukan sagarta, ita harga Allah kukan gaske take masa wai danmi zai mace ta ƴar ƙauye.

Tofa sosai ƙaramar yarinyar da yake mata kallon haka-haka ke son chaja masa lissafi, danshi kam ba ƙaramin gigitasa shagwaɓar mace take yi ba, bare kuma harda haɗi da zuciyarsa na bala'in sonta da begenta, shi yasa tabi duk ta ruɗa bawan Allah.

Sai gashi ya biye mata yana bata haƙuri, abunda ba kasafai ya fiye hakan ɗin ba, amma Ummi kam abu kaɗan zatai yayi ta rarrashinta yana bata haƙuri.

Sai da ta wanasa kamin ta sakko, suka ci gaba da firar da shi kansa yayi mamakin yadda suka shafe lokaci suna yi, kuma duk rabin firar shirmenta ne kawai take masa, yana biye mata kuma.

Ita kanta Ummi ɗin tayi mamakin yadda yau ta ɗan sake dashi duk da firar rabi da rabi shirmenta ce.

***************Washe gari aka tashi da ɗaukar azumin watan Ramadan wata mai girma da falala.

Sai wajan yamma sosai Jamilu zai zo dan haka Mama da kanta da Ummi suka shiga masa abincin buɗa baki.

Duk da dama yanzu Mama taga Ammi ta ɗan ja baya da ita ba kamar da ba, tunda dai aka kawo lefen Ummi ɗin ta lura da ita, sai itama Mamar tayi waje ta aje ta, tasan tana zaune zata dawo ne da kanta.

Yanzu ma dai a sama-sama suka haɗu ana aikin shan ruwa a tare.

Koda Ammi taga hidimar da su Mama ke yi sai ta shiga tabbayar ko baƙi za'ai ne?.

Nan ne Ammi ta tanka mata tana bata amsar cewar surukinta ne zai zo Jamilu yasha ruwa a nan.

Sai Ammi ta ɗan taɓe baki tana kallon Mama faɗi take, ai ba'a sanar dasu ba sai yanzu.

Maganganu dai zata fara sai Mama cikin hikima ta gaya mata maganar da dole ta rufe bakinta ta yi shiru kawai.

Sosai Mama ke mamakin wasu mutanen nan a yanzu, dan yanzu haka Aunty Binta kwata-kwata bata kiran Ummi koda wasa wai su gaisa, itama kuma Ummi ta rantse ta gama kiranta, tunda akwai lokacin data kira ta da kyar take amsa mata, kai daka ji zaka san badan tana so take mata maganar ba, haka lokacin da zata koma gida daga nan bayan an amshi lefe Ummin ta kira ta sun isa lafiya?, maganar data faɗama Ummin ta bata mamaki, amma saita shanye ta nuna ba komai bane, to tun lokacin Ummi ke gaya ma Mama wallahi bazata sake kiran Aunty Binta ba, dan idan ta ce zata ci gaba da kiran nata to tabbas zasuyi ɓatatta ne da ita, dan tsaf Mama tasan Ummin zata iya, itama. Aunty Bintar tayi sa'a ne sosai Ummi ke ɗaga mata ƙafa, babu ma wacce Ummi ke ɗaga ma ƙafa tana bata girmanta irin Aunty Binta ɗin, amma yanzu ta fara kaita ƙarshe.

Parlon baƙi Ummi da kanta ta gyarasa duk da irin muguwar gajiyar data yi, ga azumi shi yasa duk tayi laushi, sai mita take a ranta azumin yau ya bata wahala, danji take ƙishirwa kamar zata kada ita.

Sadda zata gama komai ta jera a parlon baƙin har biyar da rabi tayi, lokacin da zata fito sai ta iske Safiya a tsakar gidan nasu tasha wasu ƙananun kaya, ko gyale babu bare Hijab a jikinta, ta kuma samu waje ta zauna.

Haka kawai sai Ummi taji haushi ya rufe ta, yanzu idan Jamilu ya iso a haka fa zai ganta.

Bata ce mata komai ba ta shige ɗakinsu ta iske Mama a zaune da kayan shan ruwa a gabanta tana ɗan latsa ƙaramar wayar dake hannunta.

"A'a wai dama baki shirya ba?, yanzu fa Muhammed ya kira ni yaje taro Jamilun"

"Mama sai ka ce bai san gidan nan ba?, har sai anje wani taro sa?"

"Kefa kin ga inda Jamilu yake kwana wallahi kin rainasa, amma wata rana ko ance ki rinƙa faɗa masa magana koda bayan idonsa ne baza kiyi ba"

"To ni Mama bama wannan ba. Wai ya naga wancar yarinyar Safiya ta wani zo ta zauna a tsakar gida ta kuma saka ƙananun kaya?. Miye hakan yake nufi Mama?"

"Kamar yadda kika ganta nima haka na ganta, da na so nayi magana sai naga uwar tata yau neman fitina dake ji, dan haka kawai ki kyale su ki je ki shiryawarki"

Kwafa kawai Ummi tayi tana shigewa ɗakinsu, toilet ɗin ban ɗakinsu ta shiga tayo wanka a gurguje ta shirya ta fito, kwalliya ƴar kaɗan tayi, ta saka wata rigar Abaya ƴar dubai dan bata san saka wasu kaya masu nauyi wadda zasu dameta ma, dan da kyar take komai ji take zata faɗi danta ƙagara asha ruwan nan ma kamin su iso.

Har aka kira sallar mangaruba basu shigo gidan ba. Ashe sun tsaya da Baba a waje sai da sukai sallah a ƙofar gidan aka aika masu da ruwa mai sanyi da dabino.

Mama na zaune da Ummi take sanar da ita sai sun sha ruwa sunyi sallah tukunna zasu shigo gidan gaba ɗaya.

Hamdala Ummin tayi bayan tasha wani uban ruwa sosai tana cin dabino, sai zufa take tana zubewa akan kujera har wata ganin juya take sosai, shi yasa ta koma ta kwanta jiki ya mutu.

"Sai da na ce kisha ruwan nan a hankali yanzu ai ga irinta nan, kinzo jikinki ya mutu"

"Wallahi Mama cikina ma ya ƙulle"

Ummi ta faɗa tana ɓata fuska haɗe da turo baki.

"Yo ba dole ciki ya ƙulle ba, kinsha wannan uban ruwa, komai da azumi ai a hankali ake bin ciki, da cimar da zakai, saboda cikin bai saba ba"

Ita dai Ummi shiru tayi saboda sosai take jin kasala na rufe ta, ga jikinta daya mutu muruss.

Ya Muhammed ne yayi sallama yana kallon Ummi data kwanta kamar marar lafiya.

"Ke tashi kije yana parlon baƙi dan ba daɗewa zaiyi ba, zai wuce ne baya so dare yayi masa sosai"

Da kyar Ummi ta miƙe tana shirin fita taji Ya Muhammed na bawa Mama labarin iyayen kayan daya kawo na azumi masu uban yawa suna ɗakin Baba an zube.

Mama sai saka masa albarka take tana godiya tun kamin ma ta gansa.

Koda Ummi fita har lokacin Safiya na waje a wajan ma tasha ruwa.

Tunowa da waye Jamilu yasa Ummi sakin murmurshi, dan tasan ko tsirara Safiya tayi tasan wallahi bazai dube ta ba, yanzu haka idan akace ma bai san iskar data kwaso ta ba ta aje a tsakar gidan ba ba'a gardama.

Itama bata kalleta ba ta wuce ta tabar Safiya da taɓe baki tana binta da kallo.

Da sallama siririya ta shiga parlon baƙin tana sadda kanta ƙasa, saboda kallo ɗaya ta yi masa suka haɗa ido tayi saurin murguɗa masa baki haɗe da sadda kan nata ƙasa.

Duk yana ankare da yadda ta murguɗa masa bakin, sai ya saki murmurshin gefen baki kawai.

Zama tayi a nesa dashi a ƙasa, sai ta shiga gaida shi tana masa ansha ruwa lafiya?.

Amsawa yayi da wannan muryar tasa mai zurfi da taushi.

Ummi na mamakin muryar nan da Allah ya mallaka masa ita kanta cikin muryar tasa fitowa take da isa da izza.

Shiru Ummi tayi duk ta ƙasa sukuni a tare dashi sai turo baki take kanta ƙasa, sai taji saukar maganarsa yana cewa.

"Zaki min rowar abincin naki ne?"

Ɗagowa Ummi tayi da sauri sai kuma shiga satar kallonsa ganin yana latsa wayarsa ne yayi mata maganar.

"Uhum ina tabbayarki kina satar kallo na?, ko na miki kyau ne ƴar yarinya?"

Ai sai Ummi ta saki murmurshin da bata shirya sakinsa ba tana ɓata fuska ta ce.

"A'a ba rowa, bari na zuba maka. Kuma ma ai kasan na dai na fika kyau"

Ta faɗa tana miƙewa da kyar dan sosai ta gaji.

Murmurshi ya saki shima yana aje wayar tasa yana kallon yadda take zuba masa abincin jikinta sai rawa yake.

"Ohh barshi haka nan ya isa. Naga kema jikinki na kyarma zauna muci tare dan nasan yinwa ce"

Kunya ce ta kama Ummi, dan da gaske yinwar take ji, shi yasa ma jikinta ke rawa, da kuma aikin data sha, amma hada haɗi da kusancin da suka samu dashi.

Zama tayi sosai a kusa dashi a ƙasa, sai taga shima ya sakko ƙasan da gaske wai su ci abincin a tare.

Ai sai Ummi ta nemi miƙewa da sauri ya saka hannunsa yana riƙota ta koma ta zauna, da sauri kuma ya janye hannun nasa Ummi najin lokacin daya furta astagafullah.

Tabbas Ummi tasan ko kaɗan baya son taɓa ta wani lokacin ita ke ja hakan na faruwa.

"Kina sakawa ina taɓa ki, kuma al'halin baki gama zama tawa ba. But kawai idan na ci kiyi abu kiyi kawai kin gane?"

Ya faɗa fuskarsa ba wasa.

Zunɓuro baki tayi tana kallonsa kamar zatai kuka ta ce.

"Nifa na ƙoshi"

"Ba gaskiya bane"

Ya faɗa bai kalle ta ba ya fara cin abincin tare da ƙara cewa.

"Oya ki fara ci kema. Kifa saki jikinki, ni a haka na saba cin abinci da Matata"

Ai sai Ummi ta ɓata fuska ƙasa-ƙasa ta ce.

"To ni ina ruwa na?, nima sai ka bari idan na zama matar taka man"

Ta ƙare maganar tana murguɗa baki.

A mamakinta sai taji ya ce.

"Ai kin kusa zama ina koya miki yadda zaki rinƙa rayuwa da ni ne. Bana son noƙe-noƙe, ko wata kunya, dan My wife bata saba min da haka ba, kinga dai yadda take bata....

Da sauri Ummi tayi gyaran murya bata san lokacin data ce.

"Ya isa haka zan ci"

Ta faɗa bata san lokacin data saka hannunta ba ta fara ci, kamar tana cin magani, dan wani iri ta soma ji da yana maganar matarshi a kusa da ita.

Murmurshi ya saki na gefen baki dama yana sane yake mata hakan dan ya ɗan gwada ta ya gani.

Kaɗan suka ci abincin duk da irin yinwar da Ummi ke ji, amma ta kasa sakin jiki dashi, duk da yana janta da fira kaɗan-kaɗan take basa amsa saboda kwata-kwata ya ɓata yanayin da take ciki, da maganar daya sako matarshi a ciki.

Koda ya gama a tare suka fito, Ummin ta masa jagora zuwa wajan Mama, yayi mata barka da shan ruwa, da zai fito ya aje mata wasu kuɗi da kyar Mama ta amsa tana cewa, ai hidimar tayi yawa, ga kaya daya kawo harda su kuɗi kuma?.

Shi dai bai ce komai ba sai murmurshin daya saki yana jin ƙaunar matar har cikin ransa jin yadda take saka masa albarka.

Har wajan Ammi ya shiga itama kamar yadda yayi Mama haka da zai fito ya aje mata kuɗin itama.

Duk da dai sai wani binsa take da kallo, dan bazaka taɓa kallon Jamilu ka ce ma ya aje manyan ƴaƴa ba, ita sai yanzu ne ma take ƙare masa kallon tsaf, baka taɓa cewa wai ya aje kamar su Ummi a gida a matsayin ƴaƴansa ba..........

PAGE 59

*A Gurguje please masu karatu🥺😂*

*Bayan sallah da sati ɗaya*

Zaune Ummi take tana kallon Mama data tasa ta a gaba tana ɗora mata wasu maganganun mata, ita kam sai ɓata fuska take tana yi kamar zatai kuka.

"Wai bazaki amsa kisha ba Ummi?"

Amsar ɗayan kofin da Mama ke miƙa mata tayi tana sake turo baki ta kai bakinta, kurɓa ɗaya tayi sai gashi tana shirin dawowa dashi da wani irin sauri Mama ta ce mata.

"Wallahi kika sake kika maido min shi zaki sani ne. Na lura har yanzu baki san ciwon kanki ba, dan ubanki keda za'a kai gidan mai mata, har ana so a gyara ki ciki da waje, kike tsayama mutane shirme?. Kinga dai ai yadda abokiyar zaman naki take?, duk da ta fara manyanta a jikinta ba'a taɓa ganewa, saboda yadda daga gani tasan abunda take yi, keda gani kin san kullum cikin gyara take, ai shi yasa ma Jamilun ya kasa yo mata kishiya tuni tun suna yarintar su"

"To ni Mama wallahi ɗaci maganin nake jinsa"

"Kuma wallahi a haka zaki shanye sa ko zakiyi amai ne kuwa"

Da kyar tana ɓata fuska, dan wani kalar bauri take ji a cikin maganin sai zaƙi-zaƙi kaɗan. Tana shanyewa Mama ta ƙara miƙa mata wata Zuma cikin roba fara.

"Mama wai duk bai isa ba haka?"

"Amshi na ci ko?"

Mama ta faɗa tana tsare ta da ido.

Amsa tayi tana ƙara ɓata fuska, a yatsine takai bakinta kamar zatai kuka, sai kuma taji zaƙi sosai ya gauraye mata baki, saɓanin ɗayan maganin data sha mai bauri da zaƙi-zaƙi wannan sosai taji Zuma ce wacce tasha kayan haɗi, babu ɗaci bare bauri, sai wani ma ƙamshi da take yi.

Ai sai Ummi ta fara sha hankali kwance tana yi tana lashe baki.

Mama ta banka mata harara ta ce.

"Wato saboda wannan zaƙi kika ji shine yasa kikai lakwas?"

Zatai magana tana murmushi sai ƙarar wayarta dake akan cinyarta ta katse mata hanzari.

Ganin Maryam ce ƙawarta yasa ta ɗauka da zumuɗi.

"Hello Maryamah ta Mubeen bada kanki a sare kije gida ki ce ya faɗi"

Daga cikin wayar Maryam ta saki dariya ta na cewa.

"Kefa baki da mutumci wallah, ai kune manya ai tunda ku zaku fara shigewa daga ciki. Mrs J"

Wani murmurshin ta saki tana ɗan satar kallon Mama da tunda ta fara wayar Mama ta maida hankalinta jikin TV dake maƙale a bangon parlon, tana kallon wani series na India da a ake yi.

"Ke ni yaushe zaki taho ne ma?"

"Abunda na kira na faɗa miki kenan, kinga dai kince babu abunda zakiyi, saboda Mijin naki bazai samu zuwa kowanne events ba, to sai na yanke hukuncin cewar kawai na bari sai Al'hamis na zo"

"Wallahi baki isa ba, idan har sai Al'hamis kiyi zaman ki kawai bana son zuwan naki, baccin kin san ranar Juma'a ne ake ɗaura auren zaki wani ce zaki taho ana gobe ɗaurin aure?. Idan ba event's kike magana ai su Safiya zasu yi, ba sai kije nasun ba. Kuma ma banza ki tahowarki da wuri wata ƙila na shirya mana wani abun, zanma turo miki wani yadi da nake so mu ɗinka a wajan partyn, amma iya mune kaɗai zamu halacci wajan"

"Kinga kwantar da hankalinki jibi zan taho laraba kenan insha Allah. Yawwa ko ke fa, ai gara a shirya mana ko yaya ne mu ɗan chashe"

"Ohh dama tsokata kike dama ko uwar son bidi'a?"

Dariya Maryam tayi tana cewa Amaryar nan fa baki da kunya wallahi.

Wayar suke suna tsokanar juna kamar zasu cinye juna tsabar tsokanar da suke ma junansu.

Tana gama wayar Mama ta dubeta ta ce.

"Ke ni nama manta jiya da dare Binta tayi kira na wai sai Al'hamis zasu taho, wai Anam ce ba lafiya, miye da miye, sai na ce mata kawai Allah ya kaimu. Dan ma tuni inda Allah ya taimake ni

32 / 36