Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   21 / 36

60K to 63K   out of 106.4K words

ce.

"Ke kuma ga ƙullun waina can na haɗa tun ɗazu ki fito maza ki soya wainar, dan bazai yiwu na rinƙa maki abincin rana kullum kina tada kai kina ci ba, kuma ba gode bare na gode"

Ai Salma bata san lokacin data ɗago tana duban Aunty Murja ba. Duba agogon ɗakin tayi dake manne a bango ganin sha ɗaya da rabi harta kusa yi, yasa Salma zatai magana Yusura ta rigata cewa.

"Umma school fa zata tafi, kuma suna da exam's ƙarfe sha biyu"

"To ina ruwa na da exam's ɗin tata?, exam's ake zuwa ko yawon iskanci?, dan haka abunda na ce a fito kawai ayi min yawwa"

Zata juya ta tafi taji muryar Salma na faɗin.

"Gaskiya kiyi hakuri Aunty Murja, bazan iya tsayawa na soya waina ba, dan yanzu ma zan tashi na tafi naga waje na gaf da ƙure min"

"Ni kike faɗa ma haka?"

"Ai ba wani abu na ce miki ba Aunty Murja, iya gaskiyata kenan, bazan iya tsayawa na soya waina ba, abarta idan Allah yayi min dawowa da wuri zan iya soyawa ai ba wani abu bane"

"Ahh lallai kuwa ba shakka, dole wuyanki ya isa yanka, ni zaki tsaya kina ma rashin kunya?"

"Kinga Aunty Murja idan kikai haƙuri ma yau zan tattara na bar gidan nan, daga nan kuma sai idan an dawo hutu, dan haka kiyi hakuri"

"Ai dai zaki dawo ko?, to zaki zo ki iske ni ne ina zaune ai. Dama saboda yau zaki tafi shine har kika samu kwarin gwaiwar faɗa min magana haka, hmm zaki dawo ne ki iske ne ai"

"To Umma duk ba ga irinta nan ba, ai dama mai hakuri bai iya fusata ba, kin kai Aunty Salma ƙarshe ne yau, kuma kin san dai ni na ce maki zan soya wainar nan ko?"

"Wallahi Allah Yusura kina shigar min hanci, saina fyato ki tukunna, kifa fita daga ido na rufe tom"

Aunty Murja ta ƙare maganar tana kwafa haɗe da juya zata fita tana cewa.

"Kuma naga ubanda zai baki abinci yau a gidan nan"

Ta faɗa tana idasa ficewa daga ɗakin.

Salma ta taɓe baki tana ɗaga kafaɗar ta, alamar lo a jikinta. Dole ne ma yau ta bar gidan nan.

"Kinga ni Yusura zan wuce saina dawo, ina dawowa kuma zan wuce Rimaye insha Allah"

"Wai da gaske yau ɗin zaki tafi Aunty Salma?"

"Insha Allahu kuwa Yusura"

"Amma kamar zakiyi yamma fa, ki bari sai gobe tunda safe kin tafi, yanzu yaushe kika dawo har kika shirya kika tafi?"

"Hmmm insha Allah Yusura yau a gida zan kwana"

Salma ta faɗa tana ayyanawa a ranta cewar wallahi bazata ƙara kwana a gidan nan ba, itama ta gaji tana buƙatar komawa inda tafi wayo, kota ɗan huta da masifar Aunty Murja.

Sallama tayi mata haɗe da fita daga ɗakin bayan ta gama shiryawa.

Tana fita ta iske Abdul a ƙofar gidan yana shirin aika yaro ya kira ta.

Da kallo ta bisa tana rungume hannawanta a ƙirjinta ta ce.

"Wai Abdul ba mun gama magana ba jiya ne?"

"Haba Salma, wai ke abu baya wucewa a wajanki ne?"

"Na riga na faɗa maka cewar akwai wadda nake so yanzu, dan haka Abdul bazan iya aurenka ba a haka kana zargi na da iskanci tun yanzu, dan haka dan Allah ka kyale ni"

"Ke Salma dakata na ce, daga taimako?, taimakonki fa zanyi na aure ki, kina haka dake sauran wasu Mazan ma har kike tunanin yimin duk abunda kike so kuma kika ga dama?, to kije an fasa auren naki sai mi?"

Murmurshi kawai Salma ta saki tana girgiza kanta ta dubi Abdul a tsana ke ta nunasa da yatsa ta ce.

"Ya isheka haka Abdul, tun kan ajimu da kai a nan wajan kama hanya kabar ƙofar gidan nan, kuma kaje na gode da wannan shaida da kayi min, amma ka sani cewa ka tanadi amsar da zaka bada a gaban Ubangiji ranar gobe"

Tana ƙare maganar ta wucesa sake baki yana cizon yatsa.

Zuciyarta babu daɗi ta idasa school ɗin har suka shiga exam's suka fito Habiba na ankare da ita, ana fitowa daga exam Habiba ta kamo hannunta suna nufar office ɗin Mlm Jamilu.

"Ina kuma zamu je haka?"

Salma ta tabbaye ta.

"A'a office ɗin Mlm Jamilu man, zan raka ki iya ƙofar office ɗin ki shiga ki fito, tukunna naji miye ya ɓata miki rai yau ne?, naga duk baki cikin walwalarki"

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce.

"Yanzu bazaki raka ni ba dan Allah?"

"Wallahi bazan je ba, tafiya ma fa zanyi, dan Umma ce keta kira na wai su Aunty Amina zasu tafi, wani biki ne damu wallahi, ni kawai ake jira a gida na dawo mu tafi tare"

"Amm....

Kiran wayar da akai ta Habiba ta katse masu maganar da suke yi, ɗauka tayi tana cewa.

"Dan Allah gani nan nafa taho kuyi hakuri yanzu zan ƙaraso fa Umma"

Ta faɗa tana sauke wayar haɗe da duban Salma da sauri ta riƙe hannunta ta ce.

"Salma sai munyi waya kawai. Yau ɗin zaki tafi gida?"

"Eh haka nake so gaskiya yau zan wuce"

"Ƴar daɗi gida kawai dama haka kike kamar ana cizonki"

"Bazaki gane bane"

"Yanzu dai ni zan tafi muyi waya kawai komi kenan ta Mlm Jamilu bada kanki a sare kije gida ki ce ya faɗi"

Habiba ta ƙare maganar cike da tsokana tana dariya, ta wuce ta bar Salma da kewarta.

Sauke ajiyar zuciya tayi tana duban wasu ƴan mata dake nuno ta da yatsa taji suna faɗin.

"Kinga yarinyar data wuce yanzu tana cewa wai batai exam da wuri ba wai zata je ta nemi wani Malami ai tana da hanya mine-mine, dama fa bata jin magana"

Salma taga sun sake nuna wata yarinya data wuce ta yanzu.

Sai wata daga ciki ta nuna Salma dake tsaye a kusa dasu ta ce.

"Ai ko wannan dake da Mlm Jamilu nake ganin bata irin wannan abun da wasu ke yi suna nuna su wasu ne a school ɗin nan"

Ai Salma bata san lokacin data ƙaraso inda suke ba tana cewa.

"Bayin Allah lafiya dai, naga ana nuno ni?"

"A'afa ba wani abu bane, cewa akai ke da keda Mlm Jamilu ma baki cika girman kai da wasu keyi na cewar suna da wasu manya a school ɗin nan"

Can wata ta ƙara cewa.

"Ai duk school ɗin nan ba wadda Mlm Jamilu ke sakar ma fuska kamar ke"

"To ku kuwa ina kuka san ina tare dashi?"

"Ahh, yo abunda ke faruwa a duniya na ɓoya ne dama?, ai ba wadda bai san alaƙarku ba"

"A'afa baiwar Allah, kun san abunda kuka sani wadda kuma ba haka bane, ba abunda ke tsakaninmu saina ƴan uwanta taka, ɗan uwana ne, Yaya ne ga Mahaifiyata shine yasa kawai kuke ganin haka"

"Ohhhh Allah sarki, haba koda na ce shi yasa yake sakar maki fuska sosai haka kuna wasa da dariya ashe ma ƴarsa ce ke"

Murmurshin yaƙe kawai Salma ta saki tana kallonsu ta ɗaga kanta kawai alamar ai kodai hakane.

A nan ta barsu tana nufar inda aka taɓa mata kwantancen office ɗin nasa, dan ita duk zamanta bata taɓa sanin office ɗin nasa ba. Tana tafe tana tunanin yadda ƴan school ɗin basu da aiki sai gulma a yanzu da Mlm Jamilu, ta tabbata wasu ma idan taji abunda suke yaɗawa da faɗa a cikin school ɗin zatai mamaki ne sosai......

PAGE 42

*SALMA POV*

Samun waje tayi ta zauna tana tunanin inda office nashi yake, ita dai anyi mata kwatance da nan wajan, to amma ga office na Malamai nan da yawa a wajan a jere, wanne ne nashi a ciki?.

Ta shiga tabbayar kanta.

Sauke ajiyar zuciya tayi tana fiddo da wayarta, ta shiga number nashi tana jin yadda zuciyarta ke lugudan daka kamar zata fito daga ƙirjinta.

Wani miyau ta haɗe jin ya ɗauki kiran.

Karawa tayi a kunnenta tana jin saukar muryar nan tasa mai cike da kwarjini da izza a cikinta.

Sosai Salma ke mamakin hatta muryasa cikinta izza ce, komai nasa na daban ne, tasha zama tana mamakin komai na Mlm Jamilu daban yake dana kowa. Wai shin dama akwai irin wa'innan mutanen?, wa'inda take yawan ji ana suffanto su a hausa novels?, ta ɗauka kawai ana sakawa ne dan mai karatu yaji daɗin bin labarin, sai gashi ita yake faruwa a kanta, ita gani take ma yadda ake saffanto jaruman cikin littafi wannan yafi su komai.

Sai da ya ƙara yin sallama kamin taja lumfashi tana amsawa kamar mai ciwon baki.

"Salmahhh"

Taji ya kira sunanta da wata irin murya.

Ai ji Salma tayi duk duniya ba wadda ya iya kiran sunanta sai shi.

Har saida ta lumshe ido tana jin yadda zuciyarta ke ƙara bugawa a ƙirjinta sosai.

"Kizo ina office yanzu"

"Am Daddy na zo naga office ɗin cike da mutane fa"

Salma ta faɗan tana kallon wani office daban, danta ɗauka ko shine. Soma kawai take ta zille zuwan nata wajansa domin yadda take ji a yanzu bata a kusa dashi inaga kuma sunyi ido biyu dashi?.

A hankali ta sauke wayar jin ya ce mata ta shigo kawai, ai shine ya ce ta zo, so kawai ta shigo, babu ruwanta da wasu mutane.

Kamar zata miƙe sai kuma ta koma ta zauna, ganin captaiyarsu ta ajinsu ta nufo wajan tare da wata ƴar department ɗinsu. Tasan yarinyar akwai rawar kai ga ɗaukar kanta wani abu, Habiba ta taɓa nuna mata ita wai itama nan son Mlm Jamilu take, sosai akansa zata iya komai.

Tunowa da hakan yasa Salma ta taɓe baki tana jin wani iri a zuciyarta da ganinta a wajan.

Tashi tayi tsaye ganin sun shige wani office captaiya bata idasa shiga ba tana waje tana ɗan amsa waya.

Wajanta ta matsa tana mata sallama ta ce.

"Please Captaiya dan Allah ko kin san office na Mlm Jamilu?"

"Ohhh ai gashi nan inda muka shiga yanzu"

Captaiya ta faɗa tana nuna inda wannan yarinyar ta shiga.

"Okey na gode"

Nufar cikin office ɗin sallama tayi tana haɗe wani abu a maƙushinta.

Karo taci da budurwar nan, a zaune a parlon office ɗin, dan da alama ciki da parlo ne, parlon kansa ya haɗu an tsara shi, tunani ta fara inaga ciki kuma?.

Tsayawa Salma tayi jin kamar akwai baƙin da yake gani a cikin, shi yasa itama wannan ta tsaya a nan ƙila, ƙarfin hali tayi ta ce mata.

"Please dan Allah yana ciki?, ko ana iya shiga ciki please?"

Gani tayi, tayi mata wani irin kallo na raini, tana taɓe baki ta kauda kanta haɗe da cewa.

"Ohh ban sani ba gaskiya"

"Hmmm"

Salma kawai ta faɗa tana girgiza kai danta harbo jirginta, ita wai nan kishi take, tana nuna isa.

Budurwar sai taga Salma ta wucewa tana nufar cikin office ɗin.

Sakin baki tayi tana binta da kallo, ta ɗauka idan ta shiga zata ji ya koro ta amma sai taji shiru, cije baki tayi haɗe da yin kwafa.

A wajan Salma ko tana shiga taga wasu Malamai ne su biyu ɗaya mace sai wani Mlm namiji, suna magana suna nuna masa wasu takardu.

Sosai office ɗin ya bawa Salma mamaki ganin irin haɗuwarsa, ga wani ƙamshi da sanyin Ac dake busuwa.

Sallamarta suka amsa.

Mlm Jamilu ya ce.

"Shigo ki zauna"

Ya faɗa yana nuna mata wata kujera daban.

Jiki a mugun sanyaye Salma ta taka a hankali kamar wacce bata da jini a jikinta ta zauna akan kujerar daya nuna mata.

Ci gaba da ganawa da Malaman yayi, saida ya sallame su kamin a hankali ya miƙe yana dawowa inda Salma take ya zauna saitin kujerar dake kallonta.

"Sorry fa na barki kina jira"

"A'a ba komai Daddy"

Zai sake magana budurwar nan ta leƙo tana turo baki a shagwaɓe ta ce.

"Sir muna jira fa"

"Idan zaku iya jira ku jira, idan kuma zaku je ne ku dawo to lafiya lau"

Ya faɗa kawai yana dawo da dubansa inda Salma take, da kanta ke a ƙasa, zuciyarta na bugawa sosai har tana wuce misali, saboda irin kusancin da suka samu yau da dodon nata, duk da nesa ya zauna da ita har yana janyo kujerar dake kallon tata, ya matsar da ita sosai.

Budurwar tsabar baƙin ciki bata ƙara magana ba ta juya ta koma.

"But exam ɗin da kika rasa, insha Allah zan san yadda za'ai, idan ta kama a gyara ne to, idan kuma dole sai kin sake zana ta da kanki nema to"

"Tom Daddy na gode Allah ya saka da alkhairi"

"Amin. Yau kike ce zaki wuce ba?"

"Yeah Daddy gara na tafi"

"Kina gaya min irin matsalar da kike samu inda kike zaune, gaskiya ba daɗi, dole kaji kin tsani zuwa nan gaskiya"

"Sosai Daddy shi yasa ma bana son ko dawowa school sai dole"

"To miye rayuwar ma? duka rayuwar nawa take ne?, mi yasa mutane suke haka ne?, karki damu ai komai ya kusa wucewa saura semester ɗaya ta rage maku ai, kuma ɗayar nan ba'a cika yin wasu abubuwa masu fahimmanci ba a cikinta, yawanci duk maganar graduation ce tafi yawa"

"Haka ne Daddy"

"Kinfi son Katsina, naga sai murna kike zaki koma Katsina"

Murmurshi Salma ta saki kanta a ƙasa tana wasa da hannunta tana ayyanawa a ranta.

Wato dai da gaske ne Mlm Jamilu baida matsala, sai dai idan baka ma'amalance shi ba, tabbas ta gani da idonta, baida wannan girman kan, ada da take hangensa dashi, dubi yadda suke magana da ita, ya biye mata sai magana suke, kuma cikin sakin fuska da fara'a, abunda ta lura dashi shine, baya son raini ko kaɗan, duk abunda zai kawo masa matsala baya sonshi, gashi zatai shaidarsa ana cewa Malamai da yawa nada son ƴan mata, gasu duk ƴan iska ne suna lalata ƴan mata, zata iya cewa tunda take dashi maganar banza bata taɓa shiga a tsakaninsu ba, gashi da takatsantsan, yanzu ma nesa yake da ita.

Suna ta labari wani Malami ya shigo office ɗin riƙe da takardu.

Ɗagowa Salma tayi tana gaidasa ya amsa fuskarsa da ɗan mamakin ganinta sai kuma ya waske yana murmurshi suna magana da Mlm Jamilu.

Sun ɗauki lokaci suna magana yana fita wani tsoho ya shigo shima.

Shima sun daɗe suna magana zuwa can ya fita office ɗin suna magana a can da mutunan daya zo, aka bar Salma ita ɗaya a Office ɗin.

Wannan budurwar taga ta shigo office ɗin tana mata wani kallo haɗe da cewa.

"Sannunki fa da zama"

Ko kallonta Salma batai ba tana latsa wayarta data ɗakko domin rage mata zaman shirun ta ce.

"Yawwa sannu kema"

Salma ta faɗa bata kalleta ba.

Taɓe baki ta ƙarayi tana ɗaukar wani abu ta fice daga office ɗin zuwa ɗayan office ɗin.

Salma ganin time sai tafiya yake gashi tana son tafiya yau taga har ƙarfe biyu da rabi tayi uku saura yasa ta maida wayarta a jaka tana so ya shigo tayi masa sallama kawai ta tafi, sun idasa maganar ko a waya ne.

Har saida uku ta idasa kamin Mlm Jamilu ya shigo bayan ya gama sallamar kowa ya dawo yana zama ya ce.

"Sorry na barki kina jira dai"

"Ba komai Daddy"

Kallonta yayi yana murmurshi.

Salma saita tuno da maganar da Yusura ta faɗa mata akan ta sanar dashi cewa ya turo mana, idan har sonta yake da gaske zai turo ɗin.

Gyaran murya Salma tayi, tana namijin ƙoƙarin cewa.

"Uhm dama Daddy ina so na tabbaye ka ne"

"Ina jinki Mlm Salma"

Wani miyau ta haɗe, ta ɗauki kusan minti biyar tana juya maganar a zuciyarta.

Da kyar ta ce.

"Daddy da gaske kana so na da aure?"

Tayi tabbayar tana ɗagowa tana kallon fuskarsa.

Sai taga ya saki wani irin murmurshi ya ce.

"Yeah mana, da ace bana sonki bazan tsaya muna ɓata ma juna lokaci ba. But danma kin riga kin gama school da ace tun shigowar ki school ɗin nan ne muka haɗu dake da yanzu kina gida na a matsayin matata, amma yanzu ma insha Allah karki damu zan zo har Katsinar na gaisa da Baba"

Wani irin daɗi ne ya lulluɓe Salma, kamar ta tashi ta daka tsalle ta rungumesa dan murna, zuciyarta har wani motsawa take tsabar daɗi harda wasu guntun hawayen farin ciki suka taru a cikin idonta, a hankali ta shiga mayar dasu bata bari ya gani ba. Da ace yasan irin farin cikin da take ciki sai yayi mamaki ya kuma ƙara tausaya mata irin sonshi da take yi, Allah kawai ya isa shaida irin ɗunbin ƙaunarsa da take yi, ta rasa yaushe ne ma ta fara masa so irin wannan.

Kunya ta kama Salma ta miƙe tana yin namijin ƙoƙarin ƙara kallon cikin idonsa ta ce.

"Ina sonka da yawa Daddy"

Tana faɗar haka ta juya da sauri ta fice daga office ɗin, tana kallon lokacin daya saki wani irin murmushin dake ƙara ma fuskarsa kyau da haiba haɗe da kwarjini, murmurshin data tabbata mutane ɗai-ɗaine ke ganinsa a fuskar tashi, ita ɗin sa'a tayi ta kuma shigo cikin rayuwarsa da ƙafar dama........

PAGE 43

*UMMI POV*

"Tunda kika dawo Salma naga kin zama wani iri"

Aje wayarta Salma tayi bayan ta tura masa messages ya kai sau nawa amma bai duba ba. Kusan yau kwanakinta biyar da dawowa, tunda ta dawo gida idan ta kirasa baya ɗauka, messages baya maido mata, mi hakan ke nufi ne?.

Sosai lamarin Jamilu ke bata tsoro, wani lokacin idan yayi abu kamar bashi ba, wani irin murɗanɗan mutum ne mai wuyar sha'ani, idan mace bata karancesa ba tabbas zata sha wahala a tare dashi.

"Salma Innalillahi, wai tunanin mi kike ne haka?, saifa magana nake ni ɗaya, na ɗauka da kika tashi zaune zaki bani amsar tabbayar dana miki ne, sai naga kuma kina kallon cikin wayar ki kinyi shiru, mike damunki ne wai?"

Sakin ajiyar zuciya Salma tayi tana jin kanta na sara mata sosai, dan jiya kwana tayi tura masa messages ta WhatsApp amma again dai baya buɗawa bare ya

21 / 36