Mugun Icce Book Compelet Zahra Royal

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   12 / 36

33K to 36K   out of 106.4K words

/>
Tashi tayi tana murmushi zata shige ɗaki dan Yusura tuni ta shiga ɗakin ta basu waje.

Saiga Aunty Murja ta fito tana cewa.

"Wai yanzu fisbilillahi Mlm bakai mata wani faɗa ba akan wannan daren da take zuwa ta raba shi a waje?. Ace ƴarka mace ta dawo a irin wannan lokacin amma ko ama jikinka Mlm?"

"Murja....

Ƙara katse shi tayi da cewa.

"Ai Mlm dama bazaka taɓa yarda ba, amma dai a juri zuwa rafi ai wata rana tulo zai fashe wallahi"

Baba bai ƙara cewa komai ba saima girgirza kai da yayi.

Salma dake tsaye ta haɗe wani abu a maƙoshinta tana kallon Aunty Murja ta ce.

"Aunty Murja ina wuni?"

Wata uwar hararara ta ɓalla mata tana cewa.

"Munafuka da ban wuni ba zaki ganni a nan tsaye. Ki dai rinƙa jin tsoron Allah wallahi Salma, kar ace kune zaku ɗorama mahaifinku yawan jinin da zaiyi ajalinsa, dan Allah ku daure ku gyara wannan ƙazamar rayuwar taku mana"

"Murjaaaaa, yafa isheki haka, bana son irin wannan maganganun na tsegumi irin naku da Mata bana so. Ke Salma wuce ki shiga ɗaki"

Taɓe baki Aunty Murja tayi tana ɗaga ƙafaɗarta alamar ko a jikinta zata juya ta shige ɗaki tana ƙara yada maganganu ƙasa-ƙasa.

Tana shigewa Baba yabi bayanta da kallo.

"Mata-Mata halinku sai ku, ace ku dai idan ba ƴaƴan da kuka haifa ba baku taɓa yin adalci sai naku kaɗai da kuka san ciwonsu?"

Ya faɗa a fili yana ƙara girgirza kansa.

Wayarsa ce tayi ƙara dan haka ya katse masa nazarin da yake yi akan wasu Mata yadda suke ɗaukar ƴaƴan kishiya dama ita kanta kishiyar.........

PAGE 23

"Aunty Salma dan Allah ki ƙara haƙuri da Umma na aka wannan abu da take miki please"

Sauke ajiyar zuciya Salma tayi tana cire kayan Makarantar dake jikinta kamin ta zauna a hankali tana ƙara sauke lumfashi.

"Karki damu Yusura babu komai, ni bana riƙe mutum a raina ko kaɗan, ai wata rana ma bazata ganni ba bare tayi min duk wannan komai fa lokaci ne dashi Yusura"

Jiki a sanyaye Yusura ta jinjina kai ta ce.

"Tabbas kuwa Aunty Salma hakane Allah dai ya ƙara miki haƙuri"

Salma zatai magana taji ƙarar wayarta data saka chaji.

A hankali zata miƙe ɗakkota Yusura tayi saurin tashi tana cewa.

"Bari na ɗakko miki"

Komawa tayi ta zauna. Dai-dai ta kawo mata wayar na tsinkewa wani kiran ya sake shigowa.

"Au Aunty Ummi ce ma"

Salma ta faɗa tana ɗaukar wayar ta ƙara a kunne.

"Assalamu alaikum Aunty Ummi"

Daga can Ummi ta amsa mata na cewa.

"Inata kiran wayarki tun ɗazu baki kusa"

"Sorry Aunty Ummi, wallahi yanzu na dawo daga school, kin san yadda muke shan wahalar abun hawa idan yamma tayi"

"Ayyah sannu wallahi nasan kinsha wahala, ai dai an kusa gamawa kowa ya huta"

"Ai ko dai. Yasu Anam dasu Aunty Binta?"

"Suna nan kalau wallahi. Komai dai lafiya a nan ko Salma?"

"Wallahi Aunty Ummi lafiya lau. Amma dai zaki zo nan ko ai?"

"Eh zan zo insha Allah zuwa jibi cikin satin nan dai"

"Kai Aunty Ummi har sai jibi?"

"Amma dai kin san Aunty Binta bata so taji na ce zanje ko ina, idan har nazo gidanta, abunda kuma yake haɗa ni da ita kenan fa. Dan gobe ma zanje gidansu Maryam ɗita mu gaisa zanje na yini gaskiya"

"Ohhh Allah sarki Maryam, na kuwa sani Aunty Ummi, ai bazai yiwu ace kullum kai kana zaune a gida ba. Bare ma gaskiya bata so kina zuwa gidan su Maryam ɗin nan taki, kuma yarinyar akwai kirki, abotarku ta daɗe tun a shigowarmu hygiene da ita kika fara haɗuwa"

"Ai wallahi bata isa ta hanani zuwa gidansu Maryam ba wallahi, abu ne wadda bazai yiwu bama"

"Hmm Aunty Ummi sai dai kinzo, zamu sha labari ne sai dai kinzo ɗin kawai"

Salma ta faɗa tana tuno Mlm Jamilu.

Sallama sukai tana sauke wayar Yusura ta ce.

"Ashe tazo Kano itama?"

"Eh wallahi yau ta zo da yamma itama"

"Wai Aunty Salma naga sai murmurshi kike tunda kika shigo, miya faru ne a school ɗin nasan dai akwai wani abu daya faru sabo ko?"

Murmushi ta ƙara saki tana girgiza kanta ta ce.

"Bafa wani abu bane. Kawai dai abunda ya farun yau ya bani matuƙar mamaki"

"Uhm to miye shi haka?"

Gyara zama Salma tayi tana miƙama Yusura wayar dake hannunta ta ce.

"Kinga saka min chaji ki zo na faɗa miki"

Amsa tayi tana murmushi taje ta saka ta dawo ta zauna tana faɗin.

"Ina jinki Aunty Salma harna ƙagara naji ma wallahi"

Murmushi mai haɗe da dariya Salma ta saki tana girgirza kai ta ce.

"Uwar son jin labari kawai"

"Ai Aunty Salma labari fa akwai daɗin ji wallahi"

"To yayi. Ai kin san dai Mlm Jamilu shugaban school ɗinmu?"

"Yeah ina jin labarinsa dai a wajanku, kai wajanma duk wadda yayi school taku"

"Yawwa shi, a cikin labarin da kike ji nasa mi kika sani game dashi?"

"Hmm amma Aunty Salma miya kawo tabbayar nan?"

"Kawai ina son gasgata abunda na gani ne yau, dan gani nake kamar mafarki nake ba gaskiya bane"

"Tofa miya farun Aunty Salma?"

"Ki fara bani amsa dai tukunna kamin kiji"

"To dai ni dai a iya jin labarinsa da nayi a wajanku ma kaɗai daga ji yana da izza da ɗagawa harda girman kai, gashi da alama zaiyi kwarjini a fuskarsa da komai nasa ma"

"To kina tunanin mai irin wannan halin zai iya ganin Mace harya rage mata hanya, kuma babu wata magana data taɓa shiga tsakaninsu?"

"Eh to zata iya yiwuwa Aunty Salma, ai abun Allah ne, kuma ni nake ganin wata ƙila fahimtarsa ne mutane basuyi ba, idan har ka shiga rayuwarsa sosai wata ƙila zaka iya gane ba wai girman kaine dashi ko ɗagawar shi wani ne ba. Amma fa a iya hasashe na kenan fa"

Jinjina kai Salma tayi tana ɗan riƙe baki zuwa can ta ce.

"Hakan zata iya faruwa a hasashen naki tabbas"

"To amma Aunty kar dar ki ce min shine ya rage miki hanya har zuwa unguwar nan?"

Yusura ta faɗa da ɗan mamaki akan fuskarta tana nuna Salma da hannu.

Jinjina mata kai Salma tayi alamar tabbas hakane abunda ta faɗa.

Ido Yusura ta fiddo waje tana riƙe baki cike da mamaki ta ce.

"Ohh ikon Allah. Amma fa ina ganin dan gaya dare ya fara miki ne a inda ya ganki, sana wata ƙila yaga ke kaɗai ce a wajan yasa ya rage miki hanya"

"Gaskiya hakane ma Yusura, dan koda na shiga Motar babu maganar data shiga tsakaninmu sai ma tabbayar farko da yayi min cewar ina na nufa, yayi maganar kamar baya so, sai kuma da muka zo ƙofar gadon ƙaya na gaya masa inda zai aje ni, koda na fito daga Motar ban tsaya jiran mima zaije ya dawo ba na dai gode masa nayi saurin wucewa na bar inda motar take. Amma fa ni gaskiya Yusura har zuwa yanzu mamaki bai barni ba, nasan waye Mlm Jamilu fa"

"Ke kina wasa da lamari Ubangiji ne wai?, kika sani ma ko akwai wani abu da Allah ya ɓoye ke da Mlm Jamilun?"

Yusura ta faɗa da zolaya harga Allah da wasa ta faɗa tana dariya, amma sai Salma taji wata irin faɗuwar gaba a lokacin da Yusura ɗin ta faɗi maganar.

"Mtsww kefa Yusura kin cika shirme babu abunda Allah ya ɓoye ma, duk yau ne fa muka taɓa ma magana dashi, amma ko sani na baiyi ba wallahi"

"Kwantas Aunty Salma wasa nake miki fa"

Ta ƙare maganar tana dariya.

Girgirza kai kawai Salma tayi tana ɗan murmushi amma duk da haka maganar bata sake ta ba.

Tashi zatayi domin watsa ruwa suka ji an shigo ɗakin.

Aunty Murja ce ta shigo tana ɓalla ma Salma hararara ƙasa-ƙasa ta ce.

"Ke yanzu tsakaninki da Allah Makaranta kike zuwa ne ko kuwa yawon bariki?. Ki ɗaure ki gaya ma Mahaifinki gaskiya, dan wallahi wannan abun da kukeyi kuna yaudararsa da sunan wai Makaranta kuke zuwa karatu kamar dai cin amanar iyayenku ne kuke yi"

Tashi tsaye Yusura tayi tana kallon Aunty Murja da mamakin wannan lafazin nata marassa toshe da kan gado.

Salma ko ƙasa tayi da kanta bata ce komai ba.

Aunty Murja zata ƙara magana har tana nuna Salma da yatsa Yusura tayi saurin tare mata hanzari.

"Haba Umma miye haka kike yi ne dan Allah?"

"Ke dalla gafara can, ke mi kika sani game da yawon bariki, tunda ke ba wani fita kike yi ba, ai ita tasan irin tsiyar da suke shukawa idan sun fitar"

"Haba haba haba Umma dan Allah. Wannan fa abunda da kike yi ba dai-dai bane wallahi?, su Aunty Salma fa sun ɗauke ki uwa ce amma kinzo kina masu wa'innan maganganun, ya kike ganin yadda zasu rinƙa kallonki ne a zuciyarsu?"

"Sun daɗe basu kalle ni yadda suka ga dama ba. Bafa na son shishshigi Yusura, kifa fita a ido na rufe tom"

"Amm....

"Kinga kimin shiru yawwa bada ke nake magana ba, kinji abunda na ce?"

Ta ƙara maida hankalinta wajan Salma dake zaune kamar gunki tana ƙara cewa.

"Ke kuma wata rana ai gaskiya zata fito fili kowa ma yasan tsiyar da kuke tsulawa wai da sunan Makaranta kuke zuwa a'ato"

Ta ƙare maganar tana juyawa ta fice daga ɗakin.

"Kai jama'a mike damun Umma ne a rayuwarta?, mi yake shiga ganta ne haka?. Dan Allah Aunty Salma ki ƙara haƙuri dai, bazan gaji da baki haƙuri ba"

A hankali yadda Yusura bazata gani ba ta saka hannunta tana ɗauke hawayen da suka fara zubo mata tana ɗan ƙaƙalo murmushin daya fi kuka ciwo ta ce.

"Karki damu fa Yusura babu komai ai"

Komawa Yusura tayi ta zauna kusa sosai da Salma tana dafata ta ce.

"Wallahi nasan Allah kaɗai yasan irin zafin da kike ji a zuciyarki akan kalaman da Umma da take amfani dasu wajan jifanki dasu. Kiyi hakuri kiyi hakuri abunda zan iya ce miki kenan, sana dan Allah ki rinƙa yafe ma Umma, ko dan albarkaci na, dan nasan idan har baki yafe mata ba keda Aunty Ummi ƙarshe a nan gaba bazata ga da kyau ba wallahi"

"Haba dai Yusura bana riƙe mutum a raina na faɗa miki, daga zarar nayi bacci na tashi da safe to na mance da duk wani abunda ya faru a yau, sai dai ko Ummi ɗin, dan kin santa da roƙon abu a ranta"

"Hakane na sanki da haƙuri kam, amma Aunty Ummi har alwashi tasha yi akan duk sai ta rama wulaƙancin da Mutane sukai mata"

"Uhum ai halin Aunty Ummi hmm sai ita kawai"

Shiru sukai kowa na saƙa abu a cikin zuciyarsa......

PAGE 24

*UMMI POV*

Sauke lumfashi tayi tana kallon cikin wayarta ganin time yaja sosai ga dare yayi, bata fargaba sosai suna ta chatting da Maryam akan zuwan da zatai gobe gidansu, da kyar suka rabo ganin kusan sha ɗaya da rabi.

A hankali ta miƙe tana jin jikinta yayi mata tsami sosai.

Toilet ta shiga ta ɗauro alwala ta kwanciya bacci, dan su duka sun saba da yin alwalar kwanciya bacci.

Tana dawowa ta jawo jakarta ta fiddo wani man fuska mai gyara jiki sosai ta ɗan lakuta tashafa akan fuskarta kamin ta mayar tana zuwa bakin gadon ta zauna a hankali ta maƙala chaji ta ƙara sauke ajiyar zuciya a fili kamin ta gyara zamanta sosai ta hau kan gadon tana ɗaga hannunta sama ta fara addu'a a tare ta shafa da addu'ar kwanciya bacci tana gamawa ta koma a hankali ta kwanta tana jan lumfashi kaɗan ta lumshe idonta tana ƙoƙarin yin bacci amma kamar an ɗauke baccin a cikin idonta haka take ji.

Juye-juye ta fara yi tana taɓe baki haɗe da sakin tsaki, ta saki tsaki ya kai nawa tana ta juyi akan gadon.

Ta rasa kuma uwar mi take tunani da har ya hanata bacci haka.

Sai wajan ɗaya da wani abu taji bacci ya fara ɗaukarta. Sai dai kukan Anam dake can ɗakin iyayenta dake makwaftaka da wadda take kwana ne ya katse mata baccin data fara.

Wani kalar tsaki taja tana kwaɓe fuska.

Sosai yarinyar ke kuka sai rarrashinta suke amma kamar ana ƙara mata balon ɗin kukan ne.

Kusan har biyu taƙi tayi shiru.

Ummi ma kukan ne ya hanata bacci dan bata ƙaunar kukan yaro ko kaɗan, tana dai kwance amma ba bacci take ba.

Ji tayi an buɗe ƙofar ɗakin da take an shigo.

Bata nuna idonta biyu ba jin Aunty Binta ce ta ɗakko Anam sai ihu take kamar wacce ake mintsina.

"Please Ummi ɗan tashi dan Allah ki rarrasheta, wata ƙila ke tayi shiru a hannunki please"

Wata irin ashar Ummi ta danƙara a zuciyarta tana Allah ya isa, ƙiri-ƙiri an hana mutum bacci, ga gajiya da mutum ya kwaso, ai wannan ko ita ta haife ta sai haka wallahi.

Miƙewa tayi a hankali tana cin magani.

Sai dai a yadda taga fuskar Aunty Bintar taci uwar tata cin maganin, dan fuskar nan babu walwala kamar zata daki Anam ɗin dake hannunta.

Amsarta tayi tana ɓata fuska itama sosai.

Tana bata ita ta juya ta fice daga ɗakin.

Ai sai Ummi tabi bayanta da ido kawai tana jinjina rashin mutumci irin na Aunty Binta.

Yarinya kuwa sai ihu take tana ƙarawa har wani shiɗiwa take.

Ummi dole ta miƙe tsaye tana sata a kafaɗarta ta fara zagaye ɗakin da ita.

Sai gata ta fara yin shiru amma tanayi tana ƙananun koke-koke, sai sauke ajiyar zuciya take na kukan da tasha.

Wani irin jiri-jiri Ummi ta fara gani ga hannunta daya gaji sosai wadda ta saɓa Anam ɗin da shi, shi yasa ta ɗan tsaya da zagaye ɗakin tana rirrigata, a hankali ta dafe kanta tana jin yadda ya wani sara mata.

"Innalillahi, wai mi yasa su bazasu tsaya su iya rarrashin nata bane. Kamar ma fa bacci suka koma?"

Ta faɗa tana ɗan leƙa waje, tabbas ɗakinsu babu hasken filita, kwanciya suka koma suka yi.

"Yau ni ga Jaka ma kenan ko? an barni da Ƴa ni kar nayi baccin ma ko a jikinsu?. To ya za'ai na iya wata ɗaya ko fin haka a gidansu?, ai ƙila kashe ni za'ai da raina, ko a ɗora min wata cutar, bazai yiwu ba wallahi"

Kukan Anam ne ya ƙara dagula mata lissafi.

"Kai kuji ƴar banzar yarinya, tsayawar da nayi miki ce kika wani ɓare baki kina kuka?, yau ga ƴar wahalarki kema ko kike nufi?"

Sai surutu take ita ɗaya tana jin bala'in haushin Aunty Binta daga ita har Uncle Abdul ɗin da shima ya zama mijinta ce.

Rirrigata ta ƙara yi. Ga wata uwar zufa da Ummi take jinta tana yanko mata a kota ina, tana jin kamar zata faɗi, jiri sosai fa take gani, dama bata da jumurin tsayuwa dama haka take can, idan ta cika tsayuwa da yawa zata iya faɗuwa komai kuma na iya faruwa da ita ta sani.

Dan haka ganin kamar bacci ya fara ɗaukar Anam ɗin yasa Ummi zuwa har ƙofar ɗakin nasu ta shiga bubbugawa kaɗan.

Sai da ta daɗe a tsaye tana ɗan kwankwasa ƙofar, kamin azo a buɗe.

"Gata nan tayi shiru ne"

Ummi ta faɗa tana kallon Aunty Binta da bacci ne sosai a idonta harda hamma ma ta buɗe ƙofar tana yi.

Amsarta tayi kawai ta juya ta rufe ƙofar ɗakin, babu wata godiya ko yabawa.

Sosai kuma hakan da tayi yasa Ummi jin wani iri a zuciyarta, girgirza kai kawai tayi ta koma ɗakin data sauka.

Tana zuwa ta kwanta itama tana jin zafi da raɗaɗi sosai akan abunda Aunty Bintar tayi.

Wasu zafafan hawaye ne kawai taji suna zubo mata.

Hannu tasa ta shafa jin hawaye ne da gaske take yi yasa ta sakin tsaki a fili ta furta.

"Akan mi yasa zanyi kuka ma?. Hmm ai wata rana sai labari ko?, kuma wata ranar ma bata isa ta ganni ba kamar haka, to amma yaushe ne?"

Ta faɗa kamar zata saki kukan gasken sosai.

Tsaki ta ƙara ja tana jin haushin kanta akan kukan da take yi da hawaye. Tasan dai tabbas zuciyarta taji zafi akan rashin gode mata da kuma yaba mata, hasalima ko kallon kirki Aunty Bintar batai mata ba, sai ma amsar Anam ɗin tayi ta koma juya ta rufe ɗaki, kuma babu wata alamar jin daɗin abunda Ummi ɗin tayi mata, ko akan fuskarta kuwa.

Da ɓacin rai Ummi bacci ya ɗauketa.

Kiran sallar asuba ne ya tayar da ita. Miƙewa tayi tana ganin yau asubar tayi mata saurin yi, ko dan bata kwanta da wuri bane jiya?.

Toilet ta shiga tayo walwala tana shinfiɗa abun sallah ta fara yin raka'atalil fujiri kamin tabi da sallar asubahin.

Harta gama addu'o'inta ta shafa ta ɗan zauna tana karatun Alkur'ani mai girma a cikin wayarta bata ji motsinsu ba, bare su tashi sallar asuba ɗin.

Sai da gari ya ɗan fara haske sana taji motsin tashin Uncle Abdul ɗin yayo alwala ya fice daga gidan, lokacin wasu masallatan basu gama sallar asuba ɗin ba.

Ita ko Aunty Binta bata jin dama tana tashi sallar asuba, dan duk zuwan da zatai bata jin motsinta.

Tashi tayi taje ta kwanta bayan ta gama duk addu'ar da zatai.

Ta daɗe da kwanciya taji dawowarsa ya shige ɗakin nasu.

Bacci mai daɗi ne ya fara ɗaukar Ummi saboda jiya baccin da batai ba.

Gari yayi haske taji an buɗe ƙofar ɗakin an shigo.

"Ya kamata ki tashi fa"

Aunty Binta ta faɗa tana aje Anam dake wasanta akan gadon.

A hankali Ummi ta miƙe daga kwancen da take dama ta sani, idan har ba kai bacci ishashshe ba tun da daddare to fa safiya nayi a gidan Aunty Bintar baka ba ƙara wani baccin sai kuma wani daren, shima kuma baku san yadda zai zo ba, saboda Anam ɗinta rigima ce da yarinyar, bata baccin dare, wani lokacin kuka kawai take babu gaira babu dalili kuma tsabar rigima ce.

"Ina kwana?"

"Lafiya. Ki tashi kije ki ɗora min ruwan wankan Anam, da kuma ruwan zafin

12 / 36