Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
*MUGUN ICCE*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO......*
*Tsokaci*
A rayuwa, ba zaka taɓa gane wanda yake sonka ko ƙinka gaskiya ba — sai wani abu mai girma ya riske ka. A irin wannan lokaci ne zaka gane matsayinka a zuciyar mutane. Wannan labari yana fito da gaskiyar da ke cikin zuciyar ɗan adam: *mutum mugun icce ne.*
Koda makusantanka ne, koda jininka ne, kowa na iya cutar da kai. Zuciya bata da ƙashi, kuma amana tana da rauni mai sauƙin karyewa. Wannan littafi ya cika da cin amana — ba irin ta nesa ba, ta kusa, ta jini, ta aboki, ta masoyi — cin amanar da ke ragargaza zuciya.
**Zaka karanta mamaki mai ban tsoro.
Zaka ji raɗaɗin amana da ba za a iya mantawa da ita ba.
Zaka gane cewa wanda ka ɗauka tamkar garkuwa…
Shi ne ya jefa ka cikin ƙunci.
Haka rayuwa take… *mutum mugun icce ne.*
PAGE 1
*House No 26, Gadon ƙaya, Kano State Nigeria*
A hankali ta shiga buɗe idonta daya tara ruwan hawaye. A hankali hawayen suka shiga silalo mata akan fuskarta.
"Wai bazaki fito ba?, kina jina ina magana, kin mayar dani ƴar iska?"
Daga can waje tsakar gidan nasu taji maganar Aunty Murja.
Jikinta na ɗan rawa ta dafa bakin gadon da take zaune ta miƙe, tana jin wani irin jiri na ɗibarta, saboda kwana da tayi tana zazzaɓi, ga aman dake wahalar da ita.
Tana sauke lumfashi mai zafi ta idasa fitowa daga cikin ɗakin.
Tana fitowa Aunty Murja ta watsa mata wani mugun kallo tana ƙara nunata da yatsa ta ce.
"Ai wallahi Salma ni da ke ne a gidan nan, kuma tabbas sai munje asibiti ko kyamis anyi miki awon ciki, yaya za'ai ace tun daran jiya kike kwara amai kamar zaki amayar da duniya, da an kalle ki an san akwai wani abu a ƙasa tattare da ke".
Wani irin kuka ne ya turnuƙe Salma ta sake shi tana jin wani irin baƙin ciki ya rufe mata zuciya.
"Munafaka ai dole zaki fashe da kukan munafurci mana, saboda asirinki zai tuno. Yo dama ya za'ai Mlm ya bari ƴaƴansa suyi wani karatu, gaku gandama-gandama kun kasa auruwa, ai dole a fake da karatu ana yawon iskanci tunda an rasa na aure har yanzu, ace duk yawan samarin ki kin kasa samin na auri sai dai na holewa ko?. Ai kawai tsabar ya baku lasisin iskanci ne kawai shi Mlm ɗin, amma ba abunda kuke yi sai yawan iskanci ba wata makarantar da kuke zuwa yawwa"
"Wallahi Umma Salma baza ta taɓa yin abunda kike ƙoƙarin cewa ba"
"Rufe min baki, shashasha marar zuciya kawai, ko na zo na ci ub*anki yanzun nan"
Turo baki Yusura tayi tana kamo hannun Salma dake neman zubewa ƙasa tsabar yadda jikinta da babu ƙarfi kwata-kwata.
"Sake ta dalla can asibiti zamuje wallahi yau ba sai gobe ba, dole ne asan abunda taje ta kwaso ma mutane, uban naku ya zo yaji abunda take aikatawa"
"A'afa Umma kar aje aji kuny....
"Kunyar buh*un ubanki Yusura?, wai shin ko kema uwar Salma ta shanye min ke ne?, ko kuma ita ta haifar min ke ban sani ba?"
"To ai Umma abunda kike kwata-kwata bai dace ba wallahi, dan kawai Salma ta zo gidan nan a matsayin karatu ta zauna na ɗan lokaci ne fa kawai, ta gama ta tafi"
"Zaki rufe min baki ko sai na zo na fasa miki shi?"
Shiru tayi ganin yadda Salma tayi saurin girgiza mata kai. Haɗe sauran maganar kawai tayi, ba dan wai Ummar ta ce zata fasa mata bakin tayi shiru ba, sai dan kawai Salmar data nuna mata.
"Ungo nan sanya maza"
Kallon hijab ɗin tayi. Hannunta na ɗan rawa ta amsa ta sanya. Da sauri Yusura ta ƙara kama mata hannu. Aunty Murja kuma tayi gaba tana mitar suyi sauri.
Bin bayanta kawai suke har suka isa wani ƙaramin kyamis dake a cikin unguwar tasu.
"Yawwa zauna. Kai bawan Allah ana awon ciki a nan?"
Wani matashi dake tsaron kyamis ɗin ya kalleta sosai ya amsa da eh ana yi.
Salma najin lokacin da take hamdala sai ka ce an faɗi wani abun jin daɗi, sosai take mamakin matar nan ainun.
"Yanzu fisbilillahi Umma miye abun hamdala a nan ciki?, wai.....
"Dalla gafara can, rufe min baki na ce, kifa kiyaye ni Yusura, ub*an wani ya ce ma ki biyo mu ne wai?"
Zata sake magana Salma ta sake matse mata hannu alamar tayi shiru dan Allah.
Suna nan Yaron kyamis ɗin yayi awon da yake ya iya komai akwai kayan aiki dama.
Sun ɗauki lokaci kamin yaron ya kalle su ya ce.
"Yawwa hajiya a nan dai ya nuna cewar...
Katse sa tana cewa da sauri.
"Ya nuna cikin ne hala ko?"
"Noo Hajiya gaskiya a iya bancike na babu wani ciki gaskiya, ga abunda ya nuna bata da shigar ciki"
Salma bata san lokacin data runtse idonta a hankali wasu hawaye na sake zubo mata, tana sauke ajiyar zuciya a hankali.
Tana jin yadda Aunty Murja ke ƙara cewa.
"Kai Yaro anya kuwa ka san aikin ka?, ka duba da kyau ma kuwa?"
"Hajiya iya gaskiya nake faɗa miki, amma idan baki yarda ba zaku iya zuwa babban asibiti sai a sake mata wani awon"
"Dole ne ma sai munje asibitin, domin gaskiya ban yarda ba ni"
"Amma tsakani da Allah Umma wannan abun fa yayi yawa da kike yi wallahi, wannan wacce irin ƙiyayya ce ne wai?"
Saukar marin da Yusura taji ne akan ƙuncinta ne yasa ta fiddo ido waje tana duban Umma data ɗaga hannu ta zafga mata tafi, tana huci ta nunata da yatsa ta ce.
"Idan ina magana akan wannan baƙar ƙaddarar kika sake kika ƙara katse ni ko gwalashe ni, na rantse da Allah zan nuna miki cewar ni ce na haife ki ba wai ke ce kika haife ne ba, tunda naga ke baki da tunani shashasha ce ke"
"Haba Hajiya ayi haƙuri dai"
Yaron kyamis ɗin ya faɗa yana ƙoƙarin sallamarsu.
Sosai Yusura ke hawayen baƙin cikin halin Umma.
A haka suka taso suka dawo gida har lokacin Umma na mita tana faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba.
Tana shiga ɗaki ta ɗauki wayarta ta danna wata number tana ɗauka ta fara magana.
"Ke dai bari A'i wannan yarinyar Yusura ke shirin ɓata min rai"
"Mi yake faruwa ne Murja?, yi min baya ni"
A'i ta faɗa daga cikin wayar.
Gyara zama Aunty Murja tayi ta ce.
"Hmm bari A'i, kinga yarinyar nan ko miye zanyi na ma wannan yarinyar Salma sai ta ce ban iya ba, yarinyar kamar ba ni ce na haife ta ba?"
"Uhmm ai sai da na ce miki Murja kiyi duk mai yiwuwa ki datse karatun nan da yarinyar nan take. Taya za'ai iyayenta na can ƙauye daga zuwanki za'a kawo miki ƴar wata wai da sunan ta zauna karatu take, salon azo a ɗora miki hawan jini, ko azo miki da mugun abu"
"Abunda da nake zargi kenan, ko kuma so ake tazo birni ta samu miji ɗan birni, tunda a a can sun gagara su sami mijin, ƙannan-ƙannansu ma sai aure suke suna barin su, su kuwa daga ita har shegiyar ƴar uwar nan tata Ummi marar kunya mai ido a tsakar ka ai sunyi kwantai babu ɗan iskan dake zuwa masu da maganar aure, dama kuma wannan shegen ƙauye nasu idan suna ciki ai ba samun mijin zasu yi ba, shine aka fake da karatu. Nifa zargina ma kar taje tayo mana abun kunya, kin san ƴan ƙauye basu iya wayewa bafa. Ni so nake kawai nayi maganin Yusura ta daina jin tausayinta dan ub*anta, so nake nayi mata gata amma ita bata gani. Yanzu dan Allah A'i idan ana ganin Salma tare da Yusura ya za'ai har wani ya ce yana son Yusura?, nesa ba kusa ba ƴar iskar yarinyar nan Salma ta fita komai, kowanne shege sai kika ga ya zo da sunan wai Salma yake so"
"Tabɗi jam ai ko sai kin miƙe tsaye wallahi. Amma koda yake ai nake ganin ba wai aure yake kawo su ba, tunda kinga har zuwa yanzu babu wadda ya fito da sunan aure ne ya kawo sa"
"Yo ƴar iska ce ni A'i na bari ta auri wani, ina ai sai dai idan bata zaune gidan nan wallahi, zasu san illar turota karatu da saukai. Sana kuma ruwan ido ne irin nasu, wai fa basu ga wadda ya dace dasu bane, inaga mai abun hannu ake so ya fito, kwaɗayayyu kawai. Nanfa kina gani sai ubansu yayi sati har biyu ban gansa garin nan ba, yana can wajan tsofaffin Matan nan nashi, da ba abunda yake ci a wajansu sai wahala"
"To ai Murja ki ce kika zauna, ai wallahi da yanzu sai kinga dama ki barshi yaje inda suke ma, ita kuma Yusura itama da an miƙe tsaye kanta zata daina shiga al'amarin Salma"
"Nifa A'i bana so ya rinƙa zama a nan ɗin ai, nasan mi nake shiryawa ai, ke dai akwai lokacin da ni da kaina zan zo na ce ki raka ni inda za'a min maganin shegu su dukansu. Ita kuma Yusura akwai wani abu da nake jira, ba boka ba Mlm zan sa dole sai ta tsani ƴar uwar tata, zanga ƙarshen tausayi ai........
*MUGUN ICCE*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO.....*
PAGE 2
*Gwajawa Rimaye, Kankia LGA, Katsina state Nigeria*
"Mama nifa gaskiya bazan je gidan Aunty Binta ba"
Mama ta gyara zama tana duban Ummi dake turo baki gaba, ranta a ɗan ɓace ta ce.
"Ai ko wallahi sai kinje"
"Haba Mama wallahi duk lokacin dana je gidan nan raina ke ƙara ɓaci, kwata-kwata Aunty Binta kamar jaka haka take maida ni a cikin gidanta, kamar ba ƙanwarta bafa, kwata-kwata kamar ba ke ce kika haife ta ba, sai ka ce ba wacce muka fito ciki ɗaya ba. Ni gaskiya Mama gara kayi nesa da mutum shine yafi kawai"
"To umarni nake baki, kinji na gaya miki wallahi"
Wasu sabbin hawaye ne suka shiga taruwa a idon Ummi.
Tashi tayi da sauri dan idan ta ce zatai magana kuka ne zai kwafce mata. Dan ita kaɗai tasan zaman ƙuncin da take bafa dashi idan har taje gidan Aunty Binta ɗin.
Tana shiga ɗaki ta ɗauki waya hawayen dake shirin zubo mata suka samu nasarar zubowa a hankali tasa hannunta tana ɗauke su. Wata number ta danna ta kira, sai da ta tsinke kusan sau biyu ba'a ɗauka.
A hankali ta cire wayar daga kunnenta tana mamakin ƙin ɗaukar wayar.
Sake kira tayi tana addu'ar a ɗau wayar.
Sauke lumfashi tayi mai zafi jin an ɗauki wayar.
Muryar wacce taji ne yasa Ummi ɓata fuska tana faɗin.
"Ke Yusura ina mai wayar?"
"Aunty Ummi sun tafi asibiti ita da Umma"
"Asibiti kuma?"
"Eh bata jin daɗi ne, shine Umma taje ta raka ta"
Girgirza kai tayi tana sauke ajiyar zuciya zuwan can ta ce.
"Ki gaya min dai gaskiya mike faruwa da ƴar uwata?, dan nasan ba banza Aunty Murja zata raga Salma asibiti ba"
"Allah babu wani abu Aunty Ummi, kawai taje rakata ne fa"
"Is Okay kawai, idan ta dawo kice ta neme ni please"
"Okay Tom zan faɗa mata"
Ta sauke wayar tana jin babu daɗi, tana jin kuma tabbas akwai abunda Aunty Murja ke kitsawa, babu yadda za'ai ace wai haka kawai taje raka Salma asibiti, ai ko mutuwa zatai tasan da wuya Aunty Murja ta iya ɗaga kai ta kalle ta, bare harta rakata wani asibiti. Tabbas akwai dai wani abun, duk da tasan da wuya Salma ɗin ta gaya mata abunda ke faruwa, zurfin cikinta yayi yawa.
"Ki fito kije kiyi sharar tsakar gidan can Ummi, kar ma a fara surutai akan hakan kin sani kuma"
Miƙewa Ummi tayi tana ɓata fuska, gaba ɗaya zaman gidan ne ma taji ya ƙara gundirarta, gara ta tafi gidan Aunty Binta, to amma data tuna gidan Aunty Bintar ma ba wani hutu ko sakin fuska, duk sai taji duniyar inama zaka je ka huta.
A hankali ta ɗaga kanta tana addu'a a fili.
"Ya rabb ka kawo mana iyakanciwar zaman gidajen wasun nan da muke yi, ya rabb ka kawo mana lokacin aurenmu nida ƴar uwata muma mu huta, da raɓe-raɓen zuwa gidan wasu"
Ta faɗa zuciyarta na ƙaryewa sosai, dan daga ita har Salma dake a matsayin ƙanwarta sun kai shekaru Ashirin da bakwai ko da takwas ita zata kai da takwas ɗin ma. Shi yasa kwata-kwata rayuwar ke masu wahala a gidan iyayen nasu, su kansu iyayen sun fara nuna gajiyawa, bare ma Mama tafi kowa nuna cewar sune basa bada damar wani ya raɓe su bare har su bashi damar ya aure su, a kullum Ummi kuka take kwana yi idan har Mama ta fara mitar nan tata, gara ma Salma da ke karatu a Kano bata cika zama gida ba tare da Mamar ba, duk da dai su duka basa zama ɗin sosai a gidan nasu, sunfi tafiya Kano.
Tana jin lokacin data fito parlon Mamar ke ƙara cewa.
"Ai ɓata rai ma Ummi ke da Salma yanzu kuka fara, zaman gidan wasu ko gidan wani ai kune kuka jazama kanku da kanku, taya za'ai duk maneman ku a rasa na aure?, ai ko wallahi idan baku dawo cikin hankalinku ba daga ke har Salma ɗin a haka zakuyi zama da ɓacin rai, ai aure shine mutumcin ƴa mace, ko ni hankali sai yafi kwanciya bare kuma ku"
Shiru kawai Ummi tayi tana jin yadda ƙirjinta ke mata zafi da maganganun Mama. Shin ya ake so suyi ne wai?, mi yasa mutane sun kasa gane aure lokaci ne dashi?, tana tunani mai zurfi ta idasa fita daga parlon bata ce komai ba.
Tana fitowa tsakar gidan ta iske Safiya na wanke-wanke, tana ganin ta fito ta miƙe tana ɗan taɓe baki ta ce.
"Yawwa gara da kika fito ai, dama kune masu zaman gida na dindindin dan haka sai a fito a ci gaba da bauta, ni kam dama tausayi ne yasa na ɗan kama miki ai"
"Safiya ni kike gaya ma magana kai tsaye?"
"A'a to da waye nake a tsaye a nan wajan?, idan ba ke ba da waye nake ne?"
Zata sake magana Ammi ta fito tana faɗin.
"Ke kinga wuce ki bata waje ta idasa aikin, dama kuma kin san ai aikin naki ne, ko ba haka bane?"
"Amma Ammi kawai ƙanwar ƙanwata sai ta rinƙa gaya min magana kanta tsaye?"
"A'a yau naga wata maganar banza a nan. Ai yanzu tana so ta fiki girman ne nesa bama kusa ba, in gaya miki, tunda igiyar auren da kuka kasa ta hau kanku ita ta kusa hawa kanta, ai ko kin mance ne Ummi?"
Sosai taji wani malolan baƙin ciki ya rufe mata maƙogwaro kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu kota huta haka take ji.
A hankali ta ɗuka ta fara wanke-wanken, tana ji a ranta anya bazata iya fiddo da ko ma waye bama ta auresa a haka nan?, sai ya fi mata kwanciyar hankali. To amma bata jin a cikin maneman nata akwai wadda ya dace da ita, ko da ra'ayinta, kowanne ta hanga ta hango akwai babbar matsala tattare dashi, idan ka ce zakai gaggawa wajan fiddo da mijin aure dole zakai dana sani a nan gaba.
Amma ji take a yanzu ɗin gara ta zaɓi koma waye ne ta huta ma da zaman gidan da kuma zuwa gidan Aunty Binta mai kama da zaman gidan kurkuku.
*Ƙauyen Karaɗuwa, Kankia LGA, Katsina state Nigeria*
"Kiyi sauri ki tafi kasuwar nan fa Sadiya"
Sadiya ta kai ta fito tana kallon Inna ta ce.
"Amma Inna kinga fa hadari ne a garin, a bar tallar nan mana dan Allah"
"Haba jikalle ta ya za'ai abar tallar nan, mi kike so mu ci ne yau to?"
"To ni Inna"
Shigowar Sule ne yasa Sadiya yin shiru tana binsa da kallo da murmushi ta matsa kusa dashi tana cewa.
""Ya Sule ka ce ma Inna yau bazan je talla ba kaji"
Zama yayi yana duban Sadiya yana murmurshi kaɗan ya ce.
"Gaskiya kam Inna a haƙura da tallar nan yau"
"Kafa san wacece Sadiya zuwa zatai ta fita taje rashin jin data saba da ƙawayen nan nata marassa jin magana, dubi fa garin nan wai a haka take cewa hadari ne a garin tsabar bata son zuwa tallar yau"
Zama Sadiya tayi a kusa da Sule ta ce.
"Ya Sule wai babu hadari wai dan Allah?"
Ta faɗa haɗe da kwaɓe fuska.
Wata leda ya miƙa mata ya ce.
"Yanzu dai amshi wannan ki ci, idan kika gama sai ki wuce tallar gwaɗar, amma karki tsaya rashin jin nan naki, kuma karki sake na neme ki"
Amsa tayi tana murmushi haɗe buɗe ledar, ganin rogo ne da ƙuli yasa ta ƙara sakin murmurshi tana sake kallonsa tayi masa godiya.
"Ni wai Sule ya maganar, mutanen nan da suka kama ɗan gidan Rabe mai shayi?, wai har zuwa yanzu basu sako sa ba ko?"
Sule ya cire wata hula dake kansa data gama jin duniya taji jiki ya ce.
"To ai Inna lamarin garin nan fa sai a hankali, masu satar mutanen nan fa har yanzu, shigowa suke makwaftan ƙauyen nan, ni a kullum kwana da muke a cikin fargaba ke ƙara tayar min da hankali, tun muna ji daga nesa ana ɗaukar wasu karfa muma wata rana ya zo kanmu, wallahi Inna da ina da wasu kuɗi a hannu masu dama-dama da tashi kawai ya kamace mu. Har yanzu Inna yana wajansu, naji dai jiya wai ana raɗe-raɗin wai sun kira waya sai an basu million arba'in. Yanzu dan Allah Inna ina su Rabe mai shayi sukaga wata million arba'in, ai ko duka garin nan za'a tsare babu mai wa'innan maƙudan kuɗaɗen"
Wata ajiyar zuciya Inna ta sauke tana riƙe baki ta ce.
"Ohhh ikon Allah, wai kaida garinka amma ana so dole sai ya gagare