KIDA A RUWA HAUSA READ NOVELS BY BILLYN ABDULL.doc

Author :  BILLYN ABDULL Category :  Hausa Read

Chapter   5 / 36

12K to 15K   out of 106.7K words

Sarkin Bauchi Alhaji Yakubun Bauchi. Amintaccen hadimi ne kwarai da gaske, dan yana kusa da sarki saboda mutum ne mai aminci da gaskiya da amana. Gashi dai talaka amma akwai dattako da dattijantaka irin ta mutanen kirki. Matan Malam Shehu biyu ne, yaransa kuwa tara cif. Matarsa ta farko nada yara biyar, uku maza biyu mata. Yaran na kiranta da suna Inna. Matarsa ta biyu nada yara huWu, biyu mata, biyu maza. Yara na kiranta da Iya. Malam Shehu nada sha'awar yaransa maza suyi karatun boko, sai dai kasancewar sa talaka da yanda tsarin karatu yake a lokacin sai ?a?an sarakuna yasa bai fidda burin nasa a fili ba. Amma kullum yaga ?a?an sarki zasu makaranta sai ya tsaya yayta kallonsu yana murmushi abinsa da jera musu addu'ar nasara.
? ? ? Yau da gobe sai mai-martaba ya fahimci kamar Malam Shehu nada sha'awar hakan, dan haka ya tuntuSesa. Babu ko musu Malam Shehu ya amsa da zumuWinsa. Abun ya burge sarki a lokacin, domin kuwa da yawan talakawa babu abinda sukafi ?yama kamar batun bokon a wannan lokaci. Saboda kowa na tsoron a Sata masa al'adar iyalinsa da addininsa. Cike da zumuWi Malam Shehu ya nufi gida, ya tara yaransa da matansa biyu ya gaya musu ?udirinsa da albishir Win da Sarki ya masa. Ya kuma tabbatar musu zai kai yaransa manya duka uku a sakasu boko. Wato ?a?an Inna kenan uwargida. Amma sai su yaran suka saka masa kuka dan basu da sha'awar hakan. Hakama mahaifiyarsu Inna ta nuna bata so, dan kuka ta saka masa ita bata so akai mata ?a?a su koyi kafirci, lallashin duniya da bayanin gamsuwa Malam Shehu yama Inna amma ta?i saurarensa bare ta fahimceshi. Har takai ransa ya Saci ma ya fita ya bar musu gidan.
? ? ? ? Abdul-rasheed yana cikin yaran tsakkiya, dan a wajen mahaifinsu shine na uku, a Wakinsu kuwa shine na fari da Iya ta haifa. Yana da ?anne uku, mata biyu a tsakkiya sai autansu.? ?acin ran da Malam Shehu ya nuna ya dami Iya, duk da kuwa bai ambaci Abdul-rasheed a cikin wanda zai saka makaranta ba, tasan kuma saboda yana ganin shekarunsa basu kai bane. Dan a lokacin shekarar Abdul-rasheed 5 ne kawai. Haka ta yini tana sa?e-sa?e, sai dai batace da kowa komai ba har washe gari Malam Shehu ya dawo Wakinta. (Ranar kwananta kenan).
? ? ?? Bata tada zancen ba ko a ranar sai dare, bayan ta bashi abinci yaci ya gode ALLAH ta kwashe akushin daga gabansa sannan ta dawo ta zauna gefensa cike da ladabi. Da yake lokacin Wari ne kowa ya shige Wakinsa, baka jin motsin kowa sam. Cikin nutsuwa da girmamawa tace,  Malam niko in zaka bani dama ina da shawara .
? ? ? Kallonta yayi da dukkan hankalinsa, kafin ya amsa mata da,  Ina jinki Halimatu, wace shawara ce? Kuma akan minene? .
? ? ? ? Iya ta ?ara du?ar da kai irin na girmamawa.  Malam akan maganar jiyane na batun makaranta. Naga ranka ya Saci daga kai har Yaya. Dan ALLAH kayi ha?uri ka fahimceta, kasan batun bokon nan yana bama kowa tsoro, ba kuma kowa ke fahimta ba kai tsaye. Amma tunda kana so, kuma kaji ka gamsu da saka ?a?anka, mizai hana kafin Yaya ta sakko itama ta fahimta ka Wauki shi wannan yaron (haka take kiran Abdul-rasheed saboda karar kasancewarsa Wan fari) ka saka kawai. Daga baya itama nasan idan ta fahimta zata bari a saka su Bilyaminu Win .
? ?? Shiru Malam Shehu yay cike da nazarin maganar Iya. Kafin ya nisa tare da sakin murmushi irin nasu na manya.  Nagode sosai Halimatu, ALLAH yayi miki albarka. Tabbas naji daWi matu?a akan wannan shawara taki. Duk da da farko ina duba ?an?antar Abdul-rasheed ne shiyyasa ban sakashi a lissafi ba, dama sai gaba nake son kaishi shi bayan su sun fara. To amma maganarki sai ta min daWi, kuma ya bani mafita dan dama a cikin tunanin yanda zan fuskanci mai martaba nake akan hakan. Kinga yanzu dai kawai na kai Abdul-rasheed a sakashi, su kuma tunda basa so bazan matsa musu ba, su cigaba da karatunsu na mahammadiya da noma. ALLAH ya sanya musu albarka gaba Wayansu .
? ? ??  Amin malam. Idan hakan kayi ma dai-dai ne. Amma zuwa nan gaba Win dai suma a sake tuntuSarsu ko zasu canja shawara bayan sunga shi wannan yaron Win ya fara .
? ? Bai musa mata ba akan hakan. Washe gari cike da farin ciki ya kama hannun Abdul-rasheed suka nufi gidan sarki. Wannan shine mafarin fara karatun bokon Abdul-rasheed. A lokacin yana da shekara 5 a duniya, dan an haifesa a 1947 ne. A shekara ta 1953 aka saka shi a makarantar Bauchi Native Authority Primary School (wacce daga baya ta zama Kobi Primary School). Kuma Alhamdullahi sai ya kasance shima yana son karatun kuma yana maida hankali. Malama Shehu yaji matu?ar farin cikin ganin Abdul-rasheed yana da himma akan karatun, dan haka ya ?ara tsayawa a kansa sosai. Ba'a boko Abdul-rasheed ya tsaya kawai ba, har ilimin addinin ma yana ?o?ari akai dan suna zuwa malarantar allo kamar sauran yan uwansa, saSanin ?an uwan nasa da sunfi maida hankali dai akan ?an abubuwansu na yara na yau da kullum, sai kuma makarantar allo da suma suna zuwa kamar shi.
? ? ?? Makarantar tana kusa da ?ofar gidan sarki, cikin unguwar da ke cike da yara masu sanya riga doguwa da rawani ?arami, wasu kuma ke tafe da allo. Malamai suna koyar da aji da harshen Hausa a farko, amma daga baya aka fara musu harshen turanci a matsayin harshen karatu. Ya koyi rubutu da karatu, ya kuma fara sha awar duniyar da ta wuce yankinsu. A kwana a tashi ba wuya wajen UBANGIJI. Abdul-rasheed ya kammala primary Winsa aji shida (Standard 6) a 1959, yana Wauke da babban burin samun ilimin da zai sa ya taimaka wa garinsu. A Shekarar 1960 ta kawo masa sabon babi. An tafi da shi Zaria tare da sauran ?a?an manyan Arewa, inda ya shiga Government College Zaria (Barewa College), makarantar da aka san ta fi kowace a Arewa. Ya tafi yana kuka Iya nayi. Yayinda Inna ke dariyar ?eta ita da ?an uwansa, a ganinsu dai ya saka kansa a wani bala'i ne shi da uwarsa. Amma ita Iya addu'a tabishi da shi kawai, sai kewar rashinsa a kusa da ita matsayinsa na babba dake taimaka mata da aike da abubuwa na yau da kullum dake tsakanin uwa da Wa. Zama a boarding school ya koya masa nisa da iyaye da wahalar rabuwa da gida. Ya saba da rana da safiya da bugun ?aho, shiga aji da sautin turanci daga bakin malamai na Ingila, da kuma yin motsa jiki da yamma a filin kwallo. A can ne ya haWu da wasu ?ananan jaruman Arewa, waWanda daga baya za su iya zama manyan shugabanni idan UBANGIJI ya ?addara hakan a littafinsu. Tun a zuwa hutunsa na farko ?an uwansa suka fara hango canji a tare da rayuwarsa, sai dai hakan baisa sunji suna son yin karatun boko ba, hasalima babban su ana shirin masa aure ne wato Bilyaminu. Shekaru sun mi?a a rayuwar karatu ta Abdul-rasheed, yana zuwa hutu a duk lokacin da aka basu, yayi kwanaki ya koma cike da kewar gida da ?an uwansa da iyaye. A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai gashi ya kammala a 1966, yana da shaidar Cambridge School Certificate, wadda aka fi darajawa sosai a lokacin.?Ya dawo gida Bauchi cike da farin ciki da nasarori, nasarorin da suka saka iyayensa a farin ciki mara misalin kwatance. Abdul-rasheed ya kammala Secondary school cike da nasarori da suka sake faranta ran mahaifinsa, dan haka ya sake tsaya masa akan cigaba da karatun nasa. Bayan kai kawo da taimakon wani malamin su na Boarding ya samu gurbin shiga jami'a a Kano. A wannan gaSar ma dai kowa ya bishi da addu'a musamman mahaifinsa da mahaifiyarsa. Yayinda sauran ?an uwansa ke masa dariya da kallonsa a matsayin wahalalle mara aikin yi, hakama Inna mahaifiyarsu kallon abin ta dinga yi kamar wani rashin aikin yi ne, sai dai duk habaicin da take da dariya iya bata kulata ba. Haka akai masa shiri ya taho Kano karatu a shekara ta 1967, ya shiga Ahmadu Bello College a Kano, wanda daga baya aka fi sani da Abdullahi Bayero College, har ya zama Bayero University Kano (BUK) a cikin 1975. Yana karantar History and Political Science, yana ?ara fahimtar tarihin mulkin mallaka da rawar da Arewa ke ciki a Nigeria data samu nasarar ?anci kai a 1962. Cikin makaranta yake zaune, dan basu da kowa da suka sani na dangi a cikin Kano Win sam, hasali ma a cikin gidansu kaf babu wanda ya taSa zuwa garin Kano sai shi yau da ALLAH ya kawo matsayin Walibin ilimi. Zaman Kano ya buWe masa ido, ya kuma sake koya masa iya zama da mutane, ya kuma haWashi da abokai na ?warai na amana...
Rayuwar Abdul-rasheed a Kano wata irin rayuwa ce mai cike da ?alubale da darasin rayuwa. Domin kuwa ba karatu kawai ya maida hankali ayi ba harda koyon Winki. Ya fara koyon Winki ne a dalilin abokinsa Nasiru. Wanda suka haWu acikin makarantar department Winsu Waya. Da farko dai babu wata abota a tsakaninsu sai gaisuwa, sai da Abdul-rasheed ya fahimci Nasiru ?uru ne dan akwai fahimtar karatu sai dai bashi da hayaniya sam sannan suka fara abota, dan kuwa Abdul-rasheed bashi da girman kai, duk abinda bai iya ba idan ya fahimci wanda ya iya koda mace ce sai ya nema taimakon a nuna masa, ta haka ne ya samu kusanci da Nasiru, a hankali suka zama abokai dan shima dai rashin girman kan Abdul-rasheed Win ya burge Nasiru sosai. Kamar wasa ya jashi suka je gidansu wani weekend, dan kuwa Nasiru Wan garin Kano ne a anguwar ?ofar mata. A ?ofar gidan su Nasiru kuwa akwai shago da ake Winki kasancewar a bakin titi suke kusa da kasuwa, shagon kuma na yayansa ne. Tunda Abdul-rasheed ya ?yalla ido yaga shagon sai abin ya bashi sha'awa, baiyi ?auron baki ba da suka shiga gaida yayan Nasiru yay ta yaba abin, shi ko Yayan Nasiru yaji daWi ya kuma fahimci kamar Abdul-rasheed na son harkar, sai yay masa tayi. Babu musu yace aiko yana son koyar kuma ya gode. Daga haka suka saita zai dinga zuwa duk weekend koyon Winki...........
'


_Zaku sameshi a waWan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER *_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ?asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya=?G?_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: =?G?_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number =?G?_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number=?G?_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*

*_Typing=???_*








*_>???KI?A A RUWA.....!!>???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._



_Chapter 7_

_Amin afuwa wlhy gaba Waya banda nutsuwa ne an mana haihu bana yini a gida, jiya ma shaf na manta da batun posting ALLAH =??. Kuyi ha?uri ayi suna gobe idan ALLAH ya kaimu sai na dawo gaba Waya hankali kwance, ga pages babu nutsuwar editing. Ina ?ara neman afuwa=??=?O?._
__________________


*_NACE ina kuke ne?!!. Al'ummar Gombawa nake magana =؃? fulanin asali ke nan =??._*

*Shin kuna da labarin cewa kuma nesa ta matso kusa gare ku?*

_Maza kuzo ku sha labari da Wumi-Wuminsa, domin kuma fa NAKUN ya buWe muku gidan gyara da ?al?ale jikin mata ?an kwalisa a kusa da ku gabb._

*_Idan kunji ana kiran maida tsohuwa yarinya to wannan katafaren shagon ne na=?G?_*


*ALIYU HAIDAR COSMETICS PLAZA*

_ADDRESS SHOP D80 WOMAN LINE GOMBE MAIN MARKET_

*_Zaku same mu a wannan numbers Win kamar haka=?G?_*
*07068210505*
*09133081313*

_DEALER IN all kind of skin care products such as:_

moisturizer
Sun screen
Face Toner
Eye cream
Face serum
Face wash
Face scrub
Face cream
Face marsk
Body lotion
Body cream
Shower gel
Body scrub
Tube
Body oil
Body spray
Perfume
Hair crm
Hair spray and many more

*_Harma da abinda bamu lissafo ba anan. Ku dai kawai karku bari a yi babu ku. Domin kayanmu garanti ne kuma dahir ne =؃?_*

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/HCLn6awOrmP5WJmO9jPrgK?mode=ems_wa_t


__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Haka kuwa akayi, kamar wasa Abdul-rasheed ya fara zuwa koyon Winki, kasancewar yana son abun dan danan sai ga sakamako ya fara bayyana. Baya gajiya duk asabar da Lahadi sai yazo. Da Nasiru yaga yana wahala da kashe kuWaWensa ga Wan makaranta komai nasa a ?a'ide yake, ga nisa Abdul-rasheed yana jimawa baije gida Bauchi ba sai yace mizai hana duk juma'a ya dinga biyoshi sai Monday su dinga shiga makaranta tare, ya dinga weekend dai a gidansu. Da farko Abdul-rasheed yaso turjewa, sai da Nasiru ya nuna masa fushinsa sannan ya amince amma yana War-War dai, duk da kuwa kowa ya sanshi a gidan su Nasiru zuwa yanzu, kuma suna nuna masa so da kulawa. Amma shi dai baya son takura musu, yana kuma tsoron kar mahaifinsa yay faWan barinsa makaranta harna kwana uku a kowane mako batare da saninsu ba. Tun dai yana Wari-Wari har ya saki jikinsa.
? ? ? ?? Tun a farko fara koyon Winkin Abdul-rasheed akwai wata yarinya a ma?waftan su Nasiru da kullum takan wuce da safe da allo zata makaranta. Takan gaishesu idan zata wuce, hakama idan ta dawo da takan gaishesu ta shige gida. Shi dai bai taSa tambayar sunanta ba, bai kuma taSa magana da ita ba bayan gaisuwar nan da take musu a tare. Sai dai a kwana a tashi har ya haddace muryarta mai cike da nutsuwa da rashin hayaniya.
? ? ? ? Ranar wata Lahadi da yamma yana a shagon shi kaWai yana Winki ogansa Yaya Zubair yaje sayen kayan Winki zazza?ar muryar yarinyar nan ta ratsa kunnensa. ?agowa yay da sauri tare da take keke ya tsayar daga takun da yake masa. Tana tsaye daga wajen shagon ta rissina ta gaisheshi kanta a ?asa. Amsa mata yay da kulawa, kafin ya furta,  Kina son wani abu ne ?anwata? .
? ?? Kanta a ?asa ta ce,  Eh Yaya, dama kayan Winki na kawo ma Yaya Zubairu, naga kuma baya nan ma kamar .
? ?? Cike da zolaya ya ce,  Oh dan Yaya Zubairu baya nan kin fasa Winkin? .
? ?? Da sauri ta ce,  A'a zan baka ka ajiye masa daman .
? ?? Murmushi yayi a karo na farko, ya ce,  To shike nan . Yay maganar yana tasowa yazo bakin ?ofar dan ita tana daga waje har yanzu. Mi?a masa ledar tayi kanta a ?asa. Karo na farko a rayuwarsa ya zubama hannunta ido. Fara ce sol, hannunta da ?unshin jan lalli da yay mata shegen ?yau. Harga ALLAH sai da gabansa ya faWi, mazantakar ta motsa amma sai ya kauda kansa kawai ya amsa yana Wan murmushi da duba kayan ledar. Yadi ne irin nasu na maza. ?agowa yay ya sake Wan kallonta.  A ajiye kawai kenan zaki dawo ki masa bayani? .
? ? ??  A'a basai na dawo ba. ?inkin Bashir da Tasi'u ne daman. Inna tace dan ALLAH idan bata takura masa ba zuwa jibi a Winka. Dan zamuyi tafiya ne biki .
? ? ?  In sha ALLAHU za'a Winka, nima zan Winka musu da kaina. Idan kin shiga ki turo min su yanzu naga girmansu a daren nan zan yishi dan da safe zan wuce makaranta .
? ?? Godiya tai masa cike da girmamawa, sannan ya wuce kanta a ?asa. Samun kansa yay da binta da kallo. Doguwa ce sosai masha ALLAH, shekarunta bazasu wuce 14 ba, tana da Wan jiki, hakan ya nuna ne kuwa sakamakon kayan dake jikinta, zani da riga t-shirt sai kallabi disko, Tayi Wammara da gyale a ?ugunta, kasa Wauke idonsa yay harta shige gidansu, a mamakinsa ya Wan juya zai koma yana sauke ajiyar zuciyar da tazo masa a bazata kamar ance sake waigawa sai ya ganta tana le?ensa. Wuff ta shige kamar wal?iya kuwa, tana turo ?yauren zauren gidansu na katako burum. ?an tsai yay yana kallon ?ofar kamar mai tunani, sai kuma yay murmushi ya juya ya koma cikin shagon.
? ? ? Yana zama su Tasi'u ?annenta sukai sallama. Yara ne matasa da bazasu wuce 9/7years ba. Sun gaishesa da girmamawa, ya amsa musu da kulawa yana musu murmushi. Dan sun sanshi ya sansu tunda yanzu ya zama Wan anguwar duk da kwana 3 kawai yake a duk sati. Amma sau?in kansa da son kula yara yasa duk suka sanshi. A karo na farko a rayuwarsa ya tambaye su miye sunan yayarsu?. Caraf Bashir dake matsayin ?arami ya ce,  Indo .
? ? ? ? Samun kansa yay da faWin,  Masha ALLAH A'ishatu kenan. Wace makarantar kuke zuwa? .
? ? ? Yanzu kam Tasi'u ne ya ce,  Muna zuwa makarantar Malam Sallau. Yaya Indo nada ?o?ari sosai, dan duk wata tana wanke allon ta sau biyu, yanzu haka tana izu kusan ashirin.
? ? ? ??  Kai kai kuce dai yayarku Malama ce kawai? .
? ? Wannan kalma ta saka Bashir da Tasi'u tsuge masa da surutu akan yayarsu Indo. Abu kamar wasa hirar yaran ta dinga masa tasiri a zuciya, yana tare da su har akai kiran magriba, shi ya jasu suka je massalaci.? An idar da salla sun dawo sai ga Indo tana nemansu. Karo na farko da Abdul-rasheed ya samu kansa da yima Indo kallon ?urulla sosai. ?ya?y?yawar yarinya mai cikar zatin fuska da hasken fata. Suna haWa ido tai saurin juyawa zata shige gida. Amma sai ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta.
? ? ??  A'ishah! .
?? Cak ta tsaya amma ta kasa juyowa, dan haka ya ?arasa inda take ri?e

5 / 36