KIDA A RUWA HAUSA READ NOVELS BY BILLYN ABDULL.doc

Author :  BILLYN ABDULL Category :  Hausa Read

Chapter   16 / 36

45K to 48K   out of 106.7K words

Salame anguwar zoma. Sannan tana cin abinci mai inganci daga hatsi da kunu, ga mijinta ya tsaya mata da nama da abubuwa masu inganci da maijego take bu?ata bayan namu na gida. ?an Maiduguri sun iso kwana biyu da haihuwa. Hakama ?an Kano mutane uku sun iso saura sai ana gobe suna. Abubuwa fa nata ?ara armashi Alhamdullah, ana gobe suna gida ya gama cika taf da dangi tako ina, tako wane Sangare kayan arzi?i ne ke shigowa daga ?an uwa da abokan arzi?i, haihuwa tayi albarka kenan. An raWama yaro suna da safe tare da yanka ?atoton rago daga Baba. Sunan daya bama mutane mamaki da tunanin ina Abdul-rasheed ya samo wannan suna, dan kuwa suna ne da ba'a saba jiba a ?asar hausa. Amma dai kowa yayi addu'a ga jinjiri Haysam, daga haka aka cigaba da shagalin suna. Taro yayi armashi, ya kumayi daWi yanda ya kamata, anci ansha anyi asuwaki da naman kaji dana sa guda da aka yanka bayan ragon suna. Ita dai A'isha nata ido, dan kuwa ?ar gata take komai sai dai taga anayi, idan ka cire kewar mijinta da ganinsa ke mata wuya yanzu babu abinda ke damunta. Balle ga ?an uwanta zagaye da ita.
? ?? Washe garin suna bisa al'ada dangin A'isha suka wuce da ita Kanon dabo wankan jego, ta samu rakkiya daga wasu a dangin Abdul-rasheed, yayinda shi kuma sai daga baya zai je ganinsu Kanon, dan a yanzu baida damar binsu. Nasiru ma da yazo suna yana nan sai bayan sati zai koma Kano, baiyi aure ba har yanzu, amma na saka ranar auren nasa shida wata ?ar ?anwar mahaifiyarsu da suke zaune a Kaduna. Tana makaranta ne shiyyasa ake jira ta ?arasa, kuma yanzu saura kaWan Win ta kammala asha biki in sha ALLAHU...

? ? ? ? <<<<<" >>>>>

? ?? A yau Inna ta samu ba?uncin sabon jikanta Haysam Abdul-rasheed Shehu da ?arta mai jego A'ishatu. Ranta fes da farin ciki, hakama su Bashir da suka ?ara girma suna cike da farin ciki. A'isha kam farin cikin ta baya misaltawa, tunda tai aure sai yau ne take zuwa Kano shekara uku ciff. Aiko dole tai kuka, tayi kewar Inna matu?a mara misali, har tana jin kamar an rabata da itane gaba Waya. Dan tasha zama tayi kukan kewar Inna da su Tasi'u. Garama su sunje mata har sau kusan uku hutu. Amma Inna bata taSa zuwa mata ba. Tun randa aka lulluSa mata zanin aure sai yau ne suke ganin juna.
? ?? ?an uwa da abokan arzi?i da ma?wafta da basu sami damar zuwa Bauchi suna ba sunata shigowa ganin jariri Wan mutanen Bauchi. Yana shan addu'a kuwa daga bakuna masu albarka. Lallai dawowar A'isha Kano ta sake tabbatar da ita ?ar gata ce, dan kuwa jego take irin na ?an gata masu capacity. Ba aikin fari babu na ba?i sai dai taci abinda take so ta ?oshi tasha barcinta ta more. Idan kaga Haysam a hannunta abincinsa zata bashi. Amma koyaushe yana bayan Inna. A mata abinci mai rai da lafiya taci tayi nak abinta. Ai kafin kace mi ta ?ara wani uban ?yau ta murje ta sake haske da cikar jiki. A kuma yanzu ne kayan arzi?i suka ?ara bayyana kansu. Ma?erin budurcin na gaskiya ya bayyana gareta, dan kuwa tana cika shekaru sha takwas ne a duniya. Satinsu uku Abdul-rasheed ya iso Kano da shatara ta arzi?i. Shi kansa yanda A'isha ta koma sai da ya ?ara bashi mamaki, kamar jira take tazo Kanon ta sake canjawa da buWewa ne. Ga yaronsa Masha ALLAH, shima yayi Sul-Sul alamar yana samun kulawa mai daraja a wajen Inna kakar ?warai. Sai yaji ?aunar tsohuwa Inna ta ?ara girma a zuciyarsa da daraja irin ta uwa mahaifiya bawai suruka uwar mata kawai ba. Satinsa Waya ya koma Bauchi. Daga nan sai yazamto duk bayan sati Uku yake zuwa ganinsu. A haka sukai arba'in uku ciff, arba'in uku kuwa kwana 120 kenan, watanni huWu har Haysam ya fara Wan wayo na jarirai. Daga nan aka fara shiryama A'isha komawa, bayan ta zagaya dangin uwa dana uba, sai dai ta jinkirta har akai bikin Nasiru da matarsa kuma ?ar uwarsa. ?an Bauchi sunyi kara sosai dan sunzo, a lokacin ne kuma yan Bauchin suka koma da ita, amma tare da rakkiyar danginta itama.
? ? ?? Bayan A'isha ta dawo gidan aurenta sun sake gina sabuwar rayuwa da mijinta Abdul-rasheed da Wansu. Ya Wauketa zuwa Maiduguri dangin mahaifiyarsa a karo na farko, sun yo musu sati har biyu. A kuma wannan zuwa ne sha?uwa mai ?arfi ta shiga tsakanin A'isha da Yakura, idan bamu manta ba Yakura dai itace akama Abdul-rasheed tayin aurenta a lokacin bikin ?anwarsa Khadijah. Yarinya ce mai natsuwa da hankali, ga ha?uri da ilimin addini, ga ?alubalen rayuwa da take fuskanta hannun mijin mamanta saboda marainiya ce babanta ya rasu. A wannan zuwa ma su Baba Kalla sun sake kwaWaitama Abdul-rasheed auren Yakura, halin daya sake ganinta a ciki kuma yasa ya amsa babu wani jayayya, koda ya tunkari A'isha da maganar tun a can sai yaga tanata farin ciki. Hakan ne ya saka masa nutsuwa yana dawowa ya sanar ma Baba. Baba yayi murna sosai kuwa shima, ya kuma saka masa albarka. Daga haka aka shiga kai-kawon maganar aure.
Mata nada ba kishi ne basu da shi ba, zata iya yiwuwa ma sunfi matan yanzu kishi sosai. Sai dai akwai dattaku da kamun kai da sau?a?awa zuciya damuwa dama Waukar rayuwar aba komai ba. Dan haka A'isha koda ta nuna murnarta a fili a Soye tasha kuka, dan kuwa tana son mijinta sosai, amma son da take masa bazai saka ta tauyesa akan ?arin aurensa ko bijire masa ba, ita dai aljannarta take nema da burin samu a wajen UBANGIJIN da yace ai aure kuma ayi biyayya ga maza, suma kuma su sauke ha??okinmu, wanda bai sauke ba kuma zaiga sakamakonsa. Iya ?o?ari mijinta nayi akan ?yautata mata da sau?e hakkokinta dake kansa, ya Wauki Wawainiyar Innarta da karatun ?annenta su Bashir, ga kulawar da Haysam ke samu ta musamman irin ta Wan gatan Wa, to mi zaisa kuma ta butulcema ALLAH. Yayta aurensa zata bishi da addu'a da kuma fatan zaman lafiya ita da amaryar. Dan a wajenta Yakura abar a tausayama ce ga duk mai imani. Gefe Waya kuma har cikin ranta son Yakura take ji, dan haka kawai ALLAH ya haWa jininsu....

? ? ?? Haysam nada shekara Waya da wata Waya akasha bikin Abdul-rasheed da amarya Yakura, itama dai an kawota nan gidan kusa da A'isha, Alhmdllh kuma A'isha tasha yabo ga dangin mahaifin Abdul-rasheed dama na mahaifiyarsa saboda dattakon data nuna ?warai da gaske akan auren nan kamar ba ?aramar yarinya ba. Babu wanda zai ce yaga fushinta ko Sacin ranta koda a fuska ne, balle wata magana mara daWi, hatta shi kansa ango Abdul-rasheed ma da take kwana take tashi da shi zakuma ayi kishin a kansa babu wani abun ALLAH wadai da zai ce ya gani daga A'isha, hasalima wani abun ita take dagewa akan ayi. Haka dai akai biki aka tashi lafiya kowa na san barka da sanya alkairi da addu'ar zaman lafiya na har abada.
? ? ? Tsabar kunyar A'isha da nauyinta da Abdul-rasheed keji bai bar aboki ko Waya ya masa rakkiya gidan da nufin sayen bakin amarya ba, hatta kuwa da Nasiru. Haka ya shigo shi kaWai. Kai tsaye kuma Wakin A'isha ya nufa, abin mamaki sai ya samu ita harma tayi barcinta, Haysam na jikinta shima yana nashi. Ya jima a kanta tsaye yana kallonta da mamaki, har zuciyarsa na masa tambayar wai kuwa anya A'isha na sonsa? To dole yace hakan, yasha jin tarihin matan abokansa idan zasu ?ara aure akan kishi, amma ita ko da wasa babu abinda ta nuna masa mara daWi, kuma dai ance kishi nan na mata shike nuna tsantsar soyayyarsu gareka. Haka dai yayta sa?awa da kwancewarsa, daga ?arshe yay musu addu'a ita da Haysam Win ya kashe mata fitila ya fito tare da karo Wakin ya nufi Wakin amarya.
? ? ? ?? Washe gari ma Abdul-rasheed yata zuba ido yaga canji ga A'isha ko'a fuska amma shiru, sai ma wani annuri data tashi da shi da farin ciki. Wanda ya sashi kasa gane daga ina ta samosa. (Bai san daga sallar dare bane. Dan cikin dare ta farka tai alwalarta a cikin Waki a botiki, ta shiga kaima UBANGIJI bu?atunta da addu'ar zaman lafiya da kwanciyar hankali ita da amarya da shi, Alhamdullahi kuma ta tashi ranta fes babu wani damuwa balle nauyin zuciya da take fama da shi a kwana biyun nan). Haka yay ta binta da kallo, musamman da zasuyi kari yaga ita da Yakura nata shan hirarsu hankali kwance kamar ma wasu ?awaye. Kai daga ?arshe ma sai bar musu gidan yayi, koda ya dawo samunsu yay suna aiki a tsakar gida suna hirarsu cike da nishaWi da dariya. Ga Haysam a bayan Yakura a goye tana ?ulla aya da gyaWar saidawa da A'isha keyi. Ita kuma tana girki. Harga ALLAH sai ya sake jin nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali, harma da son A'isha yana sake nunkuwa a ransa. Dan haka da daddare ya sake haWasu yay musu nasiha da ro?on su Wore a yanda suka fara, su toshe kunnensu daga munafukai, su kauda idonsu daga azzalumai masu haddasa fitina a bayan fage. Sun tabbatar masa zai samesu fiye da yanda yake fata, suma kuma sun ro?eshi ya kasance adali a tsakaninsu mai tsayar da gaskiya. Shima ya amsa da tabbatarwa...
? ? ?? Tabbas Alhamdullah, babu abinda Abdul-rasheed da Ai'sha da Yakura zasu ce a wannan gaSar sai tarin godiyar ALLAH. Dan kuwa gidan aurensu ya zama gidan farin ciki da ni'imarsu da kwanciyar hankali. Bawai basa kishin bane, sunayi, sai dai kowacce tana yin kishi mai amfani wajen ganin ta ?yautata ma mijinta a Soye batare data sosa zuciyar ?ar uwarta ba. Haka shima mijin na ?o?arin yin adalci, wadda yafi so kuwa ya barma ransa ne.........
'

_Zaku sameshi a waWan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER *_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ?asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya=?G?_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: =?G?_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number =?G?_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number=?G?_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*

*_Typing=???_*








*_>???KI?A A RUWA.....!!>???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._



_Chapter 20_

__________________


_A KANO KI KE& ? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ?iyar yin girki gashi zaki yi ba?i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ?asar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZO?O mai za?i, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ?ara lafiya, akwai wanda bashi da za?i domin masu ciwon sugar da masu gudun ?iba._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ?asan rubutun nan._

INSTAGRAM
=?G? https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr
CALL/WHATSAPP
=?G? wa.me/2349030398006

TIKTOK
=?G? https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1




Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.d'?d'?>???
__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Sakanni sun zama mintuna, mintuna sun koma awoyi, awoyi sun rikiWe zuwa kwanaki, kwanaki sun haWu sun zama sati, satittika sun dun?ule zuwa wata, wattani suka haWa shekara. Shekaru sun cigaba da shuWawa. Har amarya Yakura ta cika shekara uku a gidan Abdul-rasheed. Bata samu ciki ba har yanzu, hakama A'isha tunda ta yaye Haysam shekara biyu kenan bata samu wani cikin ba. Abdul-rasheed kuwa nata sake samun Waukaka a wajen aiki da kasuwancinsa na Winki, dan zuwa yanzu ya koyar da yara da yawa aikin tela, kuma Alhamdullah suma suna cin gashin kansu, ga shagon saida kayan Winki ya buWe duk sati Nasiru na aiko masa da kaya daga kano. Wani lokacin kuma yaje da kansa yayo daga nan yayo zumunci ya siyama Inna kayan abinci ya dawo. Zuwa yanzu kusan duk Wawainiyar zuri'arsa ta dawo kansa ne. Yayima su Baba yayima yayunsa da ?annensa, yayi ma dangin mahaifiyarsa, yayima dangin matansa. Sannan ya sauke hakkin gidansa. Haysam yaro Wan shekaru huWu a duniya, ya tasa abinsa masha ALLAH, kyakkyawa mai lafiyar jiki ga gatan iyaye dana kakanni, ya tashi yaro mai shiru, mai son karatu da tambaya. Wayonsa ya girmi shekarunsa, damma baida surutu ne. Yana da shekara biyar a duniya kwatsam a Wan tsakanin sai ga A'isha da ciki, ya salam zo kaga murna wajen Abdul-rasheed da Yakura dama su Baba, cikin A'isha nada wata biyu itama Yakura ta fara nata laulayin, ya rabbi, rasa ina Abdul-rasheed zai saka kansa yayi dan farin ciki, dan harga ALLAH yana matu?ar son yara. Kamar yanda A'isha ta fara samun ciki itace ta fara haihuwa, santalelen yaro namiji a wannan karon ma, mai kammani da Abdul-rasheed shima. Ansha shagali yaro yaci suna Ja'afar. Ja'afar nada wata biyu da kwanaki itama Yakura ta sauka, itama dai ta santalo nata namijin mai kama da Abdul-rasheed, shima dai yaci suna Ma'aruff. Haysam cike yake da farin cikin samun ?anne da suka tashi tamkar tagwaye, dan kuwa ma tagwayen ake kiransu. Su Ja'afar nada shekara WaWWaya aka saka Haysam makaranta, dan kuwa ya cika shekaru shida a duniya cif.
? ? ? Duk da kuwa kafin ma sakashi makarantar tuni ya fara Waukar karatu a wajen mahaifinsa da ma A'isha da Yakura. Dan Abdul-rasheed tsaye yake akan tarbiyyar Haysam, sannan akwai sha?uwa a tsakaninsu mai girman gaske. Akoda yaushe zaka sameshi? zaune a gefen mahaifinsa yana sauraron karatun Al?ur ani ko labaran tarihi na Annabawa da jarumai. Hakama sauran litattafai dai-dai fahimtar yaro mai irin shekarunsa. Duk lokacin da mahaifinsa ya karanta masa tarihin jarumtar Annabawa data sahabban MANZON ALLAH (S.A.W) irinsu Abubakar As-Siddiq (RA). Abokin ANNABI mafi kusa kuma khalifa na farko, mai ha?uri da sanyin hali Umar Ibn Khattab (RA). Khalifa na biyu, adalin shugaba jarumi kaifi Waya. Usman ibn Affan (RA). Khalifa na uku, ya tattara Al-Qur ani cikin littafi, mai yawan ?yauta kuma mai sadaukarwa ga bayin ALLAH mabu?ata. Aliyu ibn Abi Talib (RA). Khalifa na huWu, kuma Wan uwan ANNABI, jarumi da baya tsoro sai dai kafirai suji tsoronsa, dan ya basu wuta iya wuta a filin daga, Mijin Nana Fateema ?ar MANZON ALLAH (S.A.W). Ga su Abdulr-rahaman ibn Awf (RA). Irinsu Sa'ad ibn Abi Waqqas (RA). Talha ibn Ubaidullah (RA). Zubair ibn Al-Awwam (RA) Wan uwan Ummul Muminin Khadija. Bilal ibn Rabah (RA), mai kiran salla na farko jarumi na gaske. Salmanul-farisi (RA) da ire-iren su da yawa da in lissafosu zamuyi da irin rawar da suka taka a musulunci da tsayawa kusa da MANZON ALLAH mu kammu mun san jarumai ne abin koyi da ba Haysam kawai ba ?a?anmu ma ya kamata ace muna basu tarihinsu domin su tashi da burin koyi da su ba zindi?an wannan zamanin ba da yaranmu ke koyi da su koyi mara amfani da amfanarwa. A Sangaren hikayoyi yana bashi irin nasu Iliya Wan Mai ?arfi, Jatau ?an Mariya, Sarkin Zamani, da makamantansu. Dan a wancan lokacin, ana yaWasu a gidajen? rediyo kamar su rediyo Nigeria da jaridu irinsu Gaskiya tafi Kwabo da sauransu.
? ? ? Irin waWan nan tarihi da hikayoyi sunyi tasiri matu?a a zuciyar Haysam, dan har yana ji a ransa yana son yayi koyi da su wajen hidimtawa addini. Sai dai abinda ke saka lissafinsa ruWewa shine zamanin da yake saSanin nasu ne, tunda shi bai zo zamanin ya?e-ya?e ba. Dan haka sai yayta jerama Babansa tambaya. Abdul-rasheed kuwa baya gajiya da bashi amsa, tare da kawo masa misalai akan idan su anyi ya?e-ya?e a zamaninsu shi kuma zai iya zama ?an sanda, ko SOJA ko wani dai aikin kaki domin bama ?asarsa gudummawa. Ba wani fahimta Haysam yake da ?yau ba, amma hakan na sashi jin eh lallai zai iya hakan. A haka ya fara makaranta sai abubuwansa suka sake faWaWa. Bayan yaye ?annensa Ja'afar da Ma'aruff iyayensa sun sake samun ciki kusan a tare, amma Yakura ma ta riga A'isha a wannan karon, dan haka ta rigata haihuwar Wa namiji mai kama da ?an uwansa. Shima dai yaci suna Bilal, bayan wata uku da kwanaki itama A'isha ta haihu mace. A karo na farko Abdul-rasheed ya samu mace, dan haka taci suna Halimatu mahaifiyarsa Iya kenan suna mata alkunya da (Ummie). Itama dai akasha shagalin sunanta. A wannan lokacin ma Yakura ta sa sake yin gwanne kuma, dan Bilal nada shekara Waya ta sake samun ciki, dole A'isha ta cigaba da shayar da Bilal da Ummie a tare, aka bar Yakura da laulayin sabon cikinta har ALLAH ya kaishi haihuwa ta haifi mace itama da taci sunan Inna wato Karimatu suna mata alkunya da (Mommy).
? ? ? ? ? Bayan haihuwar Mommy babu jimawa UBANGIJI ya amshi ran Baba, jiyyar kwanaki biyu rak. Wannan rasuwa ta girgiza wannan zuri'a, barema Inna data koma kamar ta ruWe. Haka dai akasha kuka da kai-kawo kowa ya ha?ura a ?arshe. Ashe wata na tafe, dan Inna na cikin takaba itama dai ciwo yay mata tsanani, ta matu?ar sakama kanta damuwar rashin baba, ashe itama ciwo ne na tafiya, itama dai a cikar wata na shida da rasa baba tabi bayansa. Su Abdul-rasheed suka sake gigicewa da ?a?anta. Nan ma akasha kuka kowa kuma ya

16 / 36