KIDA A RUWA HAUSA READ NOVELS BY BILLYN ABDULL.doc

Author :  BILLYN ABDULL Category :  Hausa Read

Chapter   12 / 36

33K to 36K   out of 106.7K words

idan ina tare da Gimbiya A'isha .
? ?? Sosai sunan ya sata nishaWi, dan haka cike da ?uruciya ta ce,  Kai kuma Sarki .
? ? ?  Shike nan kuwa, ga Sarki ga Gimbiyarsa . Ya bata amsa yana murmurshi da ?arasa gyara gadon. Ganin zai bar wajen batare daya zuge labulen ba ta ce,  Inna tace haramun ne barin gadon miji a buWe kowa ya gani, tace kullum na zuge labulen nan, kozan wanke in yayi datti ina cirewa na canja da wani kafin su bushe .
? ? ?? Shi kam dai wannan batu na bashi dariya, amma sai ya biye mata ya ce,  To Amin afuwa, bara na zuge . Ya juya ya mata yanda take so, gado ya koma ruff abinsa. Daga nan ya ce,  Jeki wanke ido na kawo miki wannan. Shayi ne, da Wan madara. Ki sha kafin ki ci wani abu ko
? ? Kai ta jinjina masa cike da ladabi da sanyin murya ta ce,  Na gode.
? ? ? ? Murmushi ya mata, ita kuma ta Wauka buta ta fice da ?ar battar garin gawayi da aka ni?a da gishiri a waje guda, sai asuwaki a cikin leda ta Wauki Waya. Ta Wan jima kafin ta koma Wakin, yana zaune a tabarma daya shimfiWa. A gabansa kofin shayin ne ya Wakko ?arami yana haWa madara ta gwangwani da sauran kayan haWin. Ta koma can ?arshen bango zata zauna ya ce ta dawo kan tabarmar. Haka ta zo ta zauna a Warare dan biyayya amma daka gani kasan a takure take bata saba zama da namiji a irin yanayin ba, gashi su biyu a Waki kawai tun jiya.
? ?? Shiru ya kasance a tsakaninsu na wasu mintuna harya kammala, ya mi?a mata kofin shayin da farantin ?osai daya juye daga leda, sai biredi guWa Waya da kazar jiya da basuci ba. Shima nashi daya haWa ya Wauka yana kallon ta.  ?auka kisha mana .
? ?? Kanta ta girgiza masa alamar a'a tana wasa da gefen zanenta .
? ? Shima sai ya ajiye nashi yana faWin,  Saboda mi? .
? ? ? ?  Ina jin kunya .
? ?  Aisha kunyar nan dole a ajiye batunta. Abdul-rasheed Winki ne fa ba wani daban ba. Yi ha?uri muci tare mu sami ladan juna. Ko kina son mutane su fara shigowa su sameni a gidan bayan ya kamata ace nayi na fita na basu waje .
? ? ? Kanta ta girgiza. Ya ce,  Yauwa to maza muci kinji ?ar albarkata. Ai yanzu mu komai mukayi a tare lada za'a saka mana a samu a aljanna kuma.
? ?? Sai ta Wago kai, ta amsa da murmushi kaWan. Wannan karon, idanuwanta sun Wan shige cikin nasa.
Kallon su ya haWu, har ta kai kowa ya kasa fara janye wa, nutsuwa ce mai girma da daraja ke ratsasu a tare, zukatamsu na ?ara jin fahimtar wata sabuwar hanya ta rayuwa da suka shiga, rayuwa irin ta soyayya mai ladabi da ?arfi da haske fiye data da, rayuwa wadda take farawa da kunya, sannan ta cigaba da aminci da yarda.
? ? ?? Yatsa Abdul-rasheed ya kai kamar zai tsone mata idon, dan haka tasa hannu da sauri ta kare. Sai ya saki dariya, itama murmushi tayi mai cike da kunya. Zuciyarta na faWa mata abin da bakinta bai iya faWa, cewa sabuwar rayuwa ta fara a garesu kamar yanda Inna ta faWa mata, kuma shi mutum ne da nutsuwarsa ke girmama kwarjininsa a idanun kowa a bayyane.
? ? ? ?  Kin tafi tunanin miye kuma Matar Abdul-rasheed? .
? ? Kai tsaye ta ce,  Tunanin ka .
 Masha ALLAH akan mi? .
Babu kwalo-kwalo ta zayyane masa kalaman Innar tata. Ya Wan tsaya kawai yana kallonta da murmushi.???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? Kafin ya cigaba da cin abincinsa yana jin girma da kimar Inna na ?aruwa a ransa. Haka dai suka karya, ya taimaka mata suka gyara wajen, ta kwashi kwanikan zuwa waje danta wanke a gaban rijiya. Shi kuma sai ya Wauki botikin ?arfe ya fara jawo mata ruwan wanke-wanken, sannan ya fara Wiba a botikin yana kaiwa randunan ruwansu Waya bayan Waya. A haka suka kammala aikin yace zai yi wanka. Ita da kanta ta Wauki ruwan takai masa bayi tare da kwandon soson wanka. Ta dawo Wakin ta saka turaren wuta ta share. A lokacin ne kuma yaro yay sallama cikin gidan Wauke da kwanika akan ture. Bata yayi tare da mata bayanin cewa Inna ce tace ya kawo. Bata san wacece Innar ba, amma taji a ranta daga gidan su Abdul-rasheed Win ne. Godiya tayi da sannu, dan haka yaron bai zauna ba ya juya ya koma. Fitarsa babu jimawa Abdul-rasheed ya shigo. Ya ce,  Sallamar wa nake ji ne kamar Amadu? .
? ? ??  Wani yaro ne dai, ban sani ba ko sunansa kenan, abinci ne ya kawo yace inji Inna .
? ??  Oh daga gidanmu ne. To ki zauna sai ki karya .
? ? Idannunta a Wan ware ta ce,  Ba yanzu muka gama karyawa ba? Na?oshi ALLAH .
? ??  To Alhamdullahi, ki ajiye sai zuwa anjima. Amma kije kema kiyi wanka kada mutane su fara shigowa suna ganinki da kaya tun na jiya .
? ?? Babu ko musu, sai ma amsa masa da tai cike da ladabi, daga haka ta Wiba ruwan itama ta wuce bayi. Lokacin data fito harya shirya, dan haka bai zauna ba yay mata sallama ya fice dan har yara sun fara shigowa gidan. Aiko itama A'isha a gurguje ta kammala saka kaya, ta zauna tai kwalliya gwargwadon iyakarta kuma dai-dai da lokacinsa. Daga nan ta fiddo ma yaran da suka fara taruwa a gidan tabarmin karauni, sai kuma ta kwaso shantu duk ta zube dan harda ?ammata. Ai daga nan suka kafa shiriritar kiWan shantu da ?ammata sa'anninta a tsakar gidan nan suna raira wa?o?in gaWa. Kafin kace mi gidan ya cika da yara. Manya dake shigowa ganin Wakin amarya kota kansu basa bi ma, sai dai su shiga su gano su saka albarka su fice abinsu batare da sun damu ba, dan wannan ba komai bane daga amaren wannan zamanin nasu saboda ?uruciya da ?arancin shekaru..

Amarya A'isha bata sake tunawa da batun Abdul-rasheed ba har yamma ta samu abokan shargalle, abincin rana da aka sake kawowa ma daga gidansu, dana safen duk sun cinye ita da ?awayen nata. Sai gab da magriba an kawo mata tuwon dare mai kawowar data kasance ?anwar Abdul-rasheed ce Khadijah da bata koma Maiduguri ba ta kora yaran duka, sannan ta saka A'isha yin wankan dole ita kuma ta rufo gidan ta hau gyara tsakar gidan da sukama kaca-kaca. ?akin dai da yake ba zama sukai ba a ciki da haskensa, sai ?an ganin Waki da ke shiga. Amma duk da haka shima sai da Khadijah ta sake sharo mata shi ta kunna turaren wuta, zata kunna fitila taga babu kalanzir. Dole ta Wauki kalbar da aka aje dan sayen kalanzir Win ta fita samun yaro ya bada a suyo sukaci karo da Abdul-rasheed ya dawo. Koda ya tambayeta ina zata haka ta sanar masa sai shi ya amshi kwalbar yace ta koma shi bari ya sayo. Haka kuwa akayi, dan haka a gurguje Khadijah ta taya A'isha shiryawa. Sai gata ta fito tsaff kamar ba itace tai buWu-buWu ba. Ta bajeta da turare. Sai ga ango ya dawo. A tare suka masa sannu suka gaisheshi, Khadijah ta amshi kalanzir Win tana zubawa a fitila shiko yana satar kallon A'isha datai masa ?yau a cikin jojin da Khadijah ta sakata sakawa. Yasan wannan kwalliya haka sai da taimakon Khadijan, dan ta fita wayo kuma ta girmeta. Khadijah na gama kunna musu fitilar tai musu sallama zata wuce. Amma ya tsaidata kan ta zauna har ya dawo massalaci dan kar A'isha taji tsoro. Haka dole ta zauna sukai salla tare, shi ko yay alwala da ruwan da A'ishan ta kawo masa a butar karfe ya fice massalacin...........
'


_Zaku sameshi a waWan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER *_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ?asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya=?G?_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: =?G?_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number =?G?_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number=?G?_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*

*_Typing=???_*








*_>???KI?A A RUWA.....!!>???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._



_Chapter 14_

__________________

https://chat.whatsapp.com/Kf6jd57OsXHCG7cODNAje6

*_Kowace mace na matu?ar son taga ta gyara kitchen Winta kodan ta kalla itama taji daWi =؃?_*

*_Dun?ule kuWin ki saya ne ke miki wahala hajiyata?_*

*_Ko tarasu a hannunki ke baki wahala saboda kokin fara sai ki kasa ki kashe?_*


*_To kwantar min da hankalinka ?awata, IMZEED VENTURE ta gama shirya miki komai ta yanda kema zaki mallaki naki cikin sau?i da rahusa._*

_Ta buWe adashin gata wanda yafi bashi kwanciyar hankali da daWi, akan farashi mai sau?i, kaya ?an zamani, gasu ingattatu. Za'a kai miki a duk inda kike. Kedai naki kawai yin zubi akan lokaci._=؃?=؃?


*_Za'a fara zubi 25th October in sha ALLAH =؃?_*

20k monthly kayan 100k
10k monthly kayan 50k

*_Arha tafi bashi, hakama adashe yafi bashi. =؃? Ga sau?i abaka tamkar ?yauta =؃?=؃?=??_*

__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Abdul-rasheed bai dawo ba sai bayan sallar isha'i. Yana shigowa Khadijah tai musu sallama ta wuce. Shi kuma ya zauna yana zolayar A'isha akan yau dami-dami tayi da baya nan?. Sai da ta ajiye masa abincin da aka kawo daga gidansu gabanshi sannan ta zauna tana bashi labari cike da farin cikin tabbacin yau Win ya mata daWi. Shima sai yaji nashi farin cikin ya sake girma, da jin damuwar yanda zai tafi ya barta nan da kwanaki kaWan dan zai koma Kano makaranta. Dole dai ya ture tunanin a ?arshe ya lallaSata sukaci abincin tare, daga nan suna hira yaga ta fara hamma yace taje ta kwanta. Shi kuma ya Wakko kayan karatunsa ya fara nazari. Daga baya shima ya kwanta a nashi gado batare da yau ma yama A'isha komai ba.
? ?? Kwanakin da suka biyo baya sun cigaba da gudana ne cike da sha?uwa a tsakanin Abdul-rasheed da A'isha. Domin kuwa cikin hikima irin ta masu ilimi yanata jan ra'ayinta da janta a jiki kamar aboki tana sake sakin jiki da shi. Gayyar yaranta kuwa na anguwa kullum tare da su take yini, a haka suka cika kwanaki goma Abdul-rasheed ya shirya komawa Kano dan kwanakin hutunsa sun ?are. Gashi yana ?arshen zango baya bu?atar wasa da karatunsa. A'isha taci kuka sosai har ya dinga jin kamar shima ya tayata, daga ?arshe dai da ?yar ya lallasheta ya tafi ya barta zukatansu cike da Waci.
? ? ? A'isha ta koma sukuku da ita, kuma yanzu tana yini ne kawai a gidanta, amma da daddare can gidan su Abdul-rasheed take zuwa ta kwana. Da safe sai ta dawo gidanta sai kuma dare taje can. Tun tana tsangwamar kanta harta saki jiki saboda ?annensa biyu da suke kusan sa'anni ?ammata. Ga Inna ba ruwanta, faWanta kawai dai idan anyi ba daidai ba. Sosai A'isha take saka hannu suyi aikin gida tare da su Alawiyya, idan zasu fita ne dai Inna ke hanata binsu, ko in zasu tafi makarantar allo. Tun abin na sakata kuka harta fahimci hakan fa shine ?a'ida da doka, tunda sauran matan yayunsa bataga suna fita ko'ina ba sai da dalili, dan haka sai ta saki jiki.
? ? ? Tun A'isha na ?irga kwanakin tafiyar Abdul-rasheed harta bari, kwanci tashi sai gashi da watanni har huWu. A lokacin ne Baba ya aika masa wasi?ar tunatarwar yazo gida ko kwana biyu yayi, koya manta yana da iyali ne yanzu. Ya kamata ya dinga sara yana duban bakin gatari. Wasi?a ta isa ga Abdul-rasheed. Kuma ya gamsu da tunatarwar Baba, sai dai baya son zuwa gida ne saboda kaucewa abinda zuciyarsa da gangar jikinsa ke raya masa akan A'isha. Yana son ya bata damar ?ara fahimtar kanta har gaSar kammala karatunsa daya rage watanni biyu rak. Dan haka ya maida sa?on wasi?ar baba da amsar ban ha?uri data neman uzirin bashi damar kaiwa zuwa watannin da suka rage masa. Acewarsa karatunsu ya Wauki zafi a yanzu kuma suna gab da fara jarabawa. Bayan an kawo wa baba amsar Abdul-rasheed dole ya ha?ura ya bishi da addu'a, dan ya fahimci manufarshi kai tsaye. Haka kuwa aka ci gaba da rarrafawa har watanni biyun Abdul-rasheed na karatu suka cika. A lokacin ya shirya baro Kanon dabo zuwa Bauchin Yakubu gida. Sun sha kuka sun sha ruWani shi da amini kuma Wan uwa Nasiru da ogansa Yaya Zubairu. Daga ?arshe dai dole suka sallamawa tunda mai rabawa ta raba, sai dai ance sabo turken wawa ne, a wannan gaSar wannan turke ne kafe da zukatan su Abdul-rasheed. Yaje yayma Innar A'isha sallama, dan dama yana zuwa duk kwanakin mako da yake yi a anguwar kullum safiya gaisheta, hakan yasa abincinsa daga gidansu A'isha kullum kwano ukun nan babu fashi a kwanakin ?arshen makon. Shiko baya gajiya da godiya da yin kuma cefane ya kai ma Inna. Ya kuma yi ?o?ari ya lallaSata ta yarda ya saka Bashir da Tasi'u a makarantar primary da ?a?an gidan su Nasiru ne kawai ke zuwa a layin. Inna ta haWa tsaraba mai yawa sai ?ar sana'ar da amarya kanyi irinta ?ulle-?ullen kayan lwaWayi. Haka Nasiru yay masa rakkiya har tasha tare da su Bashir, basu dawo gida ba sai da motar su Abdul-rasheed Win ta Waga zuwa Bauchi....

? ? _________________

? ?? BAUCHI

A bisa al'adar wannan zamanin zaman mace babu ?unshi a ?afa da hannu kamar wani zunubi ne. Kahama kitso ?a'idane wani na tsufa kina sake wani akai-akai. Wannan wajibi ne ga mace mai aure a kowane yare na arewacin ?asar. Dan haka koda Abdul-rasheed baya nan a duk sanda ya dace A'isha tayi ?unshi da kitso Inna na sakata tsefe kai cikin matan yayun Abdul-rasheed wata tai mata kitso. Hakama tana yin ?unshi tare da su dan sukan shirya yinsa ne a tare. Dan haka da wahala ka samu A'isha babu irin wannan tsaftar. Kamar dai yau a jiya Inna ta sakata yin sabon kitso, inda Magajiya ta zuba mata ?anana masu ?yau harda na gaba sak dai irin na barebari. Yau kuma suka shirya yin lalle a ?afafunsu tun safe. Haka kuwa suka sakashi har yamma yana jikinsu. Sai la'asar suka kunce, A'isha batai niyyar zuwa gidanta ba yau sam dan haka ta Sararraje suna hira da sauran facalolinta dan a gidan Waya daga cikinsu akai ?unshin. A dai-dai kuma wannan lokaci Abdul-rasheed ya iso. A gidansu ya sauka kamar yanda ya saba, dan haka Inna ta tareshi tarba mai girma. Cike da hikima irin ta manya yana zaman gaisawa da Baba ta aika akai mata kiran babbar surukarta, a soro suka tsaya, bayan ta gaisheta ta shaida mata Abdul-rasheed ne ya dawo, maza su saka A'isha ta koma gida ta gyara jikinta. Sannan su taimaka mata sauri-sauri su tayata gyara gidan shima kafin ya iso. Ta amsa da ladabi ta fice. Tana zuwa ta gwargwaWama sauran ?an uwanta dan haka suka tasa A'isha a gaba. Tana son jin ba'asi babu wanda ya bayyana mata, sai dai sunce umarnin Inna ne hakan. Girman suruka koda matsayin kishiyar uwar miji take girma gareshi a wannan lokacin, dan haka A'isha bata sake tari ba ta bisu, dan yanda Innarta zatai mata magana ko bata umarni ta bi haka Inna itama zatayi tabi dole dan matsayin uwar miji take a garesu.
? ? ? Dan danan suka taimaka mata da dukkan abinda ya dace, ruwan wankanta kanshi yasha turare kala-kala a cikinsa. Hakama Wakin suna kammala gyara mata suka baWesa da turaren wuta. Basu taSa mata gadon miji ba suka barta ta gyara da kanta suka fice zuwa nasu gidajen lokacin anata kiraye-kirayen sallar magriba. Hakan yasa cike da mamaki A'isha ta fara kici-kicin gyaran baban gado dake matsayin na mijinta Abdul-rasheed, zuciyarta kuwa cike da wasi-wasi akan mike faruwa ne wai? Gashi kafin su tafi sai da sukai mata kashedi akan ta zauna a gida karta ce zata biyosu ta jira. Bata fahimci mi suke nufi ba sai da Abdul-rasheed yay sallama yara biye da shi da kaya ni?i-ni?i. Ita jitai ma kamar ta firgita, dan haka ta fito wuff da fitilar ?wai a hannu domin haskawa, hakan ya bama Abdul-rasheed damar ganinta fes a cikin sirritaccen hasken mai cike da ?ayatar da mai kallo. Tayi ?yau cikin atamfa mai tabarma sabon Winki ne daga cikin kayan lefenta da sai yau ta saka. Turus ta tsaya tana kallonsa itama kamar yanda yake kallonta, sai dai shi nashi kallon na shau?i ne da kewa matsananciya. Itako na mamaki ne da ruWanin bazatar tasa. Sun zubama juna ido harna fin minti Waya har yaran nan suka ajiye kayan suka fice abinsu suka barsu dan saurin komawa suci tsarabar daya bayar a basu a can wajen Inna. Sai da aka kabbara salla ne hankalin Abdul-rasheed ya dawo jikinsa. Numfashi ya furzar a hankali yana janye idanunsa daga cikin na A'isha da suka tara ?walla, cike da sanyin murya ya furta,  Bani buta kada na rasa salla gaba Waya .
? ? ? Sukuku ta koma ciki kamar kazar da ?wai ya fashewa a ciki ta Wakko masa butarsa ta ?arfe, tazo gabansa ta dur?usa ta mi?a masa. Amsa yay yana kallonta shi dai, dan harga ALLAH sai ya ga ta ?ara masa cika a ido da girma, shi yana can tunaninta na hanashi sukuni da isasshen barci, itako da alama ko'a jikinta daWinta take ci, ?aramin murmushi yayi kawai, kafin ya maida hankali yayi alwalar ya fice gudu-gudu sauri-sauri dan har anyi raka'ar farko ma. Sau?in ma massalacin kusa ne da su gab.
Koda aka idar da magriba bai dawo ba, A'isha ma data

12 / 36