KIDA A RUWA HAUSA READ NOVELS BY BILLYN ABDULL.doc

Author :  BILLYN ABDULL Category :  Hausa Read

Chapter   10 / 36

27K to 30K   out of 106.7K words

rage da wanda aka cire matan Alwanka ta kawo musu, nan fa ?awayen amarya suka shiga Wiba suna saka mata a jiki ana murjeta da shi. Itako tana kai musu duka da harbinsu ?afa da hannu tana kuka. Har cikin gashin kanta ana raira wa?a, bari na Wan raira muku=؃?>?#?.

? ? Ayye yara iye TURGEZA.
Ga Turgeza yazo, Turgeza.

A wanketa da sauri, turgeza.

Lallen iya ?amshi, turgeza.

Ayye yara amarya turgeza.

Sai da ni bilyn ku=?? (magana ta gaskiya ni na ?ir?iro muku wa?ar, amma ta gaskiyar ba haka take ba, baitin farko ne kawai na gaskiya kada kakanin mu suce na musu sharri=??>?#?>?#?).

? ? ?? Sosai amarya ta dirzu da lalle. Masha ALLAH kuma sai tayi ?yau abinta, sai dai fa kowa ya daku gwargwadon iko cikin ?awayenta. Itama kanta ta jigata da kuka da harbe-harben data sha. Ana sakinta taja zaninta ta Waura, data rarumi icce tai kan ?awayen nan nata sai gudu Malam. Tuni fa kowa yay waje, masu neman wajen Suya suka nema, masu haura katanga nayi masu yin hanyar zaure nayi. Da ?yar Alwanka ta kamata ta ri?e, sai da duk suka baje sannan ta saketa, babu batun wanka, wannan lalle na jikinta haka kuma zai cigaba da zama a jikin nata har sai gobe, gefe ta koma ta dasa sabon kuka. Babu wanda ya hanata har tayi mai isarta ta gaji dan kanta ta ha?ura. Bayan komai ya lafa ?awayen amarya suka daddawo sai kuma aka Wakko abinci da miya aka baje kuma a tsakar gida da turirrika na rabo. Haka aka raba abincin ?unshi da nama kowa ya samu har ma?wafta, aka baje kuma aka fara ci ana hira da wasa da dariya. Bayan sun kammala aka aiko baranya Wakko igiyar shillo, babu jimawa ta dawo, amarya ta tashi ta saka rigarta da kallabi suka kwashi igiyar nan suka fice bayan gidan wajen wata bishiyar Saure ?atuwar gaske. Anan aka Waura wannan igiya ta Wauru kam sannan aka fara shillo, idan wannan ya sauka wannan ya hau, har yamma suna a wajen suna wa?e-wa?ensu na ?anmata cike da nishaWi. Sai gab da magriba suka dawo gidan Alwanka.
? ? ? ? Washe gari alhamis ma haka suka sha shagalinsu aka ?ara yima amarya wankan lalle kamar jiya, dan kuwa yau ma zir akai mata sai Wan kamfai aka shafeta da lalle har cikin kanta, tasha kukanta kamar jiya har yamma. Zuwa dare bayan sallar isha'i Alwanka ta tattarasu tai musu rakkiya aka maidasu gidan su A'isha. Gida kam ya gama cika da dangi tako ina. Bayan gaisuwa Alwanka tace  Ga aro na maido, ALLAH ya sanya alkairi ya fiddamu kunyar gobe. ALLAH Kuma yasa takai mutuncinta Wakinta. Nagode, Nagode ALLAH yabar zuminci .
? ? ? Atare aka amsa mata da amin. Dangi sukai godiya suma sosai ta wuce. A ranar anan gidan su A'isha suka kwana, dan kuwa Waki guda aka ware musu ita da ?awayenta. Washe gari juma'a Waurin aure, ta ko ina dangi maza sunata isowa, hakama tawagar ango da danginsa daga Bauchi, da abokansa na Bauchi dana Kano duk sun iso, zuwa ?arfe sha Waya aka Waura auren A'isha da Abdul-rasheed akan kuWi sule na gugar sule har sule goma cas. Lallai wannan yawan sadaki ya girgiza mutane, dan kuwa sule goma ba kuWin wasan yaro bane a lokacin. Abinci kala-kala tako ina ?amshin ke tashi na miyar taushe ga nama kamar a banza. Dangi kowa ka gani bakinsa a washe anatama juna sambarka, balle kuma ace Inna ai ba'a magana, tayi shar da ita cikin sabon Winki.
? ? ? Amarya kuwa na can tare da ?awayenta a Waki, sai dai a mi?a musu abinci. ?awaye sunyi wanka da kwalliya, amarya kam dai tana nan ba wanka har yanzu dai tsoffin kayanta ne a jikinta na zaman lalle, sai bayan sallar azhar kuma aka shirya yima amarya wanka dan za'a shiryata domin tafiya Bauchi. An shirya ruwan wankan amarya a cikin ?aton masaki da yasha addu'oi daga tsoffi, aka zuba lalle sai kuma ruwan turare kala uku masu ?amshi sosai, sai sabulu shima mai shegen ?amshin tsiya. Bayi aka kaishi sannan aka kira alwanka da zatai mata wanka. Aifa nan abokan wasa suka mi?e domin rakkiyar amarya bayi, tana kuka aka dannata ciki bayin, dama Alwanka an kiranta. Wa?a abokan wasan nan nata suka fara rairawa suna tafi yara na tayasu....

? ? ? ? Tsohuwa iki wanke,
kin saki Kwankwaso yeee a ?ofar soro=؃?....

(=??Ehem-ehem lamarin fa ba'a cewa komai, amma wannan wa?ar ta gaskiya ce walle bani na ?ir?ira ba=??=??).

? ? ? Kuka sosai itako amarya keyi, Alwanka kuwa na wanketa lungu da sa?o har gashinta dake dan?are da lalle. Duk wannan dattin ya fita da suke kira (SaiSi), sai ga amarya na she?i da ?yalli da ?amshi kamar ka lasheta. Zani aka bata ta Wauro aka rufeta da wani aka fito da ita sai Wakin Inna. Acan aka shafa mata mai mai ?amshin tsiya mai gurguwa, aka shafe ta da turarruka kala-kala Sannan aka bata sabon zani da riga na atamfar.... Ta saka daga cikin lefe yake, sai Wan kwali disko da wani fallen zanin na lulluSi. Aka shafa mata hoda aka saka mata jan baki amarya ta fito tsaf da ita masha ALLAH.
? ? ? To daga nan fa iyaye suka zagayeta aka shiga faWa da nasiha, itako tana ?unshe a zanin nan da take lulluSe tana kuka sosai. Bayan sun gama akasa Inna tai mata addu'a tana kuka sosai, dan yau ne karo na farko da zatai nesa da ?arta. Bayan ta kammala aka kamata aka fito da ita soro inda iyaye maza suke suma suna jira. Nan ma sabon faWa da nasiha aka buWe, gargaWi dai kam amarya ta shashi gwargwadon iko kafin a kamata zuwa ?ofa gida inda motor da za'a Wauki amarya take. Ka??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nta ce guda biyu, sai ?arama Waya da za'a saka amarya. Tuni masu zuwa sun cika kantar kuwa harda ?awayen amarya, dan haka aka sakata cikin ?aramar Innarta da Gwaggon na Sangaren uwa da uba suka shiga kusa da ita, sai a gaba direba da Nasiru ne, ango da sauran abokai kuwa tuni sun Wauki hanyar Bauchi su dama da iyaye ?an Waurin aure.
? ? ? ? Motoci na Wagawa ?ammatan amarya suka fara raira wa?a da yara....

? ?? Ayye yaraye dide, ayye yaraye naye, ayye yara iye naye yaraye!!.

?ammata kuzo roni, mi zamuyo roni? Aiko zaman lallen A'isha lale laya!.

Ke kikace kinayi da shi, shi yakace yanayi dake, har magana takai ga manya kibar mana koke-koken tsiya.

Babu mararraba ba rabawa, iccen wurma yasha harara, yasha rarraSar masu ?a?a, tunda ya kada goWiya.

Iye yaraye, ke kikace kinayi da shi, shi yakace yanayi dake!.

=؃?
? ? ? ? Su suna raira wa?a amarya na kuka mai ban tausayi. Haka motoci suka wuce jama'ar anguwa na binta da addu'ar fatan zama lafiya na har abada. Ahaka aka Wauki hanyar Bauchi. Tun masu wa?a nayi har suka gaji wasu ma suka fara barci, cikin amincin ALLAH bayan magariba suka iso Bauchi. Kai tsaye kuma gidan iyayen Abdul-rasheed aka wuce da amarya, inda suka samu tarba ta mutuntawa da girmamawa. Tarba dai kam dangin Abdul-rasheed sun yima amarya ta gata ita da danginta, yayinda take ?unshe cikin gyauton zanin da aka lulluSa mata na atamfarta mai barewa datai mata ?yau. An kawo musu abincin maraba kala-kala sukaci suka ?oshi, daga haka suka baje barci dan kowa ya gaji matu?a, ita kanta amarya tuni ta Singire da ?yar ma aka samu taci abincin.........
'

_Zaku sameshi a waWan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER *_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ?asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya=?G?_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: =?G?_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number =?G?_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number=?G?_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*


*_Typing=???_*








*_>???KI?A A RUWA.....!!>???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._



_Chapter 11_

__________________

*_NACE ina kuke ne?!!. Al'ummar Gombawa nake magana =؃? fulanin asali ke nan =??._*

*Shin kuna da labarin cewa kuma nesa ta matso kusa gare ku?*

_Maza kuzo ku sha labari da Wumi-Wuminsa, domin kuma fa NAKUN ya buWe muku gidan gyara da ?al?ale jikin mata ?an kwalisa a kusa da ku gabb._

*_Idan kunji ana kiran maida tsohuwa yarinya to wannan katafaren shagon ne na=?G?_*


*ALIYU HAIDAR COSMETICS PLAZA*

_ADDRESS SHOP D80 WOMAN LINE GOMBE MAIN MARKET_

*_Zaku same mu a wannan numbers Win kamar haka=?G?_*
*07068210505*
*09133081313*

_DEALER IN all kind of skin care products such as:_

moisturizer
Sun screen
Face Toner
Eye cream
Face serum
Face wash
Face scrub
Face cream
Face marsk
Body lotion
Body cream
Shower gel
Body scrub
Tube
Body oil
Body spray
Perfume
Hair crm
Hair spray and many more

*_Harma da abinda bamu lissafo ba anan. Ku dai kawai karku bari a yi babu ku. Domin kayanmu garanti ne kuma dahir ne =؃?_*

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/HCLn6awOrmP5WJmO9jPrgK?mode=ems_wa_t

__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Washe gari an cigaba da shan biki a Bauchi, dan anyi wankan ango da ajo Winsa. Amarya kuwa babu wanda zai ce yaga fuskarta sam dan ko wajen wankan ango da ajo bata le?o ba tana Waki ?unshe. Hakan kuwa shine dai-dai kuma shine Wa'a. A ranar kayan amarya suka iso dan su sai washe gari aka taho dasu. Gidanta dake nan jikin gidan sirukanta da sauran ?an uwansa aka sauke, sauran kayan gara kuwa gidan su abdul-rasheed.
? ? ?? A take danginta suka koma can aka hau jere, aka barta da ?awayenta ita kuma anan gidan. ?akin amarya yayi ?yau. Iyayenta sunyi ?o?ari sosai. Gado ne guda biyu, babba mai rumfa na miji, sai ?arami nata. Mai rumfa yasha ?atuwar katifa da zanin gado harda rumfarsa ta sama da filo har goma sha biyu ciff, aka saka masa labule da ake kira (Zarge shige>?#?). Dan haka gadon yay Was kamar ka zauna kaita kallo. Itama dai natan an saka katifa da zanin gado mai ?yau, sai kabot da ya sha jeren fantekoki a sama da kwalloli, sai kanta a cike da tasoshi ?ar girke dake ta ?yalli da Waukar ido na ?ar gata, sai tangarare suma na ?ar gata. Ga languna tuwo da miya kala-kala da kwanon sha. Sai kumbo manya anyi nasu dankin uwa ta raSe suma a gefe masha ALLAH, ga uwa ta raSe ta fantekoki masu murtala. Kowace kusurwa an buga darduma masu ?yau, sai labule. Sai gansarwa na garar kaka da ?oran fulani da suka sha tarde da ludaye a cikin an sakasu a ragaya aka rataye, ledar ?asa ma an baza masha ALLAH. Kai abunfa ba'a magana, dan Wakin amarya sai sambarka komai yaji, kaida ka gani kaga Wakin ?ar gata. Abin dai masha ALLAH sai wanda ya gani. Dan duk hassadarka kai kana ganin wannan Waki kasan an zubama Ai'shatu kayan ?ar gata.
? ? ? ? Suna kammalawa zuwa dare aka dawo da amarya nan, suma dangin nata nan duk suka dawo aka cigaba da shagalin biki bayan an dire musu raguna manya guda biyu na jere. Washe gari buWar kai, ranar kuma biki zai tashi, ba?i duk zasu wuce musamman ma ?an kano. An dafa farar shinkafa, sannan amarya tayi wanka yau, dan tunda aka kawota ko kaya bata canja ba, batayi wanka ba kuma, idan kaga ruwa ya taSa jikinta sai na alwala. Har yanzu bata saka Abdul-rasheed a idon taba shima haka bai ganta ba. Tunda safe aka fara mata kitso ?ana-?ana masu ?yau, sun jima sunayi dan har zuwa azhar sannan suka kammala aka haWa mata ruwa da yaji turarruka da addu'oi ta shiga wanka da kanta. Bayan wani lokaci ta fito, an bata kaya ta canja, atamfa mai tabarma da akaima Winki mai ?yau irin na wannan zamanin, yau dai gyale aka bata ta yafa ba zani ba, sabon takalmi sai tsakiyar wuya mai ?yau tanata she?i. Sosai hankalinta a tashe yake, dan yan uwanta duk sun kammala shirin su, ana gama buWar kai zasu wuce. Gida ya cika taf, dangin ango duk sun dawo nan suma. An fara yin rabo irin na al'ada ga dangin miji, bayan kammalawa ne aka fito da amarya dake lulluSe cikin gyalenta, har yanzu dangin miji dama ?an gari babu mai cewa ga kamaninta. Sabuwar tabarma aka shimfiWa aka Wora sabuwar kujerarta ?ar tsugunno a kai, ta zauna. Shinkafar nan da aka dafa fara sai gishiri kawai a cikinta, amma fa tasha mangaWa ?yallan aka juyo a ?aton bangaji aka ajiye gabanta. Tana lulluSen aka kamo hannunta biyu aka fito da su, ta haWesu waje guda kamar mai addu'a aka cika mata shi da shinkafar nan taf. A baki ta saka, sai dai babu batun taunawa ta furzar a gefenta na dama, ta ?ara cika baki ta furzar a gefenta na haggu, ta karshe ta furza a gaba, sauran ta watsata baya. Daga nan ne fa aka shiga rangaWa guWa, masu kiWan ?warya suka fara. Bayan an gama cashewa da kiWan ?warya koma muce ana cikin cashewar iyaye a cikin dangin ango suka kwashi kayan da aka basu na baye suka koma gida, aka sake shirya amarya itama aka bisu da ita can hannunta ri?e da ?warya mai ?yau. An fara kaita Wakin Inna dake matsayin uwar mijinta a yanzu. Inna tayi addu'ar zaman lafiya, ta kawo kuWi jaka biyu ta saka mata a ?waryar, danginta sukai godiya aka fito, daga nan sai Wakin marigayiya mahaifiyar Abdul-rasheed, inda danginta suka fanshi nata, ba'a nan aka tsaya ba, sai da akabi iyaye kaf, dangin uban miji dana uwa. Kafin kace mi sai ga kuWi shimili amarya ta tara a wannan ?warya, dan har makwaftansu da ake zumunci irin na mutuntawar mutanen da, makwata iyaye ne ba abokan gaba ba, nan ma sai da aka kai amarya, daga nan ne aka sake baidata gidanta inda yara da ?ammata ke cigaba da cashewa da kiWan ?warya. An maidata Wakinta, aka saka wasu cikin ?annen ango suka zauna da ita, suko ?an kano cikin hikima suka zare jikinsu duk suka gudu batare da amarya daketa kukanta ta farga ba. Balle kuma masu kiWan ?warya na wasansu har magriba. Sai bayan sun tashi ne gida ya fara komawa tsit A'isha ta fahimci da kaf yan uwanta babu. Sosai ta ?ara ?arfin kukanta, ?annen ango dake tare da ita har lokacin na lallashinta.
? ? ?? Zuwa bayan sallar isha'i an tafi an bar amarya ita kaWai a Wakinta tanata kuka, sai daga baya aka turo mata wasu ?ammata huWu su zauna da ita saboda zuwan anguna. Babu jimawa kuwa ango da abokansa suka yo masa rakkiya cikin girma. ?awayen nan sune suka amsa, dan amarya na can ?arshen bango ta rakuSe ?udundune cikin gyale. Anyi gaisuwa tsakanin ?awayen amarya da abokan ango, ?awayen amarya suka gabatar musu da abinci. Kwanika ne guda biyu dake a saman tire Win kwano da kwanon sha dake cike da ruwa an rufesu da tuma ?asa (=??Azo gaya min minene tuma ?asa akwai kyauta). Gefe suka koma su kuma abokan ango suka naWe hannayen riga suka fara Wibar girki, gefe kuma suna hira da ?awayen amarya. Bayan sun kammala akai sayen baki, anyi ?ar jayayya akan kuWi, daga ?arshe dai suka ajiye musu jaka huWu. Ita dai amarya na nan a gefe kamar ma bata san bikin da ake ba a Wakin, kukanta take dai kawai.
? ? ?Abokan ango sunyi nasiharsu ga amarya da ango, tare da addu'a. Daga haka suka mi?e tare da ?awayen amarya sukai musu sallama suka wuce. Abdul-rasheed ya mi?e dan rakasu Nasiru ya maida shi ya zaunar yana faWin,  In dai mune mun huttasheka, zauna ka lallashi min ?anwa sai munzo maka tausa . Daga haka suka fice suna dariyar kalmar sha?iyancin Nasiru. Abdul-rasheed ya bisu da kallo kawai yana murmushi. Bayan fitar tasu Wakin ya kasance shiru na fin mintuna uku, dan haka kawai shima Abdul-rasheed Win sai yake jin kansa wani iri tamkar ba shi Win ba. Yau ALLAH ya cika masa burinsa ga shi ga masoyiyarsa dai a tare da shi. Itako har yanzu kukanta take mai fita da sauti kaWan da shashsheka. A hankali ya mi?e yana mai tattare babbar rigar jikinsa ya cire gaba Waya, saman gadon mai rumfa ya Waga labulensa ya ajiyeta sannan ya taka zuwa inda take zaune a ma?ure tsakanin gado da bango. A nan ma Wan tsayawa yay kanta yana kallo na sakkanni, kafin ya kai tsugunne gabanta ya Waura hannunsa kan nata dake ri?e da gyalen da take lulluSe a ciki. ?an zabura tai na tsorata, dan haka ya saki hannun nata, sai kuma cike da tausasawa ya furta,  Ha Giwar mata, kukan ya isa haka mana. Yau fa rana ce irin ta farin ciki gaki ga Abdul-rasheed Winki, kwana da kwanaki an hana min ganinki kewa na neman kaini ?asa. Bana son kukan nan yana Waga min hankali da sukar zuciyata, kiyi ha?uri ki daina yinsa. Ina sha ALLAHU na miki al?awarin zan kwatanta daga ?o?ari irin na Inna a gareke, bazan barki kiyi doguwar kewa ba ko yin kukan rashinta a kusa dake. Zan yi ?o?arin maye miki gurbin su Bashir, haka kuma zan maye miki gurbi na ?awayenki. Zan zama adali mai ?o?arin sauke nauyin da ALLAH ya Wora masa na maye gurbin damuwarki da farin ciki, kukan ki da dariya. Kin san ina sonki matu?a A'ishatu, ba kuma zan daina ba har na koma ga UBANGIJI na in sha ALLAHU .
? ? ? Sosai kalamansa ke tasirantuwa a zuciya da gangar jikin ta, dan haka a hankali ya fara sassauta kukan nata. Da wannan damar yay amfani wajen bata umarnin mi?ewa. Babu musu ta mi?e Win, dan a nasihar da tasha an tabbatar mata biyayya ga miji shine nasararta kuma wajib ne in har ba akan saSon ALLAH ba. Sai dai

10 / 36