KIDA A RUWA HAUSA READ NOVELS BY BILLYN ABDULL.doc

Author :  BILLYN ABDULL Category :  Hausa Read

Chapter   21 / 36

60K to 63K   out of 106.7K words

ofishinsa yake zuwa suyita hira da labarin aikin soja.
A haka rayuwa ta shuWa yau da gobe kayan ALLAH. Ranar da Haysam ya kammala Secondary School, Aisha ta kasa boye hawayenta na farin ciki da na tsoron duk a lokaci Waya. Domin tana ganin Wanta zai tashi neman hanyar rayuwa ta girma da gwagwarmayar da tafi ta shekarun ?uruciyarsa girma da haWari. Domin zuwa yanzu Haysam ya gama yanke shawarar shiga aikin soja kamar yanda yasha faWa mata tun bayan al?awarin da malaminsu yay masa. A duk lokacin da ya faWa mata haka, sai ta yi shiru na dogon lokaci kafin ta ce:  Ka tafi idan hakan ne ka ga daidai, amma ka tuna da addu a. Rayuwar soja ba wasa bace Muhammad, sai dai bazan hana ka ba, ba kuma zan tunSuke maka burin mahaifinka a zuciyarka ba saboda ina jin tsoro, zan cigaba da maka addu'a da karfafawata ALLAH ya fimu sanin abinda ke Soye ai, sannan kowane bawa yana rayuwa ne da ?addararsa, kwazonsa a cin jarabawarsa ne ke bashi makoma bisa ga rahamar mahaliccinmu.
? ? ?? To a yau ma aka kammala bikin gama Secondary Winsu daya tuna mata cewar lokacin zama soja yayi amsar data bashi kenan. Sai kawai ya dur?usa ya rungumeta tare da faWin,  Mammah na gode da ?arfafawarki a gareni a koda yaushe, amma ki sani ni bana zuwa neman suna, amma zanje neman ?arfi da adalci. Na ga yadda rashin adalci ke cinye mutane, zan so in tashi da takobin gaskiya, ko da zai zama ?arshena, daga karshen dai na cika burin Abiy na kuma cika nawa burin, na kuma maida sunanki UWAR GWANI ko UWAR MAYA?I.
? ? ?? Murmushi Aisha tayi da share hawaye, ta Wagosa daga jikinta tana mai Wan dungure masa kai. Murmushi yayi yana mai risinar da idanunsa ?asa, dama idan kaga sakewa ta musamman ga Haysam to yana a gaban Mammah ne. A'isha dake hawaye itama ta kamo hannayensa cikin nata ta runtse tana addu a kamar haka,  ALLAH ya taimake ka Muhammad. Ka zama zaki mai adalci kamar yanda mahaifinku ke fata ba wanda ke cin mutane ba. Ka zama ZAKI mai amsa sunan SARKI a rundunar adalci ba Sarkin dabbobi mai mulkinsu ta ?arfi yana halakasu matsayin abincinsa ba. Ka zama ZAKI mai kassara ma?iya da karya mugayen burunsu da manufofin su. ina fatan wannan? jarumin na Abiy da Umman-Haysam (Yakura) ya zama Zaki wanda rayuwarsa ta samo asali daga haske da nagarta, daga hawaye da fata, daga ?aunar iyaye da ?an uwa da nauyin al umma. Kaje soja da fatana da addu'ata Muhammad, kaje soja da amincewata da farin cikina Muhammad Haysam. Amma ina mai gargaWinka da shaye-shaye, bana so! Bana so! Bana so Muhammad. Ka kiyaye Zina, tana ruguza bawa da zuri'arsa, bana so! Bana so! Bana so Haysam. Ka yaWa ilimi ka cigaba da neman ilimi musamman na bautama UBANGIJI, kaga dai zuwa yanzu kayi saukar Alkur'ani, ka samu ilimin hadisi mai yawan gaske, ka haddace litattafai da yawa na addini da koni mahaifiyarku kana koyar dani a yanzu. Ka tuna yan uwanka suna kiranka da suna (DADA) a yanzu saboda kai suke gani madadin mahaifinsu, idan ka Sata Wan wani kaima za'aci nasarar Sata maka su Haysam. Yau babu Innata a duniya shekararta Waya kenan da rasuwa, tunda Tasi'u yabar ?asar nan bamu sake jin labarinsa ba shekara huWu kenan, an kashe mana Bashir a aikin soja, wanda labarin rasuwarsa yasa Inna yanke jiki ta faWi bata sake lafiya ba sai da ta koma ga UBANGIJI. Haysam banda kowa sai ALLAH NA, sai ku ?a?ana guda takwas, kune uwata kune ubana, kune dangina. Babu kalar zagin da bana sha saboda na?i yin aure, ni kuma bana son nayi aure ne wani yazo ya ?untata min rayuwarku koda da harara. A kowace rayuwa zaka tsinta kanka ka tuna kai wanene dan ALLAH Haysam ka tuna .
? ? Kuka ya sar?eta, shima sai ya kwantar da kansa a cinyarta yana hawaye. Sun jima a haka kafin ta koma lallashinsu, sai kuma ta koma bashi labarai masu daWi na rayuwarta da mahaifinsu Abdul-rasheed. A haka su Ma'aruff da a yanzu suma suke js 1 Secondary suka shigo, ba jimawa Ummi da Bilal da Momy suma suka dawo. Ammar da Mimi kuwa ba'a sakasu a makaranta ba har yanzu dai. Aiko zama sukai suka zagaye Haysam da a yanzu suka maida sunansa Dada suna taya shi murnar gama Secondary. Idan ka gansu dole su burgeka su kuma baka tausayi.
? ?? Akwai zuminci mai ?arfi a tsakaninsu, akwai ginanniyar soyayyar juna mai tsafta a zukatansu, akwai sha?uwa mai rahama a tsakaninsu, akwai tausayi mai yalwa a tsakaninsu. Su ba masu arzi?i bane, amma ALLAH ya basu arzi?in farin ciki da so da ?aunar junansu, ALLAH ya basu arzi?in JARUMAR UWA mai sadaukar da farin cikinta domin gina nasu. Sun rasa uba amma suna kallon babban yayansu madadin uba a wannan lokacin. Dan kuwa shine ke musu Wawainiya irin ta uba. A dalilin gwagwarmayar talla daya sha ta kayan koli da kayan karatu dama wasu wahalhalu, da aikatau na mahaifiya da wankau, dama wasu abubuwa da tayi bayan nan, dan akwai gaSar da aka koreta a aikatau Win ma, wankin ya daina yiwuwa saboda ciwo daya kwantar da ita, Wan abinda suka samu ta koma yin abincin sayarwa safe da rana wani lokacin har tuwo da dare ta fita da shi bakin kasuwa. Kai har dakau A'isha tayi domin iyalanta, haka zatayi surfe ta maida dakan gari hannunta na baroro da fashewa amma bazata kula ba, aikin gona tasha yi ta tasa yaranta gaba suyi a biyasu, sussukar hatsi na gona ta Wure a buhu a biyata. Ga jiyyar Innarta da ciwo ya kayar, da al'amarin ya ?waSe har itace A'isha tayo a daji ta sayar dan samun abinci da kuWin maganin Inna dan abinda Haysam ke samowa a kasuwa bawai zai wadacesu bane duka amma yana rage musu sosai dan dashi ake biyan komai na karatunsa dana ?annensa. Da kuma ALLAH ya sakama abin albarka har ya kafa jarin kansa sai yazama har anan gida ana zuwa nema a saya kayan kolin, daga haka ya barma Mammahnsa wannan sanar kolin har ma da kayan karatu na yara ya maida hankali a zana jarabawar ?arshe da sukayi yau suka kammala. Sai kuma Alhmdllh yaga a gida ma kamar ALLAH yafi sanyama sanar kayan kolin ma albarka, wannan ?warin gwiwa ne ya ?arfafashi a yau ya sake tabbatar ma Mammah zai je aikin sojan da yake ji da kamar zai fasa saboda kar ya barta da nauyi, amma yanzu yana fata wannan sanar tasa data dawo gida zata taimaka musu sosai.........
'


_Zaku sameshi a waWan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER *_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ?asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya=?G?_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: =?G?_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number =?G?_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number=?G?_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*

*_Typing=???_*








*_>???KI?A A RUWA.....!!>???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._



_Chapter 26_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Link na grp


07077532253
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm


https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE
Duniyar kayan kitchen ?an yayi dake maida mata ?an ?walisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure>?p?>?p?>?p? Kisha mamaki=???? idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi>?s?>?s?.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ?yale-?yale ce da ?ayatarwa da mata sukafi bu?ata musamman ?an ?walisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link Win namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuSemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture.
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,=??=??=??=??=?? Nima Bilyn Abdull tuni na antaya __________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Addu'ar mahaifiya ba wasa ba, dan kuwa dai Haysam ya tsallaka ajin jarabawa ko muce ?addararsa ta uku bayan rayuwar jin daWi da iyaye, data maraici da uwa Waya tilo, zuwa soja a yanzu, sojan ?asa mai girma irin ?asarsa. Matakin ?addarar soja dake tafiya da fara shekarun hankali da mallakar kai da kai matsayin cikakken mutum, dan kuwa ya Wauki hanyar tsallake shekaru ashirin Win farko zuwa matakin rayuwa ta biyu a masomin cikar hankali da fara sanin ainahin micece ma duniyar, dan a wancan matakin an san duniyar ne a gaSar banbance iya abinda ?wa?walwa da zuciya kawai ke iya fuskan??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ta da karamin nisan tunani da hange.
? ?? Matakin farko na samun gurbi a NDA (Nigerian Defence Academy), Haysam Abdul-rasheed Shehu ya samu wannan gurbin Karatu da taimakon Malamin nan nasu da yay al?awari tun shekaru uku da suka shuWe wato Malam Su. Bayan Haysam ya gama Secondary School da ?wazo da halin kirki ya samu result Winsa na SSCE yayi ?yau sosai. Cike da zumuWi ya nufi ofishin Malam Su ya kai masa, ai ko ya tayashi murna ya kuma ce yaje ya shirya a gobe zasuje Kaduna wajen ?aninsa wanda yake Major a Nigerian Army, wanda kuma yake da ala?a da masu duba takardun shiga NDA (Nigerian Defence Academy).
? ? ?? Haka kuwa akayi, Mammah tai Wan cuku-cukunta ta samawa Haysam kuWin mota da Wan na guzirin cin abinci, washe gari suka Wauki hanyar Kaduna. Sun samu tarba ta muntatawa kuwa, bayan sunci sun sha Malam Sulaiman ya gana da ?aninsa. Bayan ya ?ara tisa masa wanene Haysam, da kwazon yaron da halin manya ya ce,
? ? ??  Wannan yaron bai da uba kamar yanda na gaya maka tun shekarun baya, amma yana da hali irin wanda ya fi zinariya daraja. Ka taimaka a duba takardunsa ba don alfarma ba, sai don cancanta da tabbatarwa irinsu ?asarmu ke bu?ata, dan an gina wannan burin a zuciyarsa tun kwakwalwar sa na jinjira ita da zuciyarsa. Kai da kanka zaka tabbatar da hakan kuma kayi alfahari da gina rayuwar wannan yaron akan wannan aikin watarana in sha ALLAHU .
? ? ? ? Cikin jinjina kai Major Abdullahi ya ce,  In sha ALLAHU Yaya, nama al?awarin baza'a samu kowace irin matsala ba. Dan a takardun yaron kawai na tabbatar shi Win mai ?wazo ne. Sannan a wannan zaman awannin da nayi da shi na fahimci abubuwa da yawa atare da shi masu girma da daraja. Kaje in ALLAH ya yarda zakaji labari mai daWi .
? ? ? ?  Alhamdullahi Na gode Abdullahi, idan kaimin hakan bazan gushe ba ina mai maka addu'a, domin kuwa ka taimakeni wajen cika al?awarin dana Waukama marayan ALLAH.
? ? ? Aranar suka koma kano akan za'a neme su...

><><><><><

? ? ? Bayan bincike da gwaji, an sake kiran Haysam zuwa interview a Kaduna, inda ya nuna basira, nutsuwa, da ilimi mai zurfi har ma jami an da sukai interviewn ya basu mamaki suka kuma yabama kwazonsa kwarai da gaske. Kamar wasa, sai sakamakon shigar NDA ya fito, sunan Haysam Abdul-rasheed Shehu ya fito cikin jerin waWanda aka Wauka. Kwatanta muku irin farin cikin da A'isha da Haysam da ?an uwansa harma da Malam Sulaiman sukayi Sata lokaci ne a wannan gaSar, amma dan musamu mu wuce kowa ya ?iyarsa a tashi zuciyar kawai..

^^^^^^^^^^^^^

?? 3/12/1992 shirin tafiyar Haysam ya kammala zuwa NDA, inda A'isha tai ?o?ari matu?a ta haWa masa dukkan abinda aka bu?ata daga iyaye. Ta ?ara tisa masa nasihar da a kullum bata gajiya dayi masa shi da ?an uwansa. Ranar farin ciki ga Haysam ga ahalinsa, ranar kuma kuka da alfahari.
? ? ? Haysam ya shirya cikin shigar kamala, ya goya jakarsa a baya. Cikin nutsuwarsa yazo gaban Mammah ya dur?usa, gefe A'isha ta kauda kanta kaWan tana ?o?arin maida ?wallar da suka cika mata idanu, kafin ta dawo da fuskarta garesa tana kallonsa zuciyarta cike da ?auna da fargabar rabuwa da shi, tunda ta haifesa bai taSa yin nesa da ita na abinda ya wuce sati biyu ba. Dama dai Mama Yakura ce kan Waukeshi suje Maiduguri suyi kwanaki sannan tana raye. Tunda kuma mutuwa ta Wauke mata ita ta Wauke mata mahaifinsu kuma bata taSa nesa da su ba, shine abokinta a yanzu, shene babban Wa, shine ?ani, shine yaya, shine uba ga ?annensa, shine ?awa, dole taji raWaWin nesantarsu da zai yi, sai dai bazata iya da?ile hakan ba dan tana matu?ar son shima ya samu cikar burinsa ya kuma cika burin mahaifinsu. Addu'a ta sake masa mai ratsa zuciya cikin danne kuka.  ALLAH ya sa wannan tafiya ta zama alheri a garemu baki Waya. Ka tuna da addu a, ka tuna da asalinka. Idan ka zama soja, ka zama soja mai gaskiya.
? ? ? Karo na farko Haysam ya kalleta da idanunsa da sukai jaa, murmushi yay mata irin na kwantar da hankali da ?arfafawa.  Mammah in sha ALLAHU zan yi kamar yadda kike so koma fiye da hakan. Zan zama soja don na kare ?asata da al'ummar kamar yanda kika zame mana garkuwa bayan rasa iyaye guda biyu, zanyi ha?uri koda banci ba domin wasu suci, zan sadaukar da farin ciki na dan wasu suyi, zanyi komai da ?arfin zuciya da ?arfin addu'arki. Zan kiyaye dokin UBANGIJI da biyayya ga umarnin MANZONSA.
? ? ??  ALLAH yay maka albarka .
Ta faWa kuka na ?wace mata. Shima idanunsa sun sake yin jazur sai dai babu hawayen. ?annensa ma duk sun masa addu'a. Cikin share hawaye Bilal ya ce Dada kada ka daWe fa... ka dawo da wuri!
? ? ? ??  In sha ALLAHU Bilalu na zan dawo da wuri, kai dai kaimin addu'a . Yay maganar cike da kulawa yana rungume yaron. Suma sauran duk sai suka matso suka rungume juna,  Ku kula da Mammah, kada ku barta tayi tunani ko damuwa. Kada ku sakata yawan magana ko Sacin rai. Duk wanda ya dinga mata laifin da zai Sata ranta babu ruwana da shi kona dawo, sannan bazan masa tsarabar komai ba .
? ? ? Kawuna suka shiga Waga masa. Ya Wan jajja musu hanci cikin so da jin kewarsu. Sai suka shiga yin dariya ga hawaye. Shima murmushi yay musu mai sanyi, kafin ya mi?e, kallo Waya yay Mammah yaga yanda ta du?ar da kai yasan kuka take, sai ya fice da sauri shima nashi idon na tara hawaye...

>>>>>>" <<<<<<<

? ? ? *_NIGERIAN DEFENCE ACADEMY, KADUNA_*

?? Haysam ya fito daga motar da jakarsa a kafaWa, jakar da Mammah ta zuba masa kayan da duk ta tanadar masa, bakinsa da addu'a ya shiga bin tarin sabin Waliban dake cike tam da ?ofar gate Win tamkar ba safiya ba da kallo. Yaron da aka saba gani cikin damuwar maraici da wahalhalun rayuwa da yawan shiru, yau zuciyarsa cike take da jin daWin samun cikar buri, da alfahari. Jinsa yake a yau tamkar ya fara wata sabuwar rayuwa, inama Abiy na raye ya gansa a wannan mataki, inama idan ya Waga kai ya faWa domin shi ace kunnensa zasu iya jinsa...
? ? ? A bakin ?ofar gate Win akwai jami an soja dake tsaye. Kowanne sabon Walibi sai an bincika jakarsa, an duba sunansa a cikin jerin waWanda suka samu shiga. Haysam kuwa na cikin ?an farko-farko da aka fara kira. Dan dai-dai yana tunaninsa akan Abiy aka ambaci cikakken sunan nasa Haysam Abdul-rasheed Shehu. A karo na farko sai zuciyarsa ta buga da ?arfi, goshinsa ya Wan tara zufa, amma cikin dakewarsa ya Waga kai da girmamawa ya amsa da nufar inda ake bu?atar ganinsa yana Waukar matakin soja na farko a rayuwarsa, shekarar farkon balaga dan yanzu yana da 17years a duniya da wasu watanni. A dai-dai nan kuma yay sallama da Malam Sulaiman da yay masa rakkiya. Hannunsa Malam Su ya ri?e cike da so da ?auna da jin alfaharin cika masa al?awari, fuskarsa da murmurshi ya furta,  ALLAH ya tsare ka Wana, banda wasa, banda biyema abokan banza, ka zama jarumin da ?asa zatai alfahari da kai ba kuka ba .
? ? ?? Kan Haysam a ?asa cike da girmamawa ya ce,  In sha ALLAHU Malam zakayi alfahari dani kai da su Mammah..
? ? ??  ALLAH ya tabbatar da hakan Haysam . Malam Sulaiman ya faWa yana sakar masa hannu da shafa kansa.....
? ?
Haysam na shiga ciki sai duniya ta canza. Cikin nutsuwarsa ya shiga layin ?an uwansa da wasu sojoji suketa duba su, suna karSar takardu, suna aika su wurin medical check-up.
Ana duba nauyinsu, tsayinsu, tare da basu lambar cadet. Sannan suka bi jerin sabon layin da ake rabawa sababbin Walibai uniform da kayan horo. Sai amsar uniform Win suke kuwa cike da farin ciki da zumuWi, sai manyan takalma da sauran abubuwan bu?ata na kwanakin farko.
? ? ? Sai da aka kammala musu komai daya dace a wannan lokacin Sannan aka tafi mataki na gaba. Bayan karSar kaya, an kai su wani babban hall mai Wauke da gadaje da yawa da zasu iya kai 200 ma. Kowane gado akwai katifa sabuwa fil. Nanfa bakunan wasunsu suka shiga washewar farin ciki. Wasu suna dariya, wasu suna kallon juna da murmushi. Sha?iyan ciki masu rawar kai suka fara rawa suna Waga hannuwa cikin nishaWi, yayinda wasu suka fara kiWa da ?arfen gado wasu cokula da plate da aka raba musu.
? ? ?? Dariya suka bama Sojojin da ke kula da su, dan haka suka tsaya suna kallon suna murmushi kawai. Dan basu da zaSin daya wuce su bar su suyi farin cikin farko kafin a fara horo na gaskiya, a wannan gaSar idan ma ance suyi wannan nanayen bazasu yin ba. Duk wannan abin da

21 / 36