KIDA A RUWA HAUSA READ NOVELS BY BILLYN ABDULL.doc

Author :  BILLYN ABDULL Category :  Hausa Read

Chapter   14 / 36

39K to 42K   out of 106.7K words

tsohon Wakinsu dake soron gidansu ya kwanta a can. Abinci ma aikowa yayi aka amsa aka kai masa can duk da kuwa daga gidansu aka aiko. Hajjaju amarya Indo ba jiya taji daWin gudu ba, yau ma ana yin sallar magriba ganin ya shigo yace zaiyi wanka a lokacin dan bai samu yayi da rana ba, yasan kuma bazai iya barci ba in baiyi ba. A Warare takai masa ruwan bayi, yana shiga ta sulale zata gudu, sai dai ta samu ?ofa a rufe ta gidan. Kamar zatai kuka ta juyo ta dawo. Amma mi sai dabarar shigewa ?asan gado tazo mata. Dan haka sauri-sauri ta shimfiWa tabarma ta kawo wasu ?orai da babu komai tasa a gaba-gaba ta yanda bazaka kawo da mutum a ?ar?ashin gadon ba ta shige abinta ta kwanta ko tsoro ma bata ji.
? ? ? ALLAH sarki bawan ALLAH Abdul-rasheed, hankalinsa kwance ya fito yasan dai bazata iya buWe gidan ba, koda ya shigo Wakin bai ganta ba yayi tunanin tana inda ta ma?ale Wazun da asuba. Sai ya ajiye kayan wankan yaje ya lallasota ta dawo, amma mi babu ko alamarta, da sauri ya nufi soro kofa a rufe yanda ya bari, ya sake dawowa ciki neman duniya ba A'isha. Mamaki da tsoro suka kama shi, to ta ina tabi ta fita? (Katanga), zuciyarsa ta ayyana masa. Zama yay yana dafe kansa kawai, dan wlhy kunya yake ji bazai iya zuwa gidansu ba yau kuma. Idan jiya basu gano shi ba ai yau sai su gane. Haka ya ha?ura ya mi?e ya tafi massalaci sallar isha'i. Duk abinda yake tana jinsa, daya fita kuma bata kawo a ranta ya fito ba ta fice gidan ta cigaba da kwanciya a ?ar?ashin gadon har barci yay awon gaba da ita anan.
? ?? Bayan sallar Isha'i Abdul-rasheed ya dawo, haka ya zauna shiru zuciyarsa na masa sa?e-sa?e, gefe yana ?alubalantar kansa da rashin ha?urinsa, dan ?ila da bai mata abi??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nda yay matan ba da hakan bata faru ba. Ga tsaraba ma ta kasa zama ta duba sam. In sha ALLAHU zai daure ya ri?e kansa ya bita a hankali. Da wannan tunanin ya Singire. Da asuba fitsari ya kama A'isha har yana neman zubowa, dan haka ta fito cike da sukur-sukur Win daya tada Abdul-rasheed, dan haka ya haska fitila da tunanin ko Sera ne ya shigo musu. Amma yana kunnawa ya haske A'isha na fitowa a ?asan gado. Mamakin duniya ya ishe sa, ya zuba mata ido kawai. Itako tayi tsuru-tsuru kanta a ?asa tana matse ?afafu dan fitsarin neman kufce mata yake. Fahimtar hakan da yayi ya saka shi sakin murmurshi, muryarsa a sau?a?e yace,  Amshi fitila kije kiyi .
? ?? Da sauri ta amsa kuwa ta fice. Shima ya mi?e ya sauka a gadon yana sauke ajiyar zuciya. Amma lallai yarinyar nan ta cishi wasa jiya. Yanzu nan tana ?asan gado dama duk bulayin daya dinga yi. Wato ita dai mace duk ?an?antarta akwai wayo da dabara. Da wannan tunanin ya fito da buta a hannu, baice mata komai ba ya Wauki fitila data ajiye zata fara alwala ya wuce bayi, sanda ya fito ta gama zata wuce. Dan haka cike da lallashi ya ce,  Dan ALLAH ki zauna a gida to kada kije ko ina na dawo na baki tsarabarki da sa?on Inna, kada yazam akwai abin lalacewa a ciki kinga zai lalace .
? ?? Kanta dake ?asa ta jinjina masa. Sannan sum-sum ta shige ciki. Shima yay alwala ya fita. Koda ya dawo da wannan buWe tsaraba yaja ra'ayinta, har hantsi ya fito ya fita ya sayo mata shayi, sai kuma ga kayan kari Inna ta aiko. Da lallaSa, da lallashi da kwantar da kai ya samu wannan yini dai aka yi shi lafiya. Da dare kuma ya kafa ya tsare ya nuna mata shi tayi duk yanda take so. Ganin ya?i kulata da abinda take gudun a yinin ma ko kusa da ita bai zauna ba balle ya taSa mata hannu sai ta ha?ura ta kwanta a gadonta, amma acewarta da ido Waya zatai wannan barci. Da yake shi barcin ya fita wayon bata ma san ya kwasheta ba har wanda take tsoron ya zauna a bakin gadon kusa da ita yay mata addu'ar barci sannan ya koma nashi gadon. Wannan sabon yin biris daya Wauka ya kawo masalaha a tsakaninsu, itama ta sake jiki suka koma kamar da. Sai dai kwana kusan shida kuma yaji fa yana neman halaka, a daren ya kasa ha?uri ya sake maimaita na wancan daren, koma muce abinda yafi na wancan daren dan ya sameta fiye da waccan ranar, sai dai kuma ta fitgice masa dole ya barta batare da cimma buri ba. Daga nan ne fa ta sake birkice masa. A daren washe gari kuwa bata kwana a gidan ba, ta sake gudawa gidansu cikin su Nana ta kwana. Ita kanta Innar da su Nanar basu farga da ita ba sai da asuba da Inna ta tashesu suyi salla. Rasama abin faWa tayi, yau ma sai tace su Alawiyya su rakata gida kawai.
? ? ? Kwanakin da suka biyo baya har huWu A'isha bata daina yo tsere ba. Abdul-rasheed kuma ya zuba mata ido, hasalima ya koma maida hankalinsa batun buWe wajen Winkinsa ya ?yaleta. Hakama Baba yana sane A'isha a gidan take kwana, amma bai ce komai ba sai dai yayi murmushi kawai. Koda Inna tai masa magana a cikon kwana na huWun sai cewa yay,  To mizance, tunda shi bashi da ha?uri da kawaicin barin yarinya ta sarara kaWan ma kenan. Ke kuwa naga kema haka kika dinga yi min Karima, ?arshe sai da Baba ya rakoki da tsumagiya gidan nan saboda can kike zuwa.
? ? ? ? ?  Ai kai ka jika Malam, ana maganar arzi?i saika dinga sakko wadda ba'a tambayeka ba. Amma ka bani dabara nima da tsumagiyar zan korata yau. Ina laifin yaron nan ai yayi kawaici ma. Aure wata shida haba ai a yaba masa. Abdul-rasheed da ha?uri da zurfin ciki. Su sauran ?an uwansa wa yayi wannan ha?urin. Tijjani ma da yafi kowa rashin ta idonsa ko tsallake rana yayi .? Haka ta fita tana sababi. Baba kuwa sai murmushi yake abinsa kawai...

? ? ?? Washe gari kuwa Inna ta shiryama A'isha tsaff, dan yanzu dai sune iyayen tunda babu wani nata a kusa. Kuma a wannan zamanin nasu na adalci Wa na kowa ne. Babu wani surukutar mugunta ga matar Wa da uwar miji, yanda suke ma ?a?ansu haka suke ma matan ?a?ansu saboda adalci da ?ya?y?yawar zuciya, haka suma surukan suna Waukar iyayen miji iyayensu ba irin na yanzu ba da suke ganinsu kamar koshiyoyi. Kamar ko yanda ta saba ana cikin sallar isha'i sai gata ta shigo soron gidan da sanWarta. Caraf Inna dake a soron ta dalleta da Torchlight, A'isha tai tsaye cak tsuru-tsuru da idanu, sai kuma ta du?a tana gaida Inna dake tsaye kawai tana kallonta. Batare da Inna ta amsa mata ba ta ce,  Juya muje .
? ? ? Kallonta A'isha tayi kamar zata fasa kuka, Inna ta haWe fuska kuwa ciWin-ciWin. Sum-sum ta nufi ?ofa dan tasan dai yau ruwa ya ?arema Wan kada kam. Haka Inna ta sata a gaba har gida da ?ar tsumagiyarta a hannu, badan ta daketa ba sai dan ta tsoratata. Karo na farko da Inna tazo gidan kenan, suna isa ?ofar Waki taci karo da buta, Wauketa tai ta maida gefe suka shiga Wakin. A mamakinta sai suka samu Abdul-rasheed a ciki kwance a tsakar Waki kan tabarma. Ashe ma yana gidan ta fita, baida lafiya, amma saboda wauta saita wayance da Waukar buta kamar zata fitsari daga nan ne ta sulale, butar ce Inna taci karo da ita yanzu da suna shigowa. Ganin Abdul-rasheed Win a Wakin kuma yasata fahimtar ma'anar zaman butar a waje. Tashi yay da ?yar cikin dauriya yana ma Inna sannu da zuwa. Inna dake binsa da kallo ta ce,  Lafiya kuwa ana salla kana gida Abdul-rasheed? .
? ? ??  Ba komai Inna kawai banjin daWi ne, shiyyasa ma ban shigo gidan ba Wazun da yamma .
? ??  Subahanallahi, amma shine ja'irar nan ta sulalo ta taho can. Nikam ya zanyi da A'isha jama'a. Mijinki na kwance a gida babu lafiya amma kina guduwa wani waje. A'isha wane haline wannan? Idan baki taimaki mijinki ba wa zaki taimaka. Kina son ki mutu a saki wuta ne? Ko kuwa na shirya naje Kano na gayawa Innarki halin nan da kike yi? .
? ? ? ?? Cikin sauri A'isha dake kuka ta shiga girgiza kai.  Dan ALLAH Inna kiyi ha?uri bazan ?ara ba wlhy na tuba .
? ? ??  A'a nasan zaki ?ara A'isha. Wata nawa ana abu guda. Ai gara dai na tafi Kanon nan tunda mu baki Waukemu iyaye ba. Shima Abdul-rasheed Win ne ya ?yaleki, sai kace wadda tafi ?arfinka. Kafi son kaita fama da ciwo sai ka halaka kanka ne......
? ? Inna dai nata sababi ta inda take shiga bata nan take fita ba. Taima A'isha dake dur?ushe tana kuka, taima Abdul-rasheed dake zaune kansa a ?asa kunya da ciwo duk sun dabaibayesa. Sai da tai musu tas sannan ta wuce tana sake jaddama Ai'sha idan ta sake ganin ?afarta a waje koda da rana ne ma zuwa can gidan saita zane ta, kuma sai ta tafi Kano ta sanarma Innarta. A'isha tasan aka sanarma Inna ai taga boni, dan haka ta sake rikicewa, dan Innarsu akwai zafi sosai tana da faWa, duk da tana jansu a jikinta idan sukai ba daidaiba bata raga musu, balle ma ita Win nan da take kamar ?ar fari. Dan kafin ita Inna ta haifi yara kusan biyar suna rasuwa ne itace ta fara zama, a tsakanin ta da Bashir ma wani ya rasu shiyyasa ta bashi kusan shekara biyar........
'

_Zaku sameshi a waWan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER *_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ?asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya=?G?_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: =?G?_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number =?G?_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number=?G?_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*

*_Typing=???_*








*_>???KI?A A RUWA.....!!>???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._



_Chapter 17_

__________________

_A KANO KI KE& ? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ?iyar yin girki gashi zaki yi ba?i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ?asar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZO?O mai za?i, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ?ara lafiya, akwai wanda bashi da za?i domin masu ciwon sugar da masu gudun ?iba._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ?asan rubutun nan._

INSTAGRAM
=?G? https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr
CALL/WHATSAPP
=?G? wa.me/2349030398006

TIKTOK
=?G? https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1




Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.d'?d'?>???
__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Bayan ficewar Inna Wakin yay shiru, sai shashshekar kukan A'isha daya cikashi, shi dai Abdul-rasheed yana zaune har yanzu kansa a ?asa yana saurarenta. Sai da yaga ba dainawa zatai ba sannan ya Wago cike da ?arfin hali dan da gaske baida lafiya ya zuba mata idanunsa dake jajur irin na mai ciwo. Muryarsa da sanyi sosai ya ce,  Kibar kukan nan ya isa haka, ko kina son kanki yay ciwo ne? .
? ? Kanta ta girgiza masa alamar A'a. Ya ce,  To share hawayen ya isa. Kin daiji abinda Inna tace. Ke ko tsoro ma ba?yaji kiyita kai kawo a tsakanin dare. A'isha auren soyayya mukayi bana ?iyayya ba. Mu da kanmu muka zaSi juna muka kuma so mu zama ma'aurata ba haWamu akai ba balle muce an mana auren dole ne. Kina da muhimmancin da bazan iya bari wani ya cutar dake ba balle ma ni kaina. Abinda kike gani yana faruwa tsakanina dake shi ne aure. Ina ga dole zamu fara karatu daga gobe, ba karatun Alkur'ani kawai kike bu?ata ba a rayuwa da ibada, duk da Alkur'ani yazo mana da komai, amma dole sai mun haWa da hadisi sannan zamu san su wanene mu da abinda ya kamata muyi. In sha ALLAHU hakan zai sa ki fahimci minene auren ma kansa .
? ? ? ?Kanta ta jinjina masa, sai kuma cikin rawar murya ta ce,  Kayi ha?uri bazan sake ba. Kuma dan ALLAH ka bama Inna ha?uri, sannan kace dan girman ALLAH kada taje Kano ta faWama Innata, ALLAH idan ta gaya mata zata iya zane ni, kuma tayi fushi da ni .
? ? ? ?aramin murmushi yayi, a ransa yana ayyana ga tsoro ga rashin ji. A fili kam sai yace,  Shike nan zan bata ha?uri. Nikam baki min laifin komai ba. Tashi ma kije ki wanke idonki. Kinyi sallar isha'i kuwa? .
? ? ? ?  A'a .
? ?  To maza yo alwala kizo kiyi. Sai ki matsa min lemon tsamin can a ruwan zafi ai da saura a cikin flaks Win ko? .
? ?  Eh, tun wanda kasha shayi Wazun ba'a ?ara Wiba ba ai .
? ? Yauwa to yi sallar sai ki haWa min wani shayin nasha kinji. ALLAH yay miki albarka ya shirya min ke ki daina haura katanga, dan nasan yanzu dai Shatuna ta girma, ta girmi haura katanga ta barma ?an baya ko? .
? ?? Kanta ta jinjina masa, sai kuma ta ce,  Nifa bana haura katanga ALLAH. Kullum ta ?ofa nake fita .
? ? ? Dariya yayi yanzu kam. Ya ce,  Oh oh matar Abdul-rasheed tafi Abdul-rasheed wayo .
? ?? Dariya tayi itama tana rufe fuska da tafukan hannunta. A haka ta fita a Wakin, shiko yana binta da kallo da murmushi...

? ?? Bayan A'isha tayi salla ta haWa masa shayin lemon tsami ya sha. Ita kuma ta haWa mai madara dan tace bazataci tuwo ba. Shi kuma bazai iya fita sayo mata nama ko kifin daya saba kullum ba. Dan bayi ma da ?yar ya iya fita yaje. Hira ya dinga janta da shi yanda suka saba. A hankali ta saki jiki tanata masa dariya, dan labarin ?annenta su Bashir yake ta bata da yaran gidan su Nasiru. Sai da yaga ta fara hamma sannan yace taje ta kwanta.
? ? ? Maimakon ita shi zaman lalubo litattafan da zai fara mata amfani da su ya shiga yi. Dan dama yana da burin hakan a kanta tuni. Sai da ya ajiye komai sannan yay tashi kwanciyar a ?asa ma yau, dan bai hau gadon ba. Washe gari kamar yanda yay al?awari hakan akai. Da hantsi bayan ta kammala aikin gida ya fita ya dawo sukai zaman karatu. A Sangaren Alkur'ani kam A'isha Alhamdullah, sai gyara na abinda baza'a rasa ba dai. Dan haka ya fara mata da sauran littatafai. Abin nasu kamar wasa sai ya fahimci tana Wokin karatun, cikin kwanaki kaWan kuma ta maida hankali. Har takai yanzu karatun ma yafi cinye lokacinta fiye da biyema yara masu shigo mata da rana. Sun ja kwanaki suna karatun yana buWe mata komai yanda zata fahimta da ?yau, abinda yake na kunya taita sinne kai sai yayi kamar bai ganta ba ma, a dalilin wannan karatun ya fahimci A'isha ko jini bata fara ba ashe. Eh lallai aiki babba a gabansa, dole kam ta dinga masa gudun fanfala?e ashe. Ganin tana fahimta ya haWa mata da karatun boko, sosai al'amarin ya fara bashi mamaki, dan gaskiya Alhamdullah tana da brain na fahimtar abu da wuri, gata kuma da nacin son karatun.
? ? ? Satin su uku da fara wannan karatu al'amarin UBANGIJI A'isha ta samu ba?uncin prioud Winta a bazata, babu ciwon mara babu komai. Da yake ya karantar da ita hakan sai bata ruWe ba, sai ma matsananciyar kunya data sata Soye masa, ta shiga kici-kicin gyara kanta ita kaWai. Sai dai ba'ai nisa ba tun a yinin ya ganota. Haka ya zaunar da ita ya sake mata dalla-dalla akan abinda ya shafi jinin haila, ya kuma sake koya mata yanda zata dinga tsaftace kanta da ?yau. Wato ilimin addini duniya ne, dan kuwa babu mace ?ar gata kuma sarauniya irin mai ilimin addini, mata mu farka dan ALLAH musan kammu, ba'ace karki boko ba, amma ki tuna shifa bokon nan amfaninsa nada iyaka, shiko wannan da muke Wauka ?auyanci da shine za'a mori rayuwa mafi tsada dake can gaba garemu. Ba zaki gane wannan zancen ba sai randa mala'ikan mutuwa ya ?wan?wasa miki ?ofar amsa kiran ALLAH wlhy=?-?.
? ? ? ?? Kwanaki uku A'ishatul-humairah tayi, a kwana na huWu tai wanka abinta ta koma salla, sai da ta koma sallar ne ma Abdul-rasheed ya fahimci ba?o dai ya tafi, ya zaunar da ita ya mata tambayoyi akan yanda ta tsaftace kanta. Tana Soye-Soyen fuska ta sanar masa da komai. Shi dai nashi dariya ne. Fara Winkinsa da samuwar aikin koyarwa ta rage masa zaman gida, sai dai kuma a Wan tsakanin ya gama shiryama tsuntsuwarsa. Dan kuwa a wani dare na juma'a ya maida Shatunsa cikakkiyar mace. Ya dai sha rigima mai saka ciwon kai da rakinta. Haka yayta lallashi da riritawa, dan sai da ya koma komai shike mata a wannan yinin. Ya kuma sanarma Inna cewar A'isha ta kawo mutuncinta,

14 / 36