DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Tknovels

Chapter   7 / 39

18K to 21K   out of 116.4K words

su nan wasu sun rasa hankalinsu, sun rasa tarbiyya da kamun kansu, sun rasa kyawun jikinsu wasu ma sun faɗa harkan barace-barace akan titi wasun su ma sun haukace. Duk waɗannan hanyoyin ba ta zaɓa ta bi ɗaya daga cikinsu ba ta zaɓa ta fito ta nema aiki don ta rufawa kanka asiri ta kuma ci halaliyarta. Saif irin waɗannan yaran su ya dace a ringa taimakawa".

Tun da ta fara maganar ya yi shuru yana kallon ƙasa bai ɗago kansa ba har ta gama maganar ta kai aya, kafin ya furzar da dogon numfashi a taƙaice ya furta"shikenan Anty amma dole zan yi bincike akan ta, idan na same ta da wani aibu tabbas dole a sauya ta a nemo wata".
"To ubana yadda ka ce haka za a yi". Sadda kai ƙasa ya yi yana ɗan sosa ƙeyarsa ya ce"Anty ni fa ba haka nake nufi ba, zan tafi wajen aiki sai na dawo don Allah a kula da yaran nan".
Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce da shi komai ba ya juya ya fice sai da ya fita kafin ta ce da ni"sai kin yi haƙuri da Saifullah haka yake, miskili ne na buga wa a jarida. Yana da wuyar sha'ani ga wanda bai san halinsa ba amma da zaran kun saba da shi za ki fahimci yana da daɗin zama da sauƙin kai uwa uba yana da tausayi da son taimakawa na ƙasa da shi".

Kaina kawai na iya jinjina mata don bakina ya yi mini nauyin da na kasa cewa komai, ta yi gaba ina biye da ita muka zagaya ko'ina a cikin gidan nan, kicin ɗinta tsaf-tsaf da shi ga wani uban faɗi da girma. Girmansa ya kai a haɗa falo da ɗakinmu da muka yi rayuwa a cikinsa kafin Abba ya rasu.

"Hajiya ban iya amfani da irin wannan abubuwan na zamani ba". Na yi zancen ina ƙara ƙare wa girman kicin ɗin kallo. Ta dafo kafaɗana tare da faɗin"a hankali zan koya miki komai idan na sama lokaci, kafin nan za ki na yi shara da mopping ɗin ko'ina a cikin gidan nan, amma ban da harabar gidan iya ɗakuna da falo ne sai wanke banɗakuna".
"Na gode sosai".

"Ki godewa Allah, ni yanzu zan fita wajen sana'ata amma ba zan daɗe ba zan dawo. Don haka za ki zauna da tare da Altine da su Aryan kafin na dawo". Kaina na jinjina mata kana na ce"a dawo lafiya Allah ya tsare ya ba da abin da aka fita nema". Cike da jin daɗin addu'ata ta amsa da faɗin"Amin ya Allah". Muka dawo falo ta shaida wa Altine za ta fita ta yi mata addu'ar a dawo lafiya, ta kwashe Aryan da Ayan suka yi mata rakiya har waje kana suka dawo. Ina zaune a cikin falon Altine ta dawo daga rakiyar da suka yi mata muka kalla juna ta banko mini harara kamar idanunta za su faɗo ƙasa, ba ta zauna a inda nake ba sai ta ja gefe ta zauna suna wasa da su Aryan, haka na ci gaba da zama shuru babu wanda zan yi magana da shi balle taɗi. Muna zaune a wajen har aka yi ƙiran sallan zuhur Altine ta tashi da yaran suka hau sama babu jimawa sosai suka sauƙa. Za ta wuce su fita na dakatar da ita ta hanyar faɗin.

"Anty ina zan sama ruwa na yi alwala na yi salla kar lokaci ya ƙure?". Ta watsa mini wani kallon uku saura kwata kan ta mayar mini da martani a zafafe"tun ɗazu da na tashi na je na yi sallan ba ki yi min magana ba sai yanzu? Ai na yi tunanin ba za ki yi sallar ba ne". Na rusunar da kaina ƙasa ina ci gaba da sauran abin da take faɗa daki-daki.
"Sai ki fita ta ƙofan can za ki ga fanfo ki yi alwalan ki dawo ki yi sallan a nan".

"Sallaya fa?".

"Ki yi akan ɗan kwalinki don ban yarda da tsarki da tsaftan jikinki ba". Tana gama faɗin haka ta ja hannun yaran suka fita, ƙofar da ta nuna mini na bi na yi alwalan na dawo na shimfiɗa ɗan kwalina na yi sallan akai. Ina raka'ar ƙarshe suka dawo suka zube akan kujera, na iddar da sallan na shafa addu'ar da na yi kana na juya ina duban ta"Anty akwai aikin za da a yi ne?".

"Ban sani ba wannan kuma sai dai ki jira matar gidan ta dawo, sai ta yi miki wannan bayanin da bakinta".

Tun da ta yaɓa mini wannan maganar ban ƙara cewa da ita komai ba, Ayan ya soma jan hannunta yana cewa"Anty ki tashi mu je ki yi mana alwala mu yi salla, Uncle Saif ya ce idan an ƙira salla mu na yi kar Allah ya ƙona mu a wuta". Hankaɗe shi ta yi ya faɗi bakinsa ya saki hannun kujera.
"Wai ku kam wasu irin jarababbun ƴaƴa ne haka? Babu dama ku ga mutum ya zauna yana huta wa sai kun addabe shi da jaraba, ku dai ku na gaba da ku ganni ina zaune ina hutawa. An gaya muku ni ɗin jakar uwarku ce ko ta ubanku ko kuma ni inji ce da ba na buƙatar hutu? Ubanku na can wata uwa duniya na kuma ta tsallake ku ta tafi neman duniya ni da ban haifa ba an bar ni da jalala".
Ta yi zancen tana miƙewa ta bar cikin falon, ganin yadda bakin Ayan yake zubar da jini ya tilasta mini tashi na je na ɗago sa, don tun da ya faɗi ya kasa tashi daga wajen. Ƙofar da na bi na je na yi alwala nan na nufo na wanke masa bakinsa sannan na cire masa rigarsa don ita ma ta ɓaci da jini muka dawo cikin falon, na zaunar da shi akan kujera kusa da ɗan uwansa na je na ɗauko mopper na gyara wajen.

Na zo na zauna a kusa da ni ina duban Ayan da yake ta sauƙe ajiyan zuciya akai akai. Na riƙo hannunsa kana na ce"a ina ake ajiye muku kayanku?".

"A ɗakinmu yake".

"Ina ne ɗakin nakun?". Da hannunsa ya yi mini da wata ƙofa ya ce"wancan ne". Na tashi na shiga komai guda bibbiyu ne a cikin ɗakin kala ne kawai ya bambanta su. Na buɗe sit na ɗauko masa wata riga na juya zan fita na hango Altine tsaye a ƙofar ɗakin ta naɗe hannayenta a ƙirjinta tana yi mini wani irin kallon da na gaza cewa ma'anarsa.

"Me ye kike yi a nan?".

"Riga na zo ɗaukawa Ayan".

"Saboda ke kike kula da su ko?".

Da saurina na ce"A'a Anty na jikin nasan ne ya ɓaci da jini shi ne na cire masa na zo ɗauka masa wani." Ina rufe bakina ta ƙariso cikin ɗakin ta wafce rigar daga hannuna.
"To ba zai sa wata rigar ba, haka zai wuni ba riga tun da an sa masa ya ɓata. Ai ni ba jakar gidansu ba ne da kullum ba ni da aiki sai hidimarsu".

Na yi mutuwar tsaye ina bin ta da kallo ganin yadda ta zage tana zazzago masifar babu kwama balle fulsutop. Cike da maɗaukakin mamaki na ce"amma na yi tunanin ai an ɗauke ni saboda hidimansu. To me ye ba za ki yi aikin da ya kallafa akanki ba ko don ki ci halaliyarki?".
Ta riƙe ƙugu tana kallona"madalla tun da har kin fahimci cewa an ɗauke ni domin na yi musu hidima, to na haɗa ki da girman mai yi mana ruwa da ƙanƙara ki bar ni na yi aikina kar ki yi min shishshigi akan lamarin da bai shafe ki ba. Ki yi aikinki ni ma na yi nawa don haka ki fita daga ɗakin nan".

Ban kuma cewa da ita komai ba na fita daga ɗakin cikin tsananin mamakin da ya bayyana har a kan fuskata ina fitowa na ga har sun yi bacci akan kujerar sun manne da junansu. Na bi su da kallo cike da mamakin abin da Altine ta aikata gare su.
Na koma gefe na zauna a inda na yi salla na kifa kaina akan gwiwana ban yi aune ba ni ma bacci ya kwashe ni don daren jiya ban samu na yi bacci mai kyau ba. Ƙiran sallan asr shi ya tilasta mini tashi na ina karanto sunanyen mahaliccina tsarkaka guda ɗari babu ɗaya, na fita na je na yi alwala na zo na yi zama, tun ina sallan nake jin cikina yana kukan yunwa har na iddar na shafa addu'ar da na yi.
Na kafe yaran da ido ina ta kallonsu tun ranar farko da na fara tozali da yaran na ji sun shiga raina can ƙololowa, mussamman yadda na ga suna da nutsuwa sosai kamar ba yara ba sannan ba su ƙiriniya ko kaɗan.
Ban ji sallamarsa sai gani na yi ya zauna kusa da yaran yana shafa kansu, na yi saurin gyara zamana rare da ɗaukan ɗan kwalina na ɗaura a kaina.

Na rusuna ina faɗin"sannu da dawowa ranka ya daɗe". Bai amsa mini ba ya ci gaba da shafa kan yaran ya kai hannunsa wuyan Ayan babu shiri ya waigo yana kallona haɗe da faɗin"me ya same shi na ji jikinsa da zafi gau haka?".

Na yi ƙasa da idanuna na rasa me ye zan ce da shi sai kame-kame nake yi, kafin na kai da cewa wani abun Altine ta fito fuskarta kamar gonar auduga bakinta har kunne ta zo ta zube a gabansa"Barka da dawowa Alhaji ƙarami sannunka da shigowa".
Bai amsa ba ta ya jefa mata makamamcin tambayar da ya yi mini.

"Me ya sa Ayan na ji jikinsa da zafi haka gau, kuma jikinsa babu riga?".

Ta ɗago kai muka haɗa ido da ita ta yi hanzarin kawar da nata tana faɗin"sun yi wasa a baya ne wajen bayin shuke-shuke shi ne ya jiƙa rigar, na cire masa na shiga domin ɗauka masa wani kuma sai na fito na tarar ya yi bacci. Ni kuma ban son tashin su shi yasa ban ɗaga sa ba".

Ya cije leɓansa"sun ci abinci sun yi salla?".

"Duk biyun sun yi kafin su kwanta wannan bacci da ka shigo ta tarar da su suna yi". Ya jinjina kansa yana miƙe wa tsaye"ki tada su ki yi musu wanka ki shirya su za mu fita tare". Yana dire zancen ya bi wata ƙofa ya bar cikin falon. Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ina duban Altine da take tayar da yaran ta riƙe hannunsu suka shige cikin ɗakinsu, na koma inda na taso na zauna gabaɗaya yunwa ta addabe ni, ina zaune a wajen ya fito ya sake shiga cikin wani farin sol ɗin yari haka nan ya bar kansa ba tare da ya saka hula ba amma da dukkan alamu ya gyara gashin don har wani ƙyali da sheƙi yake yi. Sai baza ƙamshi yake yi kamar wanda aka yi ɓari durom ɗin turare a jikinsa.
Ya nema waje ya zauna yana murza zoben da yake hannunsa ya ce"me ye sunanki?".

A nutse na furta"sunana Amatullah".
"A ina kike da zama sannan su waye iyayenki?".
"Mahaifina ya rasu mahaifiyata kuma ba na tare da ita yanzu, hasalima ni kaɗai nake zaune a garin nan". Ya ɗago ido yana duba na"faɗaɗa min bayanin ban ga ne ba".

Na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa kana na ce"ina zaman kaina ne bisa wasu dalili da suka tirsasa faruwan hakan".

"Mace mai zaman kanta, karuwa kenan ko kuma magajiya?". Da hanzari na ɗago ido ina kallonsa wanda shi ɗin ma ni yake kallo a ci gaba da maganan.
"Idan na faɗa ba daidai ba sai ki gyara min".
Na girgiza kaina"haka ne yadda ka faɗa". Fitowar Aryan da Ayan shi ya hana sa furzo da zancen da ya yi niyya ya tashi tsaye ya je ya riƙo hannunsu suka fita, Altine sai washe baki take yi tana ɗaga musu da faɗin su kawo mata tsaraba. Ta wuce ta shige ciki ta bar ni a wajen, baƙin cikin kalaman da ya watsa mini ya sanya har sai da na zubar da hawaye, na ji duk son da nake ji wa wannan aikin da zumuɗin da na yi a lokacin da na yi katari da samun aikin duk ya fita daga raina. Tabbas ina son wannan aikin sai dai ba zan juri wulaƙanci wannan mutumin da kuma cin zarafin Altine a gare ni ba.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_____________________________________

Page 4️⃣9️⃣

Rawan da ƙafafuna suka soma yi shi ya tilasta mini zama dirshan irin na ƴan bori, ina jin ƙirjina yana bugawa da ƙarfi da ƙarfi. Ji na yi kamar na tashi na ruga da gudu na fice daga cikin gidan, tabbas na shiryawa dukkan ƙabuluaben da zai biyo bayan samun wannan aikin sai dai ban taɓa zaton zai zo mini a ranar farko ba.
Yunwan da ta ci gaba da ƙwaƙwulan ƴaƴan hancin cikina har ina jin mayar ana musayar kifiyoyi a cikin cikina.

Ba tare da na yi shawara da zuciyata ba na tashi da nufin tafiya don har cikin raina na ji cewar ba zan iya juran wannan cin mutuncin da tozarcin ba, ina fitowa harabar gidan na ga an wangale gate ɗin mota tana shigowa, na tsaye a inda nake har ta daidaita parking ta fito ta iso inda nake.

"Ya na ganki a nan?".

"Ranki ya daɗe zan tafi ne na ga yamma ta na ta gabatowa".

"A'a wani yamma ne ta yi yanzun dududu ma ƙarfe nawa ne? Mu koma ciki". Daga haka ta yi gaba ba tare da ta tsaya sauraron jin abin da zan faɗa ba, ba ni da wani zaɓi da ya wuce na bi ta kamar yadda ta buƙata, don haka na bi ta a baya a har cikin falon gyalen kanta ta yaye yayin da take zama akan kujera tana mayar da numfashi.
"Ki zauna mana". Amon sautinta da ya sauƙa a masarrafar jina ya yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina, na zauna a ƙasa a hankali na furta"sannu da dawowa ranki ya daɗe".
Cike da kulawa ta amsa mini da faɗin"yauwa Amatullah sannu ko? Ya na ji gidan shuru kaman ƴaƴan ba sa nan".

Kafin na kai ga ba ta amsa na tsinkayo muryar Altine daga bayana tana faɗin"sun fita da Saifullah tun da ya dawo ya ce a shirya su za su fita".
"Ina suka je?".

"Bai sanar da ni inda za su ba, amma ina kyautata zaton idan suka saba zuwa suka je. Ki na son wani abu a kawo miki ne Hajiya?".
Ta ɗan lumshe idanunta kafin ta ce"ba na buƙatar komai, ku fara shirye-shiryen girkin dare tare da Amatullah, don zan yi baƙi da daren nan akwai abokan kasuwancina da za su zo mu tattaunawa. Ku shiga kicin ɗin ku duba duk akwai abun da babu ko ake buƙarin a ƙaro sai ki zo ki sanar da ni".
Daga haka ta tashi ta haura sama wanda nake kyautata zaton a nan ɗakinta yake.

"To sai ki tashi mu je ko tun da dai kunnuwanki su ji abin da ta faɗa". Altine ta yi zancen cikin ɗaure fuska tana barin cikin falon, na yi wuf na tashi na bi ta a baya muka nufin kicin ɗin. Ta fara duddube-duddube can kuma sai na ga ta tsaya tare da dafe kanta ta juyo tana kallona.
"Sai ki je ki tambayo Hajiyar abin da za a dafa, in ta faɗa sai na duba na ga abin da ya dace a sayo ko wanda za a ƙaro".

"To".

Na amsa da shi a taƙaice ina ficewa daga cikin kicin ɗin, ɗakin Hajiyar na nufa na tsaya daga ƙofar ina yin sallama sai da na yi baki biyu a na ukun ta amsa ban shiga don a tunanina bai dace na shiga har cikin turakarta ba a matsayinta na matar aure, don na sha ji n ana cewa ɗakin mace sirrinta ne.
Ta fito jikinta ɗaure da farin towel da ya tsaya daidai gwiwanta, na rusuna na gaishe ta ta amsa mini cikin wani irin yanayin da gaba ɗaya na kasa gane kansa.

"Amatullah lafiya?".

Na ɗan duƙa kaɗan kafin na amsa mata cikin faɗin"daman Anty Altine ce ta ce na zo na tambaye ki abin da za a dafa". Ta ɗan shafo saman goshinta kafin ta ce"a yi fried rice, fine apple and coconut drink, sai a soya kaji a yi paper meat". Tana gama lissafa mini jerin gwanon abubuwan da za a yi ta koma cikin ɗakin tare da turo ƙafan ta rufe gaf, na ja ƙafana na koma cikin kicin na sanar da ita abin da ta faɗa, ba ta ce da ni komai ba ta ci gaba da abin da take yi.
Ta nuno mini wasu albasa ta ce na yanka su yayin da take ficewa daga cikin kicin ɗin, babu jimawa ta dawo muka ci gaba da aikin tare sai dai ba ta ce wa da ni uhm balle umm da zaran ta ba ni umarnin abin da zan yi ba ta ƙara cewa da ni komai. Aka kawo wasu kayan wanda duk dangin kayan marmari ne, ta ce na wanke su na yi kamar yadda ta faɗa aka zuba tuban da ayaba da inibi a cikin wani ƙayataccen kwanon gilashi, aka haɗa wanda za a markaɗa a yi lemon da za a yi. Muna gama aikin ana ƙiran sallan magrib har wani juwa ne yake ɗiba na tsabar yunwar da nake ji, idanuna suka yi ƙulu-ƙulu har wani dishi-dishi nake hangowa.

Muka haɗe komai muka jere shi akan dinnig table, ni na wanke kwanukan da muka yi amfani da su wajen gudanar da girki na tsaftace kicin ɗin tsaf. Kana na je na yi alwala a inda na yi alwala na nema wani ɗan wajen na shimfiɗa ɗan kwalina na yi salla, don ba na so na je falo Hajiya ta fito ta ganni ko kuma na iske ta a ciki na hana ta rawan gaban hantsi.
Sai da na iddar da sallan na tashi na shiga ciki kamar yadda na yi tsammani kuwa na iske ta zaune a falon tana latsa wayarta da yake hannunta. Na durƙusa na gaishe ta

7 / 39