Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Tknovels
dabbobin. Hasalima ai na ga ba wannan nau'in abincin aka girka ba". Tun kafin na rufe bakina take bi na da wani irin kallo tamkar za ta rufe ni da duka. Sai da ta tashi ta zauna daga kishingiɗewar da ta yi kafin ta soma amayar da balbalin wutar zancen da yake cikinta.
"Ke har kin isa ki tisa ni a gaba ki na tuhumata akan abin da kika gani a cikin ƙwaryan tuwonki?. Ina da karfin iko a cikin gidan nan fiye da duk yadda kike tunani da hashashe, idan har kika bari na juyo kanki na saka miki ƙahon zuƙa billahillazi hatta numfashi mai kyau ma sai a gagare yi a cikin gidan balle kuma wasu abubuwan".
Na lanƙwasar da murya kafin na furta"tuba nake yi ranki ya daɗe. Ai ni ban isa na sa kafar wando ɗaya dake ba wane ni ubana dillalin Kashi. A yi mini aikin gafara". Wani tsaki mai dogon zango ta saka tana jifa na wani irin mungun kallo kwatankwacin irin kallon da mai dukiya yake yi wa ƙasƙantacce. Na sakar mata da wani lausassan murmushin da har sai da haƙwarana suka bayyana na jawo kulan abincin gabana na sa hannu na soma ci. Duk da yanda shinkafan yake sukan wuyana ina jin suna tsayiwa a maƙoƙarona hakan bai hana ci ci gaba da tura abincin ba. Na fahimci matuƙar ina son na cimma buri da muradina akan ta sai na kwantar da kai na yi mata biyyaya domin sunkuyawa gwada bai taɓa zama gajiya wa ba. Sai da na cinye abincin tas na ɗauki kular na fito waje na kai ta kicin inda a nan na sama ruwa na kwankwaɗa na sama sauƙin tsayuwar ƙayan kifin da shinkafar ta yi mini a hanyar wuya.
Na ji wani abu ya taso mini cikina ya murɗa tae na ji amai ya taso mini da hanzari na fita ta ƙofar baya na dinga kwarara amai tamkar zan amayar da dukkan kayan cikina. Sai da na gama na tashi na je na kwance baki da fuskana na zo na gyara wajen da na yi amai ɗin, gabaɗaya jikina babu ƙwari haka na baro cikin kicin ɗin na dawo ɗakin Altine ban iske ta a cikin ɗakin ba hakan ya ba ni daman kwanciya akan katifar ina mayar da numfashi jin jikina nake yi gabaɗaya ya mutu tamkar wacce aka yi wa ɗan banzan duka.
Muryar Taufik da na ji ɗazu a sashin Saif ya soma dawo mini cikin kwanyata tiryan-tiryan na lumshe idanuna da hakan ya ba wa hawaye da suka ciko mini koramar idanuna damar kwaranya a bisa fuskana.
Wata zuciyar tana raya mini ina ma da na tsaya na laɓe na ga ko da fuskarsa ce, duk da muryarsa ma kaɗai ta tabbatar mini da cewa shi ɗin ne dai, na ja dogon numfashi na fesar kafin na gyara kwanciyata na kwanta akan gadon bayana ina kallon rufin ɗakin da ya zama mini shamaki tsakanina da sararin samaniya. Na yi nisa a cikin tunanin nake yi da har ban san lokacin da Altine ta shigo cikin ɗakin ba balle tsayiwar da ta yi a kaina kamar wacce ta haɗiye taɓarya babu alamar ranƙwafawa a tattare da ita.
"Kwanciyar me ye kike yi a nan ɗin?".
Na cira kai ina dubanta kafin na ce"jikina ne gabaɗaya yake yi mini ciwo shi ne na zo na ɗan kwanta ko zan ji dama-dama".
"Ai kuwa kwanciya ba ta kama ki ba ke da kika fito neman kuɗi. Ki tashi ki je Hajiya tana ƙiranki". Ban ce da ita komai ba na tashi ina cije leɓe na fita na je ƙiran Hajiyar na iske ta tare da wasu mutane uku biyu maza ɗaya mace gefe guda ga tulin turamen atamfa an jibge su da lesuka, suna ta buga lissafi gami da rubuce-rubuce.
Na durƙusa na gaishe su suka amsa mini fuskarsu babu yabo babu fallasa kafin na ce"Hajiya ga ni an ce ki na ƙirana".
"E sashin Saifullah za ki je ki gyara masa sun fita tare da baƙonsa. Ki gyara kafin ya dawo".
Gabana ya faɗi ya yi ras na ɗan saci kallonta kafin na kai ga faɗin"Hajiya shi ya buƙaci hakan? Don na ga kamar ba ya jin daɗin zuwa cikin sashinsa da nake yi".
"Ba shi ya buƙata ni ce dai kawai na ga dacewar hakan, na san halin Saif sarai yana da wuyar sha'ani amma da zaran kin fahimci wane ne shi za ki gano tana da daɗin zama da tarin hayalen ƙwarai". Kaina kawai na jinjina na ce"to". Na tashi na nufi sashin ƙirjina yana tsananta bugu da harbawa. Na isa cikin sashin ban dawo cikin ainihin nutsuwata ba, na soma tattare falon da ko kwanunkan da aka ci abinci da kofuna yi tea ɗin ba a kwashe ba. A bayyane na tsirtar da wani tsiririn tsaki na takaicin da ya taru ya yi mini yawa, ina ƙara yarda da maganar nan da ake cewa na duk na mijin da ka gani a hanya tsaf tsaf kar ka yi saurin bakin furta yana da tsafta ɗari bisa ɗari, har sai ka ga makwancinsa sannan ka yanke hukunci.
Na ɗauko tsintsiya na share ko'ina na yi mopping na mayar da komai a cikin muhallinsa. Wasu takardun addinin da suke kan kujera na ɗauka zan mayar da su kan teburi na yi tuntuni da bakin kafet takardun suka zube daga hannuna, na runtse idanuna sa boda zafin da na ji ya ratsa har ciki kwayata, na tashi na ina tattare takardun da suka watsa na ci karo da wani hoto, na ɗauka zan mayar da shi cikin takardan tautsayi ya sanya idanuna sauƙa akan hoton. Take numfashina ya ɗauke na wucen gadi na sanƙare a wajen na gaza motsa ko da gaɓa ɗaya daga cikin jikina, illa idanun da na ƙura wa hoton jikina yan rawa tamkar an jona mini wutar lantarki.
Hoton Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe na gani tare da Muhammad Taufik cikin shiga riga ɗaga, ga wani ƙaramin yaron da ba zai haura shekaru uku a duniya ba. Hoton ya yi bala'in kyau tare da fito da su suka yi tar da su, fuskokinsu washe da maɗaukakin farin cikin da ya bayyana ƙarara.
Jikina gabaɗaya ya soma rawa da har ban san sa'ilin da na zame na yi zaman ƴan bori dirshan a ƙasa ba, na dulmiya cikin kogin tunanin da yake ƙoƙarin hautsina mini dukkan lissafin cikin kwanyata.
Me ye haɗin Muhammad Taufik kuma da Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe? Na jefa wa kaina tambayar da take zuciyata ta ba ni amsa da faɗin wataƙila masoyansa ba ina ji a kaf cikin garin nan da kewayanta babu malamin addinin da take da yawan mabiya sama da Sheik Dawood. Na ja dogon numfashi na fesar ina jina gabaɗaya wani iri wacce ba ta da maraba da majinyaciyar da ta yi shekara tana jinya.
Na mayar da hoton inda ya faɗo na ajiye takardan. Ban shiga musu cikin ɗakuna ba don ba na son na gane wa idanuna sbun fa bai halalta na gani ba, don na sha jun ana cewa ɗakin mutum sirrinsa ne musamman kuma su da suka kasance jinsin maza biyu kuma a matsayina na mace budurwa. Ina gama wa na fito na koma sashin Hajiya Muhibbat har yanzu tana tare da baƙin suna ta buga lissafi na durƙusa na yi mata sannu tare da sanar da ita cewar na gama aikin.
"Ki zauna za mu yi magana idan na sallame su".
"To". Na amsa mata da shi a taƙaice. Na zauna har duka gama lissafin suka ƙare na sinci wasu abubuwa a cikin hirarta sun duk da kuwa hirar kasuwanci ne, ƙoƙarin haɗa kayan lefe suke mai rai da motsi na fita kunyar jama'a kamar yanda na ji suna faɗi. Sai da suka gama ta ƙare tas ta sallame su suka tafi kana ta juyo gare ni.
"Na bar ki kina ta jira ko? Kin ga kayan lefe ne muke ta ƙoƙarin haɗa wa na ɗaruruwan kuɗaɗe kayan na fita kunya. Don gidan manyan mutane za a kai kayan".
Na jinjina kai kafin na furta"ai ku na ƙoƙari ma irin lissafi haka. In wasu ne ai komai sai ya sunce musu".
Ta ɗan yi jim kafin ta ce"sai dai ba na son haɗa irin waɗannan kayan na kuɗaɗe masu yawa". Cike da mamaki na ɗago kai ina kallonta kafin na kai ga furta"Hajiya me yasa? Na ga ai ƙaruwarku ne tun da ciniki za a yi muku ko kayan miliyan ɗari za a haɗa ai ribarku ne".
Ta sauƙe ajiyan zuciya wanda har sai da na ji sautinsa kafin ta sama lasisin faɗin"mafi yawancin masu haɗa irin wannan lefen na maƙudan kudaɗe bayan auren ba sa iya ba wa mata lokaci balle maganar kulawa. Daga zaran a kai ki ɗakinsa a matsayin mata to ke da ganinsa ma wataƙila sau ɗaya a cikin shekara guda shi ma ɗin sai kin yi sa'a kuma kin dage da addu'a. Amma duk wasu ababen buƙatann rayuwa ba za ki rasa su ba sai dai za ki yi rayuwa ne a zahiri kina raye amma a baɗili ruhinki ya daɗe da barin gangar jikinki".
"Duk da hakan kuwa wasu ba su da burin da ya wuce su ha sun auri irin mjini da zai haɗa musu ko da kwatankwacin irin wannan lefen ne".
"Ai kuwa kallon kitse suke yi wa rogo, da sun san tashin hankali da rashin samun nutsuwar da yake tattare da auren wani mai kuɗin da sun daɗe da dawowa hanyar gaskiya, sai dai ba dukka aka taru aka zama ɗaya akan sama na gari a cikinsu sai dai ƙalilan. Ni fa yanzu da ace ina da wata ƙanwa mace da ba ta yi aure ba ko kuma Allah ya ba n ƴaƴan mata da ba zan taɓa yi musu sha'awar su auri masu kuɗi ba sai dai masu rufin asiri. Don ina yaƙin sai sun fi samun kwanciyar hankali da nutsuwa har ma da nutsuwar ruhi da salamar zuci".
Ɓoyayyar ajiyar zuciya na sauƙe kana na ce"Allah dai kawai ya da mu dace". Gabaɗaya jikina ya yi la'asar mussamman yanayin da na ga ta shiga, duk wani wanda zai gan ta a yadda take zai iya rantsuwa da girman zatin Allah cewar ba ta da wani sauran damuwa a cikin gidan duniya, mussamman idan aka yi la'akari da irin suturun da take sanya wa, muhallin da take zaune a cikinsa da kuma motar da take murza wa.
"Za ki iya zuwa gida ki dawo idan ki na buƙatar hakan. Tun da na ga yanzu babu wani aiki sai zuws a kuma". Tana gama zancen ta tashi ta hau sama ta bar ni zaune a wajen ina bin ta da kallo.
A ƙalla na ɓata mintuna ashirin zaune a wajen kafin na tashi na fita zan je na dawo kamar yadda ta lalince ministan.Tun da na fito idanuna suke kan sashin Saifullah haka kawai wata zuciyar mini na je na dauki hoton da na gani na Muhammad Taufik tare da Sheikh Dawood. Ba tare da na yi wani dogon tunanina na nufi sashin na tura ƙofan falon a hankali na shiga ina waige-waige.
Da hanzari na je na buɗe takardan na ɗauko hoton na sama a cikin hijabina na fito na jawo ƙofar, ina fitowa na hango motarsa tana shigowa cikin gidan, na yi mutuwar tsaye a wajen na kasa gaba balle baya har ya gama daidaita parking.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
__________________________________________
Page 5️⃣9️⃣
Sai da na ja dogon numfashi a fesar daga bakina kafin na iya sarrafa kaina. Har ya fito daga cikin motar na gaza matsawa daga inda nake tsaye tamkar wacce bishiya ko kuma sassaƙen gunkin indiya. Da sauri na ga ya nufo wajen sashinsa da alama wani abun ya mance ya zo ɗauka cikin gaggawa. Sai a lokacin na sama zarafin matsa wa daga wajen na ɓoye a bayan shuke-shuken da aka ƙawata wajen da su. Ina ganin sa ya zo ya wuce ba tare da ya lura da inda nake ba, ba a bi sakon talatin ba na ga ya fito riƙe da wasu takardu a wannan lokacin da ya murzawa ƙofar makulli ya rufe ta kirif kafin ya nufi inda ya ajiye motarsa ya shiga ya fiye da mungun gudu ya fice daga cikin gidan.
Fitarsa ta yi daidai da sauƙe tagwayen ajiyan zuciyar da na yi wani yana bin wani tamkar wacce ta yi aikin fasa dutse. Na fito daga inda na ɓoye ina tafiya saɗaf-saɗaf tamkar ƙadangaruwar bayan tulu da hanzarina na nufi hanyar gate na ji an dakatar da ni.
"Malama daga ina kike? Me ya kai ki hanyar sashin Saif?". Muryar Altine mai cike da isa gami da taƙama ya sauƙo a ƙofofin kunnuwana.
Ban amsa mata ba har ta iso gabana ta tsaya riƙe da ƙugunta tana bi na da kallon tuhuma irin kallon da ma'aikacin ɗan sanda yake yi wa mutumin da aka kama bisa zargin ta'addanci.
"Ban yarda da ke ba tabbas akwai abin da kike ɓoye wa. Kuma kawai abin da ya kai ki sashin Saifullah". Sai da na harhaɗo jarumta na yafawa wa kaina kafin na sama zarafin faɗin"Hajiya ce ta ce na je na gyara sashin".
"Tun ɗazu kuma gyaran sashin kike yi? Uwar iya magana da iyayi".
"Na riga da na faɗa miki iya gaskiyata, ya rage na ki ki yarda da abin da na faɗa ko akasin hakan". Ina dasa aya a zancen na raɓa ta gefenta na yi tafiyata, da farko gida na yi niyyan wucewa amma yadda na ga Altine ta ɗaura idonta a kaina ya sa ni sauya shawara, na je wajen Baba Mai gadi na zauna. Ta fi mintuna goma sha biyar a tsaye a wajen ita ba ta yi gaba balle baya tana ta aikin banko mini harara tamkar ƙwayoyin idanunta za su faɗo ƙasa.
"Lafiya kuwa yau me ye yake faruwa tsakaninki da uwar-gijiyartakin?". Furucin Baba Mai gadi ya dawo da ni izuwa cikin duniyar zahiri daga karatun wasiƙan jakin da na afka na wucen gadin.
"Babu komai Baba, daman wajenka na zo neman wani taimako".
Ya gyara zamansa yana fuskantana da kyau da hakan ya ba ni ƙarfin gwiwa da karsashin ci gaba da zancen.
"Akwai wani babban malamin addini da ya yi shura a gefensa kuma sunansa ya ɗaukaka ya zagaye ko'ina a cikin ƙasar nan har ma da kewayenta." Tun kafin na dire zancen ya katse mini hanzari ta hanyar faɗin"wannan ba kowa kike magana a kansa ba fa ce baƙin Balarabe".
"Anya kuwa shi ne? Wannan ɗin fa sunansa Sheikh Dawood aka yi masa kirari da gaskiya dokin ƙarfe". Ya murmusa kafin ya furta"ai mu a nan cikin jarafi an fi sanin sa da sunan baƙin Balarabe. Yana zuwa tafsirin alƙur'ani sosai a cikin garin nan. Ina tunanin babu garin da ya tara masoya fiye da wannan garin namun indan ya zo hatta mai martaba Sarki dakatar da komai yake yi ya je ya saurari wa'azinsa, kusancin da yake da shi da mai martaba ya sa shi ba shi auran ƙanwarsa ƴar autarsu ya aure ta sai dai ta rasu shekaru biyu da suka wuce, mutum ne mai tarin ilmin addini har ma da na zamani don na taɓa jin an ce yana shugabanci a wata jami'a".
"Don Allah Baba kaman da wani irin lokaci yake zuwa garin nan ɗin? Sannan in ya zo yana yin kamar kwana nawa kafin ya tafi?".
Sai da ya kalle ni kafin ya ce"yana iya zuwa a ko wani lokaci sai dai ta fi zuwa a lokacin sanyi kamar irin yanayin da muke ciki yanzu. Sannan idan ya zo yana gabatar da wa'azi a wurare daban-daban kuma a mabanbantan lokuta hatta wa'azin mata yana gabatarwa a masallacin Sarki".
Na ɗan yi jim kafin can na ce"shin ko yana da wani alaƙa ne tsakanin shi da wannan baƙon da ya zo cikin gidan nan?".
"Wai Sultan?".
"Sultan kuma?".
"Ƙwarai da gaske sunansa Sultan don tun sanin da na yi masa haka ake ƙiransa da shi. Amma asalin sunansa Muhammad".
Mamakin zantukansa suka gana ni samun damar cewa komai illa sadda kaina ƙasa da na yi ina tufka da warwara a cikin raina. Ta ya ya Muhammad Taufik ɗin da na sani zai ya rikiɗe ya koma amsa sunan Sultan?. Sannan me ye haƙiƙanin alaƙarsa da Sheik Dawood da har na ga hoton su tare? Hoto ne da aka yi shi cikin lokacin zallan farin ciki da annashuwa da har ya bayyana akan fuskokinsu. Kuma a cikin gida aka yi sa balle ma na ce a wajen gabatar da wa'azi suka haɗu aka yi hoton.
"Amma ƴar nan lafiya kike ta yi min wannan tambayoyin?".
"Lafiya ƙalau Baba, tun ranar da na ga wannan baƙon ne na ga suna kama da shi Sheikh ɗin to shi ne nake ta tunanin ko sun haɗa jini da shi ne. Ko wani dangantaka ta kusa ko ta nisa?". Na ƙarƙare zancen cikin sigar jefa masa tambaya a faƙaice.
"Ban ma taɓa lura da kaman da suke yi ba sai yanzu da kika furta nake zumo kamar a idanuna. Sultan dai kam abokin Saifullahi tun na ƙuruciya wani sa'ilin ma a nan cikin gidan suke ƙarar da hutun makaranta, ban taɓa jin labarin akwai alaƙa tsakaninsa da Sheikhi ta kusa ko ta nisa ba. Na san dai Sheikhi yana da azurki ƴaƴa sai da mafi yawansu mata ne ɗansa na miji ɗaya ne tal kuma bai cika bayyana fuskarsa ba".
"To shi Sultan bayan abokan da yake tsakaninsu da Saif su na da wani alaƙa da masu gidan nan ne?".
Kallon da ya watsa mini ya sani tabbatar wa kaina cewar na kwafsa kuma na wuce gona da iri har ina ƙoƙarin tsallake iyaka ba tare da na farga ko na ankare ba.
"Wannan irin tambayoyin ƴar nan sai ka ce ina gaban alkali".
Na murmusa kafin na ce"yi haƙuri Baba kawai na ga kamar ta sun ne ta yi tsananin yawa shi yasa nake tambaya".
"Ba laifi kika yi don kin tambayi abin da ya shige miki duhu ko ya jefa ki cikin shakku ba, ai magabata sun ce tambaya