Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Tknovels
yawa sun sha kawo min farmaƙi Allah yana kuɓutar da ni, da kuma taimakon Ummata don ita ma ba ta yarda na yi irin rayuwar da take yi ba tana ba n tsaro da kariya ta kowacce fuska".
Ƙirjina ya yi mini nauyin gaske da na kasa cewa komai illa bin ta da ido nake yi, ganin yanayin da na shiga ya sa ta sauya maganan.
"Ina ta suturu ma na mance ba na nuna miki wuraren". Na saki taƙaitaccen murmushi da hakan ya ba ta damar ɗaura daga inda ta tsaya"kin ga layin nan shi ne layin na isa. Duk wanda kika gani ya fito daga cikin layin nan to ya ci ya tada kai ne, don duk wanda ya zo ya gina muhalli a cikin layin wani ƙusa ne daga gwamnatin ko kuma wani hamshaƙin ɗan kasuwa, ko kuwa irin wanda iyayensu suke sato kuɗin gwamnatin su tara musu idan aka rasa abin da a yi da shi sai a zo nan a gidan gidaje da shi, ana zuwa hutawa duk ranakun ƙarshen mako mafi yawan ƴan matan gidanmu nan suke zuwa suna sheƙe ayarsu da zaran yamma ta kawo kai za ki ga kowacce yarinya mai ji da kanta ta ci kwalliya ta zo bakin layin nan ta tsaya daidai lokacin da masu gidajen suke dawowa daga aiki, idan kin kasance cikin masu rabo daga nan sai ki dace wani Alhajin ya yi wuf da ke shikenan kakarki ta yanke saƙa".
Na sauƙe numfashi mai nauyi ina ƙarewa faɗin layin kallo sai da na ƙare masa kallon tsaf kafin na furta"Lalle kuwa layin na isa, ga tankama-tankaman gidaje da shimfiɗaɗɗun tituna".
"Sai ma kin ga cikin gidansu aljannar duniya kenan, ga faffaɗan filin tsakar gida ya kai rabin wani unguwan".
"To su ina matayensu da suke cin karensu babu babbaka, ko ba su da iyali ne?".
"Su na da su wasu sun su ma har da ƴaƴansu. Sai dai mataye da ƴaƴansu duk suna can Abuja birnin tarayya wasu ma ba sa ƙasar gabaɗaya. Nan gidan kawai wajen shaƙatawa ne da more rayuwar duniya". Na ji shuru ina ƙara bin layin da kallo shuru yake ko'ina babu hayaniyar kowa da alama kowa yana cikin gidajensu ba sa fitowa sai da wani dalili mai ƙwari. Muka ci gaba da tafiya ina ta kallon layin da manyan gidajensu, haka muka karaɗe dukkan girman layin daga nan suka gargaɗa har cikin kasuwa ta nuna mini wurare da yawa, ba mu dawo ba sai da gari ta soma duhu daga yanayin duhun garin na tabbatar da cewa an yi ƙiran sallan magrib.
Muna dawowa gidan muka iske manyan motoci a ƙofan gidan tamkar ana gudanar da gagarumin biki ko kuma walima.
Ga mutane maza da mata tsaye cirko-cirko a ƙofar gidan, maza kama daga kan samari, tsaka tsakiya da kuma dattawa babban wani abin takaici har wa manyan mutane da aƙalla za su kai sa'an Abbana a shekaru. Sai da muka rarraɓe kafin muka sama hanyar shiga cikin gidan kowacce budurwa ta ci wanka ta caɓa ado kamar za su tafi gasar kyau na duniya. Kowacce ta tsuke cikin ɗamammun kayan da ba su tamaika da komai wacce rufe tsiraicinsu ba, ga ƙarin gashi da farata rututu a hannayensu kamar masu cin moshe.
Na buɗe ƙofar ɗakina na shiga na hango wasu baƙaƙen ledodi guda biyu na saki hamdala don na kwaso yunwa kamar zan ci babu, na zauna na jawo ledar ina buɗe wa biredi ne da wainar fulawa guda biyar a leda sai kuma ruwan shayi ƙulle a leda, gefe guda kuma ga can ledar pure water an jingine a gefe. Na san babu wanda zai kawo mini wannan abun face Aminu don haka ban yi wata-wata na ɓula ruwan shayin na tsoma zuƙa ina haɗawa da buredi ina danne wa da wainar fulawan sai da na ci wainar guda uku na zuƙe ruwan shayin na ɗaura da ruwan pure water ɗaya na yi hamdala na tashi na ɗauri pure water ɗaya na zuba a buta na fito na yi alwala na koma ciki.
Sallan magrib na yi ban tashi daga wajen ba har sai da na yi sallan isha'i, na zauna na zabga tagumi tamkar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar uwa da ubanta. Tunani barkatai suka dinga yi mini yawa a cikin kaina suna kai kawo a cikin kwanyata.
Tunanin gida da ƴan uwana suka faɗo mini a raina tamkar faɗuwar aradu, ban san sa'ilin da hawaye suka fara kwaranyo mini daga idanuna ba kamar da bakin ƙwarya.
"Anty Sawwama ki gafarce ni babu yadda zan yi ne ba ni da wani mafita saman da wannan. Ya zama dole ne na yi nisa da ku ko don kwanciyar hankalinku da nawa rayuwata ta gama tarwatsewa don haka ba zan zama matsala a cikin taku rayuwar ba".
A bayyane na yi maganar wasu hawayen suna rige-rigen fitowa daga idanuna suna wanke mini fuska yayin da suke sauƙa har izuwa tudun wuyana, na daɗe ina kukan da dukkan ƙarfina har sai da numfashina ya soma sarkafewa kafin na zame na kwanta akan bayana ina kallon rufin ɗakin da ya zama shamaki tsakanina da sararin samaniya.
Kamar daga sama na ji sauƙar muryan La'aniyatu a na'urar naɗan sautina.
"Har kin kwanta ne?".
Na tashi na zauna"a'a yaushe kika shigo ban ji ko sallamarki ba?". Ba ta amsa mini ba har sai da ta nema waje ta zauna kana ta ce"ban yi sallamar ba ne, daman na zo ne mu yi hira don Ummata ta yi baƙi daga wata ƙasa daban sun tafi otel za su gana". Na waro idanuna waje cike da mamaki"a cikin daren nan?".
Ta riƙe haɓa"yo mai ma aka yi da maza? Ai duk wani taron da za a yi wanda manyan mutane za su halarce shi to cikin duhun daren yin sa tare da taƙaitattun mutane".
Na jinjina kai tare da kawar da zancen ta hanyar faɗin"ina so na nema aikin da zan yi na dinga rufawa kaina asiri, ni wallahi ko wankau ne ma ko surfe zan yi". Ta bi ni da wani irin kallo kwatankwacin irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce.
"Yanzu ke a layin nan kin ga alamar wanda gidan da za su kawo surfe? Ai tuni bature ya kawo sauƙi ban ƙi ba dai wankau ɗin". Na yi saurin faɗin"don Allah ina san samu wankau ɗin?". Ta ɗan yi shuru kafin ta ce"gaskiya ba na ce ba don gidajen layin nan ma ba su cika zama ba amma dai ba za a rasa ba, wataƙila sai dai ki dinga bin gida-gida ki za a dace".
Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau kamar kazar da aka watsawa ruwan gishiri na tuna rayuwata ta baya lokacin da Abba yake raye a cikin duniya, rayuwa kenan wai yau a ce nake neman aikin wankau don na ciyar da kaina, hasali a lokacin baya ba a taɓa sauƙe tukunya a cikin gidanmu sai dai ba daɗi amma tabbas za mu ci mu ƙoshi. Ko ruwan da za mu jiƙa maƙoshinmu bai taɓa yanke mana ba. Na ja dogon numfashi na fesar ina zabga tagumi.
"Lafiya kuwa na ga duk yanayinki ya sauya?". Kalaman La'aniyatu ya dawo da ni cikin hayyacina.
"Babu komai kawai wani abun na tuna. Na gode da kulawarki a gare ni, mu tashi lafiya". Murmushi kawai ta sakar mini ba tare da ta ce da ni komai ta tashi ta fice.
Na zauna na yi jigum ina ta tunanin abin duniya, wasu hawayen masu zafi suka ciko mini kurmin idaniyata, na tuna Umma lokacin da ta yi watsi da ni ta ƙi ba ni ko wani irin ƙofar da zan yi mata bayyana balle har ta fahimce ni. Na daɗe zaune ina tunanin na ji an bankaɗo labulen ɗakin an shigo na cira kai ina kallon Aminu har ya shigo ya zauna.
"Na ga saƙo na gode sosai Allah ya saka da alkhairi".
Ya ɗago ya kalle ni"in ce dai ki na lissa adadin kwanakin da kika yi a cikin gidan nan yanzu ko?". Na bi shi da kallon mamaki sai dai na danne mamakin da kalamansa suka shayar da ni na ce"ina sake da yawan kwanakin. Kuma in sha Allah kwanan nan zan nema aikin da zan dinga ɗaukan ɗawainiyya kaina da shi". Ya yi ƙuri yana kallona"wani irin aiki ke nan?".
"Wankau ko kuma aikatau".
Cikin maɗaukakin mamaki ya ce"da kuɗin wankau da aikatau ɗin za ki ɗauki nauyin kanki?".
"In sha Allah". Na amsa da shi cike da dukkanin ƙwarin gwiwa.
"Kar ki yaudari kanki Amatullah babu ta inda sana'ar wankau zai riƙe. Yadda kiken nan mace iya mace sura iya sura diri iya diri, ki na da kyawun sura ta yadda duk wani lafiyayyen namijin da ya yi ido huɗu da ke dole sha'awarsa ta motsa. Idan kin iya allonki to tabbas za ki yi moriyar bariki za ki ja zarenki shekaru aru-aru, don yanzu haka ma akwai hamshaƙan mazan da suke ganin gilmawarki a cikin gidan nan kuma sun yaba za su saki baki aljihu matuƙar kika ba su dama".
Na runtse idanuna"ba zan taɓa aikata zina ba a cikin rayuwata". Ya yi saurin taran numfashina"ba ki shirya aikata zina ba kika shigo bariki". Ya miƙe tsaye ya tsaya"ki yi wa kanki karatun ta nutsu. Don tallafina gare ki na sati guda ne kuma yau an ci kwana biyu saura kwanaki biyar". Yana dasa aya a nan ya cika bujensa da iska ya fice ya bar ni zaune na kasa ƙwaƙwƙwaran motsi.
Na ja dogon numfashi na fesar ina yi wa zantukansa tankaɗe da rairaya. Na cije leɓansa saboda bugawan da ƙirjina yake yi. Dole ne zai na yi zina kafin na sama abin da zan ɗauki nauyin kaina da shi? Tambayar da na jefawa kaina ke nan da tsawon daren na gaza samun amsarsa.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
__________________________________
Page 4️⃣4️⃣
Haka na ƙarar da dukkan tsawon daren ina tunanin ina saƙa da warwara a cikin raina. Tabbas dole na tashi na nema na kaina in bay haka kuma na ji ana yi, sai dai ta ina zan fara wai ƙoƙarin cire wando ta kai. Ina zaune a inda na iddar da sallan asubahi ina ƙarewa ɗakin kallo cikin dubu, haƙiƙa ina buƙatar wasu abubuwan buƙatan rayuwa kamar kayan sawa, abinci da wasu ƙananun abubuwan. ban yi aune ba na ji wasu hawaye suna zubo miji daga idanuna wanda ban san dalilin zubar su ba, ban goge su ba kamar yadda ban yi wani yuƙurin haka su zuba ba.
"Anty Sawwama ku yafe ni na san ba jefa ku cikin tashin hankali na rashina. Na san na shayar da ruhinku ɗacin baƙin ciki, sai dai na yi muku alƙawarin ba zan taɓa sauƙa daga turban da kuka ɗaura ni a kai ba zan ci gaba da kare mutumcina da tsayawa akan gwadaben da na taso a kai". Ina rufe bakina na kai hannu ina goge fuskana tare da miƙe wa tsaye na ci ragowar abin da na bari jiya. Sai da gari ya yi haske na fito waje so nake yi na yi wanka amma ba ni da abubuwa da yawa da za su taimaka mini wajen gudanar da hakan, sai na tsaya ruwa, na nema bokiti, soso da kuma sabulu uwa uba kayan da zan sauya idan na yi wankan.
Ina dab da fitowa daga cikin ɗakin muka yi kiciɓus da La'aniyatu tana shigo wa na matsa mata ta shigo, muka tsaya muna kallon juna ina da ita kafin ta ce"ina za ki je kuma da safiyar nan? Na yi tunanin ma zan zo na samu ba ki tashi daga bacci ba".
"Ina so na fita ne na je neman aiki don na ga rayuwar ba za ta yiyu a haka ba".
Ta yi ƙuri tana kallona"kin dade dai sai kin nema aikin nan?".
"To ya ya kike so na yi, Aminu ya shaida mini cewar ɗawainiyyar ciyar da ni na tsawon sati guda kawai zai yi wanda yanzu haka ya rage kwanaki huɗu rak, idan ban fita na nema ba ya ya kike so na yi da raina a lokacin da ya janye tallafinsa a gare ni". Na yi maganar ina ƙoƙarin ficewa ta riƙo hannuna"ki bi a hankali dai mutanen unguwan nan ba ababen yarda ba ne". Kaina kawai na jinjina mata na yi ficewa ta na bar ta a cikin ɗakin, sai da na fito ƙofar gidan na sauƙe numfashi mai zafi ina ƙarewa gabar da yamma kudu da arewa kallo.
"Ya Zuljalali wal ikram ga baiwarka nan". Na yi furucin a bayyane cikin sanyin jiki haɗe da na murya, na salwantar da aƙalla mintuna uku a tsaye kafin na ja ƙafafuna na bar ƙofan gidan na yi dogon tafiya kafin na iso bakin wani tankamemen gidan da aka ƙawata da shukayen koren fure. Na ƙarar da mintuna ina kallon gidan kafin na isa na ƙwanƙwasa gate ɗin wani mutum ya fito ya buɗe ƙaramin ƙofan gidan gare ɗin yana jefa na da wani irin kallo.
Na tsuguna har ƙasa na gaishe shi sai dai maimakon ya amsa mini sai ya jefo mini wats tambayar cikin zafin rai.
"Ke me ye kike yi a nan wajen?".
"Na zo neman aiki ne?". Ya watsa mini wani ƙazamin kallo"ce miki aka yi ana neman masu aiki a gidan nan? To su masu aikinsu tun daga Abuja ake kawo musu kamfani suke zuwa su cike takarda su zayyana irin wacce suke so a kawo musu su zaɓa, ki tashi ki bar ƙofar gidan nan tun kafin na ɓata miki rai". Na haɗe hannayena waje guda alamar roƙo"don Allah ka taimaka mini na shiga cikin gidan na yi musu magana da kaina, wallahi ina tsananin buƙatar aikin nan ne".
"Ke zan haɗa da Allah ai ki taimake ni ki tashi daga nan wajen tun kafin masu gidan su fito. Don idan suka fito da ni da ke duk ba za mu ji daɗi ba". Yana rufe bakinsa aka buɗo ƙofar gidan yana faɗin"wai ina ka shiga ne ina ta ƙiranka?". Cikin rawar jiki ya ce"Allah ya huce zuciyarka ranka ya daɗe ka daɗe ka yi shekaru irin na dabino, na ɗan fito waje ne amma ban yi nisa ba".
"Ka zo ka buɗe min gate zan fita amma ba zan daɗe ba zan dawo".
"To ranka ya daɗe a dawo lafiya". Har sun juya za su koma ciki idanun mai gidan ya sauƙa a kaina ya tsaya cak yana ƙare mini kallon tsaf.
"Wannan yarinyar fa me ye take yi a nan wajen?".
"Irin masu zuwa neman aikin nan ne, na ce da ita gidan nan ba a buƙatar wata mai aiki amma ta ƙi tafiya sai magiya take ta faman yi min". Maigidan ya ɗan matso kusa da n tare da zura dukkan hannayensa cikin aljihun doguwar rigar jallabiyar da take jikinsa fara sol, har izuwa lokacin idanunsa a kaina ya furta"ƴan mata me ye kike buƙata?".
"Aiki nake nema ranka ya daɗe ni wallahi ko wankau ne ma ko raino zan yi". Ya yi shuru yana ci gaba da kallo na har sai da na tsargu da kaina na yi ƙasa da ƙwayoyin idanuna ƙasa kafin ya ce"to shigo daga ciki mana sai mu yi magana". Raina a wanke fes ban kawo komai a cikin zuciyata ba na yi masa godiya muka shiga cikin gidan.
Babban gida ne iyakar kallona ban hango ƙarshensa ba, ga wajen ajiye motoci da aka jera wasu rantsatstsun motoci. Duk girman gidan talis ne mamaye a ƙasa ga wasu shuke-shuke masu ɗaukar hankali da daɗin ƙamshi. Yana gaba ina bin sa a baya har muka isa cikin falon da aka ƙawata da duk wasu nau'in ababen jin daɗi da more rayuwar gidan duniya.
"Ga waje ki zauna bari na ƙira Madam ɗin". Ya yi zancen yana nuna mini kujerar zama, na zauna a ƙasa dirshan ina jiran dawowar da tare da matarta san babu jimawa ya dawo hannunsa ɗauke da wani tray ya ajiye mini a gabana, ruwan gora ne da lemon kwali sai kuma kofi su kenan a bisa kan trayn ɗin.
"Ga ruwa ki jiƙa maƙoshinki kafin ta fito, ta ɗan shiga wanka ne amma babu jimawa za ta fito sai ku yi magana da ita wataƙila ba za'a rasa gurbin da za a ba ki aiki ba. Don na ga alamar kamar a buƙace kike da aikin ko?".
Na yi hanzarin gyaɗa masa kaina"e wallahi ina son aikin. In dai har Allah ya sa na dace da samunsa".
Ya murmusa kafin ya ce"ki jira ta fito bari na shiga na ba ku waje". Kaina kawai na gyaɗa masa kai ya tashi ya taka wasu matakala ya haye sama, na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya tare da runtse idanuna na ɗaga hannayena sama ina zabgawa Allah godiya da ya tarfawa garina nono na dace da samun aikin da nake biɗa.
Na ji an dafo kafaɗana ta baya na yi saurin buɗe lumshashshun idanuna tare da waigawa, cak numfashina ya tsaya cak na wucen gadi bisa mummunan gamon da idanuna suka yi.
Maigidan na gani tsaye a gabana daga shi dai ɗan bante zandardar da shi mai faffaɗan ƙirji. Na yi zumbur na miƙe tamkar wacce aka tsigarawa matsilli jikina gabaɗaya yana rawa na ce"ranka ya daɗe ko zan je na jira ta a waje ne?".
"Ai babu wanda mace ma a cikin gidan nan, ni kaɗai nake rayuwa a cikin gidan, amma zan ji daɗi idan ke kika amince kika ba ni abin da mace take ba wa mijinta".
"Amma ka san ba mace a cikin gidan ka ce na shigo har da cewa na jira ta tana zuwa?". Cike da tashin damuwa balle kunyar abin da ya aikata ya ɗage kafaɗa ya ce"to hakan laifi ne don na gayyato kyakykyawar mace kamar cikin gidana?". Ya ƙare zancen yana ƙara nufo inda nake, na ɗaura hannu a ka na kurma ihu.
"Idan ka matso inda nake sai na yi mata ihu wallahi".
Da mamakina sai na ga ya bushe da dariya yana faɗin"ai ko lasifika za ki ɗauko babu wanda zai ji sautinki balle har ya kawo miki