DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Tknovels

Chapter   4 / 39

9K to 12K   out of 116.4K words

ɗauki. Ki ba ni haɗin kai kawai mu yi abun ne dukka ba zai wuce mintuna ashirin zuwa talatinsa ƙarƙarinta mu yi awa ɗaya, sannan zan ba ki duk adadin kuɗin da kike buƙata ki je ki kashe wutar gabanki".
Hawaye suka fara zuba daga idanuna"ka ji tsoron Allah ka sani duk abin da kake yi yana sama yana kallonka. Sannan akwai ranar da za a haska duk abin da ka aikata lokacin da kake raye a gaban dukkan halittun duniya daga na farko har zuwa na ƙarshe, shin kai ba ka tsoron irin wannan ranar?".

Ya yi sakeke yana kallo na"kin ga Malama duk wannan maganganun nakin ba su za su saka na ƙi aiwatar da abin da na yi niyya a kanki ba". Da sauri na juya zan fita ya riƙo gefen hijabina, ban yi wata-wata ba na fice hijabin na bar masa na fantsala da gudu na yi wajen ƙofa Allah ya rufa mini asiri na ji ƙofar a buɗe na fice ƙafata tamkar zai taɓo ƙeyata tsabar saurin da nake falfalawa.
"Baiwar Allah lafiya na ga kin fito cikin tashin hankali?". Mai gadin ya tare ni da zancen da na kasa samun sukunin amsa masa. Na soma jan gate ɗin kamar zan cire ta.

"Ki yi a hankali bari na buɗe miki".

Ya zare sakaran jikin ƙofan ya buɗe na fita sai da na fito na lura da yanayin da nake ciki, na ware ɗan kwalin kaina na yafa a kaina na lulluɓe wuyana zuwa ƙirjina da shi, ko takalmina ban ɗauko ba na fita tsabar kiɗima da ruɗewar da nake cikinsa. Na ji an buɗe ƙofar na yi saurin waigawa, mai gadin ne ya fito ya zuba mini ido cikin takaici yake faɗin"wannan dalilin ne ya sa tun farko na ce ki bar ƙofar gidan nan don in har Allah ya fito ya kan ki na san abin da zai faru kenan. Gidan nan da kike babu wata mace a cikinsa shi kaɗai yake zaune shi ma kuma sai ya ɗebi lokaci bai zo ba. Idan kuwa ya zo to har ya tafi duk daren duniya sai ya kawo mace wacce za su kwana tare. Kin gan ni nan ni ma da nake wannan aikin ba a son raina ba ne kawai dai don ba yadda zan yi ne, wannan ne hanyar cin abincina. Ƙarbi wannan ki hijabin ki saka na matata ne na ƙarbo miki a ciki".

Hawaye suna gudun famfalaƙi a fuskana na miƙa hannu na ƙarba hijabin na saka na suturta jikina. Na tsuguna har ƙasa ina yi masa godiya ya amsa yana ta saka mini albarka. Har na tashi zan tafi ya tsayar da ni.

"Ƴata ki kasance mai taka tsantsan don duk yawancin gidajen unguwan nan ba mutanen Allah ba ne a cikinsu. Idan har ba ku rasa abin da za su sanya a baki salati ba ke da iyayenki to ki yi haƙuri da wannan neman aiki don akwai hatsari a cikinsa sosai. Gwara ki zauna a gida tare da iyayenki idan ma ya zama dole neman aiki to mahaifinki ki ya fi dace ya fita ya nema ya kawo muku".

"To Baba na gode sosai". Na amsa masa har zuwa lokacin hawaye suna wanke mini fuskana, ya cire silifas ɗin ƙafarsa ya ba ni na saka ya umarce ni da har na ƙara ko da bin layin balle na zo kusa da gidan. Haka na bar ƙofar gidan ina kuka da takaicin abin da ya faru.

Ina cikin tafiya takalmin ya tsinke na ji kamar na ɗaura hannu a ka na ta zabga ihu ko zan ji sauƙi halin da nake ciki. Haka na riƙo takalmin a hannu ga rana ga yunwar da take ƙwaƙular ƴaƴan hanjina na dawo gida, na sama ƙofar ɗakin a kulle da makulin na san La'aniyatu ce ta rufe ɗakin don ita na bari a cikinsa.
Kafin na shiga ɗakinsu ta fito kamar ta san abin da zan tambaye ta ta miƙo mini ɗan makullina, na karɓa ba tare da na ce da ita komai ba na buɗe ɗakin na shiga na zube akan tabarma kamar kayan wanki ina sakin wani irin kuka mai ratsa zuciyar mai saurare.

"Wai me ya faru ne kin fita kuma kin dawo ki na kuka?". Ban iya cewa da ita komai ba saboda yadda kukan ya gama galabaitar da ni. Ta ɗago ni tare da kwantar da kaina a bisa cinyoyinta tana ƙara maimata mini tambayar a karo na biyu.
"Wai me yake faruwa ne Amatullah?".

"Me yasa mutane ba su da tausayi ne? Me yasa masu kuɗi ba sa tausayi na ƙasa da su? Me yasa masu kuɗi ba sa tausayin masu rauni? Wani irin al'umma ce muke rayuwa a cikin da babu tausayi balle jin ƙai?. Kowa babu Allah a cikin zuciyarsa kowa saɓon Allah da kaucewa koyarwa Annabinmu Muhammadu kawai aka saka a gaba. Ta ina za a sama yadda ake so? Me yasa masifo da bala'i ba za su baibaiye al'umma ba?".

Shuru ya biyo bayan zancena na ƙarshe na tsawon mintuna kafin ta kawar da shi ta hanyar faɗin"wai me ya faru ne?". Na kwashe komai tiryan-tiryan na sanar da ita ta daɗe ba ta yi magana kafin can ta ce"kin ga hakan kaɗai ya isa ya tabbatar miki da cewar sauran matan da kika gani a cikin gidan nan su ma dole ce ya sanya su aikata abin da suke aikatawa na haramci ba wai don son zuciyoyinsu ba".

Na tashi na zaune"babu wani uzuri cikin aikata saɓon Allah. In sha Allah zan ci gaba da nema har na dace da na ƙwarai". Ta yunƙura za ta yi magana na dakatar da ita"ki taya ni da addu'a kawai". Ta ja numfashi ta fesar kafin ta ce"shikenan Allah ya sa ki dace".

"Amin". Na amsa da shi, ta tashi ta fita ta bar ni a cikin ɗakin, na kwanta ina tunanin mafita ga bahaguwar rayuwata.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

________________________________________

Page 4️⃣5️⃣

Tun da na shiga cikin ɗakin ban fito sai alwalan da na fito na yi na koma ciki na zauna, a nan na yi sallan zuhur, na yi asr har magrib. Yunwa ya dinga ƙwaƙulan kayan cikina na dafe cikina ta faman murtsukuku a wajen kamar zan mutu, ina mayar da wani irin numfashi da ƙarfi da ƙarfi da ƙyar na iya tashi na zauna ina salati tare da karanto dukkanin wani addu'ar da ya fara zuwa bakina.
Ganin yunwa yana neman raba ni da numfashina idanuna har wani dishi-dishi yake yi mini ga wani irin nauyin da kaina ya yi mini na bala'in gaske. Da rarrabe na fito ƙofar ɗaki na dinga warara amai tamkar zan amayar da dukkan kayan cikina sosai nake aman har jikina yana rawa kamar ana jona mini wutar lantarki.
"Sannu Amatullah ba ki da lafiya ne?". Na tsinkayo muryar La'aniyatu a bisa cikin kwanyata, na kasa ba ta amsa da kalmomin baki ila gyaɗa mata kaina da na yi alamar e ta taimaka mini na tashi tsaye sai dai ƙafafuna sun kasa ɗaukar nauyina.

Muka koma ciki na kwanta lamau kamar ruwa na kasa tashi balle na ɗaga ko da ƴatsan hannuna.
"Wai me yake damunki ne?". Na yi jarumtar faɗin"yunwa nake ji wallahi ji nake yi kamar numfashina zai tsaya cak".
"Bari na kawo miki abinci sai ki ci". Ta ƙare zancen tare da tashi ta fita babu jimawa ta kawo mini biredi da ruwan shayi da babu ko madara a cikinsa, na tashi jikina yana rawa na amsa na ɓula ledar na soma zuƙa ina turawa da biredin sai da na ci ya fi rabin biredin kana na ƙarisa zuƙe ruwan shayin na koma na kwanta ina mayar da numfarfashi.

"Sannu! Ya jikin na kin?".

"Yunwar ce fa kawai".

Cike da tausaya wa ta ce"ba ki ci abinci ba ne tun safe?". Hawaye suka ziraro mini daga gefe da gefen idanuna kana na ce"ban ci ba Aminun yau gabaɗaya bai shigo ba". Ta sauƙe numfashi mai ƙarfi da har sai da na jiyo sautin fitar sa"na ji fa Ummanta suna waya da shi yana cewa ya yi tafiya can wani gari, kuma ina tabbatar miki da cewar da wata matar zai dawo ya kawo ta cikin gidan nan".
"Yanzu haka zan zauna kenan babu ci babu sha har sai ya dawo daga tafiyar da ya yi ke nan?. Dole na tashi na nema yadda zan taimaki kaina, ki riƙe ni na tashi na zauna na yi salla".

Na wangale baki da ido tana duba na"salla kuma? Ba ki da lafiyan ma ba za ki huta ba? Ban taɓa ganin macen da take girmama ibada sama da ke ba. Tun da kika zo gidan nan ban taɓa ganin kin yi fashin salla ba". Cike da matsanancin mamaki nake bin ta da kallo na gaza cewa komai har ta gama zancen ta ƙare.

"Salla kam ai ko da lafiya ko akasin hakan dole ce akan dukkan wani musulmi mai hankali kuma balagagge. Matuƙar kana cikin hankalinka dole ka yi salla ka bautawa Ubangijinka".
Ta sauƙe numfashi kafin ta ce"tirƙashi! Ni dai na tashi ne kawai a matsayin musulma amma duk wasu abubuwan da suke cikin musulunci ban san su ba kuma ba na aikata su. Sallar ce kawai ita kuma bai fi a sati na yi sau biyu ba shi ma sai na ga dama, tun da nake Mahaifiyata ba ta taɓa nuna min cewa salla dole ne a kaina ba balle ta koyar da ni sauran wasu abubuwan addini".

"Ko ba ta koyar da ke ba ke ya dace ki tashi ki nema ilmi ki nema ilmin addininki domin inganta rayuwarki ta gidan duniya da kuma na lahira. Kin ga hatta wannan sunan da ake ƙiranki La'aniyatu ba shi da gurbi a cikin addinin musulunci, domin fassara Annabinmu ya koyar da mu cewa mu sanya wa ƴaƴanmu sunane masu kyau da ma'ana domin suna linzami shi yasa ake so a dinga sanya wa ƴaƴa sunayen salihan bayi, masu imani da zuciyar tausayi waɗanda suka yi wa addinin musluncin hidima da ƙarfinsu, lokacinsu da kuma dukiyansu".

"To me ye fassaran sunan nawan?".

"Kalmar La'aniyatu kalmar labarci ne da yake nufin tsinanniya ko kuma wani abun da aka kwashe masa albarka". Ta dafe ƙirji"tsinanniya kuma?". Na gyaɗa mata kaina"ƙwarai kuwa a duk lokacin da aka ƙira sunanki hakan na nufin ana ƙiran ki da tsinanniya ne". Ta yi shuru na lura gabaɗaya jikinta ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jifa da ruwan gishiri, na dafa kafadunta cikin sigar ƙafafa gwiwa na ce"kar ki wani damu fa, ai har yanzu lokaci bai ƙure ba. Za ki iya sauya sunan zuwa duk sunan da kike so mai ma'ana da asali gami da tushe".
"Ba zan ma fara wannan garajen ba Amatullah, na san ma Ummata ba za ta taɓa barin na yi hakan ba. Tun da ƙaddarata ta faɗo a haka babu yanda zan yi face na rumgume ta yadda ta zo min".

Zan yi magana ta ɗaga mini hannu alamar ba ta son jin komai daga gare ni"Amatullah kar ki kawo min rikici da ruɗu a cikin rayuwata. Na yi kowa sanin wace ce Ummanta don ita ta haife ni hakan ba zai hana ta hukunta ni idan na bujire mata ba, ba abin wahala ba ne a wajen ta ta saka a haukata ni. Don haka maganin bari kar a fara Hausawa suka ce zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki". Ina ƙare zancen ta tashi ta fita da sauri ba tare da ta ba ni damar cewa komai ba. Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina dafe jikin gini na tashi na fito na yi alwala na koma ciki na gabatar da sallan isha'i. Ina zaune a inda na yi sallan aka ɗago labulen ɗakin akan shigo.
Wata matasjiyar budurwa ce ta tsuke cikin shirgar ƙananan kaya dogon wandon da aka tsatstsaga gwiwansa sai kuma wata rigar da babu hannu a jikinta, ta tula uban gashin doki a kanta da ya sauƙo har bayan wuyanta tana taunar chewgum da yake ba da sautin ɗas ɗas.

"Ke ce Amatullah?".

Na gyaɗa kaina"e ni ce".

"To ki zo Hajiya Babba tana son ganawa da ke a cikin ɗakinta".

"Na shiga uku! Allah ya sa ba wani laifin na yi ba". Na galla mini harara"wannan kuma idan kin je za ki ji ko ma me nene. Ni dai na isar da saƙo". Tana dire zancen ta juya ta fice ta bar ni cikin tarin zulumi da fargaban abin da zan je na tarar. Cikin mutuwar jiki na tashi na fito na nufi ɗakin Hajiya Babba na tsaya daga waje ina kwaɗa sallama sai da ta ba ni iznin shiga kana na shiga. Tana zaune akan kujera ta ɗaura ƙafarta ɗaya akan ɗaya na zauna a ƙasa tare da gaishe ta ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa.

"Hajiya sannu da hutawa, an ce wai ki na nema na". Na ajiye wayar da take latsa wa ta fuskanto ni da kyau tare da faɗin"kwananki nawa a cikin gidan nan?". Ƙirjina ya buga na shiga tsoron kar ta ce na haɗa nawa ya nawa na bar cikin gidan don na ga hakan ba wani abu ne mai wahala a wajenta ba. Kafin na ba ta amsa ta ci gaba da cewa"na lura har yanzu ba ki fara mu'amala da kowa ba balle har ki sama kuɗin da za ki dinga biyan kuɗin hayan ɗakinki. Sannan har zuwa wannan lokacin Aminu shi yake ɗaukan nauyin ci da shanki, shin dama ba ki shiryawa rayuwar bariki ba kika saka ƙafa kika fito daga gidanku? Ba ki tanadin guzurin irin rayuwar nan ba kika baro gaban iyayenki?".

Jikina gabaɗaya ya yi laushi na kasa cewa da ita komai illa sadda kaina ƙasa da na yi da hakan ya ba wa hawayen da nake dako damar tsiyaya. Muryata can ƙasan maƙoshina na furta"Hajiya in sha Allah zan nema sana'ar da zan din ga ɗaukar ɗawainiyyar kaina da shi kwanan nan".

"Wane irin sana'a kenan?".

"Kowani irin aiki idan zan samu na cikin gida, ko wankau ne ko kuma rauno....". Tun kafin na rufe bakina ta katse mini numfashina"wankau dai da na sani?". Na gyaɗa mata kaina alamar e da hakan ya ba ta damar zarce wa da faɗin"mace kamar ki ta tsaya tana yin wankau ai wannan abin a duba lamarin ne, yadda kike da dirin nan ga kuma kyawun sura da ko mace ƴar uwarki ce ta gan ki sai ta ƙara bin ki da kallo balle kuma ɗa namiji. Me ye zai hana ki yi amfani da damar da Allah ya ba ki wajen cin duniyarki da tsinken sakace".

"Ban gane abin da kike nufi ba?".

Ta gyara zamanta kafin ta ce"ina nufin akwai maza masu kumbon susa masu hannu da maiƙo da suke neman mata ire-irenku ruwa a jallo. Ba don komai ba sai don biyan buƙatar kansu kuma ba sa ƙyashin kashewa mace ko nawa ne matuƙar za su sama abin da suke so a wajen ta, idan ma tsoronk ɗaukar ciki ne yanzu zamani ya zo da abubuwa da yawa, ana amfani da comdon domin hana ɗaukar ciki. Idan kin yi dace ma wasu mazan ba sai kun kwanta da su ba kawai da zaran sun sama nutsuwa da ke shikenan buƙatarsu ta biya. Sannan idan duk hakan bai yi miki ba kawai wata hanya mai sauƙin gaske, akwai matan manyan mutane a cikin ƙasar nan da kewaye da mazajen suka tara musu dukiyar da ko za su yi shekaru ɗari a duniya ba za su iya cinye shi ba, duk wani nau'in jin daɗi na duniya suna samunsa su ci abin da suke so su sha abin da ransu yake so, su sa suturar da duk suka ga dama sannan su hau duk kalar motar da suka yi ra'ayi, su je duk ƙasar da suka zaɓa, su kashe duk adadin kuɗin da suke so. Sai dai matsalarsu guda ɗaya ce jal ita ce ba sa samun lokaci da kulawa mazajen su. Wannan dalilin ya san da yawa da cikinsu suka soma neman maza a waje sai dai masu wayo a cikinsu ba maza suke bi ba, mata ƴan uwansu suke sawa a nemo musu su yi duk abin da za su yi da mijinsu na aure da ita. Su kan ɗauki dukkan nauyinta su yi mata komai da komai, su jiyar da ita daɗin da ba ta taɓa jin makamancin sa".


Tun da ta soma zancen nake bin ta da ido har ta kai aya. Na numfasa kafin na ce"shin Hajiya aikata hakan yana daga cikin sharaɗin zama a cikin gidanki ne?". Ta watsa mini wani wulaƙantaccen kallo kafin ta amsa mini a taƙaice
"A'a".

"To in dai har hakan ba shi ne sharaɗin zama a cikin gidanki ba. Ina so ki ba ni dama na je na nema aikin da zan riƙe kaina da shi ba sai na bi wannan hanyar da duk kika zayyana ba". Ta yi banza da ni ba tare da ta ce da ni uffan ba haka na ci gaba da zama ba ta ce da ni ci kanki ba. Har sai da na gaji don kaina na ce"Hajiya zan iya tafiya?". Ta yi mini wani kallo ta wutsiyar idonta kafin ta ce"wai dama ba ki tafi ba? Za ki iya tafiya".

"Na gode mu kwana lafiya".

Na furta yayin da nake tashi na fice daga ɗakin, tun kafin na isa cikin ɗakina hawaye suke zuba daga idanuna har na isa, na rufa ƙofar na rufe tare da jingina a jikin ƙofar ina sulalewa a hankali har zuwa ƙasa. Na kifa kai da gwiwana ina saki wani irin gigitaccen kuka mai ratsa zuciya. Na raba dare ina kuka kamar raina zai fita kafin wani wahalallen bacci ya ɗauke ni ban tashi sai da gari ya fara yin gaske, na tashi a firgice saboda mafarkin da na yi da Abba.
Wai ya zo cikin ɗakin sanye da fararen kaya ya taɓo kafaɗana na ɗago kaina ina kallonsa yayin da hawaye yake zuba daga idanuna. Fuskarsa ɗauke

4 / 39